Author : Maman Fareesa Category : Romance
delu tace oh mlm Kodai mutuwa tayi?"arikice yace ina tunanin hakan....arude tace meye abinyi ?"
Waigawa yyi yace jeki rufe gdn tunda bbu kowa bbu musu taje ta rufe tadawo tasamesa yakaita dakinsa yarufe da buhu sai zare ido yake yace delu kirufamun asiri dan ALLAH tace lahhh bbu komai wlh bbu Wanda zaiji .
Gobe cikin dare kasata abaro ka kaita karshen gari can bakin titi ,maana kafitar d ita dg garin nan ..
Da safe sai auren dole...muce ta gudu sbd zaamata auren dole,,,cikin murna yace yauwa ngd sosae matata ALLAH yabarmu tare...tace ameen..
Haka kuwa akayi d asubar fari yaje yakaita ya yasar da ita ya nufo gd bebari aka gansaba...
da safe gurin 10am yah Suleiman ne tafe zaya gd sai gudu yake sbd bayaso azahar tayi masa ,saidai tundg nesa yaga kamar mace kwance gefen titi...har ya wuce kuma yadawo dan yaga ba irin macutan nan neba da ake hada baki dasu acuci mutumda su..
Parking yyi yafito....
Share..
๐๐mmn fareesa ceโ๐ปโ๐ป
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA !
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story &written by mmn fareesa
Dedicate to all my fans๐
๐
ฟ29&30
NOT EDITED
parking yyi yafito"ahankali yanufeta "saidai me?" Yana kallonta yaji wani mummunan fad'uwar gaba Wanda baisan dalilinsa.
Matsawa yyi gab da inda take kwance fuskarta na kallon Gabas"yakalleta yaga bbu alamar numfashi atare d ita kuma yasan ba mutuwa tayi ba dan da tafara warii"
Yatsina fuska yyi ganin bbu kowa mutane nata wucewa amota har yajuya ...wata zuciyar tace hmmm kataimaki me bukatar taimako !afili yace bansantaba!tunawa yyi da my angel dinsa ,shin in itace awannan halin ba'a taimaka mata aibazaiji dadiba..da azama had'e da karfin gwuiwa yabude gdn baya yatattare hannun rigarsa yazo ya sungumeta yasakata yakoma gdn gaba yaja motar."azuciyarsa yana tambayar kansa me yafaru d yarinyar nan?"ya'akayi taji rauni haka?"dg gani yarinyace gsky...wata zuciyar tace kakaita hospital kawai...
Hakafa yah Suleiman yyita sharar gudu cikin awa 2d Rabi suka iso Kd basu tsaya ko inaba sai hospital, bayan yyi parking yafito yashiga ciki bbu jimawa suka fito d nurse akayi emergency d iftihal yyinda yah Suleiman yawuce masjeed,bayan yadawo yyi zaman awa2amma shiru bbu Dr d'in da yafito
Ji yyi yagaji da jira tashi yyi yaje yyi sallar la'asar yadawo shiru...can saiga wata nurse zata wuce sai kallon kurullah takewa cpt Suleiman ,shikuwa yana ganin hakan yatamke fuska....cikin iyayi tace sannu ko!banza yyi d ita "ahankali tace kayi hkuri naga tunda aka shiga d patient d'in ka basu fi....wani mugun kallo yyi mata ."
Atake taji yamata kwarjini ...adede lokacin kuma Dr jabeer yafito duk yyi gumi d wasu doctors yakalli cpt Suleiman yace kasameni a office. "
Cpt Suleiman ya juya had'e da tashi cikin nutsuwa ya nufi office din Dr din yyinda nurses dinketa jin inama ace wannan gwarzon nmjin nasune..lolx
Bayan ya zauna Dr yacire glass din dke fuskarsa yace gsky akwai matsala babba da yarinyar nan!cpt yace wacce matsala kenan?"
Dr yace Kaine yayanta ko mijinta?"
Yatsina fuska yyi had'e da yin kicin kicin d rai yace meyasa kamun wannan tambayar ne?"Dr yace hmmm sbd dole sai su zasu sani ne...shiru yyi can yace ok ni yayantane yatsinci kansa da fadar hakan ...saidai kuma yaji haushin fadin hakan dayyi,Dr yace to gsky yarinyar nan dukane aka mata ba nawasaba akai!
Wanda sanadin hakan tayi loosing memory d'in ta...inna lillahi wa inna ilaihir raju un kawai cpt Suleiman ke maimaitawa ...cikin damuwa yace meye mafita Dr?"
