Author : Maman Fareesa Category : Romance
Ku nan kaida ita !
"Ahankali yace mungode"
Ummi tace ALLAH yabaka ladar,kaje kafara yin break din sai muje ka kaini gunta nadubata ko?"cpt yace to dama ni gun aiki zantafi....abbu yace ai bbu damuwa kije ki kula da ita anjima nima naje nadubata.
Amma yaushe zaa sallameta?"
Cpt yace gobe ne"abbu yace to shikenan, nan ya wuce dining area yyi break fast yagama,alokacin abbu yafita...
Fitowa sukayi shida Ummi ,Fatima Auta nabiye dasu d basket a hannunta ,sai turo baki take ita atafi da ita.
Bayan Ummi ta shiga, cpt ya karbi basket din dg gun auta,yasaka gidan bays ,yazagayo dan yashiga...jin muryar Ummi yyi tana rarrashinta auta....kallonta yyi had'e da mata wani kallo d gudu tabar gun bbu ko waiwaye..
Sukuwa sukabar gdn.
Gudu take taji taci karo da mutum,tana d'agowa taga yah Usman ne yakafeta da ido....sunkuyadda kanta tayi cikin inda inda tace dama dama k..ka kayi hkuri pls ban ganiba....
Meyasa kike gudu?"yafad'a kamar bayason mgn"
"Ahankali tace toba Ummi bace ta tafi tabarniba,shine yah Suleiman yyi ta hararata ko" tafad'a cikin sugar shagwaba"lumshe ido yyi yace aikin girma da ake dke anguwa!kuka kada nakoma ganin kina gudu kinjiko?"
Ahankali tace to "
Murya qasa qasa yace ki kalleni mana!yabukaceta dan turo baki tayi tace um um bazan iyaba......kafin yyi mgn yah yaseer dke nufosu agadarance yace kai Usman meye hadinka da ita?"bacin kasan ita nake so ....afusace Usman yadaga masa hannu da cewa kullllllll!kada kasake cewa matata wai ita kakeso yafad'a cike da kishi....
Dariyar rainin hankali yaseer yyi ,hade da cewa kasake cemata matarka sauna maka illah"yafad'a had'e da nufar fatima yana mata murmushi.... Da sauri yah Usman yabank'adesa hade da tsayawa gaban Fatima ita kuma tana bayansa.....baki bude yah yaseer yke kallon yah Usman da mamaki yace hmmm zankuwa had'a maka jini d majina yanxun kuwa....Fatima dke bayan yah Usman tace pls yaya kada kabiye masa kaji?"tafada tana kuka ganin zasuyi fada sbd ita..
Afusace yah yaseer yakaiwa yah Usman wani punch ...tuni ya Usman yaduke yahankado sa hade da kaimasa nausa ta ko ina ....kukan murna Fatima keyi tana cewa yauwa yah Usman dina kaima sa laga laga.... Adede nan yah Yusuf yamusu tsawa dan duk yaga komai dama yabari yaga insun fara game din waye loosed?
shikuwa yah Usman jibgarsa kawai yake yakumbura masa fuska dan shima akwai zuciya....afusace yah Yusuf yakaraso yashiga tsakanunsu ,nan kowa yyi gefe ,yyinda Fatima tayi tsaye tana zare ido..
Yah Yusuf yakalli yaseer yace mitts kaji kunya wlh ace kaninka yamaka duka gaban mace meyafi haka kunya?"
Yah Usman sai huci yake yafinciki hannun Fatima sukabar gun ,shikuwa yaseer bbu kunya yajuya yatafi d mugun guduri aransa...
Yyinda yah Yusuf yanufi get dan daukar mota adedenan zubaida ta shigo get din,rungume hannuwansa yyi akirji yakafeta da ido....kamar anceta waiga idonta tsab cikin nasa..
