Author : Maman Fareesa Category : Romance
da cewa keeeeee!oya muje ki karbi hukuncin laifinki...marairaice masa tafara,amma yyi gaba had'e da yima ta banxa adoletabisa...
Tana tafe tana kallon su yah Usman da Fatima sai Habib da Rukayya suna mgn da alamadai suna son junansu,tsaki tayi tace afili oh dg ni sai yaseer kebamu dace wadanda zamu auraba.
"Wata zuciyar tace ai Habiba tafiku hkri da kawaici ga shiru shiru,sannan matsalarta wankan tarwad'ace ba faraba ,shikuma yah yaseer yafison mace fara da wannan tunanin ta yi sallama abed room din yah Yusuf..
WAIWAYE.
baffa habu kuwa yana ajiye ....
share
📚📚mmn fareesa ce✍🏻✍🏻
AWESOME WRITER'S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA !
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
(bansan ita bace)
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
NOT EDITED
🅿39&40
Baffa habu kuwa yana ajiye nah nah yakoma gd yafadawa inna delu yadda yyi tace suyi shiru abunsu...
Kwana2 da faruwar hakan ,baba atine taji shiru bbu labarin auren nah nah dame gari ,kuma tasami labarin abinda yafaru".
Dan haka ta nufi gdn baffa habu da niyar taje ta dawo da ita gd.
"Bayan tayi sallama tasami inna delu na surfe suka gaisa", yyinda baffa dke cikin daki gabansa ke mugun fad'uwa"
Muryar baba atine yaji tana cewa ,yayan na ciki?"ina nah nah ne?"
Wuf yafito had'e da karb'e zancen da cewa yo wacce nahnah ?"bacin tun jiya tacemun zata gd ,kina nufin batajeba?"
Cikin mamaki da rashin fahimta baba atine tace hmmmm dan ALLAH kufahimtar dani wlh bangane ba kada kucemun bakusan inda takeba....delu ta karbe da cewa dallah kada kiraina mana hankali "yaya y'ar nagunki kice bata nan!
Kuka baba atine tafashe dashi tace wato bacin auren dolen dakake shirin yi mata ,shine kuka batar da ita ko me?"
"Wai yaya kai wanne irin mutum ne?"
Kaci amanar zumunci kuma insha ALLAH zakaga sakamako"
Ace y'ar kaninka Ku sanwaltar masa da ita bacin bagunka yabartaba"aguna yabarta sbd son zuciya ka kwaceta dg guna to bara kaji...
Afusace baffa habu yakatseta da cewa keeeeeee ! Atineki kiyayeni wlh"
Bansan inda ta tafi ba ,can kutashafa kokuma nace ketasha fa,inaso yanxun kibarmun gd tunda bakida mutunci.... Cikin kuka atine tace bbu damuwa zantafi ,saidai inaso kasani d'an hakkin da ka raina shike tsone maka ido...
Inaji ajikina sai nah nah tadawo insha ALLAH tazama abar kwatance kuma ina zargin dasaka hannunka ta bata..
"Yanxun in mlm yadawo kace masa me?"
"Afusace yace nace masa uwarki?"
Murmushin takaici tayi kafin tayi mgn Maimuna (kishiyar delu tayi sallama dan sadda abun yafaru tana k'auye gun suna)
Delu kuwa yatsina fuska tayi dan tana kishin Maimuna"acikin su atinece kawai ta amsa sallamar..
Maimuna tace lfy atine kike kuka?"
Tsaki baffa d delu sukayi atare..yyinda atine cikin kuka take sanar da ita abinda yafaru...
Salati kawai take yi tana mamakin halin mijin nata...afusace delu ta kalli baffa tace dan ALLAH mlm ni kakoresu ko sumin shiru...bata rufe bakiba atine tace hmmmm basai yakoremuba nizan fita ita kuma gdn mijintane...
Amma inaso kisani namiji duk yadda kike da shi baida tabbas kibi sannu wannan hura hancin banaki bne,kaikuma kaje kaida ALLAH inajiye maka tsoron haduwarka da Mlm wlh...bata jira amsarsuba dg shi har delun ta fice dg gidan tana hawaye...
Maimuna bata sake cemusu uffanba tabude dakinta ta shige tanajiyosu suna zaginta itada atine,amma bata kulasuba.,,,,
Haka atine ta koma cikin k'unci da damuwa agd tana adduar ALLAH yasa nahnah bagurbatacciyar hanya ta biba..
Burinta mlm da kuluwa sudawo gd"
********
Tanayin sallama tasami yah Yusuf kishingid'e kan 3seeter yana waya sai murmushi yake Wanda yafito masa da kyawunsa .
