ko a yinin ranar ma kashe ta na yi saboda ba na so damu na fi son a bar ni na gama ji da abin da ke damuna wannan duka dukan da Yallaɓai ya yi mini ba.
Ban ɗauka a daran ya dawo ba sai farkawa na yi cikin dare na ganshi kwance kusa da ni. Da safe kuma na dai gaishe shi na addinin da ya ce mace ta gaida mijinta ya amsa a daƙushe shima, muryata ta shaƙe da safe tunda kukan da na yi ta yi jiya ya saka min mura mai zai shi ne ma ya yi min mgana.
"Sannu Mura kike yi?
Ya faɗa lokacin da ya dawo daga kai su Jidda makaranta an saka su wata tahfiz can gaba damu kaɗan asabar da lahadi. Salisu na gida ba ya jin daɗi. Ya ji ni ina ta attishawa ne sai ya yi min sannu na amsa kuma shi da kanshi ya je ya dafo min shayin citta ya kawo min na sha sai na ɗan samu sauki sannan ya duba cikin box ɗin mu na mganguna ya samo min mganin mura ya ba ni na sha sai ya ce na kwanta na huta har yana gyara min kwanciya ya na rufamin bargo da ya ke kuma mganin kamar ya na saka barci sai barci ya ɗauke ni sai wajen sha ɗaya na farka na tashi ina mutsike ido wayata na kunna na ga 11 na safe ta gota gashi yau ɗin asabar.
A kasalance na sauko daga kan gado ina hamma tiolet na shiga na kama ruwa yunwa na ji ina ji sai na tafi kitchen sai na ga Yallaɓai ya soya doya ya rage min ita na diɓa zuwa falon yara daga nan na ke jin tashin muryoyi kamar ba ta Yallaɓai shi kaɗai ba sai da na gama cin doya na kora da ruwan shayi sannan na kai kofin da filet kitchen ni kaina wajen duk ya yi min kazanta jiya Saude ba ta zo ba ni kuma ban yi ba.
Bedroom na koma na sako hijabi da takalmi na yi sallama a falon Yallaɓai suka amsa min sannan na tura ƙofa na shiga.
"Uncle Abba kai ne tafe ba labari."
Na faɗa ina karisowa cikin falo, lokaci ɗaya ina ɗan tari kaɗan.
"E. Na shigo duba wani fili sai na kira Yallaban ki ya ce yana gida na ƙariso. Ina zuwa ke na fara tambaya ya ce ba ki jin daɗi kin kwanta "
Ina zama saman kujera mai zaman mutum ɗaya na ce" E wallahi sannu da zuwa."
Na faɗa ina kallon Yallaɓai ta gefen ido ya na zaune a gefen Kawun na shi ya duƙar da kai ƙasa.
"Sannu ya muran to?
Sai na ce da sauƙi ina tambayan ya mutanen gida. Mu ɗan yi hira saboda ni dai muna shiri da shi kuma har muka gama Yallaɓai bai saka mana baki ba, ban daɗe ba na tashi na koma falon su Jidda.
Daga Yallaɓai har Uncle Abba sun bi bayan Sadiya da kallo har ta fice kafin Yallaɓai ya sauke ajiyar zuciya ya na faɗin" Ka ga abin da na ke faɗa maka ko? Kwata kwata na kasa gane kanta."
"To daman ina za ka gane kanta ka yi mata kishiya."..
Yallaɓai ya ce" Ai ba ta sani ba."
"Ko?
Uncle Abba ya faɗa ya na kallon Yusuf. Shi kuma sai ya gyaɗa kai kafin ya ce" Yes. Domin na roƙe su kar su faɗa mata sai ta faraji daga bakina."
Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce" Ni kuma sai na ke tunanin kamar ta sani Tafida."
Ido Yusuf ya saka masa kafin ya ce" Ta sani?
To wa ya faɗa mata?
Abba ya zaƙuda kaffaɗa kafin ya ce"oho amma ka yi tunanin me ka yi mata da ta sauya maka haka? Ni kaina na ga duk ta yi wani iri kamar ba Sadiya ba."
Yusuf ya yi shuru ya na tunanin kai bai yarda ta sani ba in ta sani me ya sa ba ta yi masa mganar ba. Sai dai ya fi yarda ƙila ta na ji dai a jikinta domin an ce mata in za a yi musu abokiyar zama suna ji a jikinsu.
"Ba ta sani ba gaskiya rigimarta ce kawai ta tashi."
Ya faɗa cikin jadaddawa.
"To sai ka sanar da ita da wuri kafin ta sani a wani wajen."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce" In sha Allahu.
Daga nan suka cigaba da tattaunawa duk a kan ba tun dai.
*Janafty*
*TKG*
03.
FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622
Ni ko ina barin falo ɗaki na koma na ɗau wayata na kunna na kira Saude sai balaraba ta ɗauka tana faɗa mini Saude ba ta da lafiya zazzaɓi ya rufe ta. Amma ta ji sauƙi, fatan samun lafiya na yi mata sai ta ce min ko ina buƙatar ganin ta ne? Ai sai ta rarrafo ta zo tunda ta ji sauƙi.
Da sauri na ce" A'a ta bar shi kawai in ta ƙara jin sauƙi sai ta zo."
Sai muka yi sallama bayan na ce ta haɗa ni da Sauden na yi mata sannu sai ta ce mini ta shiga makewayi mun rabu akan zan sake kiranta in sha Allahu.
Ajiyar zuciya na sauke ina mai riƙe ƙuguna aikin da ke gabana kawai na ke hasashe jiya ba a gyara gidan ba ga wanke wanke mai yawa ba a yi ba in dai ba ina so a zo gidana a tafi da ni a baki a bangaren kazanta ba ne. Dole na sauke son jiki na gyara gidana wayata na ɗauka zuwa kitchen na kunna karatun Qur'ni cikin suratul Maryam saboda ina son suran sosai ta na yi mini daɗi.
Kaye kaye na fara yi a kitchen ɗin saboda ina so na fara gyara shi bayan na gama sai in yi wanke wanke na goge kitchen ɗin a lokacin da Yallaɓai ya shigo ina kwashe dattin da ke cikin filet ɗin wajen sink ina zubawa a cikin leda na ji shigowarsa ni kuma ina ta bin karatun na yi kamar ban gan shi ba na gama tara dattin na ɗau ledan zan fitar can waje sai ya saka hanny ya karɓa ban tsaya masa jayayya ba na sakar masa na koma ina goge saman dirowers ɗin kitchen ɗin da wani ƙaramin towel saboda ma kar ya zo ya dame ni har ƙure volume ɗin wayata na yi da karatun na ji buɗe kofarsa da dawowarsa na kuma ji a jikina ni ya ke ta kallo amma ban juya ba ina cigaba da aikina lokaci ɗaya ina bin karatuna ga shi na tsuke cikin riga da wando amma jeans ɗin mai ɓudewa ta kasa ne sai wata ƙaramar riga amma na saka wani ƙaramin hijabi wanda ba zai dame ni ba saboda baƙon da muke dashi.
Ni ban ji lokacin da ya taho ba kawai jin kansa na yi ya ɗoramin a saman kafaɗata. Na ɗan tsaya haka sai kuma kawai na basar na cigaba da aikina kuma ban dakata da jin karatun ba, leƙa fuskata ya ke yi har ya na shafa mini kumatu saboda dai na kula shi amman ban yi ba. Domin ni Yallaɓai duk wani abu da zai yi ko zai ƙara yi ya daina burgeni tunda abin na shi duk munafunci ne, gani na yi yana saka yatsa ya na latsa min gefen cikina kamar ya na so ya yi min cakulkuli da sauri na ƙwace jikina ina kallon shi.
Marairaicewa ya yi ya na min wani kallo wanda a da kallon nan ya ke rikitani amma yau wallahi ko kaɗan ban ji wani abu ba, sai ma na koma na cigaba da aikina lokaci ɗaya ina faɗin.
"Karatun Qur'ani ne fa."
Na faɗa ina cigaba da bin karatun, shi kuma sai ya ƙara biyoni sai ji na yi ya rumgume ni ta baya ya sagalo kansa ta tsakanin wuyana sannan hannayensa ya sargafe su ta cikina ya matse ni, kiss ya yi ta min a wuyana da gefen bakina amma na ki bashi wata dama kawai sai ya zura hannunsa ya ɗauko wayar dake gefena ya tsaida karatun na ɗago a zafafe zan masa masifa da sauri ya haɗe bakin mu waje ɗaya duk iya ƙokarina yau na kasa kwatan kaina domin ya yi min bake bake ne ya rufe ni ruf ɗin da na kasa ƙwatar kaina amma har ya yi kiɗan shi ya yi rawan shi ban yi ƙwaƙwaran motsi ba, yau sai na ji kwata kwata bakin Yallaɓai kamar miyansa ya koma mini maɗaci domin wata zuciyar na faɗa mini ya yi ma Gimbiya irin wannan shi ne kema ya zo yana yi miki tuni na ji kamar zan yi amai, na kasa haɗiye miyan bakina a gaban shi ya na kallona na saka hannu ina goge bakina kamar ya shafa min wani cuta.
Hannuna ya riƙe caraf ya na wani tsare ido.
"Cuta na saka miki da kike goge bakin Sadiya?
Sai na kalle shi, tunda ya aure na zama ba tashi ba sai dai ya rika kirana da sunana Sadiya kawai gatsal. Tun daga nan na san na fara ganin iskancin namiji tun kafin ma su tare su fara zaman auren.
