Author : Maman Fareesa Category : Romance
yafita dan kiransu...
Abbu yajiyo yakalli abida yace lallai dan Adam kenan dg yau zakibar gdn nan kin gama zamansa.,,
Ummi kuwa tazo mak'ura dan jitake yau bbu abinda zai hana tadaki mm zulai ko ita, ko ita..
Yah Yusuf kuwa yana sanardasu sak'on yafito.
"Mm zulai kuwa ta tsorata da jin kiransu ake da jijjifin nan" jiki bbu kwari tabi Abba dan jin kiran me ake musu..
Suna shiga taga yaseer da abida kai duke dg nan cikinta yafara juyawa had'e da jin gabanta na dukan Tara Tara.. Lolx
Ko gaisawa basuyiba abbu yakalli abida yace ke mamaita abinda kika fada"bbu inda inda ta sanar da su komai....tun kafin ta ida mm zulai ta fara borin kunya wai sharri ne zaa mata..
Sbd bacin rai da bak'in ciki Abba bece komai ba yafita...mm zulai na kokarin binsa Ummi ta cafkota had'e da makata ga bango tahau nusarta...
Gaba daya abbu yasha mamakin Ummi ganin yadda take dukan mm zulai sai ihu take ,ya yarda da akace mai hkri bai iya fushiba...
afusace yacewa su yaseer sufita itakuma abida ta tafi gd sun sallameta...
Abbu naganin sun fita yazauna kan kujera yana kallon su be rababa dukda dai anfi jibgar mm zulai duk da itama tanad'an kai duka...
Saidai Ummi ta jigata mm zulai sannan tabarta ,yyinda abbu yadauke kansa dg kallon su har mm zulai ta fita..
Zama Ummi ta yi tana nishi ,abbu yagirgiza kai yace banso kika daketaba ,amma bazancemata komai ba saidai duk radda ta sake makamancin hkn zanbasu mamaki wlh..
Ummi tace gsky alh mubar musu gdn ,nagaji da mugun halin matar nan da ya'yanta ,sannan gsky kajanye auren Habiba da yaseer gsky,yanxun in su mommy sun dawo suna sami irin Sharrin da aka soma usman zasuji dadi?dame zasuji ?"batan y'ar su ko kazafin da akama Usman?
Murmushiin takaici abbu yyi yace ah ah gsky bazan janyeba kisaka ido munata addua ,sannan maganar brain gd bata tasoba dan bata isa ba sbd ita muraba zumunci wlh dan insha ALLAH Ibrahim yakusa dawowa befi 5weeks ba sbd karatun su Muhammad Aida sunkai 1month da dawowa ma,sannan kuma bazan bari suji maganarba dan bbu dadi..
Kuma wlh koda sunci galabar yimasa sharrin nibazan yardaba sbd Usman yaron kirkine...Ummi ta katsesa da cewa hkne wlh ALLAH yashiryeta inxata shiryu ,sukuma ALLAH yamaidosu lfy ,,
"Yace ameen"
"Ahankali abbu yace dama inada niyar yimiki mgn inna gama karatu ,sai wadandan suka shigo"
Ummi tace to inajinka ALLAH yasa alkhairi ne,,,
Murmushi yyi yace shine insha ALLAH "
Dama maganar auren Dana ce zanyi wa Suleiman ne da wannan yarinyar"shine yau amasjeed nike ma liman maganar had'e da Neman shawararsa ...shine yamun tuni akan gsky akwai kuskure idan na aurarda yarinyar bbu San in iyayanta ,dadai da sanunsune to bbu damuwa, shine na tambayi Suleiman yanxun dazamu shigo gd a ina yatsinceta?"
Shine yacemun dg garin da yatsinceta zuwa nan awa4,gashi bata hayya cinta bara muje aduba iyayanta.
Amma nace masa yabari konan da zuwa sati 2ko 3sannan ta warware sosai koba da itaba sai muje garin da hotanta abinciki iyayanta..
Ummi tace wannan gsky ne alh nima nayi tunanin hakan "to amma yanxun anfasa auren ko?"
Abbu yace eh amma kuma tunda narigada nayi niyar ya aureta ,bayan anga iyayenta indai sunbasa bbu damuwa zai aureta dan hakanan naji kaunar yarinyar tamkar y'a ta...
Ummi tace wlh ko ni to ALLAH dai yabata lfy "yace ameen....kafin Ummi ta yi mgn yah Suleiman yashigo parlourn yaduka har kasa yagaidasu..