Sarai yaji sallamar ta sai yyi mata banxa"
Ita kuma tana tsaye bakin k'ofar tak'i karasowa ,tunda bai amsaba.
Sauraronsa take dan tagane da mace yake wayar...sai wani kwantar da murya yake qasa qasa yana mgn.
Wani haushi taji Wanda batasan daliliba ,kwalla taji a idonta tana tausayin kanta ,wani gefen na xuciyarta nasanar da ita ko ya aureki keda banxa duk daya kuke agunsa tunda da wacce yake so ..
Tunawa tayi da mukhtar saurayinta dake mugun sonta"lumshe ido tayi tana mugun jin haushin yah Yusuf kuma tasha alwashin tambayar mama wanne sharrune zatamai ?
Kodan kada ta auresa ta yarda zatayi hakan....muryarsa taji yana cewa baby bye zankiraki latter..
Yatsina fuska tayi ta bankomasa harara,cikin rashin SAA suka hada ido da ita. "
"Wayyo jitayi hangar cikinta ta kad'a"
Ta shi yyi tsaye yace ZUBAIDAAAAAAA!
Nikike harara?"
Atsorace tace ah ah dan ALLAH kayi hkuri kada kai nakeba...doguwar tsuka yaja yace hmmm wlh inna kamaki zakiji jiki ,oya ni dallah kibiyoni kina fama da wasu shanyayyun idanuwa naki mitts...yyi tsaki.
Bed room suka nufa yabude ward rope yafito da tulin kayan wankinsa sunfi kala 12harda su suit da jeans yace ta wanke nanda awa daya intagama ta wanke toilet d'in da tayis d'in bango..
Kamar tasaki ihu sbd bakin ciki da bacin rai ayau ta tabbatar yah Yusuf mugune na karshe kuma baya k'aunarta ko kad'an.
Jiki bbu kwari ta kwashi kayan ta nufi toilet.
Shikuwa yayi kwanciyarsa kan bed ya lumshe ido..
A cikin toilet kuwa tana wanki tana tsinemasa yafi dubu bbu adadi tana mugun jin tsanarsa da haushinsa,said hawayen bakin ciki take ga wahalar wanki .
Da k'yar ta idar da abinda yasata dan takai2 hours aciki sadda ta fito anata kiran magrib..
Fuska bbu walwala ta iso gefensa yana shirin tashi yayo alwallah tace yaya nagama!
Harara yagalla mata yace ainasani basai kin fadaba ,kije kiyi sallah kidawo kisake karban hukunci sbd nakamaki kina hararata..
Ihu da kuka tasaka Wanda bata tab'ayi agabansaba da shure shure....lumshe ido yyi yana kallonta ganin yadda take abu tamkar wata yarinyar karama"
Ahankali yace ko kimun shiru ko na dakeki da belt kina jina?"
Cikin kuka tace dan ALLAH yaya kayi hkuri nagaji ne wlh bazan sakeba...juyawa yyi yace kisake mana ,kibaccemun da gani...da gudu ta fice ta na nishi.
Shikuwa girgiza kai yyi yawuce toilet abinsa..
***** ****** *****
Yah Suleiman kuwa suna fita dg parlourn yacika ta yanajin haushinta yanufi parlourn Ummi yyinda iftihal kebiye dashi...
Zama yyi ransa adagule agefensa yajita kawai ta aza kanta akafad'arsa had'e da rike mata hannu guda tana wasa dashi Lamar yarinya....
Wani yarrrrrrrr!yaji da kasala ajikinsa amma bbu yadda zaiyi tunda baa hayyacinta takeba .
Murya qasa qasa yace oh baby kiyi mgn pls kinji ko anfasa wannan auren kinji?"
Itadai kallonsa take amma batayi mgn ba ,hannunsa dake cikin nata yakwace had'e da Janata hanci yace hmmm insha ALLAH kinkusa warkewa kona huta da aurnki da akeson azamun..
Amamakinsa sai yaga tasa hannunta taja masa hanci harda sajen fuskarsa ,besan sadda yyi murmushi ba dan Sak yadda angel d'in sa kemasa in suna wasa tayi masa..
By surprise yaga tayi murmushin itama yadda taga yyi ..wani fad'uwar gaba yaji ganin hakoranta da wushiryarta irin na iftinsa ne.
Wata zuciyar tace hmmm kabi ahankali ,gixone kawai dan itace aranka ,amma basa wani kama....hannunsa data rike had'e da azasa saman goshinta yadawo da shi hayyacinsa.
Kalonta yyi ,"ahankali yace sannu kin kusa warkewa ai Dr zaizo yamiki dressing gun,dan yafahimci gurin raunin kemata zafi...