"Sorry mana. "
Ya faɗa ya na riƙe duka hannayena cikin shagwaɓa har ya na wani karya wuya. Na yi masa banza ban yi mgana ba sai kawai ya sake ni ya riƙe duka kunnuwansa yana faɗin" Sorry. Haba mana Sadiya ta."
Ya faɗa lokaci ɗaya ya na ƙara marairaicewa na kalle shi na ƙara kallon shi wai yau ni ce Yallaɓai ya kalla ya ce ya na dai dai da ni, to ai shi ne zan gani in zai iya da ni ganin ya hana ni aikina sai bina ya ke yi ya na min magiya dole na ce na haƙura sai ya rumgumeni ya na mai sumbatar goshina kafin ya sake ni ya kuma bi ni da kallo ya na faɗin" Za mu samu abin karyawa ni da kawun na ki?
Ya dai ci darajan Uncle Abba da ba zan yi ba amma saboda darajan mai daraja sai na amsa da toh duk zamansa a kitchen ya ga ina aiki bai tambayi ina Saude har sai da ya fita sannan ya ƙara dawowa.
"Ina Saude? Ba za ta zo ba ne"
"Ba ta da lafiya."
Amsar da na bashi a takauce kenan sai ya juya yana mai faɗin Allah ya ba ta lafiya da harara na rakashi har ya fice sannan na yi ƙaramin tsaki ina mamakin halin maza na ƙara yarda da aka ce ba su da kunya tun daga ranar farko kunyar abin da Yallaɓai ya aikata min ya fita daga jikinsa ya daina nuna tsoro ko kunya ya yi aure ban sani ba, ban san tunanin shi ba, shi a tunanin shi ban sani ba sai ranar da ya ga dama sai ya faɗa mini ƙila ma bayan Gimbiyan ta tare, Ma'u ta cuceni da halin da na shiga cikin kwanakin gwara ma ban ji mganar ba sai a lokacin da ya ga damar faɗa min ga shi ta dalilinta sauran farincikina a kwanakin da ya kamata na yi shi ta yi silan ruguzamin shi, ni kam ai tsakani da Ma'u sai Allah ya isa kuma da ikon Allah duk wani sharrinta sai ya koma kanta.
Ina aikina ina tunane tunane baƙin ciki na kara samun muhalli a cikin raina. Dankali na fere na soya musu da kwai sai na sake dafa musu ruwan tea na kai musu Uncle Abba na ta yi mini sannu. A falon na bar su suna karyawa ni kuma na koma na cigaba da aikina sai da na gama wanke wanke sannan na yi sharan ɗakunan gabaɗaya na wanke Tiolet ɗin mu da na su Jidda duka kuma na yi mopping gidan amma ban da falon Yallaɓai kirchen na gyara shi na goge shi tas ban zauna ba sai da na ɗora girki gwara na yi hutun gabaɗaya.
Shi ma girkin saboda Uncle Abba ne domin ya na gidan bai tafi ba har bayan azahar sannan suka fita tare da Yallaɓai bayan ya ce mini daga masallaci zai raka Uncle Abba anguwa ba su suka dawo ba sai bayan La'asar lokacin har na yi wanka tun ɗazu abinci kuma tuni na daɗe da gamawa Jalop ɗin shinkafa da Nama ɗan sauran da ya rage mana na saka a ciki. Sai kuma daman na haɗa zoɓo har ma ya yi sanyi shi na cika wani jug ɗina da shi kuma sai da suka shanye shi, Sai wajajen Biyar Uncle Abba ya yi mana sallama ya tafi bayan ya ba ni 10k ya ce na yara ne na karɓa ina godiya tare suka fita da Yallaɓai bayan tafiyar su ne na gyara falon na tattara abin da suka ɓata zuwa kitchen falon su Jidda na koma na kunna Mbc bollywood sai wani indian film da suke yi series ya ɗau hankalina mai suna Habibi da'im da kuma gargaliyan Labarci su ke mgana to ina ɗan tsinta sosai film ɗin ya ja hankalina tuni na fahimci a dai dai wannan lokacin suke saka cigaba film din sau shidda a sati ban da jumma'a da asabar a raina na saka cewa zan dinga bin shi dramar ta ɗau hankalina.
Ƙarfe bakwai a ka gama film ɗin sai na ga sun fara shima wani ban tsaya ba na tashi yin salla su jidda tun wajen shidda da kwata suka shigo gidan a kafa suke dawowa tun da makarantar ba nisa har sun sauya kaya sun ci abinci. Tare da su muka yi salla sannan na ce su ɗauko Qur'ani mu yi karatu muna cikin karatun ne wayata da ke kan kujeran da na tashi a kai ta fara neman ɗauki alamun ana kirana Baby ce ta yi saurin ta shi ta ɗauko min ta na faɗa min Abba ne, har za ta ɗauka na fizge wayar ina faɗin.
