ARNE Rayuwar Da Aka Ki By Surayyah M.S

Author :  Surayyah M.S Category :  Romance

Chapter   12 / 22

33K to 36K   out of 63.8K words

ba tare da yace komai ba"

Shiru abban yayi zuciyar sa na kuna' jin sautin kukan kamil din gwanin tausayi

Janyo sa yayi zuwa kan kujera ya mika masa ruwa ya Sha

Kamil meya faru abba ya fada ya na kallon sa

Shiru yayi sabida har yanzu kwakwlwar sa bata tan tance masa abun da zai fara CE ma abba ba

Mariya CE? Da sauri yace ah'a abba ba ita bace

Toh meye ne kamil fada min naji

Ehmmmm uhmmm abba dama enaso na tafi ne

Ka tafi? Ena kenan

"Wani bugun zuciyar sa ta farayi ""a take"

"Yace AB..bb...ah enasoo naje garin iyaye na ne ,Inda muka fito...."

What kamil? Abba ya fada da dagun murya

Uhm wannan ai maganan banza ne.kai yanzu zaka ma gane enda kuka fito ranar a dan shekarun ka da

basu fi 13 ba

"Eh abba zan gane""'"

"Ah ah kamil,na hana wannan tafiya"

Ba enda za kaje saboda

"Banga dalili ba,"

Wahala kawae zaka je kasha wa kasani?

Yanzu duk guri ya zanca

Wani hawayen ne ya sauko masa bazata

Take ya tsuguna yace abba dan Allah ka bari naje

Wallhy na maka alkwarin ba abunda xAi faru

Kamil baza ka je ko ena ba nagama magana

Tashi kaje ka kwanta gobe ZAmU koma gida tare

Aikuwa jin ambaton gida yasa kamil turjewa awajen ya kamo kafan abba yana rokon sa ta Allah

Tun abba na binsa da lallabi har ya fara daga masa murya'

"Sosai abban ya fara Nuna Bacin ransa akn maganan'"""

Shiko kamil fir yaki ya dena; ga wani hawayen ban mamaki da ya ke bin idon sa

Na CE in wani Abu aka ma a gidan tun wuri kafada min

Amma ka San Allah? ba zan bari kasa kan ka cikin hatsari akan aikin banza ba

Abbbba don..All..ah

kamin shiru kamil ya fada a tsawace

Tuni Hajiya Zainab ta bayyana sanye da hijab

Ganin kamil sheme sheme aka sa tayi yana kuka

shima abban na tsaye na hushi

Lapya kuwa Alhj?kamil meye haka ta so

Da Sauri ya mike ya nufo wajen ta mummy dan Allah kice abba ya yayi hakuri ya barni naje

"Kamil son"" just calm down ya isa haka"

"Zo nan ,"

muje ka kwanta gobe da safe zamuyi magana

U've been crying tun dazu ena jin ka

"Ke Zainab ki barsa sai ya Fada min dalilin sa na tirjewa akan wannan tafiya,,,I mean"

For God sake kamil ba haka yake ba

Ya fada hankalin sa a tashe

Hakane Alhj kafadi gaskiya

ni nasan bazaiyu tafiyan nan ba dalili ba

Ehen kema kin gani ko

"Dan shiru tayi sannan tace ""je can dakin ka jira ni son tashi ena zuwa nima"

Sum sum kamil ya mike ya nufi daki

Abba na binsa da kallo

Uhmm Alhj ni zan yi kokrin masa magana duk abun da ake ciki da safe zan sanar da kai komai insha

Allahu

"Yawwa Zainab, dan Allah kiyi kokri"

Sam bana son ganin sa a haka

Sosai damuwa ta bayyana fuskar sa

Bakomai Alhj sai da safen

## zaune ta same sa ya hada kai da gwiwa

Yayi shiru

Son ta fada tare da dafa sa

Tell me meya faru?meya sa zaka tafi?

Mariya CE koh?

Wani sauke ajiyan zuci yayi ya dago Kansa ya kalle ta

Mummy kawae Shhhh kamil don' lie to me

Ok don bamu muka haife ka ba shine bamu da matsayin da zamuji damuwar ka

Ko?

Noo mummy ba haka bane

Toh just tell me mana kamil ta fada cikin fada

"Look abban ka baida lapya"" tun a UK yake fama, amma banga tashin hankali a fusakr sa kamr na yanzun"

nan ba

Me kake tunani_?baza mu iya cike gurbin iyaye n ka bako

Da Sauri ya riko hannun ta yace nooo mummy

Ki daina fadan haka dan Allah kinsan hakan ba gaskiya bane

Kamil ka fada mn toh ena jin ka

Kallon ta yayi a nitse

"Yace muummy promise me bazaki Fada ma Abba exactly abunda nake boye masa ba ""!"