Murdo k'ofar akayi ,Ummi ce tashigo had'e da samun guri ta zauna .
Shikuwa yah Suleiman saikok'arin zameta yake daga jikinsa amma taki yarda saima kokarin hawaye takeyi...
"Ahankali Ummi ta ce kayi hkuri banana kaji?kayiwa abbunka biyayya bazaka taba tab'ewaba duniya da lahira insha ALLAH.
Auren nan kadaukesa amatsayin kaddara dakuma jahadi ,ko yanxun kaga yadda take makale dakai bacin kuba maharraman juna bane auren shine maslaha agareku har ALLAH yasa tasamu lfy.
Sannan inaso kabawa makiyanka kunya gun yima abbunka biyayya tunda anamaka wani zato mummuna akanta kuma raina yabaci matuk'a..
Yah Suleiman yyi yakatseta da cewa insha ALLAH Ummi zanyi biyayya ga abbu sannan zankarbi rayuwa aduk yadda tazomun.
Sannan wannan matar kibarta Ummi kada kibiyemata dan batada hankali,amma duk ranar data kaini bango wlh zatayi nadamar dabata tabayiba arayuwarta.
Ummi tace bbu komai ALLAH yyimaka albarka yakaremun kai aduk inda kake ,kuma insha ALLAH iftihal zata bayyana mudai cigaba da addua.
" cikin jin dad'in addu ar ta yace to Ummi bara natafi masjeed "
Mike wa yyi tsaye ...tuni y'ar tawa itama ta mik'e... Lolx,ahankali yace dan ALLAH Ummi ki riketa natafi masjid, gsky kada narasa jam'i!
"Tasowa Ummi ta yi Yakama hannunta,tuni tafara turjewa tana hawaye,shikuwa gogan sai aikomata da harara take yi,hanyar fita yyi yana cewa dan ALLAH Ummi kuyi mata wanka awanke mata gashinta sbd tsami take wlh..
Girgiza kai Ummi ta yi tace hmmm banana kenan itada akama dinki aka aiba ,a wankesaba ,adai mata wankan da dubara.
Bece komai ba yafita.
Ita kuwa sai da Ummi takira Fatima da Habiba suka tayata rarrashinta ,sannan tadena botsarewa.
Yah sulaiman be shigo gdn ba sai da akayi isha'i....
Part din sa yanufa ...
Share..
📚📚mmn fareesa ce✍🏻✍🏻
AWESOME WRITER'S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA !
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
(bansan ita bace)
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story &written by mmn fareesa
🅿41&42
Part dinsa yanufa yaje yawatso ruwa bayan yagama shirinsa yasha coffee ya kunna TV yana kallon news.
Befi minti 5 ba da fara kallon ...aka murdo k'ofar had'e da yin sallama. "
d'agowa yyi yaga fatimace had'e da iftihal ta rik'e mata hannu....kicin kicin d fuska yyi had'e da tashi tsaye yasan tana iya hawa jikinsa.
Harara yabankowa Fatima atsawace yace meyasa kika kamun ita adaki?"
Cikin inda inda tace dan ALLAH yaya kayi hkuri wlh tun dazu ta keta hawaye sai waige waige take kota ganka,shine byn anmata dubara tayi wanka Ummi ta ce nakata ,saika maido ta ta kwanta....
Tsaki yyi ya harari iftihal d'in had'e da cewa kumuje can!
Ita dai sai rarraba ido take tana son zuwa gunsa gashi yatsare gd,ganin yanufi k'ofar fita yasaka Fatima Jan hannunta suka bi bayansa...
Part din ummi suka nufa,samu yyi ba kowa a parlourn.
Bayan yazauna ,yyinda suke tsaye ,yace taci abinci da maganinta?"
Fatima ta ce eh taci"
Yace ok mikomin ledar maganin!bbu musu ta je ta dakko saman frige d'in da ke parlour, yyinda iftihal tayi zaune kan carpet tana hawaye...
Bayan tabasa yafito da maganin bacci yazuba alemo yazo gab da ita yasaka mata abaki....turewa tayi tana kallon sa ido cikin ido ....hararar ta yyi had'e da tura mata robar lemon abaki ..
"badan tasoba tasha ,Ta's sannan yatashi had'e da cewa Fatima dke zaune kikaita dakinku ta kwanta gobe Dr jabeer da wuri zaizo yaduba ta.
Bbu musu ta ce to had'e da Jan hannunta amma sai ta turje ....wata tsawa yyimata yana harararta har Fatima sai da ta tsorata da tsawar."