'"Ko ba Abba ba."
Na faɗa ina balla mata harara da sauri takoma kusa da ƴar'uwanta ta zauna ta na wani fiki fiki da ido. Na yi mamakin ganin Anty Zabba na kira a cikin raina na gane dalilin kiran kawai sai na mike sanye da hijabin da na yi sallah Jidda na kallah kafin na ce" Ku cigaba kafin na dawo." Sai ta amsa min ni kuma sai na bi ta ƙofar kitchen zuwa cikin ɗakin mu na barci.
Wayar ta katse lokacin da na kai zaune gefen gado amma cikin lokaci sai ga wani kiran na ta ya sake shigomin, sai na ɗauka ina mai dai dai ta yanayina. Gaisawa muka yi da tambayan iyalan juna kamar yadda muka saba.
Sai kuma muka yi shuru na wani lokaci saboda gaskiya mu ba abokan mgana da juna ba ne sosai.
"Jiya ina ta kiran wayar ki a kashe."
Ita ta fara kauda shurun, sai na ce" E. Wallahi."
Daga nan sai na yi shuru ina jin sautin mirmishinta kafin ta ce" Sadiya ya muka ji da wannan jarabawar rayuwar! Na ji shima Tafidan na ki an ƙaƙaba masa wata matar."
Gimbiya ce ko?
Ban yi mamaki saboda ni na san kowa ya sani a tunanin Yallaɓai ni ce kaɗai ban sani ba tunda bai sanar min ba.
"E. A ina kika ji labari hala?
Na tambaya sai ta ce min Jamila ta faɗa mata jiya suka yi waya suna cikin wayar ma sai ta katse ba ta ma karisa ba ta labarin ba, ina ga shi ya sa ba ta ji an ce a yi shuru kar na ji ba."
"Sadiya akwai zafi na sani. Ni kaina har yau ban fita daga wannan zafin da Usman ya haddasa mini ba."
"Uhmm."
Kawai na iya cewa zafi ai ba ma sai an faɗa ba. Ita kuma sai ta cigaba da faɗin" Kishi fa gaskiya ne Sadiya sai wanda aka yi mawa ya ke sanin haƙikanin zafin abin. In ka nuna damuwa a ce ka ɗaga hankalinka wane wane Alhalin ba wanda ya san irin zafin da kake ji acikin zuciyarka."
"Kwarai."
Na bata amsa sai ta cigaba da fadin" Ki daure Sadiya akwai zafi amma ki daure. Dangin mazajen mu suna neman ganin gazawarmu ce shi ya sa, shi na wajena ya auri yarinyar ogansa shi kuma na wajen ki ya auri yaruwansa duka fa domin a kaimu ƙasa ne kuma Allah ya fi su, ki daure zafin zai ta ƙaruwa barin ma in sun fara zama tare amma ki yi ta addu'a da ikon Allah za ki samu komai da sauƙi kin ji ko?
'"Na ji. Kuma in sha Allahu ba damuwa."
Mun dade muna mgana ta na ta bani shawarwari sai a lokacin ta ke faɗa min ashe a lokacin mganar auran ya Usman da ta dawo gida ba yaji ta yi ba ta ce kawai ta zo gida ne ta samu kwanciyar hankali amma dangin miji suka buga mata tambarin ta yi yaji, ni kaina na sha mamaki na ce mata mu ma haka aka ce mana wai kin yi tashin hankali har da su yin yaji.
"Uhm wallahi ni ban yi yaji ba. Da amincewarsa na taho gida Sadiya. Gwara mu yi nesa da juna sai na samu damar rage jin zafinsa domin a zauna lafiya. Ba gashi an yi ba kuma muna zaune gida ɗaya da ita ba sai dai tana bangarenta ina nawa, ni dai ina zaman musulunci da ita, itama haka amma ba zan yi zaman daɗi da kishiya ba Sadiya shima ai na faɗa masa matarsa ta yi rayuwarta nima na yi tawa ni da ƴaƴana."
"Shi ne alheri ma."
Domin ban ga amfanin haɗa kai da kishiya yanzu ba kai ya waye ban da mutanen da wa ke maida kishiya yar'uwa wallahi gazarwar ki ta ke nema in kuma ta samu sai ta yaƙe ki.
Anty Zabba ta yi ta bani wasu labarai ta na faɗa min na zama jaruma. Shawarar da za ta bani kar na ce zan bibiye ta na ɗauke kaina a kanta sai na zauna lafiya amma kar na sakar mata kar kuma na ƙi ba ta dama a yi zaman musulunci wanda ba zai wuce jaje ko taya murna ba, ta yi na ta rayuwar nima na yi tawa