What!! kamil ban maka wannan alkwari ba just tel me kawae

Mummy amma yanzu kikace baida lpya fa .na tabbata in kika Fada hankalin sa zai fi haka tashi

Ok ok fine shikenan enajin ka*

Nan kamil ya bata labrin duk abunda ya faru har yay silar zuwan sa nan

"Jin sa takeyi shiru, Sosai jikin ta yay sanyi, numfashi ta sauke tare da jin jina ma hali Erin na mariya"

"Batayi wata wata ba ta mike tsye..kamil son""!"

ka kwnta ka huta

Na maka alkawari zaka tafi gobe insha Allahu

Murmushi ya mayar mata sannan ya haura gadon nasa

"Yace nagode mummy""itama"

Gudnite ta masa ta fice abunta

Surayyahms

:

ARNE

by

Surayyahms

*AM££NCI WRIT£R'S ASSOCIATION *

Page77

"Bata bude idon ta sai a gadon asibiti,"

Mummy ta hango tayi zugum ta rafka urban tagumi a gefe

"Wani hawayen takaici da bakin ciki suka soma gangarowa da ga idanun ta ,...a ranta tana cewa yanzu"

na rabu da twin soul kenan

"Bazan iya rayuwa ba kai ba kamil,"

Cikin wannan tunanin kuka mai karfi ya kufce mata bazata

Ai ko da Sauri hj mariya da hj shafa suka nufo kusa da ita

"Faryal ,alhmdullhi ya jikin"

Kukan me ki keyi kuma mummy ta Fada tana kallon ta

Wurgi tayi ta hannun mummyn data kai zata tallabo ta

"Ni Ku kyleni, ta ke ce wa cikin kukan"

Haba faryal maman ki kike CE ta kyale ki ?

"Barta kawae shafa ,naga alaman wasu almatsusai na yawo kan ta ne"

Ki duba yarda take so ya kashe kanta akan wani wawa shasha

Mummy ni dai kice ya kamil ya dawo

"Bazan Fada ba uwata,.. Ke kar kiga kina gadon asibiti yanzun nan zan mini ta tas"

Don haka kar ki sake kiramin sunan wani kamil anan

"Marar kunya kawae,to ki bisa yawon gantalin mana nasan kin cika masoyiyar sa"

"Tsaya mariya ya isa haka .kibi ta a hankali mana ,ahalin yanzu bata cikin hankalin ta"

"Da Allah shafa kyaleni,faryal da like ganin ta ba abin ta a hankali"

Itako kuka kawae tkeyi kamar zata fd da ranta

"Kiyi shiru mama na kinji,za a dawo miki da kamil din ki hj shafa ta Fada tana goge mata hawaye"

A hakai ta rrarshe ta har suka samu suka koma gida

Karfe 7na safe haji Zainab ta gama ba wa alhj bayanin tafiyar kamil

Amma fa alhaj ena fatan ba zaka CE zaka tuhumi mariya akan zancen nan ba...don' na tabbata kamil

bazai min karya ba

Yace min ma da sannin ta ya bar gidan

Ah a Zainab Dama jiki na ya bani akwae hannun mariya acikin lamarin nan

Meya sa zaki ce kar na tuhu me ta

"Alhj da ka daiyi abunda na gaya makan kawae,"

Ko wace uwa hakan take so ma yar 'ta.

Amma ka zuba mata idon dai na dan lokaci

Kar ka mata maganan kamil din

Wata kila hakan yasa

Don' Allah Alhj I'm dai kwanciyar hankali kake so ma kamil

Komai zai dai daita insha allahu

"Dan shiru alhaji yayai kafin yace"" zainab_hakkin mu ne da kamil ne ya nemi asalin sa nasani"

Amma .......ah ah Alhj ai mun gama magana ya kama ta ka zama mutum na farko da zaka karfafa masa

gwiwa shima ba so yake ya barka ba

Toh shikenan ena shi kamil din

Mikewa tayi suka shigo tare

abba gani

"Naji bayanin Ku son,amma da sharadi"

Ina son ka min alkawari in ka tafi

"Zaka sanar da ni duk halinda kake ciki,?"

