gidanta ne? Ballanta ni na riƙa shiryawa ina bin ka? Na yi muku kara da kawaici masu yawa amma na ga daga kai har ita ba ku san zuru ba shi ya sa na ce bari in yi magana in ka manta in ƙara tunatar da kai wannan dai shiga haƙƙi ne."
Na faɗa ina yarfa hannu da ya ke san ya san bai da gaskiya bai yi faɗa ba
Sai kawai ya ce" To ki yi haƙuri ba za a ƙara ba. Ban ɗauka hakan zai ɓata miki rai ba ne"
Tsabar takaici na kasa mgana sai kallon shi kawai na ke yi.
"Ita ce ba ta son zaman ita kaɗai shi ya sa na ke ɗaukota mu zo nan ko za ta samu sakewa."
"Ba ta son zama ita kaɗai ko kai ne ba ta son kana yi mata nisa?
"To in ma haka ne laifi ne?
Ya faɗa ya na sosa ƙeya har ya na min ƴar dariya.
"Ba shakka. To ƙarshen soyayya dai ai mun ga Laila da Majnun"
Kawai sai ya riƙo ni ya na faɗin" To ni ai ke ce Lailata ni kuma Majnun ɗin ki"
Ture shi na yi ina hararanshi wai ni Yallaɓai zai yi ma wayau.
"Oh ni dai na faɗa maka ba na so."
"To ya kike son a yi yanzu?
"Ka daina kwaso min ita ba na so. Ta tsaya iya matsayinta ban hana ta zuwa gaishe mu ba amma kar kuma a mai da zuwan ya zama na ibada mana."
"To shike nan ba za a ƙara ba. Shi ke nan ko?
Sai na gyaɗa masa kai saboda ya ga na ɗan zafafa sai ya rumgumeni ya na faɗin" Kai My Sady rigima."
Tureshi na yi ina faɗin" ba rigima ba ce gaskiya ne."
Ni ban san yadda suka ƙare ba fita ya yi ya bar ni a cikin ɗaki ban kuma san me ya faɗa mata ba amma tun daga ranar ta daina biyo min miji tana zuwa falona ta na min karairaya ba, shima ɗin ya daina kwaso min ita hakan ya fi kowa ya zauna in da Allah ya ajiye shi wannan dai da gida ɗaya muke da ta kashe ni da bariki ba ma gida ɗaya ba amma ba ta barni na huta ba
Ni da Ya Aina ta tare da Ya Balki muka kafsa kayan saka Rana. Biyu muka raba. Kashi daya namu kashi ɗaya na dangin Babansu Marwa. Namu Gwammaja muka je dashi muka raba har da Ya Murja. An cire ma mutanen Yashe na su sai kuma can ƴan gandun albasa. Sannam mu ma muka cire namu. Na Amina lokacin Datti na gida shi aka ba ma da zai koma makaranta ya tafin mata dashi. Na Ya Auwal da Ya Hamza kuma an faɗa musu suka ce kawai a rabar ba sai an ijiye musu ba, shi Gwaggo ta ce za ta aika dashi maƙota ita kuma Ya Aina daman tun a can mun ɗibar mata na ta, ita da Marwa da maƙota tare da mutanenta. Kowa ya na ta fatan alheri ni na kira Marwa da kaina ta na makaranta muka yi magana ta ce min ya ce a Rano za ta zauna na ce daman ya faɗa ba shi da in da ya fi Rano gida shi a wajen shi, kuma can ne ya gina ƙaton gida da daɗewa. Ta dai ce suna waya lafiya lau ana ta shan soyayya na ce to ta dake ta kama shi gam a hannu ta shiga zuciyarsa sosai kafin ta ayi aurin wanda in aka yin auren kuma shi kenan.
Yallaɓai na ji na ina wayar sai da na gama ya ce min wai ni uwar banza ce, na ce na ji bakomai ƙaramar uwa abokiyar wasa.