Sbd tsoro kamar ta saki fitsari a wando,Aida gudu tayi part dinsu jin yana cewa taxo,koda yaga hakan sai ya rufa mata baya..
Bangaren su yah Suleiman kuwa ahanya yake sanar da Ummi akan yarinyar bata mgn kuma bata saba da kowa ba sai shi.
Nasiha da rarrashinsa tayi akan yyi hkuri ya kula da ita da duk na ko wane ,da haka kuka iso room d'in.
Tun kafin su Shiga Ummi kejin fad'uwar gaba,har suka Shiga da sallama cpt na gaba ,ai iftihal na ganinsa da sauri ta ta shi sai hawaye take ta nufesa da nufin fadawa jikinsa.
atsawace yace ......
Share
📚📚mmn fareesa ce✍🏻✍🏻
AWESOME WRITER' ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
(bansan ita bace)
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story &written by mmn fareesa
NOT EDITED
🅿35&36
Atsawace yace keeeeeeeee!had'e da saurin janyewa dan kada ta fad'a masa ajiki".
Ummi dake bayansa tayiwa iftihal kuri da ido tana tuna kamar tasan mai irin fuskarta ko wadda suke kama da ita. "
"Ahankali tace haba babana?" meye haka? "Kasan fa bata hayyacinta ko?" batare da ya kalletaba yace kiyi hkri Ummi!
Batayi mgn ba taja hannun iftihal dake tsaye gefen yah Suleiman tana hawaye....tirjewa tashiga yi ,Sam bazata bitaba....nurse d'in da suke zaune a room din ta taso da dubara ta zaunar da ita kan bed ,sannan Ummi ta zauna cike da tausayinta.
Shikuwa gogan fuskar nan murtuk ,dasun hada ido da iftihal sai ya aiko mata da harara ,abinda bai saniba ,Ummi na lura da shi...
Basket din dasukazo dashine Ummi ta nufa ,tahadawa iftihal komai a plate had'e da tea mai kauri tabawa nurse din ta ce tayi feeding d'in patient d'in. "Yyinda yah Suleiman kebinsu da ido....
Nurse d'in tafara kokarin feeding nata, amma me?"
Tak'i yarda .....kallonta kawai yah Suleiman yyi ta nutsu tarika Karba...hararansa Ummi ta yi tace hmmm dani kake magana ,wato bazaka dena hantararmusu y'a ba ko"?shin in y'ar uwarkace take cikin wannan halin zakaso amata hakan?"ahankali yace ah ah pls Ummi ki yi shiru duk ga yara kinamun fad'a ....girgiza kai tayi batace komai ba...hakadai aka lallabata tayi break aka bata magani ,bbu jimawa bacci yyi gaba da ita ..itadai Ummi sai kallon ta take ,tanajin kaunarta hade da tausayinta."
Bayan nurse d'in ta fita ,Ummi ta yiwa yah Suleiman Ta's dg karshe kuma tamasa nasiha ,wacce tashigesa sosai ,yyi kuma alk'awarin cewa zai kula da patient d'in sa iya bakin iyawarsa...
Ummi taji dadi tayita saka masa albarka...har yanufi k'ofar fita dan tafiya office sai kuma ya juyo ,"ahankali yace Ummi idan ta ta shi dg baccin kimata dubara tayi wanka ,amma kada kibari wannan kilbabbar nurse din ta mata plsssssss!
"Da mamaki Ummi ta kallesa ,amma saitace to shikenan adawo lfy"
"Yace ameen"
********
Da gudu xubaida tashige parlourn mm zulai ta na nishi hade da waiwaye taga ko biyota yyi"
Tsaki mm zulai ta yi tace keeeeeee!lfy?kika shigomun atsorace ko Wannan d'an iskanne yabiyoki?"
Yaseer dke kwance kan 2seeter sbd dukan d Usman yyi masa yace ke dallah shine ko nashi bane ?"