Bayan sun amsa ,nan abbu kesanar dashi anfasa auren ......murmushi yyi har fararen hakoransa suka fito.
" Wanda Rabon dayi irinsa tun kafin iftinsa ta bata"ahankali yace hkne abbu ai dama tun sadda kayanke hukuncin nafara maka mgn kace kagama yanke hukunci wlh dama abinda zantunatar dakai kenan saikaki saurarata..
Abbu yace hkne yanxun dai naga kana murmushi akan ance anfasa auren ko?"
To ba'a fasaba"insha ALLAH ,inharmun samu iyayanta zan nema maka auranta...
"Ahankali yace to abbu had'e da tashi dan Baron parlourn adaidai nan kuma, Fatima ta fito rik'e da hannun iftihal."
Dukawa tayi tagaidasu abbu da yah Suleiman ,yyinda iftihal ke tsaye tana raba ido.
Yah Suleiman yasaci kallonta ...suka hada ido lumshe idonsa yyi dan saiyaga tamasa bala'in kama da angel dinsa..
Gurinsa ta matsa .... da sauri yanufi k'ofar dan fita tuni tabi bayansa shikuwa besan tabiyosaba..
Ummi kuwa girgiza kai kawai take yi ta kalli Fatima had'e da cewa muje kitchen ahada break fast! Amma yarinyar nan tayi brush?"
Fatima ta ce eh wlh tayi da kanta bansan Wanda ya koyar da ita ba...abbu dke shirin barin parlourn yace eh gsky yarinyar Nada saurin ruk'e abu..
************
Abba kuwa koda yafita sashensa ya wuce rai bbu dadi dan mm zulai ta kasa Bango...yana nan zaune ta shigo kamar an jehota da bakinta afashe tana matsar ido..
Tsaki Abba yyi yace wlh naso tamiki Wanda kika kasa tashi ,bakida tausayi baikda mutunci ,ace wai yan uwana su kikebi da sharri ....cikin jin haushin kalamansa tace wato bazaka dauki matakiba ko?"akan dukan datamun"
Hararar ta yyi had'e da Jan doguwar tsuka yace wlh daba dan yaranmu ba wlh da tuni zamana dke yakare amma wlh ko baran badad'e saina kara aure ..
Sbd zama dake ke daya matsalace...zaro ido tayi had'e da cewa mekace?"
"Yace abinda kunnanki yaji" bejira amsartaba yabar dakin da nufin yaje yabawa abbu hkri.
Ita kuwa yabarta da baki fashe tanata masifarta ,had'e da jiran yaseer yashigo tazagesa Ta's tunda yana gani abida ta tona mata asiri yakyale..
Haka kuwa akayi yaje yabawa abbu hkri da sanardashi zai kara aure indai yasamu wacce tamasa,abbu kuwa yagoya masa baya sosai ,sannan suka kira yaseer suka masa Ta's sannan aka kira Yusuf sukace yyi shiru kada yabari Usman d'in yaji maganar yace to ....
Yah Suleiman kuwa tafiya yake besan tana bi.....
Share
๐๐mmn fareesa ce โ๐ปโ๐ป
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
๐
ฟ45&46
NOT EDITED
Yah Suleiman kuwa tafiya yake besan tana biye dashiba har suka zo daf da d'akinsa "kamar ance yajuyo yaganta bayansa tana raba ido..
Tausayinta yaji yasan dashi kadai ta saba" ahankali tace baby xo nan !
Yafad'a had'e da mik'o mata hannu yana nuna mata ta biyosa .....bbu musu tamkar taji ta nufosa ,suka shiga atare .
Zama yyi kan kujera yanuna mata gefensa alamar ta zauna ....kin zama tayi tana kokarin hawa jikinsa da sauri yace stop it...
Hannunsa yasa yazaunar da ita kan carpet had'e da murde mata kunne sosai....kamar yana rad'a yace kidemun haka kina son had'a jikina da naki...mutsu mutsu ta fara had'e da aza hannunta cikin nasa tanason yasake kunnan..wani irin yanayi yaji jin hannunsa anata da sauri yacika mata kunne.,,,
Alama yyita Mata akan ta dena masa halam"yyinda tamasa kuri da ido tana kallon sa tamkar tasonsa.
Hura mata iskar bakinsa yyi ..hakan yasa ta fara kyafta idanunta ta na turo baki...besan sadda yasaki wani lallausan murmushi ba ganin yadda tayi masa irin yadda iftinsa ke masa in yatsokaneta..