"Kin kusa ijiye na ki surukin fa Sadiya"
Ya faɗa ya na dariya nima ina taya shi na kuma ce masa ko Jidda ce haka zan zaunar da ita ina karanta mata.
"Ba shakka uwar zamani."
"Na gode Uban zamani."
Yallaɓai ya yi fafur ya ce shi kam Dattijon zamani ne ba da shi da zama uban zamani ba.
Bayan fitan shi na zauna ina tunani Jidda na cikin shekaru na sha biyar amma ba ta fara al'ada ba, sai dai ta fara ƙirgan dangi na gansu sun tsiro a ƙirjinta ban damu ba ƙila yanayin jikinta ne amma tabbas ta na gabda farawa nan ba daɗewa ba, girma fa ya kama ni wasa wasa Jidda ta kusa kaiwa munzali. Ni kaɗai a ƙasan raina na ke musu add'an Allah ya tsare min su da dukkan tsarewansa wataƙila su kaɗai ne yayana anan gidan duniya.
****
Friday.
Munnira ce ta samu ɓari ni ban ma sani ba sai da Hauwa ta yi min waya ta na faɗa min tun da gaskiya mun kwana biyu ba mu haɗu da juna ba. Na dai san ta na da cikin tun da mun yi zencen da Hauwa kwanaki da ta zo gidana.
Kuma kamar haɗin bakin itama Hauwan ta samu ciki ɗan wata ɗaya ta yi ɓarin shi amma da ta je ganin gida ne a Rano ta ce ma ba ta san dashi ba. To itama Munnira ta samu ɓari ta zame a banɗaki ta faɗi gefen cikin shikenan sai jini kwananta ɗaya a asibiti aka sallamota ta dawo gida. Ni da Hauwa mun je asibitin shi ne bayan ta koma gida muka tsara za mu je mu yini ranar jumma'a. Na kuma faɗa ma Yallaɓai ya ce sai mun dawo.
Su Jidda a gida na ce zan bar su tare da Saude tun da na yi mata waya na ce in sun taso daga makaranta ta zo gida ina jiranta. Tun safe na gama ayyukana har da faten wake mai hanta na yi ma Munnira domin ta ce na taho mata da abin daɗi. Hauwa na zauna zaman jira tun da ita ce za ta biyo min, kawai ina zaune ina zaman jiranta sai ga wayar Yallaɓai bayan mun gaisa da ya ke yau ya bar gidana da yamma zai koma gidan Gimbiya.
"Kun tafi ne?
"A'a me ya faru?
Na tambaya saboda na ji mamakin tambayarsa.
"Daman zan ce ne ku jira Daugther ta taho yanzu da mota sai ta ɗauke ku, ku tafi tare gabaɗaya."
Tuni na ji raina ya ɓaci Yallabai akwai sanabe da tsegemu. Yanzu haka ta ce za ta je ne zai ce ai mu ma za mu je ta biyo mu tafi tare.
"Na faɗa mata ta biyo ta gida ku wuce."
Har ya gama mganarsa ma, na so na danne ma zuciyata na amsa masa sai kuma na ga in na yi shuru ba amfani.
"Yallaɓai yaushe muka fara fita anguwa da matarka?
Sai ya yi shuru.
"Ka bar mu tafi kawai. Ba ta san gidan ba ne? mu haɗu a can"
"To ni na ce ta biyo ta nan ta ɗaukeku ku wuce ko ban isa ba ne?
"Ka isa."
"To tun da na isa a yi yadda na ce."
Ya na gama faɗin haka ya katse kiran ya bar ni da ƙunƙuni. Da Hauwa ta zo na faɗa mata itama sai da ta ce topha sanabe daman kun saba fita tare ne?
"Ina fa? Sanabe ne da gulma irin ta ɗa namiji ta na da mota mu kuma ba mu da ita ta zo ta yi mana lift mana."
Hauwa na dariya ta ce ba shakka masu mota.