Sannan kamin alkwari zaka dawo nan ba da dadewa ba

Had cikin ransa baiso ya dauki wannan alkwari ba amma ba yadda ya iya

Ya so ace ya bar rayuwr su ne gaba daya

Don' bazai iya zama yaga faryal a matsayin matar Khalid ba

"Kamil kayi shiru ena jinka ,in ba wannan alkwari ba tafiya"

Aha ah abba na maka alkawri zan aika ta hakan

Yawwa son Allah ya maka albarka

Tare suka taka masa har bakin motar sa

Son kaji abubuwan Dana Fada maka ko

Just take care

Ta fada tana dn murmushi

Nagode mummy kema ki kula kinji zan kira ku

Yawwa shiga kar kayi dare kan hanya tafada tana goge

Guntun hawayen ta

Wani godiya yayi wa Allah da haji ta juya kan maganan bata Fada korar sa haji tayi ba

Amma meyasa mummy tafa ma abba abunda ke tsakni na da faryal?

"Marairaice fuska yayi cikin kishi da takaici yana cewa maybe ma kafin na dawo ta aure shi,amma"

bakomai nima zanyi kokari ma mance da ke

I wil just try my best naga na sami abunda zan je nema bye faryal ya fada tare da goge guntun kwallan

sa

Gudu ya shigayi sosai...bai tsaya ba sanda ya gansa cikin garin yola hotel ya nufa kafiin gobe yA fara

aikin sa

Ranr Sam mariya bata gane kan Alhj badan abincin da take zama aci atare wannan karon ko kulawa baiyi

ba

Kuma bataji yayi maganan kamil ba

Faryal baki da lpya ne ? Abban ya tambaye ta durkushe gaban sa

"Lpyana lau abba ,ah ah princess's"

Yau sati na biyu gidan nan na lura sai an miki Fada cin abinci

Ko akwae matsala ne

Wani zuciyan ne yace mata ki fada ma abba komai ki huta

Wani kuma yana ah'a kin manta da maganan mummy? zata iya Daura muku sharrin da zai iya rabaki da

martaba idonn mahaifin ki har ma kamil

"Faryal ""abba ya saka kiran ta"

Cikin wani irin sautin kuka ta amsa babu komai abba

Ke kar kice zaki mana wani shashancin tsiya anan haj mariya ta haura mata da fada

Wani mugun kallo tabi mummyn ta dashi a kasa kasa cikin xuciyan ta na cewa

Bayan kin cuce ni kin raba ni da farin ciki na .....

Na FASA jin tsoron naki

Wallhy sai na Fada ma abba komai

Kuma yay kamil baya gidan nan kin kore sa kema kima sa vayani kiji in da dadi

Haba mariya karki na daga mata murya haka abba ya na Fada Yana lura da kowanne su

Wani kallon baraza na tama mumyn tace

Abba dama ni da.Yaya kamil

Ke ya isa haka karki sake bude bakin ki an an

Tashi ki wuce ki bamu waje Sha sha kawae

Mummy ta ka rasa tana huci

Mariya Ashe bazaki bri ba

Tashi ki Shiga ciki princesss

Da gdu faryal ta haura sama tana Dada sautin kukan ta

Daure fuska tai tama tana huci

Wai nikam mariya ena kamil ne abba ya fada yana maida kallon sa wajn ta

"Ni ban sani ba Alhj,"

Zuciya fal da tsoron kallon da yake mata

Ta mike ta nufi sama itama

Bin ta yayi da kallo yace hmm mariya kenan....

Bazan taba aura ma faryal wanda bata so ba.Indai Nina haife ta

Surayyhms :

ARNE

by

Surayyahms

*AM££NCI WRIT£R'S ASSOCIATION *

Page78

Har gado ta bita ta fin ciko ta zuwa kasa

Tashi matsiyaciya Yau zaki Fada min ranar da muka dawo SAA ni da ke a gidan nan

Idon ta a bushe ta mike tana kallon mummyn

Janyo ta tayi tace faryal meye kike tunanin zaki Fada ma baban ki dazu?

Wato kina Neman Tona min asiri ko

Bamuyi dake bazaki Fada masa kinsan komai ba?

