Turken Gida Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   37 / 48

108K to 111K   out of 141.5K words

ɓace ne.

"Yusuf yau fa Anty Bahijja ta ce min ba ta ga abin da aurena da kai ya tsinana maka ba. Ta ce wai na wanke gaba na baka ka sha na mallake ka, shi ya sa na shiga na fita zan liƙa ma Kawu Abba ɗiyar yayata saboda shima a maida shi shanyayye kamar ka."

"To ina ruwanta in kin shanye ni? Sannan uban wa ya faɗa musu labarin Kawu da Marwa."

In kuka na ce" Munafuka Ma'u ce, shi yasa na ce maka sai na haɗa su da hukuma"

"Ban ɗauka haka ta ke ba. Ma'u nan ta ba ni mamaki ".

Ya faɗa cikin bacin rai kafin ya cigaba da faɗin" Me ya sa na ki kirani da abin ya faru ba? Kin san dai ba zan zura idi a ci miki mutumci ba. Duk wanda ya ci miki mutumci to tamkar nawa mutumci ya ci."
.
Na kasa mgana sai kuka kawai na ke yi ina faɗin ya kai ni offishin yan sanda.

"Ki yi hakuri mu koma gida a zauna a yi mgana."

A fusace na ce" Ba zan zauna da kowa ba Yusuf hukuma ce za ta tuhume su."

"A'a."

"To ka sauke ni na tari adaidaita"

"Na ce a'a."

Ya faɗa a fusace cikin tsawa, kamar zai dake ni daga gani ran maza ya ɓaci.

"Babu wani hukuma. Ni nan zan tsaya miki sai na ji dalilin wannan kazafin da cin mutumci. Ki daina kuka ki bar min komai a hannuna kawai."

"Ni dai a'a ka bari na kai su ƙara."

"Na ce a'a ba za ki bi umarnina ba ne Sadiya?

Ya yayyaƙomin kamar zai dake ni ai sai na yi shuru

"Ko ba ki yarda da ni ba ne? Ko domin Anty Bahijja na yayata sai na zauna na zura ido a ci zarafin ki? Ba zan bar wannan mganar ba sai na ji dalilin wannan tozarcin. Na rantse da wanda raina ke hannun shi sai na tada ma duk wanda ya yi silan a taruwa a ci miki zarafi ki hankali shima"

Ya faɗa a fusace har ya na dukan sitayari duk fusata ta sai da na koma na yi shuru saboda na ga Yallaɓai ya harzuka. Daman ya kan daɗe ran shi bai ɓaci ba in kuma ran shi ya ɓaci to ba shi da kyau.
Sai na koma gefe ina maida numfashi ina jera ajiyar zuciya.

"Na maida ke gida ko gidan Alhaji?

"Mu je gidan Ya Aina."

Na faɗa ba tare da wani tunani ba sai ya yi shuru bai yi mgana ba ana ta kuma cigaba da kiran wayarsa

"Nene ina tare da Sadiya. Zan taho gidan yanzu in sha Allahu."

Na ji ya na faɗa sai na ɗaga kai na kalle shi, ya na waya ne kuma Nenen da ya ambata ya sa na gane da ita ya ke waya.

"Nene gidan Yayarta zan kai ta. Yanzu zan dawo gida, ki kuma sanar da Bahijja ba Sadiya ta tozarta ba ni ta tozarta na kuma gode mata."

Sai na zo."

Ya faɗa kafin ya kashe wayar haka muka yi tafiyar nan shuru ni ina ta sauke ajiyar zuciya shi kuma ya na ta tsula gudu ba daɗewa muka iso gidan Ya Aina ya sauke ni kuma bai ce min komai ba ya juya motar a fusace ya bar layin ni kuma na taka na shiga gidan Ya Aina da sallama cikin muryata da ke shaƙe saboda kukan da shaƙa kamar an yi min mutuwa.