Matar nan haka taɓata mana lokaci mu da muka ce yini za mu je mu yi sai 2 da wani abu na rana sai ga ta zo. Har mamakin yadda ta ke cin kwalliya na ke yi in za ta fita. Allah ya sa nima da gayu na ta zo ta ganni ballantana ta ce ganin idone. Ita ta ɗauke mu a motar ta kamfanin toyota ce. Accord ina gidan gaba Hauwa na gidan baya har gidan Munnira itama da ta ganmu tare sai da ta yi min mgana.
"Ke kuma wani ci baya ne ya same ki yawo da kishiya."
Ina dariya na ce" Yallaɓai ne ya siyo min wannan wulaƙancin"
Nan ba ta labarin yadda muka yi dashi Munnira ta buga shewa kafin ta ce" Ki yi zuciya ki yi mota Hajiya. Amma tabbas an nuna miki kafacinty mota yau ɗin nan"
Ni kaina sai da na yi dariya na ce to ai ina sana'ata domin na kama sana'ar Hijabai hannu biyu kuma ina samu sosai yanzu har kaduna na ke aika ma Amina.
"In sana'ata in da rai da rabo.."
"Jariri za ya zamo ango."
Hauwa ta karishe min muka tafa. Can falo muka bar Gimbiya a falo muna ciki muna hira muna shewa.
Ba mu bar gidan ba sai shidda har gida muka kai Hauwa nima ta kawo ni gida nan ta yi sallar mangariba da ya ke ta san miji na ta ne sai ba ta tsaya ba ta tuka kanta zuwa gida ciki dai gashi nan ya bayyana daga gani ta na da girman ciki sosai.
Mun je gidan Munnira da sati ɗaya Gimbiya ta je Rano ta yi sati Hajiyar Tafida kafa ta motsa ranar da za ta dawo gabaɗaya muka tafi ni da Yallabai da yara muka gaisheta sannan muka ɗauko Gimbiya muka dawo gida Kano.
Rayuwa ta yi nisa kwanaki na ta gangarawa. Tuni Gimbiya har ya fara zuwa awo sannan suna ta siyayyan kayan haihuwa ta bakin mijinta. Yadda Yallaɓai ke rawan jiki kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba, sai dai na yi masa uziri bayan tsawon shekaru bakwai ba a yi haihuwa a gidan shi ba abin mamaki ba ne domin ya nuna zumuɗi, bq shi ba hatta yan'uwan shi da nata suna ta ɗoki kowa fatan shi Gimbiya ta buɗe ido lafiya.
Nima har acikin raina ina mata fatan haka. Kuma daman gashi Yallabai kuɗi ya ke samu kwangiloli ne ya yi ta yin su akai akai buɗi ko ta ko'ina tun cikin ta na wata takwas komai na haihuwa sun gama tanadar shi har ragunan da zai yanka firɗa firɗa suna can Rano. Hauwa ta ke faɗa min ita kuma kannenta ke kiranta suna kawo mata wani rahoton
Ni dai na koma gefe na zama yar kallo abin jaje na yi abin murna ma na yi amma ni kaina na san duk abin da ke cikin Gimbiya in ya fito duniya zai ga gata. Duk da shi uban gayyar da kan shi ya ce min namiji ne aka gani a scan ɗin ta. Ban ji haushi ba domin nima ya nuna ma ƴaƴana gata da so shi da ƴan'uwan shi, shi ya sa na danne kishina ban taɓa nuna masa wani abu kan ɓare ɓaren da ya ke yi a kan cikin Gimbiya ba.
*Janafty*
*TKG02020B*
Tun da cikin Gimbiya ya kai watan fitowarsa duniya Yallaɓai ya tattara gabaɗaya hankalin shi a kanta. Da a ce ya ga fuska zai ce ne na bashi dama ya koma can da zama har sai ta haihu tun da ga shi anguwan zoma. Sai dai bai samu wannan fuskar ba, ko da ya ke mene ne maraba da abin da ya ke yi. In ya na gidanta ba koda yaushe ya ke leƙomu ba sai dai ya kira waya in ko ya na gidana kwana kawai ke kawo shi tun safe zai fita ya je gidan Gimbiya daga nan sai ya wuce wajen aiki da daddare ma can ya ke raba dare sai sha ɗaya ya ke dawowa wata rana ma har sha biyun dare ya na kaiwa.