Itama murmushin tayi masa..adedenan wayarsa tayi ringing dubawa yyi yaga Dr jabeer ne.
Byn sun gaisa Dr yace gani ak'ofar gidanku.. Cpt yace ok kashigo kacewa mai gadi yakawoka part dina..
Suna gama wayar sai yatsintsi kansa da kinson Dr jabeer yaganta bbu hijab ko d'an kwali,tashi yyi had'e da Jan hannunta yace oya muje kisaka hijab Dr yazo yaduba ki ko?"
Itadai kallonsa take har suka fito suka nufi part d'in Ummi,nan yacewa Fatima ta kamata hijab bbu musu ta kawo akasaka mata..
Wow masha ALLAH ifti tayi kyau sosai shikansa gogan kuri da ido yyimata har sai da Ummi ta ce kuje mana inya dubata kudawo tayi break fast.
"Ahankali yace to Ummi " amma azuciyarsa da tambayoyi fal dan tambayar kansa yake meyasa yake ganin yarinyar nan namasa kama da Angel dinsa?"
Jiki bbu kwari Yakama hannunta sukaje sukasami har Dr jabeer yashigo yazauna jiransu...byn sun sake gaisawa Dr yace masha ALLAH cpt gsky naga tanasamun kulawa sosai to acigaba dan ALLAH. "
Yah Suleiman yace bbu komai zaa cigaba.
Nan Dr yafara aikinsa yyinda iftihal sai botsare botsare takeyi saidai da yah Suleiman yakalleta take nutsuwa..
Bayan yagama dubata"cikin xolaya Dr yace oh cpt naga patient d'in taka tana nutsuwa daka tsawatar mata koda idone ,ma'ana inkakalleta..
Murmushin gefen baki yyi yace oh Dr har kasamana ido...dariya Dr yyi sukayi sallama ,shikuma yah Suleiman yajata dan suje suyi break fast..
**********
Mm zulai ce ta fito dg bed room d'in ta zuwa waiting parlour sbd taji muryar yaseer.
Tun kan ta ida k'arasowa take jifarsa da matsiyacin kallo...yyinda duk yasha jinin jikinsa .
Zama tayi kan 2seeter tana girgiza k'afa afusace tace yaseer kabani mmaki wlh amatsayina na uwar da haifeka kana gani kiri kiri atonamun asiri agabanka baza ka karyata "wato inma naji kunya Nita shafa ko?"
"Ahankali yace pls mm kiyi hkri yawuce ,kema kinsan karyarmu takare tunda yah Yusuf yakamamu yazanyi ne dan ALLAH?"
Afusace tace yazakayi d'in uwarka ,muna fiki to wlh bara kaji dg kai har Yusuf d'in zaku gane shayi ruwane WL....
Da sauri Rukayya ta katseta da cewa pls mama kidaina haka mana,yanxun keko abinda yafaru dazun besama iznah agareki dan ALLAH kidaina nufar kowa da sharri in mgn ta ta yi miki zafi kigafarceni..
Tashi mm zulai ta yi had'e da Jan doguwar tsuka tace dg yau in ina abu kika koma samun baki ban yafemikiba...kallon yaseer tayi tace shasha dakai dani kake zancen ta fada had'e da barin parlourn..
Rukayya dasuke break tayi murmushi mai ciwo hade da nema ma uwarta shiriya,yyinda zubaida na gefe ko uffan bataceba.,,,
BYN KWANA 2
Sannu ahankali cpt yafara sabawa da iftihal wacce ayanxun yake kira da baby,Dan dataji yace baby to tasan da ita yake da sauri zata je gunsa..
Cikin ikon ALLAH kuma duk ta warke ciwon dke bisa kanta da taimakon Dr jabeer..
Ayanxun haka har tasan dakin yah Suleiman koba a kaitaba tana zuwa da kanta taita kallonsa ko yabata sweet d biscuit taci amma dai bata mgn.
Gefe daya kuwa yaseer na nan yasaka idonsa akanta jira yake yasamu dama hakarsa ta cimma ruwa..
Zubaida kuwa yanxun bata Bari suna haduwa da yah Yusuf dataji muryarsa zata gudu ,kuma duk yana ankare da ita soyake yaga iya gudunta..
Sannan itama tana Neman hanyar dazata ma wannan marar hankalin yarinyar illa(haka su mm zulai ke kiran ifti) dan haka kawai take jin zafinta...