*Janafty*
*TKG018*

*Littafin TURKEN GIDA, 1k ne akan manhajar Telegram.*
09069067488

Na shiga gidan Ya Aina ko gani ba na yi saboda tashin hankali da damuwa. Tafe na ke ina jefa ƙafuwana ba tare da na san in da za su faɗa ba. Ya Aina na hanga a ɗan karamin madafinta dake tsakar gida sai ƙannen Marwa na gefen ɗakinta a kan tarbarma suna cin abinci. Ko sallama ma ban yi ba ni dai kawai na shigo kuma na dumfari ɗakin Ya Aina so na ke yi na samu waje ni kaɗai na fashe da kuka na yi kuka mai ƙara mai sauti ko zan ci ɗan sauƙi sauƙi abin da ke taso min daga ƙasan zuciyata.

"Laa Mama ga Umma Sadiya."

Na ji wani cikin yaran ya faɗa amma ba zan iya gane ko waye a cikin su ba. Ni dai ƙafafuwana na taka suka shigar da ni falon Ya Aina sannan lokaci ɗaya na zube a saman cafet ɗin ɗakin tare da fashewa da kuka mai sautin da har a tsakar gida ana jiyo kukana.

Da gudu Ya Aina ta shigo ina jin salatinta.
"Innalillahi me zan gani Sadiya?
Ta faɗa lokaci ɗaya ta na zama kusa da ni ta saka hannu ta ɗago ni ta na mai kiran sunana.

"Sadiya"

"Ke Sadiya me ya faru?

Ta ke faɗa cikin tashin hankali da damuwa. Ban buɗe idanuwana ba amma na ɗora kaina a saman cinyarta ina cigaba da rera kukana, sai na ji kamar jikina ya na wani irin yam tsikar jikina sun tashi yam! Zuciyata na ji ta buɗe ina so na yi kuka mai yawan da na daɗe ban yi irin shi ba. Sannan ji na a saman cinyar Ya Aina ya ƙara raunana raunina da ya sa na ji kamar tsawon shekaru ban samu kafaɗan da zai tallafeni ba, shi ya sa na daɗe ban yi kukan da na ke jin yau ya na tahowa daga ƙasan zuciyata ba.

"Kai ku koma ku cigaba da cin abincin ku."

Na ji ta na faɗa, sai na ɗan buɗe idanuwana da suka kumbura saboda kuka sai na gansu sun yi jere a bakin kofa suna kallon mu. Maganarta ya sa suka fara fita ɗaya bayan ɗaya amma fuskokinsu dañkare da mamakin ganina ina kuka.

  Sai da suka fice sannan Ya Aina ta ƙara maida hankalinta a kaina.
"Sadiya me ke faruwa ne? 
Nan ma na yi mata shuru ina ta kuka hawaye da majina na zuba lokaci ɗaya.

"Ko wani abu ya faru tsakanin ki da Baban su Jidda ne?

Sai na ƙara ma kukana Volume amma na kasa mgana.

"Sadiya ki bar kukan nan ki yi min bayani. Duk kin ɗaga min hankali."

Ina shassheƙa na ce" Ki bar ni na yi kuka Ya Aina.. ki bar ni na yi kukan da zuciyata za ta samu natsuwa."
Na ƙarishe faɗa ina mai ƙara fashewa da kuka sai ta ƙyaleni ina ta kukana amma ta saka hannunta guda ɗaya a bayana ta na bubbugawa alaman lallashi mun fi karfin sama da mintina ashirin sannan kukan ya fara ɗaukewa sai shessheƙa da kuma jan majina.

"Sadiya me ke faruwa?

Ta faɗa ta na kallona dai-dai lokacin da na tashi daga saman cinyarta ina faman goge hawayena da ɗankwalina da ya zame daga saman kaina.

"Ya Aina Ma'u ta ba da gudummuwa an tozartani yau a dangin su Yusuf"

"Ma'u kuma?

Ya Aina ta maimaita sunan ta cikin mamaki. Kawai sai na ji sabon kuka ya taso min ina kukan ina labarta ma Ya Aina abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe.

"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un"

"Anty Bahijja ta ci min mutumci ta kirani dangin bokaye  da asiri. Ta ce aurena da Yusuf ba ta ga amfanin shi ba, Ya Aina wai ni suke zargi da ƙoƙarin zubar da cikin Amaryan Yallaɓai? Duk ta dalilin Ma'u. Domin ita ce ta ba su damar duk abin da suka yi min Ya Aina."

Na ƙarishe faɗa ina gunjin kuka da ƙarfi saboda sai na ji kamar a alokacin ma abin ya ke faruwa.