Dr yace to agsky da wuya kuma bbu wuya"?yace kamarya?"Dr yace eh to indai yanxun ko wani lokaci kadan nan gaba taga Wanda tasani ko tashak'u dashi to zata dawo normal ta warke ...inkuma bbu Wanda tasani harta gansa to gsky sai tajima ta warke !amma zamu azata kan magani ina fatan kafahimta?"
Cpt yace eh to yanxun ciwon dke kanta fa?Dr yace munyimata dinki kuma insha ALLAH nanda 2days zai warke indai yasamu kula dukda naga fatarta mai kyauce zata yi saurin warkewa indai ana kula d ita sbd ciwon yanason kula dan yanxun itafa tamkar jinjira take sai abinda a ka nuna mata zatayi...cikin wani yanayi cpt yatashi tsaye yace bara naje gun cashier nabiya kud'i na wuce gd kafin ta farka,Dr yace ok ,,,,
Bayan yagama biyan makudan kudin da aka rubuta masa yawuce gd.
A parlour yasami ummy tana shirya diner dan lokacin 5ta gota...zama yyi yana gaida ita ,amsawa tayi had'e da cewa oh babana shiru sai yanxun tun karfe2:pm niketa dubar hanyarka amma shiru sai yanxun lfy dai ko?"
"Yace lfy lau wlh watace na taimaka....nan yasanar da ita komai game da ita harda loosing memory d'in datayi...cikin tausayi Ummi tace wayyo ALLAH amma natausaya mata komaiye dalilin hakan?" ALLAH masani"
Cpt yace eh anjima zan koma kihada abinci saina kai mata ko?"Ummi tace to amma dan ALLAH babana ka bits ahankali tunda ance kamar jinjira take nasanka d zafin zuciya "ALLAH shixai baka ladar tunda danshi kayi ,amma saika daure d'a duk nakowane in ALLAH yasa ta warke sai a sadata da iyayenta ko?"
Ta shi yyi yace to Ummi zankiyaye yafice dg parlour part d'in su yawuce yaje yyi wanka had'e da yin arwallah .
Bayan yafito yashirya cikin suit farare sai kamshi yake zabgawa yyi masifar kyau ,masjeed ya wuce bedawoba saida akayi isha'i
Gun Ummi yanufa yasamu ta had'a masa komai a basket,abbu na gefenta yana dinner, nan yagaida abbu,anan yake jajanta masa dan Ummi ta fada masa kuma yamasa nasiha akan yabi y'ar mutane ahankali banda hantara..
Fuska bbu walwala yadauki basket din yafice ....axuciyarsa yanajin haushin yarinyar sai wani cewa ake yabita ahankali shifa gsky bbu dole ...wata zuciyar tace kada kazobe ladarka !kayine dan ALLAH..
Ahaka ya iso asibitin straight office in Dr yanufa yasameshi zai fita, nan suka gaisa Dr yace oh shiru shiru baka dawoba sai yanxun amma acikin wannan lokacin zata farko insha ALLAH "cpt yace to ALLAH yasa.
Dr yace dama gd zani room8 ne room dinta na cire mata drip magunguna nanan bayan taci abinci tasha ,amma katabbatar kamata brush ,kuma tea ne zata fara shaaaa.sbd hanjin ya warware"
Cpt yadan yatsina fuska yace ok amma ni gsky bbu brush aguna Dr yace akwai a toilet sabo ma "yace ok yana niyar tafiya... Dr yace amma kai zaka kwana d ita ko ?" Cikin kosawa d maganarsa yace ah ah menene?"yace to ai gsky kasamu wacce zata kwana d ita da matsala abar patient ta kwana ita d'aya..
Wani haushi cpt Suleiman yaji wai shizai kwana gunta kenan?"
Cikin jin haushi yabar office in saidaifa Dr yafara zargin anya wannan hadadden sojan y'ar uwarsace..
Cpt na fita yanufi room 8saidai besan dalilin dayasa gabansa faduwaba kawaidai yatura k'ofar yashiga.
Maida k'ofar yyi yarufe bayan yashiga...
Share...