Atsorace tace kirana yyi wlh wai nazo!nidai gsky mama kinjamun "yanxun bansan abinda zaimunba wlh....afusace mm zulai ta ce yakasheki yyi gunduwa gudunduwa da namanki ,karshe kenan ko?" Ai wlh dani suke mgn duk Wanda yace sai sani a rana toni a wuta zansashi...shims Usman yanxun yyiwa yaseer haka shida Yusuf suka taran masa to wlh ni kabarni da Usman din dan har nagama tunanin sharrin dazanmasa har fatimar tace bata k'aunarsa wlh....dariya yaseer ya kece da ita had'e da cewa da kyau my sweet mama ,shiyasa nake sonki...murmushi tayi tace hmmm aini bata wasa bace...zubaida dake raba ido tace ni bara naje na shirya inada lakcures da karfe 12:30yanxun kuma 12:00,naga su Fatima d Rukayya basuje skul ba yau lfy dai ko?"tsaki mm zulai ta yi tace matsalarsu ce k'ila sunada dalili.
Abinda zan gaya miki ki dena nuns tsoron dan banxan yaron nan ,shima zansaki kimasa sharri dg nan ai afasa auren naku!da sauri zubaida tace pls mama gsky kiyi hkri bazan iyaba yaje yagane nabani gunsa, yanxunma bansan me zemunba...tsaki yaseer yyi yace ke wani lokacin wawoyace wlh !mm xulai datakasa mgn dan zubaida ta kuleta ,sai kallonsu take...turo baki zubaida tayi tace gsky kadena cemun wawiya ....ni natafi nashirya zuwa skul...
Yah yusuf dake lab'e yana saurarensu ,yyi ajiyar zuciya yajuya dan komawa bakin get yajirata tazo wucewa"sai yakamata.amma yaso yashiga cikin parlourn to amma jin mugayen kalaman mm zulai da yaseer yasa yak'i shiga."
Azuciyar sa tunani yake akan rashin tsoron ALLAH irin na mm zulai dakuma muguwar tarbiya datake ba y'ayanta tana bata musu rayuwarsu da mugayen halayenta,afili yace oh to zancigaba da bibiyar yaseer naga wanne sharrine zata sakashi yyi ma usman?
Motarsa yabude yazauna yarufe ,yana tunanin dole yakula da tarbiyyar zubaida tunda ALLAH yasa tana tsoronta,kuma yalura wani abun duk mama zulai kesata yi ,kobada son rantaba..yananan yana zancen xuci yaganta ta cire gyale tasaka hijab sannan tasakashi a hand bag d'in ta... Koba afad'aba yasan mm zulai ta tursata tasaka gyale ,amma dan ta yi masa biyayya tasaka hijab....da sauri yafito dg motar fuska atamke gab da zata fita yace keeeeee!arazane ta juyo,cikin isa yace zo nan,"matairai cewa tayi tace pls yah yah kayi hkuri wlh na dena bazan koma "zantafi skul nakusayin latti...tsakin da yyine yasakata yin shiru.... Cikin tsawa yace inkin dawo dg skul kisameni a part d'inmu inkika bari nasake nemanki hmmmmn sorry for your self wlh.... Bejira ansartaba yashige motarsa ,itakuma ta fita dg gidan...
A hospital kuwa ,tun bayan tafiyar cpt Suleiman Ummi ke tsare da iftihal har Dr jabeer yashigo suka gaisa yadubata yaga bbu laifi tafara samun lfy, kallon Ummi yyi yace mama takusa tashi yanxun bbu jimawa ,amma ina gani amata wanka sbd takara samun lfy ....Ummi tace ok bbu damuwa, nan yafice Ummi ta wuce toilet tayi arwalla bayan tagama sallah takira Habiba akan su shirya lunch a basket yanxun zata kira abbu inzai tafo yatafo dashi...bayan bata gama wayar ta waigo taga iftihal ta ta shi ta bude ido tanata kallonta..