"Innalillahi. Ita Ma'un ce ta aikata haka? Amma ta ba ni mamaki matuƙa ban taɓa tunanin haka daga gare ta ba."

"Ba in ina cewa munafuka ba ce sai a riƙa ganin laifina ba? Yanzu dai kun yarda ko? to Ma'u ta daɗe ta na ci duduniyata a dangin Yallaɓai ta daɗe ta na son rana irin ta yau ta faru sai yau burinta ya cika."

Na faɗa ina goge idanuwana da hannuna kamar wata yarinya.

Ya Aina ta kasa mgana saboda lamerin ne ya zo mata cikin ba za tan da ba ta taɓa tunani ko tsammani ba. Salati kawai ta ke yi ta na ɗaukowa ta na direwa.

"Ma'u ce ta je ta faɗa ma Anty Bahijja dangin mahaifiyata yan asiri ne, sannan ita kuma Amaryan Yallaɓai ta ƙara da cewa ta na gidan ma Inna Mariya ta kawo min asiri. Sannan kuma ta ce wai yadda na gama shanye Yallaɓai haka na ke so na tusa ma Kawu Marwa domin shima a shanye shi da asiri tun da mu ƴan na gada ne ba na haya ba."

"Na shiga uku ni Aina. A ina suka ji labarim Marwan? Ko shi Abban ne ya faɗa?

"Ma'u ce ta fasa maganar. Ita kuma Ya Murja ce ta faɗa mata. Ba ina faɗa muku munafuka ce kuna ganin kamar ban da haƙuri ba? Uhm ni kaɗai na san wace ce Ma'u da kaidin ta."

Na faɗa ina mai ɗaura ɗankwali na rufe kaina kukan ya tsaya amma zafin da ke cikin zuciyata ya kasa raguwa.

"Ma'u. Lalle ko Ma'u ta ba ni matuƙar mamaki."

Ta fada ta na mai yin tagumi cikin ɗimuwa.

"Shi ya sa na ce an zo ƙarshe wallahi tallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da su Ya Aina. Ba zan bar wannan kazafin da suka yi min ya tafi a banza ba."

Sai ta kalleni kafin ta ce" Shi Babansu Jidda me ya ce?
"Me kuwa? Ya ce shima zai ɗau mataki amma ba shi zai hana ni ɗau nawa matakin ba."

"Alhajinmu ya sa ni?

"Ke kaɗai kika san abin da ya faru."

Na bata amsa ina kallonta sai kawai ta miƙe tana faɗin" Ya zama dole ya sani domin magana ce da ta shafi zumunci. Kuma ni kaina ba zan so a bar maganar ba gwara a ɗau mataki tun da ya shafi zuru'armu ya kuma shafi auran ki da mutumcin ki, ya zama wajibi a shiga wannan mganar domin a yi min lamarin tufkan hanci."

"Wa za ki kira?

Na tambayeta ganin ta na ɗaukan wayarta.

"Hamza zan kira. Shi sai ya kira Alhajinmu."

Sai na yi shuru saboda na san Ya Hamza zai ba ni dukkan goyon baya har sai ya ga an ƙwatamin haƙƙina. Da dai Ya Abubakar ne daman ba zan saka ran ya goyi bayana ya bar Ma'u ba amma kuma ya sani wannan karon ba gudu ba ja da baya ni da Ma'u har abada sannan sai hukuma ta shata mana layi a tsakaninmu.

A gabana Ya Aina ta zauna ta labartama Ya Hamza duk abin da ya faru ta ƙarishe da cewa" Sadiya ta zo min ciki kuka na fitan hayyaci. Hamza Ma'u ba ta kyauta ba, kuma tun da ta taɓa auren Sadiya bai kamata a yi shuru ba. Ka kira Alhaji ka faɗa mishi sai a san yadda za a shiga mganar. Domin Sadiya ta ce ba za ta yarda ba sai ta kai ta ƙara hukuma."

