Ina Tare Da Ita 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   2 / 26

3K to 6K   out of 77.9K words

y'ar gatan yayanta,amma ni bazaki baniba?"da sauri tace ah ah gashi mommy na kinsan fa yah ile yahanani rowa d zagi d raina mutane ,da zuwa gun wani nmj Wanda ba dan uwana ba....yace duk bbu kyau Wanda yyi hakan to zai mutu ,hakane?"cikin jin dadi yadda Suleiman yake koyawa yarta tarbiyya ta kwarai tace hakane mana ,muje namiki wankan amma d safe kibani araba abawa yan uwanki kinjiko?"iftihal tace to ,nan sukaje mommy ta yi mata wanka tasaka mata doguwar Riga ta bacci ,nan ta fice xuwa part din yah Suleiman tana xuwa taga baya dakin g wayarsa iPhone 7ajiye kan bed d sauri ta dauka dan tasan key d'in ta tanaso tayi game, fitowa tayi wayar na hannunta ,ta koma part din su..

Yah Suleiman kuwa koda yaje part din Ummi ,nasiha ta masa akan yarage zafin xuciyar nan ta sa da saurin fushi ,kuma yarage shagwaba iftihal dan zaijawo mata bakin jini cikin gidan.. Cikin ladabi ya amsa da to zai kiyaye saidai fa azuciyar yaji bazai fasa jida angel d'in sa ba ,hira sukayi d Ummi har abbu yashigo akayi dashi dg bisani yah Suleiman yyimusu sallama yabar part din dan bayaso angel insa tayi bacci basuyi sallama ba ,yana shiga yasami dakin bata ciki ,duba wayarsa yyi yaga bata gun ...dan murmushin gefen baki yyi dan yasan tana gunta tana game...

"Ficewa yyi yanufi part din su."

********

Iftihal kuwa koda ta je parlour da wayar ,mommy batayi mamakiba dan atunaninta yah Suleiman ne yabata ,su Osman d muhamma dke zaune suna ta surutu ,Osman yace ke wlh kimaidawa yaya wayarsa kosai kinfasa masa scream d'in ta?"cikin yarinta tace mommy kinga yah osman yana Jana!mommy ta hararesa tace me ruwanka d ita?"

Hararan iftihal yyi yace haba yarinyar zan mamaki ,da anyimiki abu ,saiki gayawa yaya ko?"ai jiya ina ganin yaya yaseer yaita cin zalinki damuna mota zamu tafi skul,duk da bakimasa komai ba shine ita kuma wawiyar zubaida taruka cemiki mai kwala kwalan idanuwa.... nasio nayi mgn amma inasan yah yaseer dukana zaiyi na shareta amma wlh nima zankamata ne ...tsawa mommy ta yi masa hade da cewa ban hanaku kamun magarnar wani ba?"Duke Wanda yaci zalinta shida ALLAH...

"Ahankali iftihal ta mike tsaye wai dan taje ta dakko sweet ta sha abed room din mommy ta na tashi wayar ta fad'o kasa atake taci screen.

Zaro idonu duka yan cikinta parlourn sukayi ,hade d salati ,da sauri mommy ta dauki wayar taga yadda tayi ,wani irin kunya,d nauyi taji na yah Suleiman duk d bega wayarba ,wata zuciyar tace mata akwai matsala gsky Dan wannan wayar tanada tsada ..

Usman kuwa ,cikin rawar jiki yace hmmm wata yau zasu bats da yah ile dinta daga dawowarsa ko kwana be yiba .....iftihal dake tsaye tana zare ido, tasaki kuka jin ance zasu bata itada yah ile d'in ta .

Fisgota mommy ta yi hade da dauketa d mari tasaki kuka dan jin azabar zafin Marin ,har daddy dke bed room d'in sa yaji yafito yana tambayar lfy?"

Mommy ta sanar dashi irin aika aikar da iftihal tayi, kafin daddy yyi mgn yah Suleiman yyi sallama ......

📚📚mmn fareesa ce✍🏻✍🏻

AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)

INA TARE DA ITA !

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

(bansan ita bace)

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

Ina jin dad'in yadda kukeson wannan novel dg farasa ansamu 4grp duk na fans nasa ngd sosae🤝🤝

🅿7&8

""Mommy ta sanar da shi irin aika aikar da iftihal tayi kafin daddy yyi mgn yah Suleiman yyi sallama...

