Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   23 / 48

66K to 69K   out of 141.5K words

daga kaduna a ranar da daddare wanka kawai ya yi ko abinci bai tsaya ya ci ba ya ce Jidda ta zo ya kaita can gidan.
Muna zaune a falo ni da ita da Baby, ban yi magana ba kuma ko ɗago kaina ban na kalle shi ba ina zaune ina yanke kumbana sai da na ji ya ce.

"Ki haɗo kayan da ɗan yawa Jidda."

Sai ta kalle shi, nima na ɗago ina kallon shi amma ban yi magana ba.

"Abba can zan koma?

Sai ya girgiza kai kafin ya ce" Ba daɗewa sosai ba. Umman ta ku ba ta jin daɗi ne kwana biyu shi ya sa."
Yadda ba ni ya ke faɗa mawa ba nima ko sai na yi kamar ban ji ba amma kuma a ƙasan raina na ji kamar Yallaɓai ya wuce gona da iri. Ni fa na haifi Jidda amma sai ya riƙa nuna min kamar Gimbiya ce uwar ta ba ni ba.

Ina zaune ina kallon ikon Allah, har Jidda ta haɗo kayanta da yawa a ƙaramar jakar ta. Baby kuma na wajen Yallaɓai ta riƙe mai hannu ta na faɗin itama za ta je, sai ya kalleni kafin ya ce" Zan ta fi da Baby in zan dawo sai mu dawo tare."

"Sai kun dawo."

Haka na faɗa ba tare da na ɗago na kalle shi ba, Jidda ta ce min Umma zan tafi? Itama ban kalle ta ba na ce sai ta dawo. Kuma bai saka Yallaɓai ya kalleni ya yi min wata mgana ba. Ina zaune har suka fice ya na riƙe da Baby da shi da kansa ya sanya mata hijabin jikinta suka fice suka bar ni, na yi ta ƙoƙarin na danne amma na kasa sannan ga shi tun wajen takwas da wani abu suka fita ba Yallaɓai ya dawo gidan ba sai goma da rabi kuma ya bar min abinci ya yi kwantai na yi masa ta yi ya ce min cikinsa ya cika tea kawai zai sha da haushi ya kamani na yi wucewata ɗaki a raina na ce sai dai ya koma can Gimbiyar ta baka ko kuma ka shiga kitchen ka haɗa da kanka.

Bayan na kwantar da Baby a ɗaki na yi mata addu'an barci na koma ɗaki na yi shirin kwanciya na kuma yi kwanciyata shi ya na can falo ya na aiki a system ina ga ya na ta jiran Tea ne ya gaji ya ga ban kawo ba ya miƙe ya nema ma kansa mafita. Ni dai ko da ya dawo ɗaki na yi barci sai da asuba ne ya ke ce min wai jiya sai ya ji ni shuru?

"Barci ne ya ɗauke ni."

Haka na faɗa masa kai tsaye. Na kuma haɗe raina, kamar ya fahimta ne sai bai ƙara min mganar ba, ni fa bai faɗa min baki da baki Gimbiya ba ta da lafiya ba kuma ni ban tambaya ba, sai Munnira ce da ta kirani a waya ta na faɗa min wai ko ciki ne da ita? Sai da gabana ya faɗi amma ban nuna mata ba na ce ban sani ba gaskiya. Ni ban je ba saboda wanda ya ijiyeni bai faɗa min ba, bai kuma ce na je ba nima ban tusa kaina ba shi a tunanin shi ai na ji ya na faɗa lalle Yallaɓai ya manta halina ne shi ya sa.

Har Hauwa ta je ta dubata ta biyo gidana ta na gaya min gida cike can ta bar su Anty Bahijja da Anty Maimuna.
Ita ce ma na buɗe ma baki na tambayeta me ke damun Gimbiyar?

"Ciwon kai. Sai maleria da ya saka jininta ya hau sosai."

"Allah ya ba ta lafiya."