๐๐mmn fareesa ceโ๐ปโ๐ป
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story &written by mmn fareesa
๐
ฟ31&32
Maida k'ofar yyi yarufe bayan yashiga "ajiye basket d'in hannunsa yyi yazauna kan wata farar kujera dke gab da gadon", d'agowa yyi hade da aza idanunsa kan baby face d'in ta yana kallonta idanunta arufe....shiru yyi yana tunani Ashe dai akwai masu kyau haka,shifa ada iftihal ce kawai yake tsayawa yakallah ta birgeshi bbu wata macen daya tsaya yyiwa kallon minti5 in aka cire familynsa....tsaki yyi azuciyarsa yace to me ruwana d kyawun ta?" Agogon dke daure atsintsiyar hannunsa yakallah yaga 7:40tsaki yyi yana d'agowa ...adedenan iftihal ta farka ,kallonta yacigaba da yi yana wani hade rai "don yaga me zatayi ko tadawo normal ne?"
Ita kuwa koda suka had'a ido da shi kallonsa taci gaba dayi ,can kuma tayita kallon room d'in " koda yaga haka yasan tabbas bata haiyacinta.
Tashi yyi yashiga toilet,yyinda taita kallon k'ofar toilet din har yafito da wata silver da mah clean d brush a hannunsa gun basket d'in yanufa yadakko robar faro yanu gun gadon.
dab da ita yatsaya cikin sweet voice insa yace ya jikinki?"shiru tayi tanata kallonsa "tausayinta yaji d kansa yasan yanxun ko mgn sai ankoya mata kenan"
Lallausan tafin hannunsa yasaka yadako kanta yajingina pillow din jikin bango ,sannan yad'an matsar d ita jikin pillow din ta jingina dashi."
marclean din yamatsa jikin brush d'in yabude ruwan yazuba abakinsa yakuskure ,sannan yafara brush d'in, yyinda tamasa k'uri d ido tana kallon sa har yagama yakuskure bakinsa ya zubar d ruwan a silver... wani brush d'in sabo yasake sakawa mahclean d'in yamik'a mata kallonsa tayi bata karba ba....atsawace yace ungo mana!zare ido taitayi bata karb'a ba afili yace yah salam!
"Kyawawan hannayenta yakalla yamika nasa hannun Yakama yasakamata brush d'in aciki yyinda yamata alama yanuna mata tayi, aiko yaga tayi bbu musu yazuba mata ruwan ta kuskure bakinta tana hawaye bbu magana dai....kayan yamayar bayan ta gama ,koda yaga tana hawaye yasan k'ila ko kanta ne ke ciwo sbd buguwar datayi,yaji tausayinta ....gun basket d'in yanufa yahad'a mata tea mai kauri yasheka sbd zafi..""
Gefen bed din yazauna gab da ita yakurb'i tea din sau2 sannan yabata bbu musu ta karb'a,ta yi yadda taga yyi,yo ai tuni ta shanye shi Ta's tana tsotsan baki...kuri yyi mata yana kallonta dan ta masa kama da angel dinsa in tanashan abu mai dadi yadda take intana karama ....hannunta dayaji cikin nasane yadawo da shi tunaninsa....wani yarrrrrrr!
Yaji hade da shock tuni yayi saurin janye hannunsa yatashi dg kusa da ita "
Shiru tayi dai yyinda cup dinke hannunta ta na kallo "alamomi sun nuna tea din be ishetaba.
Koda yaga ne hakan gun basket d'in yasake nufa yazubo mata faten dankali d wake yaji kifi d alaiyahu sai kamshi ketashi.
Kujerar dke kusa d gadon yazauna yafuskanceta ,yyi 2spoon sannan yafara feeding NATA ,aiko tayita karba har suka idar, alokacin 9:pm tayi ,tashi yyi zai fice dg room d'in kamar ance yajuyo kawai yaganta ta biyosa ko d'an kwali bbu...
Afili yace oh my God?"
Kallonta yyi sai yanxunma yalura da tulin gashinta dan bbu Dan kwali akanta ga goshinta da cikinkan anmata d'inki,doguwar rigace jikinta robber..
"Fasa fitar yyi yadawo " ita tasake dawowa tayi zaune kasa gabansa....tunawa yyi da magun gunanta,yanaso takoma kan bed gashi batajin meyake cewa balle yace ta zauna kuma bayaso yatab'a gsky ...wayarsa yafito yakira a reception aturo masa wata nurse.
"bayan yakira yakalleta yaga tana hawaye ta takure gu daya ,sai fiki fiki take d ido"
Fuskarsa yadauke dg dubanta ,yanajin duk yaka gara yabar asibitin dai baisaba zama gu daya ba gsky.