Mummy ni na gaji ne..gwnda abba yasan komai

"Nagaji da. ""* bata kara sa ba taji tas a fusknta"

Kin gaji da min biyyayya a matsayina na uwarki ko

Mummmy just shut up tafada cikin wani razannanen tsawa da ita kan ta faryal sanda ta ja da baya

Na baki kwana biyu tal kidawo cikin hankalin ki in ba haka wallhy zamu sa kafan wando daya dake

"Mu zuba ""*ta fada tare da fice waa cikin tsananin fushi"

"Kuka hade da tsoro ne ya kama ta lokaci daya"""

xUbewa awjen akasa tayi tana maimai ta kalmar ennalihhi wa enna ilahi rajiun cikin kuka

Satin kamil hudu a yola Da sassafe cikin kauyen mayo balwa ya fice ya nufi anguwr da suka tashi da su

"papa, duk da ma ya Sha yawo cikin kwanakin""' ga uban kashe kudi daya yi wajen Neman taimakon mutane"

Sosai wuri ya canza da kyr yake gane hanya 'domin kuwa a

Lokacin da yA bar gurin su kadai ne a bayan anguwar duk jeji ne gefen su

Gashi yanzu wajen ya sauya gine gine sun cika ko ena

Gefe ya samu ya zauna yana tunanin ta ena zai fara ..gashi Dama nan ne waje na karshe a cikin list din sa

Can ya hango wani mai shayi da ya masa mugun kama da wani mai sayar da sigari da daya ke karami

Mikewa yayi ya Shiga motar sa ya nufe sa

Da sallamr su suka gaisa

Ogah lpyaa dai ko

Ko kana tambaya ne?

Ahh lpya lau

Amma dan Allah anan garin ka tashi?

Eh ogah ni cikakken dan garin nan ne

Dan juya wa kamil yayi yana Dada duba anguwan da kyw ko zaiga wani abun da zai kama kwatancen sa

da shi

Lpya dai ko ogah? Ko ka bace kwatance ne

"Ehhh toh*"" kace anan ka taso ko? Tabbas kuwa ogah anan ba enda ban SANI ba ma kenan"

Toh ko kasan wani ana Kiran sa kawu James abashi?dan kwantncen kammani ya masa yace

Amma fa ya Dade yanzu na maka na yaran ta ne

"Dan waro ido waje mai shayi yayi ,"

Tabbbb kai kuma meya ha daka da shi....

Kasan shi ne?

Eh kai na san shi mana abokin baba na ne ai

Ena mijin aunty vicky

Da Sauri kamil yace eh

Cikin tsananin mamaki mai shayi yace amma ogah me zai hada balarabe da wannan katon Arnen

Dan dariya kmil yayi yace ni dai in ka San enda zan same shi ka Fada min ko ka taimaka ka kaini yanzu

"Ah""'a gaskiya bazan iya ba ogah chaabbbb"

Don naga ma Ku masu kudi ba ruwan ku ne shyasa na kula ka

Amma duniya ba yarda gaskiya

Ni bazan baka adress ba kuma bana binka ko ena

Kaga tfiya ta

Da Sauri kamil ya fito daga cikin motar yabi bayan sa

Haba bawan allah ka taimaka min ko wani Abu kake so ai sai ayi magana

Nasan na daga ka kan sana'arka ka taimaka pls

Gaskiya ko zan gaya maka da sharadi sai naji ka waye ne kai

Kar na samu cikin hatsari duka da kawu James

Dan dariya kamil yayi yace wannan ba matsala bace

"Suna na kamil,daga garin abuja nake"

Wanda nake nema kawu na ne yayan mahaifiya ta

Mahaifiya?kana nufin kawu James Nada wata yar uwa da ta wuce joanah ne?

What kasan mama na? Kamil yafa da a da burce

Me kake nufi maman ka ogah?

Bayan sun mutu ita da mijin ta da danta da dadewa

Cikin wani irin yanayi kamil yace ban mutu ba

Ena Raye ....

Ah'ah bangane me kake Fada ba fa

Kai waye ne...mee hadin ka da mutuwar su

Harda hawaye

Dan Allah ka kaini gidan kawu James

Na roke ka

Cikin mamaki da daurewar kai mai shayi yace wai kana nufin kaima dan su joana ne?

Ta ena?