Hauwa ke faɗa min Anty Bahijja ta ce ta ɗauka ciki ne Gimbiya ke da shi sai da a ka je asibiti sannan a ka ce ba ciki ba ne, ni dai na yi shuru ban ce komai ba ina nazari ni kaɗai.
Sai da ta ce ta ga ai Jidda a can ta na tambayanta ko ta koma can ne gabaɗaya sai wai Anty Bahijja ta ce e ai jeka ka dawon bai da amfani gwara ta dawo wajen Gimbiyar gabaɗaya.

"Haka ta ce miki?

Na faɗa cikin mamaki ina kallon Hauwa.

"E mana. Anty Maimuna ma na wajen ta kada ba ki ta ce ai daman Jidda ai yar gidan Gimbiyar ce shi ya sa Tafida ya ba ta ita."

Kai kawai na jinjina a raina ina girmama tunanin Yallaɓai, ina ga ya manta da ni ce na haifi Jidda ba Gimbiya ba. Hauwa ta tafi ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ta dira a gidana da yamma domin ta na shigowa ana ta kiraye kirayen sallar mangariba ne.
Na karɓe ta hannu bibbiyu kamar yadda na saba kamar ma ba zama ta zo yi ba. Sai da na ce ta zauna ita da Sulaihat ne, na tashi domin na kawo musu ruwa ta ce na bar shi kawai ta zo ne domin ta na son yin magana da ni sai na dawo na zauna ita kuma sai ta ce ma Sulaihat ta je ta zauna tare da Baby.

Sai da ta fice ne sannan ta juyo ta na kallona kafin ta ce" Sadiya kin kyauta kenan?
Cikin mamaki na kalleta kafin na ce" Me na yi kuma?
"Laifi ki ka yi mana."
"Laifin me?
Na faɗa ina ƙara tambayanta domin ni dai ban san na aikata wani abu ba.

"Kishi ne ya hana ki zuwa ki duba Gimbiya da jiki?

Sai kawai na yi wani sansarai ina kallon Anty Bahijja.

"E kalle ni dakyau. To in ba kishi ba menene? Ai ciwo ya wuce wasa ko da ba ki taɓa zuwa gidanta ba tunda yanzu rashin lafiya ne sai ki danne komai ki je ki duba ta ko bakomai a matsayinku ɗaya da ita kamar yadda kike matar Tafida itama haka take matarsa. Da auren shekaru da wanda aka ɗaura yau ai duk sunan su aure ko?

"Haka ne."

Na bata amsa ina shanye mamakina.

"To ba ki kyauta ba. Da na ji an ce ba ki zo ba kin san halina yar gaskiya da gaskiya ce na ce sai na zo na faɗa miki ba ki kyauta ba, shima Tafida na kira shi a waya na yi masa faɗa ya ce ya sha'afa ne amma zai kawo ki domin ki duba ta."

Sai kawai na zaune ni dai ban ce komai ba ina kallon Anty Bahijja. In tsaya ma yi mata wani bayani ma ɓata lokaci ne sai kawai na ce ta yi haƙuri zan je na duba ta in sha Allahu sai ta miƙe lokaci ɗaya ta na faɗin" Yakamata. Su kansu masu taya ki kishin su Hauwa duk sun je sun duba ta."

"Zan je nima in sha Allahu."

Ta ce Allah ya sa har da na rakasu haraba ta na min shaguɓe.

"Sadiya kowa ya san mu mata muna da kishi amma ɓoyewa ake yi. Ki daina bayyanawa  gudun kar Gimbiya ta fahimta ta raina ki. Ga shi ta na son ki ta na son mijinki da ƴaƴanki ko domin haka ba za ki danne komai ki je ki gaishe ta ba?

"Gaskiya ne. A yi haƙuri na yi kuskure."