Jiri ƙiri Yallaɓai ya san gaskiya kuma ya ke ta ke ta. E mana rashin aldaci ya ke nuna min kuma ai ya sani ba wai bai sani ba ni tun da ai kowa ya aikata mai kyau ya na sane. In ma mara kyau ɗin ne duk ya na sane. Ban dai taɓa magana ba saboda yanzu ina cewa uffan sai cibi ya zama ƙari tsab zai ce ni lokacin da na yi cikin bai kulani da ni ba ne? Ko ƴan'uwansa su ji labari su je hassada ne, shi ya sa ban taɓa ɗaga baki na yi masa mgana ba, kuma har a cikin zuciyata ina yi mata fatan ta sauka lafiya. Shi da kan shi ya zo ya na faɗa min ya yi ma Nene magana ta kira Hajiyar Tafida a samu wacce za ta zo ta zauna da Gimbiyar har ta haihu. Na ce hakan ya kamata kwana biyu tsakani kuma ya zo ya na faɗa min autar su Hajiyar ita ce Baaba Asma'u ta zo za ta zauna da ita har ta sauka lafiya. Amma zuwanta bai hana shi sintiri a gidan ba sai dai ya rage ba kamar lokacin da ba kowa ba.
Cikin Gimbiya ya fita watan haihuwan shi har ya shiga wattani goma. In za a ƙirga ma ainihin wattanin cikin kafin ya koma baya kimanin watanni sha ɗaya kenan. Duk Yallaɓai ya tashi hankalinshi sun je asibiti an ce haihuwan ba ta taso ba, a cikin satin nan ma naguda ta ta so mata gadan gadan kamar za ta haihun suna zuwa asibiti kuma komai ya tsaya nan suka kwana shuru aka dubata suka ce ba haihuwa ba ne dole suka koma gida da cewa nan da sati ɗaya in ba ta haihu da kanta ba za su yi mata C.S ne domin ceto abin da ke cikinta lafiya.
Sati ɗaya bai cika ba wata ranar jumma'a da daddare 20 ga watan october 2016 misalin ƙarfe biyu da rabi na dare. Gimbiya ta fara zubar jini. Hankali tashe Baaba Asma'u ta kira wayar Yallaɓai ranar ya na gida na ne, barcin sa ma ya yi nauyi ni ce na tashi da vibration ya ishe ni. Ina ganin Baaba Asma'u na san mganar Gimbiya ce ni na ɗauki kiran ba ta bari na yi mgana ba cikin tashin hankali ta ce masa Gimbiyar na zubar da jini ni kaina na ruɗe saboda zubar jini ga mai naguda haɗari ne babba ban san lokacin da na ɗaka ma Yallabai uban duka a gadon baya ba ya tashi a firgice. Ina faɗa masa abin da ke faruwa ya sake firgicewa da haka zai fita daga shi sai gajeren wando da vest sai da na ce ya dawo na rarumo masa jallabiyansa ya saka na damƙa masa key ɗin motar shi, kamar zan bi shi sai kuma na fasa bai kamata na bar yara su kaɗai a gida kuma ga dare ba amma hankali ya tashi ko bayan tafiyar shi ban iya komawa barci ba ina zaune ina ta addu'an Allah ya sauwake ta lafiya duk da ba na salla ina hutu ban kwanta ba carbi na ɗauka ina ta hailala da yi ma Allah kirari ban san barci ya kwashe ni ba sai misalin ƙarfe biyar saura na asuba kiran wayar Yallaɓai ya tashe ni da cewa an yi ma Gimbiya C.S. An samu nasaran ciro ɗa Namaji har a cikin zuciyata na yi farinciki na yi ta taya Yallaɓai murna muka rabu da shi da cewa shima ba daɗewa yanzu zai taho gida.