Tun kan ya ida karasowa yaji kukanta..Osman na ganinsa yyi saurin cewa yauwa yaya wlh iftihal ta fasa maka waya mommy ta mareta....Wata harara yah Suleiman ya aiko masa da ita alokacin yanufi gun iftihal ta fada jikinsa tana dafe da kuncinta,kallonta yyi yanajin zafin kukanta har cikin ransa ,d'agowa yyi yaga mommy d daddy sun dan sunku yadda d kai alamar sunajin nauyinsa..." Ahankali yace daddy shine kabari agabanka aka mararmun ita sbd wata waya can wadda ni iftihal tafimun ita mahimmanci dan takashe aiko bata fasataba ,dole yau tafashe sbd haka ALLAH yarubuta...

Cikin mamakin maganganun sa Wanda tsakaninshi d ALLAH yake fad'a daddy yace wlh my son bansan abinda yafaruba ina ciki naji ihunta nafito nasamu aika aikar da tayi amma kayi hkuri .....sabar iftihal yyi ransa bace yabar parlourn baisake mgn ba...

Mommy datayi zaune sbd mamaki takasa mgn tasan ma bazai kulataba tunda ta tabo yar lelansa,saidai tayi mamakin yadda yanuna bedamuba ko ajikinsa koma takan wayar bebiba tasan k'ila gobe bazai shigo sashenba"ajiyar zuciya tayi tace daddyn yara kaga ikon ALLAH ko?"murmushi yyi yace hmmm wlh nima dama raina yabani bazai cemata komaiba ,gsky tsakanunmu d yaron nan sai addua ,mommy tace gsky Amma yanxun sai a canxa mishi wata ko?"yace ah ah kinsan zai sake fushi yace biyansa mukayi kidai Adana wannan yanxun nasan zuwa safe yahuce saiki basa ya zare sim card nasa ,mommy tace to gsky hakan yyi,daddy yace dama nabude masa account ina saka masa kudi aciki inason insiya masa mota ,banason inzai tafi makaranta sai ankaisa gun dawowa yahau ta haya, toko kudin basu cikaba nacika nasiya masa,ALLAH yyi masa albarka..

Cikin murna mommy ta ce ameen gsky alh ka kyauta nasan zaiji dadi sosai!murmushi daddy yyi hade da mik'e wa tsaye yace aiko dai amma ke yanxun kunyi fada da d'an naki fushi yake dke ....yar dariya tayi tace zamu shirya ai,nan daddy yabar parlourn yyinda mommy ta sallami yaran tabi bayansa dan tasan yah Suleiman bazaibar iftihal ta kwana anan ba ,daya gama rarrashinta gun Ummi zai kaita...

*******

Yah Suleiman kuwa part dinsa ya wuce d iftihal suka zauna kan kujera tana saman cinyarsa yanata aikin rarrashi ,cikin shagwaba tace yah ile wai yah Usman yace ai zamu bata dakai tunda nayi maka banna?"shiyasa nake kuka"tafin hannunsa yasaka yagoge mata hawayenta ya girgiza kai hade da cewa ah ah my angel bazamu bataba sbd wata waya can ,ai zanma canxa wata sainaka agyara screen din waccan sai kirika game da ita ko?"dariya tayi tace eh fa yaya hakane ,ainasan bazamu bataba ko?"yace eh abu d'aya ne zaisa mu bata!tace to minene?" sai nadena banaso mub'ata!ahankali yace indai kika bari wani nmj Wanda ba d'an gidan nan ba yadaukeki ko kika zauna ajikinsa to aranar zamu bata dke....dan zaro ido tayi tace um um ai bazanyiba ma..

Yace to shikenan ,jiya kinje skul ?,tace eh naje ,yace to kinga yanxun 9:43pm muje gun Ummi ki kwana sbd skul karkiyi latti."

Cikin shagwaba hade da kwantar da kanta ajikinsa tace um um ni gunka zan kwana...lumshe ido yyi yace no kinga yanxun kin girma kuma hakan bbu kyau muje kinji my little angel ?"tashi tayi batayi mgn ba ,sabarta yasakeyi suka nufi part d'in ummi.

"Ahanya sai janta yakeyi d mgn amma taki kulasa ,yasan haushi taji ,to amma garadai kada ta kwana gunsa dan abaya sadda take kwana gunsa, mama zulai ca tarikayi yana tattab'e ta saiya lalatata ,abun yyi masa ciwo to dandai alokacin mommy ta take mata burki,akan cewa ta yarda da yah Suleiman 100% inda yaseer ne baza bari ya kwana d yartaba,hakan yasa dg ranar yaji bayaso su kwana gu d'aya..