Sai ta wayance ta na min dariya wai ta na sona ina da fahimta wani lokacin in ban so rashin kunya ba. Ni Allah na tuba yaushe na taɓa mata rashin kunya! Iya biyayya fa ina yi musu da ba su girmansu su ne ba su iya kama girman na su ba haka na dawo cikin gidana ina ta juya maganganun Anty Bahijja a ƙasan raina ba kowa ya ja min wannan wulaƙancin ba sai Yallaɓai kuma wallahi ba zan ƙyale shi ba.
A ranar daman zai koma gidan Gimbiya ba nan zai sauka ba, kuma na ce ba zan kira shi a waya ba sai ya zo za mu yi ta ƙare, ya kirani a daren mun yi sallama daman haka ya ke da safen litini bayan Baby ta tafi makaranta da wuri na shirya na riga shi fita kafin shi ya baro can zuwa gidana sai dai muka haɗu a can ni da shi bai ma san na zo ba sai ita Gimbiyar ne ta je ta kira shi. Ba kuma sanin gidan na yi ba, Hauwa na kira ta yi mini kwatan cen gidan Allah ya taimake ni gidan ma ya na bakin titi ne, sai da na sauka adaidaita na yi tambaya a ka nuna min ina buga get ɗin sai ga ta ta zo ta buɗe min.

Ba ma shi ba, har ita na san ta yi mamakin ganina. Kuma ni dai yadda ake zuzuta rashin lafiyan na ta ban ga haka ba. Da bakinta ta ke faɗa min ta ji sauƙi, saboda na ganta cikin gayunta ne domin ai ba su yi tsamnanin ganina ba. Yallaɓai kuma ta ce yanzu ya dawo daga kai Jidda makaranta ina falo ta bar ni, ta je ciki ta kawo min lemu da ruwa ta ce abin karyawa na ce na karya daga gida duk da ina tunanin su kansu ba su karya ba.

Gidanta itama ya yi kyau duk da iya falo na gani. Amma falon ya yi kyau ƙwarai kayanta duka yan waje ne forum, tare suka fito da Yallaɓan ya na sanye da Jallabiya da ya ganni zaune sai da ya nuna mamakin sa.

"Shi ne kuma ba ki kirani na zo na kawo ki ba Madam?

Ya faɗa ya na zama a gefena.
Har ya na rumgumoni.
"Gud morning"
Ko amsa shi ban yi ba na juya ina kallon Gimbiya kafin na ce" Ki yi hakuri kar ki ga ban zo duba ki ba. Ni bai faɗa min ba ki da lafiya ba."

Kanta na ƙasa ta na wasa da hijabin da bayan shiganta ta sako shi ta ce" Laa bakomai wallahi."
Shi kuma ni ya ke kallo kafin ya ce" Ki ji tsoron Allah ban faɗa miki ba ta jin daɗi ba?
Kallonsa na yi tare da balla masa harara kafin na ce" Ka dai yi magana da Jidda amma ni baka kalle ni ka ce Sadiya Gimbiya ba ta da lafiya ba. Ka ja ita ta ga laifina sannan yan'uwanka ma sun ga laifina tunda an biyo ni har gida an ce saboda kishi ne ya sa ban zo na duba ta ba, shi ya sa yau bayan Baby ta tafi makaranta na taho domin na wanke laifina. Ki yi hakuri ba kishi ne ya hana ni zuwa na duba ki ba."

Daga ita har shi sun ɗan ji wanni iri, ni kuma ban damu ba sai na miƙe daman na tsaya a hanya na siya ayaba da kankana na ijiye mata saman center table ɗin dake tsakiyar falon lokaci ɗaya ina faɗin.

"Amarya Allah ya ƙara lafiya."

Ta amsa da Amin itama ta na miƙewa kafin ta ce" Ni fa ban ji wani abu ba. Ciwon ma ba sosai ba ne kawai su Anty Bahijja ne suka tambayeni kin zo na ce a'a amma ba da wata manufa na faɗa musu ba."
Sai na juyo ina kallonta kafin na ce" Kar ki damu fa. Bakomai."
Na faɗa ina mata murmishi shi kuma Gogan ya na zaune ya kasa mgana sai da na juya ina ce masa tafiya zan yi sannan ya ce na jira shi mana ya yi wanka sai mu fita tare.