Da asuban na faɗa ma su Jidda sun yi ƙani suna ta tsallen murna musamman ma Baby, Jidda dai sai dai ta yi mirmishi shine ƙololiyar nuna farincikinta Baby ce uwar tsalle tsalle ta na murna. Ta so ma ba za ta je Tahfez ba sai da na yi mata jan ido sannan ta bi Jidda suka tafi. Ni kuma na gyara gidan na yi ma Yallaɓai abun karyawa tun da ya ce min zai dawo gida, ina buɗe datan wayata na ga an yi saƙonni da yawa a group ɗin gidan su Yallaɓai ina shiga na ga Anty Bahijja ce ta sanar da an samu ƙaruwa a gidan Tafida Gimbiya ta haihu an samu Sadauki. Sai tagging ɗin sa ake yi ana masa murna ni ma na shiga na yi tagging ɗin sa na ce.
"Alhamdulillah. Ina ta ya ka murna Yallaɓai. Allah ya raya ita kuma Maijego Allah ya ba ta lafiyar shayarwa."
Mimisco ce kaɗai ta amsa da Amin sai Suwaiba da ta zolaye ni da cewa saura ke sai kawai na tura mata emojin mirmishi daga nan na kashe data na ijiye wayar. Yallaɓai sai wajen goma saura ya dawo gidan duk ya gaji ga barci a idanuwansa na tarbe shi cikin murna ya rumgumeni ya na ce min ya gaji sannan kuma ya na jin barci sai na ja shi tiolet na taimaka masa ya yi wanka ya so ya fara kwanciya sai na matsa masa a kan ya fara ƙaryawa sannan ya kwanta to muna saman dining ɗin ne ya ke ba ni labarin yadda komai ya faru. Ashe suna zuwa ne lokitoci suka ce a yi gaggawan saka hannu a yi mata C.S saboda cibiya ce ta sarƙe wuyan yaron. Nan ta ke ya saka hannu aka shiga da ita tiyata sai asuba suka fito da ita, ta na can ɗakin hutu yanzu haka Baaba Asma'u ya baro tare da ita sai Nene da Anty Bahijja.
"Ta farfaɗo kuwa?
"E sai da ta farfaɗo sannan na taho ai."
Sai na ce to alhamdulillah tun da ta farfaɗo na ce masa ina so na je asibitin sai ya ce na bari ya huta in ya tashi sai mu tafi tare. Haka ko a ka yi shi na jira sai bayan azahar ya tashi daga barci ya sake yin wanka ni kuma lokacin na dafa kuskus mai karas da kabeji shi muka ci kafin mu tafi sannan kuma na ɗiba a kola wanda muka tafi da shi asibitin. A asibitin da ta ke zuwa dai anan ne ta haihu asibitin nan cike har da ƴan Rano sun zo mota guda su Anty Bahijja da su Anty Maimuna suna a gefen gado. Na gaishe su sama sama kamar yadda ke tsakaninmu tun faruwan abin da ya faru sannan na gaisa da Maijego an kuma ba ni yaro na ɗauka kamar Yallaɓai ya yi haki shi ya sa sai ya ɗauko fuskar Baby ban damu da mutanen da ke ɗakin ba na kalli Yallaɓai ina faɗin.
"Yallaɓai kama su ke yi da Baby fa? Fuskarsa fuskar Baby kuma ai fuskar ta na ka ne ko?
Sai ya leƙo ta kusa da ni shima ya na kallon shi kafin ya ce" Sai da kika faɗa na lura."
Nasara na gefe ta ce itama ta ce ai wannan sak mai sunan Anty Maimuna ne.
Buɗe bakin Anty Bahijja sai ta ce haba ai wannan ya fita kyau. Ita kuma Baaba