" ahankali yace wai angel wannan fushin na men'e?"

"Ni bbu komai"

Adede nan sukayi knocking ak'ofar Ummi ,Ummi datake tare d abbu sukaji knock tashi tayi tazo ta tambayi waye ,taji muryar Suleiman d iftihal...budewa tayi tace lfy?"

"Yace lfy lau"

Yafada hade da mika mata iftihal yace gata Ummi ta kwana anan d safe zankawo mata yuni foam NATA ashirya mata ta tafi skul.

Ummi tace miyasa zata kwanaa nan?"

Nan yalabarta mata abinda yafaru."

Murmushi tayi tace gsky mommy bata kyautaba data mararmun ya',wato fushi kayi da ita kenan?"iftihal ta karbe maganar da cewa eh Ummi bbu ruwanmu da ita mun bata ko yaya?"

Yace eh"

Nan yyimusu sallama Yakoma side nasa.....

Washe gari tu tun gun karfe 6:30 yah Suleiman yafito yanufi part din mommy har bed room d'in ta yashiga yabude ward rod d'in itfihal yakwaso mata yunifoam NATA da skul bag d sandals d sock's yafito gab da zai fita mommy ta fito dg part din daddy murmushi tayi afili tace oh ni zainab har yanxun fushi ake dani ,yyimda yah Suleiman yama fits shibaima gantaba.

Bayan yaje sun gaisa d Ummi yabata yunifoam d'in yajawo iftihal suka gaisa yabaro part din Yakoma nasa dan yakara bacci..

da misalin karfe 7:30 duk yaran gidan sun gama shirinsu na zuwa skul ,sun firfito iftihal na rike d lunch box d'in ta ,zubaida dke bayanta taga sweet d biscuit ahannunta d sauri tace keeeee!iftihal ta waigo ta tsaya ,fuska daure zubaida tace bani sweet d'in... bata rai iftihal tayi tace ah ah ba mommy ta bakuba ,Wannan nawane ........kafinzuzubaida tace wani abu yah Yusuf (Wanda ke bima yah Suleiman) yace ke xonan "turo baki zubaida tayi azuciyarta tace gsky mutumin nan yafara shiga rayuwata amma sai na ja masa sharri tukum ....gab dashi taje ,kafeta yyi d ido can yace jiya Vance kigyaramun dakinaba?" marairaicewa tayi tace namanta yaya wlh amma zan gyara maka ,tsaki yyi yace inbaki gyaraba yau sai jikinki yagaya miki ,stupit kawai mitts yyi tsaki, kallon iftihal yyi yace ke kuma kije yah Suleiman nakiranki....

Sum sum ta wuce ,ai sai zubaida tabita abaya ,akuma lokacin yaseer ya yanko kwana dan su hadu bakin get driver yakaisu skul tare ,yana ganin iftihal yace ke xonan..jikinta har rawa yake ta nufi guns a ,yyinda d zubaida ta kwace su sweets din dke hannunta d biscuits.

Shikuwa yaseer kunnenta ya murde, tasaki k'ara alokacin kuma Osman dke tsaye yana kallonsu ,yana kokarin xuwa dan sanarda yah Suleiman ,kawai yaga yaseer ya wankamata mari ....tuni iftihal tasaki razanannan k'ara, adedenan sukayi muryar yah Suleiman yana cewa ......

Share..

📚📚mmn fareesa ce✍🏻✍🏻

AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)



INA TARE DA ITA !

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

(bansan ita bace)

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story &written by mmn fareesa

🅿9&10

Adede nan sukaji muryar yah Suleiman yana cewa kutsaya a inda kuke duk Wanda yagudu shine babban kuskuren dazaiyi arayuwarsa... Yafad'a yana tunkarosu ,fuska bbu annuri idanun nan nasa sunyi jajir sai huci yake alamar ran yan maza yabaci..wayyo ALLAH ai tuni suka rud'e dan basuyi zaton zai gansuba ,zubaida kamar tasaki fitsari a wando sbd tsabar firgita yyinda yaseer jikinsa keta rawa tsoro fal aransa yasan koyayi ihu mama zulai bazata jisaba balle taka masa agaji dan be manta irin suburbudar da yah Suleiman yyi masaba sadda yyiwa Ummi rashin kunya..... da gudu iftihal ta fad'a jikinsa tana kukan shagwaba da Sauri ya yajanyeta ajikinsa yamik'awa usman ita yyi gun zubaida da tayi kneeling ,shikuwa yaseer yyi tsaye sai wani cin mgn yake amma fa aransa tsoro ne fal...