"Ta yi min dai-dai. "

Ya Hamza ya faɗa kafin ya cigaba da faɗin" Ni ban yi mamakin abin da Ma'u ta aikata ba daman can halinta ne ta na wani muƙu muƙu na munafunci ba Sadiya ni nan Hamza Muhamamad Yashe jinin Sadiya ba zan bari cin zarafin da a ka yi mata ya tashi a banza ba. Sannan duk wanda ya taɓa zuru'an Mama kamar zuru'an Gwaggo ya taɓa. Sannan duk wanda ya nemi tozarta zuru'an Gwaggo kamar zuru'an Alhaji ya taɓa. Kuma taɓa waɗanan zuru'an dai-dai ya ke da ka taɓa mana mutumcin mu da darajan mu, kuma taɓa darajanmu dai-dai ya ke da ka nemi faɗa damu. Saboda haka wannan lamarin ba Sadiya kaɗai ya shafa, har damu gabaɗaya."

  "Gaskiya ne wannan."

"Sabo da haka, yanzu zan kira Alhaji a waya na faɗa masa abin da ke faruwa. Ya kamata ya sani saboda abu ne da ya shafi auren Sadiya. Sannan za a yi zama zan kira Auwalu jibi asabar mu shigo Kano. Ba Ma'u ba har Baaba sai an kira. Za ta ci ubanta sai mun ji in yayar Yusuf ita ce jininta ba Sadiya ba. Kuma daga wannan a yi mata iyaka da komai yadda za ta fahimci Sadiya ma ta na da gata."

"Haka ne gaskiya ne. Haka yakamata a yi."

Nan take ya ce ta ba ni wayar da ya ke a speaker ta saka wayar shi ya sa na ji komai. bayan na amsa mun gaisa ya ce" An ce kina ta kuka? To ki share hawayen ki, mu ƴan'uwanki za mu tsaya miki har sai gaskiya ta bayyana. Shi Yusuf ɗin me ya ce? Ko wani mataki ya ce zai ɗauka?

"Ya ce zai ɗau mataki amma bai faɗa min matakin da zai ɗauka ba."

"Ok. Daman ai na can gidan su matakin na hannun shi, mu kuma na mu na gida mu ne za mu gyara lamarin. Ki kwantar da hankalin ki, in ba za ki koma gida ki yi kwanciyar nan ki samu natsuwa har zuwa da safe. Amma shi kan shi Yusuf ɗin in bai wanke ki a wajen yan'uwansa da zargin da suka zarge ki ba, za mu saka baki mu mu ɗaukan miki mataki, ba ta yuyuwa a ɓata miki suna sannan a bar shi ya tafi a banza"

Bai kashe wayarsa ba sai da ya jadaddamin na kwantar da hankalina wannan karon Ma'u ta ƙai ƙarshe kuma sai ya ga ƙarshenta. Sai na ji hankalina ya kwanta ba tabbaci gareni akan Ya Hamza ba. Ina da kyakyawan yaƙini a kan zai tsaya a kan wannan mganar har sai an ƙwatomin haƙƙina kamar yadda ya faɗa, sai na ji hankalina ya ɗan kwanta ko hukuma ba ta shiga ciki ba, hukumar ƴan'uwana za su tsaya min har sai gaskiya ta yi halinta. Har sai ainihin fuskar Ma'u ta bayyana a gaban kowa ya gane ta.

  Ya Aina ta dafa min ruwa zafi na sha da bombita. Ta ce na kwanta na huta ciki na shiga na haye gadonta kuma cikin ikon Allah na ɗan samu barci amma zuwa huɗu da rabi na tashi lokacin Marwa ta dawo daga asibiti ba ta dameni da tambaya ba ƙila Ya Aina ta ce kar ta dame ni ne, amma dai mun gaisa har ina zolayanta da Amaryan kawu ta fita ta na faɗin" Kai Umma."

Tsakar gida na fita na yo alwala na iske Ya Aina ta tankaɗen garin tuwo. Yaran duk ba sa nan sun tafi hadda yamma, ɗaki na koma na ta da salla, ina cikin sallar na ji muryan Rahila sai da na idar sai ga ta sun shigo ita da Ya Aina.

"Ah Sadiyalle daman kina nan?

Ta fada ta na ƙoƙarin zama a saman kujera.
Sai da na ɗago ina faɗin" Ga ni ko kin gani Rahilatu."
Sai lokacin muka haɗa ido ta ga yadda idanuwana suka kumbura saboda kuka.

"Ciwon ido kike yi?