Murmushi Ummi tayi ,ahankali ta mata gefen bed d'in ta kama hannun ta ,ta mikar da ita ,tsaye bbu musu ta mike suka nufi toilet ,kasancewa da komai aciki da dubara Ummi taimaka mata ta cire mata Riga dg ita sai inner wear's ,ta nuna mata tayi wankan amma bata fahimtaba...harzata fita ta tuna da abinda yah Suleiman yace ,sai tadawo ta wanke mata fuska da hannuwa had'e da kafafunta ,sannan tamayar mata da rigarta suka fito ta .
Babu jimawa abbu yayi sallama yashigo ,iftihal harta ta shi ,koda taga ba yah Suleiman bane saita koma ta zauna...
Abbu dketa kallonta da tausayinta ,yace wa Ummi yamai jikin?"
"Tace da sauki"
Yace k'ila abasu sallama yau ko?
Ummi tace eh gsky da alamar hakan.
Kallonta abbu yyi ganin tana hawaye,yace kukan me takeyi?"
Ummi tace Aida kashigo catake babana ne,shine dataga bashineba take kuka ayadda na fahimta......nan tasanar dashi sabon da patient d'in yah Suleiman tayi dashi...kafin sbbu yyi mgn yah Suleiman yyi sallama yashigo ,Ummi ta amsa iftihal naganinsa ta sakko dg kan gadon...yyinda yaketa addua a zuciyarsa ALLAH yasa kada tafad'o masa ajiki agaban abbu....kafin yagama tunani yajita jikinsa ......hannunsa yasaka yajanyeta suka nufi gefen bed din , yazaunar da ita yagaidasu abbu d Ummi ,bayan sun gaisa yyi shiru ganin hawayen datakeyi.....tunowa yyi da ahanya yasiya mata biscuit da big bomb da chacoolat,da sauri yafito dasu dg aljihun rigarsa yasakamata ahannu sai.. kallo take tayi kuri da ido kamar mai nazari,yyinda yyi Mata kuri da ido yana kallon tsantsar kyau nata...muryar ummi yaji tana cewa ga lunch kayi serving naku kuci...
Abbu yakatseta da cewa ,kafin nan yafasa sweet dasu biscuit d'in nan yabata naga tana kallon su.
Karba yyi yafasa yaci sannan yasaka mata abaki...yana tashi dan kamsta abinci ...tasaki su sweet d'in ta ta shi tsaye dan biyosa....azuciyarsa yace oh ni naga ta kaina...Ummi ce ta ce jeka zauna bara nakamuku ,nan tayi serving nasu a plate daya ta mika masa ,tana gabansa zaune cikin jin nauyin ganin abbu d Ummi na nan yafara bata ...taki karba,abakinsa yakai sannan itama yabata ta karba.....koda abbu yalurada da yah Suleiman na jin nauyinsa sai yafice ,yacewa Ummi zaije gun Dr jabeer suyi mgn yakarbomata sallama.
Ummi tace to"
Nan yafice dg room din.
Iftihal kuwa duk sadda yabata bata karba sai yaci tukum take karba ahaka sukaci tare harsuka gama ,Wanda yyi mamakin kansa daya iya cin abinci da wata ,bacinyasaba da angel d'in sa kawai yake iya cin abincin...
Abbu ne yashigo yace to ansallameta kuma kullum Dr zaizo yadubata ,kuhada komai muje muyi sallar la'asar sai muwuce gd ,Ummi tace to ,nan abbu da yah Suleiman suka fita..
Bayan sun dawo dg masjeed suka fito had'e da Shiga mota ,wacce iftihal duk ta tsorata harda hawaye ,kuma agdn baya suka zauna ga k'ugunta ga na yah Suleiman ,koda yaga hakan Hand chief nasa yafito da shi mai k'amshi yasa hannu yagoge mata hawayenta,sai son hawa jikinsa take shikuwa yana jajjan yewa ,yyinda su abbu d Ummi na lura dasu .