Eh ka kaini zaka ji komai acahn

Nan suka nufi gidan James tafiyan minti ashirin

Da saurin sa ya biyo bayan mati mai shayi yana cewa ena wanda kace na maganan yar uwata joana

Chak ya tsay ganin tsaban kywu na halitta da Allah ya zuba ma kamil da yayi tsayuwar sa jilin motar sa

Bawon Allah ya fada sannan kamil ya juya

Karin farko na hada idon sa da kawu James yasan shi din ne

"Wani kuka ne ya kufce masa""* duk rayuwar sa da iyayen sa suke dawo masa a zuciyar sa"

Cikin mamaki da dimuwa mati da kawu James su ke kallon sa

Tallobo sa yayi yace lpya kuwa dan samari

Meya faru kake kuka haka

Rungume kawu yayi yace kawu nine fa

Raphael

Da sauri ya dagosa ya kalle sa idonsa tam da hawye RA..Pha...el

hannu na bari yakai fuskan kamil din

Sai yanzu ne yake ganin tsan tsan kamanin sa da iyayen sa

Eh nine kawu James ni ne raphael ban mutu ba

Wani kuka kawun ya fashe dashi shima ya tsungunna

Rapheal mafarki nake ko fatalwa nake gani

Mati ka duba min shine ?

Mati kam tuni yayi suman tsaye

Cikin wani mamakin kamil yace mati Dama kaine? Da gudu mati ya taho shima ya rungume sa ya na

hawaye

Abokina Ashe Kaine?raphale dama baka mutu ba

Ban mutu ba mati Kaine ka canza haka ban gane ka ba

Kaine dai ka canza raphel wallhy na dauka wani balarabe ne ya bata hanya

Muje ciki kawu James ya fada yana kamo hannun kamil din

Surayyya

:

ARNE

by

Surayyahms

*AM££NCI WRIT£R'S ASSOCIATION *

Page79

"Mariya kenan, kina wani abu kamr baki da maths"

Ni dama na lura da faryal tun tuni baza ta iya jure rashin kamil din kusa da ita ba

"Tafiyar san Shika dai ke damun ta yanzu,"

Mtsww shafa yarin yar nan fa ta fara wuce gona da iri

Ni fa nagaji da llabata daga yaznu ubanta zan naci

"Don dolen ta zata fitar da wannan maitan son kamil din data kulla a ranta""'"

Ja'irar yarinyar dubi Inda ta jeme ta rame kwanakin nan

"hmmm Ke mariya mtsaln ki kenan ai ke"""""" baki San yadda ake cinye yaro da siyasa ba ne wai?"

"Ena wannan malamin su na islmiya, mal mamman ko?."

Eh mai shi kuma zai min shafa

Yawwa ki kira sa yazu da yamma

Ni zan Fada miki abunda zkice in yazo

"Ai ni da kin bi shawara ta tun farko wallhy da sai dai faryal ta ga ba kamil gidan nan ""* amma badai tasan"

mena ke ciki ba

Ay kam shfaa kin ga da hakan nayi baza ta na kokarin barazanar Fada ma uban tan ba ai

.......

Hijabi ta saka futchia pink har kasa wanda ya mata kywu duk ma rama ya fara bayyana a fuskan ta

Rusunawa tayi ta gaida mallam mamman dake zaunee a farfajiyan bishiyoyin dake gidan

"Nasiha ya Shiga mata sosai akan rayuwa,musammamn ma hakuri da kuma biyayya ma iyaye"

Nasha mamaki da haj tace min kina fito na fito da ita akan zabin data miki

Faryal nasan bazaki fahinci muhimmancin son da iyaye ke mana ba saboda wata rana zasu hana mu

"abunda Mike matukar so ,kila ma su sauya mana da wanda ran mu baya so"

"Amma kisani fa,uwa ita kadai CE wanda Allah ya kwatanta soyarrta da nasa,"

"akan mu,"

yazo mana a bakin manyan malamaii Allah yana CEwa yana son bawan sa ninki 70 fiye da yadda

mahaifiyrsa take son sa

".sannan cikin kashi uku,a mutanen da Allah baya karban komai daga cikin aikin ladan su a duniya da wani"

"bautan su,na farkon su shine mutumin da ya juya bya wa iyaye"" ya turje musu"",ya kyalesu,"

"Ga hadisai nan kala kala,duk munyi dake anan faryal,Inda wani mutum ya tambayi manzon Allah"

"saw,wani mutum yafi dacewa da cancanta ka kywta ta masa, sanda Manzon (swA)mu ya kira uwa sau uku kafin yace uba,hakan kinga na nuna miki muhimmancin bin umarnin mahaifiya kenan"

.

"Abu na karshe da zan gaya miki visa ruwaya kala kala,fushin uwa musiba ne a rayuwar mu koda mune da"

"gaskiya,muddin gaskiyar ki ba akan wani abun da zai saba ma dokokin Allah bane toh mafi alkhairi shine kiyi hakuri ki amince da bukatar mahaifiya ko ya yake"

"Kar ki manta,hakuri anayin sa ne

12 / 22