Kafin na ba ta amsa Ya Aina ta ce" Kuka ta yi."
Sai ta kara kallona kafin ta koma kuma ta na kallon Ya Aina.

"Me ya faru?

"Daga ina kike da yamman nan?

Ya Aina ta katse mata tambaryarta.

"Makociyata ce ƙanwarta ta haihu. Shi ne muka haɗu gabaɗaya muka taho barka muna zuwa na ga anguwarku ne sai na ce su wuce bari na shigo mu gaisa."

"Me ya faru?

Rahila ta tambaya bayan ta dire maganarta.

"Lamarin ne abin mamaki da takaici."

"Wai me ya faru don Allah?

Nan Ya Aina ta labarta mata dukkan abin da ya faru sai Rahila ta saki Sahla da ke hannunta ta na shan nono kafin ta ce" Innalillahi kai Ma'u ta yi asara. Kai jama'a wannan wani irin cin zarafi ne da cin mutumci?

Ta faɗa har idanuwanta ya na kawo ƙwalla
Ni ta kalla ni ko na dukar da kaina ne kawai ban yi magana ba, saboda ana ƙara maganar abin ne ina jin ƙunar zuciyata na ƙara ƙamari.

"Duk abin da ke faruwa tsakanin Ma'u da Sadiya ban taɓa ba ma Sadiya gaskiya ba sai dai na ba ma ita Ma'u saboda dai kar ta ji a ranta muna wareta saboda ita ba cikin mu ta ke ba. Amma ni kaina na san Ma'u da wani abu a ranta game da Sadiya. Sai dai har ga Allah ban taɓa tunanin ta yi nisa haka ba. Ban taɓa tunanin za ta iya ba da goyon baya a ci zarafin Sadiya ba. Ban taɓa tunanin za ta je ta kai mganganu masu muni haka ba, mene ne riban ta ? Me ta samu? Har wata can ta fi mata jininta? Mene ne riban abin da ta aikata?

"Riban ta na tozarta. Ribanta a ci mutumcina na muzanta na wulaƙanta a idon duniya. Daman ta faɗa min a ranar da aka fasa auranta da Ya HamzaCds cewa sai ta yi sanadiyar muzgunama rayuwata kamar yadda na hana ta farincikinta nima sai ta hana ni nawa farincikin. Kuma ta daɗe ta na yi min bita da ƙulli wannan ne dai ya yi munin da ba zai ɓoyu ba."

Na faɗa ina maida hawayen da suka cika min ƙwarmin idaanuwana.

"Ba shakka."

In ji Rahila kafin Ya Aina ta karɓe da faɗin" Shi ne daman ta ke riƙe da shi? To ai abin da kika yi ba laifi ba ne. Ta dalilinki aka samu masalaha sannan aka cece taɓarɓarewan zumuncin mu gabaɗaya."

"Uhumm. Ni fa mamaki na ke yi wai Ma'u ce za ta yi ma Sadiya haka? Me ta tsare mata? Me ya sa ta yi haka? Har da zuwa ta na ba da labaran da ba su da tushe ballatana makama."
Rahila ta faɗa ta na ƙara bayyana mamakinta.

"To ai duk komai ya zo karshe. Domin Hamza ya ce ba za a bar mganar ba za a yi zama na musamman."

"Sosai. Ko ni ban goyo bayan a bar mganar ba. Ita kanta Ya Murja hakan sai ya zame mata darasi da kwashe wasu labaarn ta na faɗa mata."

Ya Aina ta ce" Kar ma ta yi hankali ita ta sani. Amma yaushe kana Babba ka riƙa bin yaro ƙarami kana gaya masa maganganu. Ni fa ban ɗauka za ta fita da mganar Marwa ba har sai da na ce mata ya ce ba ya so kowa ya ji sai sun gama dai-daitawa da ita Marwan sai ya je ya sanar da magabantan shi amman shi ne ta je ta faɗa ma Ma'u ita kuma ta je ta sanar ma ƙanwar uwarta."

Ya Aina ta ƙarishe faɗa cikin bayyana zafin abin har a cikin zuciyarta.

"Wata Marwan? Me ya samu ita Marwa ɗin?

Ya Aina ce ta sanar da ita abin ake ciki.
"Shi ne fa ta je ta kwashe ta faɗa ma Ma'u ita kuma ta sanar

37 / 48