Bayan sun iso gd suka nufi part d'in su ,zama yah Suleiman yyi a 2seeter iftihal tazo ya haye saman cinyarsa.....gaba daya su Fatima da Habiba dke zaune a parlourn suka Shiga mamaki dakuma wacece wannan yarinyar ....tsawar dadukaji yah Suleiman yyi mata had'e ja mata kunne yatureta dg jikin sa har kanta yanigi kujeta...d'agowa yah Suleiman yyi suka had'a ido da abbu dke tsaye yana kallonsu da alama ran abbun yabaci ..
Beyi mgn ba yakalli Fatima yace kije dakin Yusuf kice masa nace yasanar da kowa yanxun za'a yi family meeting yana fadin hakan yafice dg parlourn..
Duk sai yaji jikinsa yyi sanyi dan bayaso yabatawa iyayensa rai.
Kallon iftihal yyi dke...
Share
📚📚mmn fareesa ce✍🏻✍🏻
AWESOME WRITER'S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
(bansan ita bace)
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story &written by mmn fareesa
Naga korafe korafenku akan cewa wai Ummi bata gane iftihal tana y'atta,wayace ita ta haifeta?mommy ce mahaifiyarta kuma har yanzun basu ga junaba,wasu na cewa baidace yaki ganetaba sbd shakuwarsu ,kunmanta sunan novel din? dan haka duk wacce taji zata iya bina tacigaba da bina wadda ta ji bazata iyaba to bbu dole dan babu wacce ma jawo nace dole ta karanta..
NOT EDITED
🅿37&38
Kallon iftihal yyi dketa hawaye dafe da kanta!"
Wani tausayinta yaji azuciyarsa."
Da sauri yasa hannu ya mik'ar da ita tsaye ,had'e da lailaya Mata gun data bugu".
Habiba kuwa sunsha mamakin wannan lamari.....bata auneba sukaga Yakama hannunta yana mata mgn batadai jin abinda yake cewa...
Yah Suleiman dke rike da hannun iftihal yakalli habiba ganin yadda taketa kallon su yace malama Ki fita nace!
Bbu musu ta fice dg parlourn.
Tana fita yakalleta "ahankali yace sorry kinji?"
Itadai kallonsa take batayi mgn ba "hannunta Yakama sukaje gefen frige yabata swan water tasha ,aitana gamawa tafada jikinsa tayi luf akan faffad'an kirjinsa...
Yah salam kawai yace afili...da dubara yadagota ,yajata suka nufi babban parlourn gdn inda ake meeting d'in.
Hannunsa cikin nata suka shiga sai rarraraba ido take ,ai tun kafin su zauna take kokarin hawa jikinsa....yyinda jamaar gun sun cika d mamakin,wacece wannan yarinyar?
Mm zulai kuwa baki bude take kallon su da mamaki da kuma tambayoyi fal aranta"
Amma burinta taji ,dalilin meeting d'in.
Zubaida kuwa wani haushin iftihal da kishinta taji ganin sun zauna ,ga k'ugunsa ga na ta,yarik'e hannunta ,kanta akafad'arsa yana mata rad'a akunne.wani bakin ciki taji ,tuni tafara kokarin su had'a ido da iftihal ta harareta...sallamar su yah Yusuf ce da abbu tasata saurin nutsuwa...
Shikuwa yah Suleiman sarai da gayya yabar iftihal ta aza kanta akafad'arsa sbd yanaso mm zulai ta ji haushi...kuma taji haushin sai harara take aiko masa da ita..yyinda sauran mazan sai kallon su suke bbu Wanda yatambayi ba'asi..
Gyaran murya abbu yyi yace ina yaseer?"