**** ***** *****
Abbas ne tafe yana hawayen bakin cikin b'atan masoyiyarsa nah nah dan dawowarsa kenan yasamu Hutu shine yana shigowa garin aka tsegwanta masa lamarin..
Be tsaya ko inaba sai gdn mlm Haruna bbu Neman iso yabanka kai ,hankali tashe"
Yana shiga yasamu baba atine zaune ta yi tagumi, Jidda tayi matashi da cinyarta ,duk tarame tayi baki,kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa..
Koda taga yanayin Abbas tasan yasamu lbrin batan nah nah ne..
Zama yyi kamar karamin Yaro ,yana kuka had'e da cewa dan ALLAH ina nahnarsa ta tafi?"bazai iya rayuwaba bbu ita..
Cikin kuka atine tace saidai muyita addua baffanta habu shine si
lar komai.
Amma kasan ai su mlm basa ganin ko?"
Abbas yace eh haka nayi yanxun ..........adedenan mlm da kuluwa suka yi sallama acikin gdn.
Da kayansu Niki nik'i ahannunsu,da gudu Jidda ta tashi...
Share
๐๐mmn fareesa ceโ๐ปโ๐ป
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story &written by mmn fareesa
Wannan page din nakine my lovely Fadeela dan Fulani nabaki shi hakak malak๐๐
NOT EDITED
๐
ฟ47&48
"Da gudu Jidda ta tashi ta fad'a jikinsa tana murnar dawowarsu gd lfy" yinda kuluwa ke kallon atine d Abbas ganin kamar akwai damuwa atare dasu".
Mlm hruna ma yalura da hakan"atine sai gabanta ke dukan sittin sittin sbd batasan shin mlm da kuluwa zasu fahimce taba...
Abbas cikin damuwa yagaisu mlm ya amsa da fara'a had'e da zama shida kuluwa kan tabarmar dke tsakar gidan ashimfide.
Byn sun zauna ,atine itama tahaidasu had'e da tambayar jikin kuluwa mlm yace ta warke sarai bbu damuwa mun godewa ALLAH daya bata lfy...
Fuskar mlm da mamaki yace atine!
Ina nah nah ?"
Tunda Muka shigo bangantaba "wlh tana raina yarinyar nan, amma aiyanxun nima nayi waya sai indunga mgn da kowa wani abirni yacemun nasiya yakoyamun yadda ake amfani da ita.....hawayen d atine keyi yasashi katse maganar"
da sauri yace subhanallahi atine meke fatuwa kke kuka?"
Kuluwa ta karbe da cewa gsky Mlm akwai wani abu daya faru marar kyau da bama nan ,dan tunda Muka shigo naga yanayinsu nasan bbu lfy"
Mlm yace atine dan ALLAH kiyi mgn!
cikin kuka tace yaya nah nah ta bata bamusan inda take ba tund... Azabure mlm yace atineeeeeeeee!kada kicemun y'ata tabata....Abbas yace eh wlh mlm da gskene...
Innalillahi wa inna ilaihir raju un kawai mlm ke maimaitawa"atsawace yace mekike har nah nah dkeda hankali tabata....atine tahau basa hkri had'e da sanar dashi komai daya faru dabasunan.....tun kan ta kai aya mlm ke kuka kamar Yaro.
Azuciyar sa kuwa tunawa yake da amanar da yadauka akan yarinyar nan lallai dole yahukunta baffa habu...
Itama innakuluwa kukan take yyinda Abbas yadaure yana rarrashinsu.
Tashi mlm yyi yakalli kuluwa yace yau nadawo yau kuma zankoma domin na nemota aduk inda take sbd amanar da na d'auka akanta...
Dg Abbas har atine mamakin kalaman mlm suke ,sundaiyi shirune dan suna ko baya haiyacinsa."
Kuluwa na hawaye ta e eh mlm kaje kanemo mana ita ALLAH natare da mai gsky inama fatan alkhairi had'e da adduar samun nassara akan abinda kake nema...
"" Abbas jiki bbu kwari yafita dg gidan had'e da yiwa mlm fatan dacewa,,,
Jidda kuwa kuka take ganin iyayenta nayi gashi mlm yaja jakar kayansa da,zai tafi da ita..