Cikin tsawa had'e da k'araji yah Suleiman yacewa zubaida meta miki haka kuka tsaneta?"saikace ba jininki bace?"yafada had'e da kokarin zare belt din dke k'ugunsa....gaba d'aya zubaida tagama firgita..wani gigitaccen mari lafiyayye yama 2wanda jinta na wucin gadi yadauke yasaka belt din iya k'arfinsa yacigaba da dukanta sai ihu take tana cewa ta bari bazata sake cin zalin iftihal ba ,aigogan bemaasan tanayiba dan ya zuciya said a duk yafashe matajiki yabarta tana ihu da fad'uwa gurin..

Cikin tsawa yace inkundawo dg skul kisameni a dakina kinji ko bakijiba?"ya

Fada cikin k'araji ,awahalce tace to ...gun yaseer dke tsaye yyi had'e da saka kafarsa yatad'esa ...tuni yafad'i k'asa yasaki ihu wata shak'a yah Suleiman yabisa yyi masa had'e da saka gwuwarsa yadaki cikinsa....zubaida dke duke tana kukan azaba da sauri ta ta shi ganin yah Suleiman na niyar raba yah yaseer d ransa dan tari kawai yakeyi ,yayinda yah Suleiman keta huci yana fadar zaka sake tabamun iftihal dina?"

Da gudu ta ta shi ta nufi part dinsu..shikuwa Usman dke tare da iftihal da sauri yacikata dan yakira daddy domin yana gd betafi office ba,d gudu yyi hanyar bangarensu .....

Zubaida kuwa cikin tashin hankali taje ta sanar da mama zulai ,alokacin Abba na toilet yana wanka ,ai saita bugi kujera tace yau kuwa zaayi yaki agidan nan ,tab'arya zansaka nadakesa agaba na nakastashi yadda inma yak'wallafa ransa ga tsinannar iftihal din to wlh sai dai yakalleta...tayi wuf d gudu ta dakko tabarya suka fito aguje ....adede lokacin yaseer numfashinsa na kokarin fita sbd shak'a d galabaituwar da yyi agun yah Suleiman...

Su mama zulai na isowa d gudu tayi gun yah Suleiman zata bugama sa tabaryar aka....iftihal tayi k'ara iya karfinta tace yah ileeeeeeeeeeee! ka gudu "da sauri ya waigo .....cikin zafin nama nasu na sojojin yyi sauri ya kauce tabaryar ta daki kan yaseer atake goshinsa yafashe....adedenan su daddy da Osman suka iso kuma daddy yaga komai.

Salati yyi had'e da cewa meke shirin faruwane ?"ko me yafaru?"

Ai mama zulai na ganinsa saita saki ihu tana cewa ai Suleiman zai kashe yaseer......salati daddy yyi yace hmmm nafa gani d idona dukansa kikasoyi ALLAH yatsaresa kika daki yaseer... cikin borin kunya tace oh sharri zakamun wato ka kare d'an gwal din naku ko?"ok ai nagane tunda sbd y'arku yyi dole kace haka....Usman yace lah mama bahaka akayiba ,nan yasanar dasu komai ..

Kukan muna furci mm zulai tafara had'e da cewa ,duk kulline ba gsky bne ta nufi gun yaseer dke magashiyan itada zubaida..

Shikuwa yah Suleiman beyi mgn ba dan har yanzun zuciyarsa zafi take masa ,yasan mudin bebi ahankaliba to har mama zulai din zai iya shak'a sbd haka yakauda kansa gefe yajingina d bango, iftihal maganin hakan tasaki lunch box nata ta nufi gunsa, yana ganinta yaduka ,tsawonsu yazo daidai ,faskarsa tasa hannu tana shafawa d kansa had'e da cewa yah ile mama bataji maka ciwoba ?"ta fada had'e da shafa goshinsa ....ji yayi duk zuciyarsa tayi sanyi ta lafa ,murmushi yyi yace eh my angel kinyi kokarin cewa na gudu ,muje nakaiki skul nasan kinyi latti sbd waddannan shirmammun...

Juyowa yyi yaga bbu mama zulai d yaseer had'e da zubaida sai abbu da daddy suna mgn atsaye ......muryar driver yaji yana cewa iftihal ke ake jira kun makara ma"yah Suleiman yace to gata amma kasanar askul akwai uxurin da ya tsaidasu..nan yaradawa iftihal wata mgn ,murmushi tayi tabi bayan driver.