"Ita kuwa bewarv ALLAH hawaye kawai take yi tabi fatimar" suka nufi can part din su na mata.
Suna fita yyi ajiyar zuciya afili yace gsky anhadani da aiki dan wannan kwailar yarinyar tacika takura wlh...mitts yaja tsaki had'e da ficewa dg parlourn ...
********
Abbane zaune a bed room d'in sa yana tunanin rashin kyautawar zulai ga abbu dan koshi bazai iya yimasa rashin kunyaba...
Bbu zato kawai yaganta kamar anjehota sai huci take kamar kububuwa."
Afusa yace ke lfy?" zaki shigomun daki bbu ko sallama "
Tana huci tace kaikasanta"
Kabani mamaki wlh Kiri kiri ka mareni agaban yara da waccan muguwar matar taje ta ji dad'in yimun dariya da yadamun habaici ko?"
Tsaki abba yyi yace eh namareki zulai kiyi abinda kika gadama ,Yayana nefa! Aiko dan ni kin raga masa ga jifar d'ansu da kikayita yo mugun kalami,inda kece aka ma hakan zakiji dadi?"
Cikin jin haushin begoyi bayantaba tace oho nidai dg yau kada ka koma yimun haka gaban yara wlh!
da mamaki yace inna koma fa?"
Tace rayuka su baci dan bazan d'aukaba.
Besake mata mgn ba saima yashige toilet abinsa,yabarta tana ta kumfar baki.
Ita fita tayi ,aranta tace dole nacanza shiri sbd naga kaima kanason muzantani kadaina goyon bayana da Wannan tunanin ta iso parlourn ta tasamu zubaida kwance kan 2seeter.
Zama tayi tace ke lfy ?"
Zubaida tace lfy lau kaina kemun ciwo(taboyene gudun kada ta ce yanxun zata Sata tayiwa yah Yusuf d'in wani sharrin)
Zama tayi tace dg gobe Usman zaigane bashida wayo dan har nagama shirya irin makirkincin dazan masa yadda ko iyayan nasu dke zaman kasar waje zasuji tsanarsa...
Dan insuna takamar kud'i garesu dan y'ar su ta bata subar gari suga masu kudi ko?"
To insun dawo zasu samu shima Usman d'in yalalace...Rukayya dke shigowa taji kalaman mm zulai salati tayi kuma afili..
Tsaki mm zulai ta yi tace wlh ko ki fita kona tsinemiki yanxun !kaf a y'ayana kece zakka mitts...
Cikin mamaki had'e da nemama mata shiriya tabar parlourn.
Itadai zubaida tsabar gajiya yasa ko maganar basosai takeyiba .
Suna nan saiga yaseer yashigo aka cigaba da magana da shi...said a zai fita mm zulai ta ce gab da asuba zankamaka yarinyar saika kaita dakinsa kadai gane yadda komai zai tafi ko?"
Yaseer yace eh amma to ita abidar ba gd take tafiya ba?"
Mm zulai ta ce eh ,amma yau nace ta kwana sbd wannan plane d'in kuma nace mata ko antambayeta tace eh shine yace tazo nan girin su kwana...
Yaseer yace amma ta amince bbu musu ko?"
Mm zulai ta ce yotaki yarda ai dg ranar zan sallameta dg aiki na nemi wata,tunda ladidima korarta nayi ,gudun kada wata rana ta tonamun asiri tafadi cewa dasaka hannuna iftihal ta bata.....
Yaseer yace eh gsky ne"
Tace hakene"
Agogo yakalla yace to ni saida safenku ,nan sukayi sallama ya wuce dakinsa..
Saidai me kwata kwata yakasa bacci ,kyakkyawar fuskarta kawai yake gani inyarufe idonsa..
Sai juyi yake afili yace dole insan yadda zaayi na huta da wannan babyn duk da bantaba aikata zina ba ,amma gsky xuciyata ta kwadaitu da ita..
Da wannan tunanin had'e d juye juyen yyi bacci.
Washe gari tun karfe ,5:12am yaseer yatashi yanata zagaye yaga duka samarin sun fita masjeed sai yaje yataho da yarinyar yadda dasun dawo zasu ganta ace Usman ne yabata ta, dg nan k'ila abbu yace dole ya aureta tunda yabatata ...
Dan tunda yarasa Fatima to shima yarasa.
Yana nan ta window ysna ganin fitarsu hardasu abbu da Abba da sauri ya fito...yana fitowa yaga mm zulai da yarinyar sun nufo part d'in.
Tsayawa yyi suka karaso ,cikin rad'a mm zulai ta ce to kuje ciki gata nan ,nasanar da ita komai!