Nurse dince ta shigo da sallama,fuska atamke ya amsa ,cikin English yace tabata magani yanxun ta maida ita kan bed"nan ta amsa dan taga bbu wasa afuskarsa.
Ita kuwa iftihal kallon su take tana sauraronsu"jin nurse d'in ta kama hannun ta yasata kwacewa ta mike zata hau cinyar cpt atsawace yace keeeeeeee!har saida ta tsorata ta dafe kanta sai hawaye take yyinda yacigaba da harararsu itada nurse d'in. "
wani gefen na xuciyarsa yace kabita sannu sbd matsalar ta ,yanzun in iftihal dinkace daba'a San inda takeba aka mata hakan aibazakaji dadiba...
Tashi yyi yasa hannunsa yamikar d ita tseye ,har gefen bed din yazaunar d ita, yakalli nurse din yace dataketa kallonsu yace zaki iya tafiya."
"Ahankali tace y'allab'ai ai Dr jabeer yace ,kafin ta kwanta bacci nakaita toilet....shiru yyi azuciyarsa yace yyi tunani gsky Dan nidai bazan iya kaita toilet ba." Afili yace kije byn minti10 kidawo .
"Batayi mgn ba ta fice"
ruwa yadakko yaduba magungunan yaba vitamin C sai yasa bakinsa yakora da ruwa ,sannan yabata tasha ...bayan ta gama yamaida pillow din kan bed din yakwantar da ita.
Aji yar zuciya yyi azuciyarsa yana cewa d matsala gsky"....shigowar nurse dince tadawo dashi tunaninsa ,gun iftihal ta nufa ta dagota hade da mikar da ita taja hannun ta ,ita kuwa d'agowa tayi tana kallonsa tana hawaye... Jiyyi tabashi tausayi ,tashi yyi yace wa nurse d'in muje kibimun ita ahankali....be auneba yaga ta janye hannunta dg na nurse din tafada jikinsa.....
Wani mugun shock yaji jin nashanunta sun daki kirjinsa....lumshe idonsa yyi hade da janyeta dg jikin sa yanuna mata shushiga toilet din"
Itadai nurse sai aikin kallonsu take dan atunaninta matarsace....bayan sun shiga toilet din d dubara nurse din tasata tayi fitsari ,sannan ta fito da ita ...shikuwa yana zaune idanunsa alumshe.
Koda suka fito nurse din ta fice ,ita kuwa gunsa ta nufa tana kokarin hawa jikinsa yabude idonsa...da sauri yabatarai yace oh wuce kije ki kwantar,yafada hade da nuna mata bed.
Wucewa tayi tana waiwayensa taje ta zauna kan bed din dan bata fahimci meyake nufiba .
Koda yaga haka sai ya tashi yaje yakwantar da ita ,yaduba agogonsa yaga har 10:pm tayi toilet yawuce yyi arwalla yazo yyi sallar d nafilarsa dayakeyi kullum akan ALLAH yabaiyana masa angel dinsa lfy.
Bayan ya idar yakira Ummi yace mata anan zai kwana tunda bbu Wanda yasani nata,tace to shikenan sukayi sallama..
Lemo d ruwa yasha kawai yazauna kan kujera bacci yafada daukarsa,,yyinda tuni iftihal ta yi bacci.
Haka kuwa akayi shi yana kan kujera ita tana kan bed ahaka sukayi bacci..
Washe gari...
Share..
๐๐mmn fareesa ce
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA !
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
Masu min magana ta PC atura musu dg farko kuyi hkuri bnida lokaci gsky Ku bincika a wasu grps din dan bana posting a PC..
๐
ฟ33&34
Washe gari tun karfe 5:30am cpt yatashi kasancewar yasaka alarm"bayan yyi arwallah yanufi masjeed din dke cikin asibitin.
bayan yadawo yazo yaduba ta yaga bacci take"azkar yaci gaba dayi dg nan bacci yyi awan gaba dashi."
Iftihal kuwa baccinta take tana juyi harta farka,ta tashi tsaye ta isa gun cpt tasaka hannunta dan ta shafa fuskarsa ...yabude idonsa yana mamakin ta afili yace oh daban tashiba fa sai ta tabani"mitts yaja tsaki....Dr jabeer ne yyi sallama" cpt ya amsa tare da basa hannu yyinda iftihal ta ke tsaye gefen cpt sai zare ido take kamar ace ,cas ta gudu...Dr ne yyi murmushi bayan sun gma gaisawa yace masha ALLAH patient d'in taka bbu laifi taji sauki,bara na sake duba ta"
Cpt yace eh bbu laifi tafara samun lfy saidaifa bata mgn !Dr yace eh ai dama bazatayiba sai nan gaba "ahankali tukum.