"A'a bari kawai na tafi kar Saude ta zo ba ta same ni ba."
   
Ganin na dage ba zan tsaya ba ne dole ya sa ya ce bari ya zo ya kaini gida sai ya dawo har zan ce ya bar shi daga baya kuma sai na yi shuru saboda ina so mu ƙare ta ni da shi.
Ya ɗauko ni a mota muna hanya zai kai ni gida ya ga tun da muka ɗau hanya ban yi masa mgana ba sai ya kama kan shi.

"Ki yi hakuri na ɗauka kin ji lokacin da na ke faɗa ma Jidda ne."

"Oh.."

Na faɗa ba tare da na kalle shi ba ina ma ƙoƙarin sassauta fushina ne.

"Kin ji ko?

Sai na kalle shi kafin na ce" Ni fa abu ɗaya ya ɓata min rai yadda ka ja zamin zagi wajen yan'uwanka? Ka faɗa min ne? Ko kuwa don kana magana da Jidda sai ya zama da ni ka ke? Ni ba za ka iya faɗa min baki da baki ba Yallaɓai?

Na faɗa ina mai ƙuresa da ido sai ya gano kuskuren shi nan da nan ya fara ba ni haƙuri.

"Ki yi hakuri don Allah. Na yi kuskure."

Na haɗe rai ina faɗin" Burin ka daman yan'uwanka su ga laifina. Sannan matarka ta ji haushina ban zo na gaisheta ba. Ka kyauta Yallaɓai ka kyauta kawai zan ce maka."

"Duk na ji kuma na amsa laifina. Na ce ki yi haƙuri."

"Hakuri ai zama dole. Amma dai ba ka kyauta ba. Ko maganar zuwa gidanta da ban taɓa yi ba laifinka ne itama in za ta zo gidana ai kai ka ke kawo ta ba ta taɓa zuwa ita kaɗai ba sai dai ku zo tare da ita ko ka kawo ta ka maida ta. Ni ka taɓa ce min na zo mu je? Sai na yi tunanin ba ku gayyata ta shi ya sa ban tusa kaina ba amma kuma daga baya sai ni a ga laifina! Ko saboda ni ce Sadiya uwar laifi?

Na faɗa ina kallon shi, saboda wallahi abin ya ɓata min rai matuƙa.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Duk na amsa laifina. Ki yi hakuri haka ba zai ƙara faruwa ba."

Shuru na yi masa ban yi mgana ba sai ya riƙe min hannu da hannun shi guda ɗaya, ɗayan kuma ya na tuki dashi.

"Am Sorry kin ji"

Na ƙara yi masa banza sai ya matse hannuna shi ya sa na kalle shi kafin ya marairaice ya na faɗin" Na ce fa a yi haƙuri ba shikenan sai a huce haka nan ba?

"Na haƙura amma bayan wannan akwai wata mganar mu da ni kai."

"Me kuma na yi?

Ko kallon shi ban yi ba sai ma hannuna da na zare cikin na shi na yi gefe da fuskata ina kallon wucewar motoci fuskata a haɗe.

"Sadiya ta."

Sai na juya ina kallon shi.

"Me kuma ya sake faruwa?

Ya faɗa duk ya wani kama kanshi ba gaskiya. Sai ni kuma na ɗauke kaina kafin na ce" In mun je ai za ka ji."
Sai ya yi shuru kamar ya na tunani kafin ya gyaɗa kai ya na mai faɗin" Shi ke nan ni sarkin laifi. Zan sake ba da haƙuri wannan karon ma."
Ko ƙala ban ƙara ce masa ba har muka isa gida, a waje ya ijiye motar na ce masa ya shigo cikin gida mu yi magana kafin ya wuce.

A falon farko muka tsaya ya na goye da hannayensa a bayan sa ya na kallona
Ni kuma sai na sauke mayafin kaina ina faɗin.