Babu d daddy suka kira yah Suleiman ,bayan iso gab dasu yaduka yagaishesu ,nan suka sake tambayarsa meya faru?yasanar dasu atakaice,nasiha abbu yyi masa akan yarage zafin zuciyar nan tasa ,duk Wanda yyi laifi ak'annensa yyi masa hukunci daidai laifinsa ,ya amsa d to yyi godiya ,nan daddy yace my son kashirya yanxun zaka rakani wani gu...kafin yah Suleiman yyi mgn abban yaseer ya iso yana huci d alamar mm zulai ta zugoshi.

Cikin bacin rai yace kai Suleiman me yaseer yyi maka kamasa irin wannan dukan?"

Daddy yace my son jeka abinka , bbu musu yah Suleiman yyi tafiyarsa dama yyi niyar bazai yi mgn ba.. Daddy yakalli Abba yace abban yara damu zakayi mgn bada yaroba ....tsaki yyi yace wlh Ibrahim ka kiyayeni ,aidama tuni zulai tasanar dani ana cutata dan ni tallarkane sai yanxun Nagano hakan sbd y'arka yyiwa yaseer haka?"

Daddy yabude baki zaiyi mgn abu yagirgiza masa kai alamar yyi shiru ,shiru daddy yyi .....abbu yace gsky kabani mamaki abdullahi wato har mace ta isa tashiga tsakanunka da yan uwanka ko ?"

Abba yace ni kurabu dani har gdn zan bari gaba d'aya ma ,yana fadin hakan fuuuuuu yabar gurin...abbu yagirgiza kai yace ALLAH ya kyauta....

********

Bayan yah Suleiman yyi wanka ta shirya cikin kananun kaya jeans dark blue d shirt Orange sai kamshi yake, yyi masifar yin kyau,gun motar daddy yaje yatsaya befi 10 minit ba daddy yaxo ,suka shige had'e da Barin gdn..

Amota daddy yace my son gsky karage fushin nan naka,shine kaki zuwa ciki dan kana fushi d mommy nka ko?"kajirani a parking space, itakuma tanacan ta shirya maka break fast kaki zuwa kayi ko?"ajiyar zuciya yyi kamar yaro yace to daddy meyasa tadakarmun angel?"yar dariya daddy yyi yace horo ta mata ,nan yace to na hakura daddy yace yauwa my son kokaifa..adedenan suka iso gun sayarda mota ,bayan daddy yy parking suka fito had'e da Shiga ciki ,shidai yah Suleiman yyi mamaki azuciyarsa yace ko wa daddy zai siyawa mota?"shiru yyi dai nan suka matsa gun motocin daddy yace my son zabi wacce tamaka"ware ido yah Suleiman yyi ,daddy yace yes kazaba ,rungume daddy yyi yana murna had'e da godiya dan yaje dad'in motar nan dama gobe ake bath day d'in hafeez friend dinsa sai kawai yafaka motarsa,cikin jindadi yazaba daddy yabiya kud'in suka bar gurin da xumar zaa kamusu ita har gd .

Haka ko akayi bayan sun dawo aka kawota gd ,Ummi d abbu sunji dadi sai godiya suke ma daddy dan duk tsaye suke suna kallon motar harda mommy d yah Suleiman din ,gogan kuwa beyi mgn ba ,mommy tace my son wai baka huceba ne?"yar murmushi yyi yace nafa huce ,mommy kimun sakwara da miyar kifi zanci d rana ,cikin jin dadi tace to shikenan ,nan kowa yawatse aka basa d motarsa yana kiran my angel dinsa tadawo dg skul ya nunamata yaga irin farin cikin dazatayi..

Mama zulai ce tsaye a parlourn sai huci take gefenta yaseer ne kwance kan3 seeter ga bandage agoshinsa ammasa dressing gun,cikin bacin rai tace dole nadauki mataki wlh dg gobe xuwa jibi hakata zata cimma ruwa ai wlh dani suke mgn sana tarwatsamusu farinciki ...

Ace kana kwance bbu lfy har asiyawa wannan dan iska mota kai ko mashin bakadashi ,sannan ubanku motarsa ta ji jiki meyasa be canxa masaba ?"

Cikin jin jiki yaseer yace gsky kidau mataki ..

Hahahahahahahaha!mama zulai takece d dariya tace yo ai dole ne ,zan nuna musu na hakura ayau shima wawan

2 / 26