Yakallesu baki daya yace kuyi hkuri kuma kicigaba damun addua nasamu nassara sannan yanxun zanje gidan baffa naga masa mgn in har ba'a gantaba to wlh kotuce zata rabamu dashi !zan nuna masa kuransa gurin na ajiye yan uwantaka gefe..
Atine tace eh gsky kayimasa Ta's da muguwar matarsa delu"
Mlm yyimusu bankwana yana hawaye dan har cikin zuciyarsa yana junta tamkar Jidda y'ar sa.
Gidan baffa yaje bbu ko sallama ya kunno kansa aciki, delu dake tsaye tana shanyar kaya tace oh Ashe kundawo garin?
Doguwar tsuka mlm yyi had'e da cewa bansaniba ina habu mijinki take ne....baffa k'okarin fitowa dg toilet ya katse mlm da cewa yanxun Haruna ni kake kira da habu ko?"
Mlm yace eh baccin habu ko kanada wani sunan ne ?"
Baffa yace kuyimun rashin kunya lokacinkune !amma meke tafe dakai? "Delu ta karbe zancen da cewa ai gara ka tambayesa kaji yashigo mana gd bbu KO sallama sai masifa yake da kumfar baki....
Wani mugun kallon tsana mlm yyimata had'e da cewa ai dole kice haka tunda kunci amabata sbd son zuciya da kwadayi to bari kaji yanxun zanje na nemi y'ata aduk inda take, saidai inhar nadawo kotuce zata rabamu ....kekuma muna mata barikiji kurciyya zanmiki kibata batttttt agarin nan,yana fadin hakan yafice bejira amsar suba ......
Delu kuwa ta tsorata dan azatonta da gske yake, sai raba ido take tana tambayar baffa mlm zai iya mata kurciyya?
" baffa yace ah ah"
Shirudai tayi amma bata yardaba...
************
Yana fita motar zuwa binni yahau said a akayi tafiyar awa4 sannan mlm yasauka akd.
Gurin wani almajirinsa yasauka dkeda gd da matarsa 1suna zaune a unguwr kawo.
Cikin wani daki dke soro aka saukarda mlm bayan yakimtsa yahuta ,yasanar da ayuba dalilin zuwansa..
Ayuba yyi mamaki sosai dg baya yama fatan samun nassara had'e da bashi shawarar yaruk'a nuna pics nata yana tambaya gurare k'ila aganeta mlm kuwa yyi na'am da shawarar ayuba..
Washe gari tun karfe 10am mlm yafa fits Neman iftihal yanata tambayawa saidai me?
Kowa cayake bai gantaba tunsafe yake yawo har dare saidai in lokacin sallah yyi yaje yyi haka yadawo masaukin rai bbu Dadi amma yyi alkawari azuciyarsa in yyi sati ko 2ne zai tafi Kano ko adace tunda rannan ya tambayi atine ko zanbincika duka kauyen tace eh dan haka garuwa zaitabi ko k'ila adace.
Washe gari mlm d ayuba ne Suna gaisawa ,ayuba tace nikuwa mlm inada wata shawara da zanbaka k'ila inkabita atace aga y'ar taka...
Mlm yace to ina jinka mecece shawarar?"
Ayuba yace ina ...
Bana bukatar tanx ko๐๐ปโคsharhi kawai nake bukata in kunyi acigaba inbakuyiba kuji shiru..
Share
๐๐mmn fareesa ceโ๐ปโ๐ป
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story &written by mmn fareesa
NOT EDITED
๐
ฟ49&50
Ayuba yace ina ganin mukai photon ta agdn TV kawai k'ila adace "
Mlm yyi ajiyar zuciya had'e da cewa gsky naji dad'in shawarar nan
taka!muje ka kaini ko ?danni bansan gdn TV na garin nan
ba"ayuba yace bbu komai bara na fito da mashin sai muje inkaika ,kaima ka huta da yawo kana nuna photon ta..
Mlm yace to ngd sosae "nan ayuba yafito da mashin mlm yahau suka nufi gdn TV dke Kd..
**********
Yah Suleiman ne tsaye gaban mirror yana fesa body sprays yyi masifar kyau ammafa fuskarsa bbu annuri dan yau beyimafarki
n angel d'in sa ba ,kasancewar yasaba da yin mafarkinta ko wacce rana amma yau beyiba"
Yuni foam nasa nasojoji yasaka ,yana d'aura belt a k'ugunsa iftihal ta shigo da gudu ta fad'a jikinsa tana hawaye...
d'agota yyi dg jikin sa"cikin damuwa yace dame zanji ne pls