"Yallaɓai."

"Na'am"

"Na ce ko dai kai da Gimbiya ne kuka haifa min Jidda ne?

Sai ya kalleni cikin mamaki kafin ya ce" Me ya kawo wannan mganar? Har ya na wani shan mur.

Kai tsaye na ce" Abin da ya kawota shi ne. Labari na ji a gari an ce ka ba ma Gimbiya Jidda halak malak ni kuma da na ji labari sai na ce ba ka gaya min ba, ban san da wannan mganar ba."
Na faɗa ina mai kallon shi sai ya wani rausayar dakai kafin ya ce" Ba har abada na ba ta ba. Daman ai yarta ce. Saboda ba ta jin daɗi ne kwana biyu nan ya sa na ce ta ɗan zauna da ita. Ina tunanin ai ba ki da matsala da hakan ko?

"Ta ya ka san ba ni da matsalan da hakan tun da baka faɗa min ba?

Sai ya yi kasaƙe ya na kallona ni kuma sai na ƙare ware masa ido kafin na ce" E. Ai ba ka yi magana da ni ballatana ka fahimci ko ina da matsala ko ba ni da shi?
Sai ya yi shuru kawai ya na kallona, ni kuma na riƙe kugu ina cigaba da faɗin.

"A matsayina na mahaifiyar Jidda ban da mutumcin da za ka yi mgana da ni Yallaɓai? Sai dai na ga kana aiwatar da duk abin da ranka ya so maka kai kaɗai? Ko a farkon tarewan Gimbiya da Jidda ta ke zuwa ta kwana da ita ka nemi shawara ta.? Duk da dai ba zan hana ba amma aƙalla dai ka daraja sunana na uwa ka yi magana da ni ba wai na riƙa jin maganar abin da ya shafi ƴaƴana a gari ni ban sani ba."

"Sadiya ba ki da kara ne? Ba za ki yi ma Gimbiya kara ba?

A fusace na ce" Ita na yi mata kara shi ya sa kaga ban yi magana ba sai yanzu. Kai ne ba ka yi min kara ba Yallaɓai. Sam ba ka yi min kara ba."

"Laifi ne domin na zar tar da Umarni kan Jidda ban shawarce ki ba Sadiya?

"Ba laifi ba ne amma a kalla dai ka daraja ni. Ai ba ci baya ba ne in ka ce min Sadiya Jidda za ta koma wajen Gimbiya na wani lokaci ai kasan ba zan ce komai ba amma dai zan ji daɗi a raina ka martabani ko?

"To ki yi hakuri. Na ji ban kyauta ba shike nan ko?

Sai na ɗan sassauta fushina ina mai juya fuska, mirmishi ya yi har ina jin sautin mirmishi kafin ya ce"Madam ki yi hakuri kin ji ko?
"Ni fa ba rai na ne ya ɓaci ba kawai na faɗa maka ne domin ka kiyaye. Ba na so kar ka sake yi min haka ina gidan nan in abu ya shafe ni ko ƴaƴana ka daina abu ba tare da ka yi magana da ni ba."

"An bari. Kuma za a yi mgana da ke in sha Allahu."

Sai na sauke numfashi na koma na zauna ba ta re da na yi magana ba sai shima ya zo ya zauna a kusa da ni ya na faɗin" Shiken ko faɗan ya ƙare ko?
Ya faɗa ya na rumgumoni zuwa jikinsa.

"Ni ban yi faɗa ba."

Na faɗa ina sunne kai a saman kirjinasa.

Saman kaina ya sumbata kafin ya ce" To in ba faɗa ba me kenan kika yi? Tun a mota sai faɗa kike yi min mun zo gida ma ban tsira ba. Alhalin kuma nima kin yi min wani abu da ya sosa min rai kuma kema kin sani amma ban yi miki mgana ba, ko faɗa ma ban yi miki ba."

Sai

23 / 48