Mm zulai ta ce baya nan yana gun bath day d'in abokinsa....kafin abbu yyi mgn yaseer yashigo parlourn yasha kananun kaya da wani d'an iskan aski can ciki yyi sallama suna had'a ido da Habiba yawurga mata harara,sannan yyi sallama yanemi guri yazauna ...byn yazauna yana waigowa idanunsa suka hasko masa iftihal.
Sake ware idonsa yyi azuciyarsa yace oh lallai akwai kyau nan gurin,gsky tamun ,wannan zuk'ekiyar babyn dg gani zatayi sugar "afili yace wow wace ce wannan?" She is very beautiful... Wata uwar harara yah Suleiman ya bankomasa ,tuni yyi tsit had'e da cigaba da yin salatin da abbu yace ayi dan bude taro da addua.
Bayan ansha addua,abbu yace to alhmdllh masha ALLAH ,dalilin wannan taro shine sbd Suleiman nayisa da wannan yarinyar dake kusada shi....afusace mm zulai ta ce gsky ayimana gwari gwari yadda zamu fahimta ba ayita dogon bayaniba....cikin tsawa Abba abdullahi yace kada nasake jin bakinki ina ruwanki ne?"
"Murmushin takaici abbu yyi ,had'e da zayyane musu yadda yah Suleiman yatsintsi patient d'in sa da matsalarta".. tuni suka dauki salati dajin hakan sannan sukayi fatan samun lfy gareta..
Ita kuwa mm zulai ko gezau batace komai ba ,dan haka kawai taji tsanar yarinyar da kinta azuciyarta..
Abbu yace sannan masu irin wannan matsalar tamkar yara suke ,ko yanxun kunganta ga jikinsa ga nata sbd bata hayyacinta,dan haka na yanke shawarar gobe bayan antaso dg masjeed za'a d'aura auren su da ita sbd gsky yawan shigemasa datake dukda lalurace akwai matsala ,gara ace da aure tsakanunsu,dg bays insha ALLAH taji sauki saimu sadata da iyayanta" in sunyarda yacigaba da aurenta inbasu yardaba to saisu rabu..ita kuma iftihal in ALLAH yasa tadawo sai amusu aurensu ko kuwa ?"
Duk yan cikinta parlourn sunyi tsit ,yyinda yah Suleiman keta gumi sbd tashin hankali jiyake dama besantaba ,yanxun in iftinshi tadawo tasami yamata irin wannan cin amanar mezaice mata?" yakare kansa...da sauri yace abbu pls katsay....cikin tsawa abbu yace nagama mgn banason musu inkuma ban isa da kaiba to ?"
Mm zulai ta ta shi tsaye had'e da yatsina fuska tana gatsine tace hmmmm duniya kenan"yagama dadironshi da ita za'a cemana wai bata lfy ,bacin sun gama shek'e ayarsu,shine sbd ba'son ya auri y'ar uwarsa za'ace ya auri karuwa....tas Ta's kakeji..
Abba Abdullahi ya wankama mm zulai mari ,had'e da nunata da yatsa yace ke har kin isa ki kira Suleiman da manemin mata... Afusace Ummi ta mik'e kamar zata shak'i mm zulai ta ce ni ban hafi fasikiba!kuma bazan haifesaba har abada.
Tana fadin hakan tafice,yyinda abbu yagirgiza kai yabita ,shikuwa Abba tsaki yyi yace kisameni adakina!bejira amsartaba yafita shima.
Yah Suleiman kuwa inbacin dukan Tara Tara bbu abinda kirjinsa keyi ,wani haushin patient d'in tasa yaji..amma sai yadaure dayake shi nmjin duniya ne,tashi yyi ransa adagule Yakama hannunta suka fice.
Yyinda yaseer yaha hadiyi yawu ,azuciyar sa yace anxo gurin tunda batada hankali yadda nikeda son farar mace ai dole nalashi xumarta gsky...gani yyi anata fita shima yafito.
Yah Yusuf kuwa gab da zasu fita yabankowa zubaida harara had'e