Cpt yace to amma gsky kasallameta yau " Dr yace ah ah gsky kayi hkuri zuwa gobe tukum muga yanayin jikin nata kokuwa?"
Yace to shikenan nizanje gd na shirya nakamata break na wuce office ..Dr yace to amma dai kafara bata ko tea ne d maganinta sai amata allurar bacci
sannan katafi,kasan ita kamar baby take ,ko yanxun kaga gata agefenka ....katsesa yyi da cewa eh wlh inaga ma zan sami mai kula da ita jiyafa da binama zatayi"Dr yyi murmushi yace hmmm shiyasa nace kamar baby take yanxun, sbd sadda ta far ka dakai taci karo da kai tasaba dan haka da wuya tasaba da wani bayanka ,sbd tamkar jaririne daya saba da uwarsa ,to haka kaima zata ruka daukarka tamkar uba agareta dan kai tasaba gani aida sauk'i tundama jininka ce ba bareba ....katsesa yyi da cewa pls kaduba ta ,Dan yafara k'osawa da maganarsa..kallonsa yamaida gunta yaga tana hawaye ,nuni yamata kan ta koma bisa bed juyowa yyi yakalli Dr dke kallonsu...yace to kaga hawayen datakeyi?"cpt yace eh Dr yace duk sadda kaga hakan to wani abu takeso,ayanxun na fahimta yunwa takeji"cpt yace to bara nahada mata tea d'in .....nan yanufi gun basket din yyinda Dr yamata dubaru na likitoci yaduba ta.
Cpt kuwa byn yahad'a mata tea d'in toilet ya wuce yafito da brush d silver ahannunsa,adedenan Dr yace inta gama kakirani nazo namata allurar !cpt yace to..
Gefen bed din yazauna yamik'a mata brush d'in bbu musu ta karba tayi tagama kamar jiya,nan yamayar ,yadawo yabata tea d'in tasha,sannan yaje yakira Dr ,suka dawo ta re ,sunsha fama da ita tukum ta tsaya aka mata allurar.
"Sannan cpt ya nufo gd byn yaga tayi bacci."
********
Mama zulai ce tsaye a parlourn ta itada zubaida tana cemata ,kiyi sauri ki karbomun dinkin anjima shizan saka"yyinda Rukayya ke zaune kan 2seeter tana kallon su..zubaida tace oh mama kinds San yanxun inna fita bai saniba wlh mugun duka zaimun ko yabani mugun punershment da gara dukan dashi ma.....atsawace tace kutuwar ubansa shi Yusuf din ,akace shina haifawa ke ne kokuwa?"ke kuma sakara kina nuna masa tsoro ko?"sai kace keba rainona bace ,har wannan k'aramin kwaron zai takaki to bazaki tambayesa ba ,dole kije sbd inada iko dke ehe....Rukayya ce ta katseta da cewa haba mama miyasa kike hakane?
Ai yah Yusuf kobashi zai aureta ya isa da ita tunda yayantane ,kuma hakan na nuna yadamu da tarbiyyarta ken...
Wata ashar mm zulai ta bankoma Rukayya ,hade d cewa in ina mgn kika sake samun baki wlh saikin ji jiki ,ni wlh inbacin gd nahaifeki da sai ince musayamun ke akayi sbd kwata kwata bakya kishina kuma bakijin mgn ta...
Cikin jin haushin halin mahaifiyarta tace kiyi hkru ,tafada had'e da ficewa a parlourn.
Kallon zubaida tayi mm zulai ta ce oya maza kitafi ina jiranki bbu musu ta fice,Amma tana tsoron yagane ta fita be saniba..
sad'af sad'af take tafiya harta fito ta nufi get....yah Yusuf da ke shirin fita yana dakinsa yahangeta ta window, akuma lokacin cpt yashigo da motarsa ,zubaida NATA gaidashi yyi mata banxa.
Yah Yusuf kuwa ,kwafa yyi afili yace zankamaki wlh.
Cpt kuwa part din su yanufa ,yaje yashirya cikin kakinsa ,sannan yanufi sashen Ummi yasamesu tare da abbu zai fita ,bayan sun gaisa suka masa yah mai jiki yace da sauki,nan Ummi tace to ga break fast d'in