Yaseer yace ok muje ko"bbu musu ta bisa mm zulai ta juya ta tafi...
Acikin corridor d'in ssshen suka Shiva kasan cewar daka Shiga zakaga kofofin dakunansu Jere ,dan haka suk a nufi dakin yaseer da ita...
Zama yyi yace mata yanxun zankaiki dakinsa ki kwanta kan gadonsa kicire dan kwali kijiri mu duk abinda aka tambayeki kifadi yadda mama ta zayyanemiki..
Yah Yusuf daya yanxun yadawo daukar touch light sbd kafin akabbara sallah zaiyi karatun kur ani,yaji mgn sama sama da kus kus har zai wuce yadawo jin ak'ofar dakin yaseer ne .
Ahankali ya matsa jikin k'ofar yakashe kunnansa...
Share.
📚📚mmn fareesa ce✍🏻✍🏻
AWESOME WRITER'S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
(bansan ita bace)
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
Wannan page din nakine HASIK kiyi yadda kikeso dashi ina mugun jidake😍😍
🅿43&44
"Ahankali ya matsa jikin k'ofar yakashe kunnansa yana sauraran sautin maganarsu".
Cikin mamakin yaseer had'e da jin tsanar sa yyi yunkurin bude k'ofar dan azatonsa yaseer d'in ne yakawo wata mace adakinsa...
Amma jin yaseer na cewa kinutsu bbu komai yanxun bbu jimawa zasu dawo dg masjeed.
Muje inkaiki dakin Usman d'in.... Zaro ido yah Yusuf yyi atake yatuna kalaman mm zulai akan Usman d'in ,sadda yalabe yajisu"
Azuciyarsa yace nasan maganinku,,,,sai kawai yyi saurin matsawa dg jikin k'ofar jin sunnufo k'ofar... Hannunsa yarumgume a kirji yana passing k'ofar ."
Murdowa sukayi yaseer ne agaba"saidai yana d'ago kansa yyi 4eyes da yah Yusuf yana masa kallon tuhuma...
Wayyo tashin hankali "da za'a auna jinin yaseer alokacin da yyi mugun hawa sbd tsoro da fargabar asirinsu yatonu..
" abida kuwa kasa motsi tayi "bbu abinda take sai danasani,,,,wadda akace k'eyace....
Cikin tsabar yaudara da bugun cikin mutum Yusuf yyi gyaran murya yace oh subhanallahi!
dama abinda kake aikatawa kenan?kai fasikine?" aiko zansanar da kowa agdan nan ,kodan kada a aura maka Habiba wlh tir da mugun halink....da sauri yaseer yakatsesa da cewa wlh !wlh!wlh !
Ban aikata abinda kake zargimmu dashiba ko abida?"
"cikin tsoro tace eh"
Tsaki yyi yace to tunda bakinku daya da ita bbu damuwa zanje yanxun insanardasu dan nasan angama sallah....muryar abida yaji tana cewa nidai Dan ALLAH zan fadi gaskiya kada kafad'a....yatsinafuska yyi had'e da watso mata mugun kallo yace aikin banxa ke har wata gsky ce dake.,,,
Yaseer jikinsa sai rawa yake dan beson abata masa suna kuma baidamu asirin mm zulai yatonuba ,dan haka yace pls yaya kasauraremu zamu fadi gaskiya....
Yusuf azuciyar sa yace anxo gurin."
Kallonsu yyi yace kubiyoni..bbu musu suka bisa .
A part din Ummi suka nufa ,byn Yusuf yashiga suka bi bayansa, Ummi na zaune kan carpet tana lazimi..yyinda abbu ke kan 2seeter yana karatun alkur'ani mai girma.,,,,
Da tambayoyi fal afuskar abbu ya amsa sallamar su bayan yakai aya..
Yusuf ne yafara cewa abbu ina kwana?"
Abbu yace lfy lau lfy dai ko?"naganku haka tun gari be ida haskeba?"
Yusuf yakalli abida had'e da cewa ke kimana bayani... Yyinda Ummi tayi musu kuri tana sauraron ta ji mesuke tafe dashi.dan tunda tagansu gabanta ke fad'uwa..
Bbu boye boye abida ta zayyane musu komai akan abinda mm zulai ta sakata tayi dan tasan kobata fad'aba korarta z'a ayi ga suna mata kallon y'ar iska.
Salati kawai abbu keyi yana mamakin mugun Hali irin na zulai ,sainan yana jin tausayin Usman dabecimata komai ba tabisa da sharri haka .
Cikin bacin rai abbu yace wa yusuk jeka kiramun abdullahi da matarsa...nan yah Yusuf