Author : Maman Fareesa Category : Romance
toga amanar abokina nan ki kula....yah Suleiman yakatsesa da cewa mitts dallah mlmya isa !ke kuma muje yafada fuska daure..
Murya kasak'asa tace yaya kaga lallen kuma bakace yyi kyauba. "
Banza yyi da ita yabude mata gidan baya ,tashige ,itama ai sai yan Jan ajin suka motsa.
Ta daure fuska duk yana dubanta a madubi .....wayarsa ce tayi ringing yana dubawa yyi murmushi had'e da d'agawa yyi sallama yans cewa my mommy kin manta da danki..
Ah ah mommy ina kula da ita ,yanxunma muna tare,ok abata Ku kaisa..
Share..
๐๐. Mmn fareesa ceโโ
[6/28, 10:01 PM] Mmn fareesa: AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story
&
written
by
Mmn fareesa
Kuyi hkuri my fans da yadda kuke samun posting d'ina ba kamar daba ,abubuwa sai ahankali, amma innaga comments kujini xuwa dare nagode...๐ค๐ผ๐ค๐ผ
NOT EDITED
๐
ฟ83&84
"" yanxun ma muna tare abata Ku gaisa ne?"juyowa yyi yaga yadda taketa shan k'amshi ,beyi mgn ba"yamik'a mata wayar,kasancewar yasan tasan koda wa yake mgn..
Tsintar kanta tayi da jin fad'uwar gaba"cikin dauriya tace salamu alaikum!d'if mommy ta yi sbd sak muryar IFTIHAL taji!muryar baby ce ta katseta gun cewa ina uwuni?"
"Ahankali tace lfy lau y'ata amma yasunanki?
Cikin inda inda tace baby.... amma...hello net work yyi halinsa wayar ta tsinke" mik'a masa kawai tayi tak'i mgn ,shikuma yaki karba har sai da cpt salim yace ana miko maka wayarka abokina,yafad'a cikin sigar tsokana"
Banza yyi dashi yacigaba da driving d'in sa.
Yyinda baby kejin muryar mommy kamar suntaba mgn da ita ko kuma tasanta ,hakanan taji k'aunar matar tun kafin ta ganta.
"Parking yyi had'e da kallon cpt salim yace to mlm zaka iya fita zuwa 3:00pm muhadu a barrack " murmushi yyi had'e da kallon baby ya ce amaryarmu to asauka lfy !
"Murmushi tayi had'e da cewa ALLAH yasa "
Byn yafice yah Suleiman batare da yajuyoba yace zaki iya dawowa gaba tunda yafita"yatsina fuska ta yi "ahankali tace ah ah barshi namma yayi!
Afusace yace what?"
Kina nufin driver dinki zanzama?"
Cikin dakiya tace inbazaka maidani gd ba nafito natari adaidaita...katseta yyi da cewa bara nafito nasaki ta karfin tsiya naga zaki iya hanawa"
Fitowa yyi yana nad'e hannun rugarsa....da sauri ta yi wuf kafin yabude tawuntsula takoma gidan gaba batare da ta fito dg motarba..koda yabude yahangota ,murmushi yyi yace hmmm haba yarinyar nan wlh zankamaki ,naga kwanan nan kin maidani abokin wasanki"da ki tsaya mana namiki maganin rashin kunya..""""
Batayi mgn ba tasharesa da haka yabude motar yajasu ,ko parking be gamaba ta bude murfin motar ta fice yana kiranta tayi banza dashi..
Direct part d'in Ummi ta wuce,tasamesu a parlour zama tayi tanama Ummi sannu da gd su Fatima nata santin kunshinta,dining ta wuce danyin lunch.,,,,,,
Yah Suleiman kuwa part d'in sa yanufa yaje yyi wanka yacanxa kakinsa yanufo sashen Ummi da kwalin wayar baby ahannunsa da ice cream dinta daya fara narkewa"
Ummi ce kawai a parlourn nan yazauna yasanar da ita batun tafiyarsa Lagos yanxun,tamasa fatan alkhairi da samun nasara ,sannan yaje yaci abinci,yana jiyo surutunsu Fatima amma beji alamar mgnar baby ba har ya idar da cin abincin..
Kallon Ummi yyi yace ina yarin yar nan?"
Girgiza kai tayi tace tana bed room d'ina tana jeramun kaya a wardrobe "tasameni inashiryawa shine ta karba,murmushi yakuccemasa sbd yaji dad'in yadda take kyautatama mahaifiyarsa.
" ahankali yace dama sallama zan mata ,nabata sakonta gashi kibata....katsesa Ummi tayi tace ah ah shiga kuyi ban kwana halin rai!
Tashi yyi yanufi bed room d'in, tun bakin k'ofar yaji tana ta yan wakokinta ,sallama yyi yahangeta tana gyara bed"sarai taji muryarsa aciki ta amsa had'e da juyawa ta kalli Wadrop.
Cikin husky voice yace baby nikike juyawa baya?"waimiyasa kikeson batamun rai ne?"amma yyi kyau dan kinga nadamu dakene ko kuwa...katsesa tayi ashagwabe gurin cewa haba yaya yanxun adalcine ka kaini amun lalle amma kaki yabawa dan ALLAH sannan kuma kayita dauremun fuska agaban abokinka ,dan yasan basona kakeba dukda dama nasan din basona kakeba am....maganar ta mak'ale sbd kukan dayaci k'arfin ta...
Dafe kansa yyi yanajin wani tausayinta"ahankali yace yah salam!pls baby kiyi shiru haka ,indai kunshine aiyyi kyau ko yanxun ma shinazo nagani nakuma yi miki pics innatafi narunga kalla gakuma wayarki ko...
Saurin kallon sa tayi yad'aga mata kai had'e da zaro hanunsa merike da kwalin wayar dake bayansa yamik'a mata, batasan sadda tasaki murmushi ba tana zuba godiya da ihun murna gakuma hawaye afuskarta ...hannunta guda yarik'e "ahankali yace to ya isa haka ihun yanxun aikin huce ko?" Munshirya !
cikin damuwa tace eh yaya nah amma banason inga na wuni bangankaba ai"
Cikin rarrashi yace aiga waya ko ?yanxun muje kishiryamun kayana na wuce ,kada ayita jirana bbu dadi...
To tace had'e da bin bayansa,suka fito parlour, cikin xumudi taba Ummi wayar ,sannan suka nufi sashensa..
Zama yyi kan bed yanuna mata trolley d'in sa yace tashirya masa Kananun kaya set2 yunifoam set5.
Wardrop d'in ta bude "saida tayi tasbihi ganin yawan suturarsa ,nantafara shiryama sa harda na ciki ,tsab duk abinda yake bukata saida tashiryamasa.
Byn ta idar tarik'e trolley d'in had'e da cewa yaya muje ko?"
Tashi yyi yace to na gode sosai baby sim card dinki yana cikin wayar amma sai zuwa gobe zaifa aiki amma inmun sauka zankira Ummi tabaki muyi mgn "
Cikin shagwaba ta ce to shikenan amma ina key din dakinka?"zarosa yyi dg aljihu yace gashi aringa ygaramun kullum kinji my baby?"
Ahankali tace to yaya ALLAH yatsare yabada SAA "
Lumshe ido yyi yace ameen,,adedenan driver yabude masa gdn baya dan yashiga,su Ummi yahango da su Yusuf d Fatima tsayawa yyi suka iso suka masa ban kwana da fatan alkhairi.
Baby kuwa taki tafiya haryashiga motar"ahankali yamiko mata hannu ganin zatayi masa kuka,bbu musu ta miko masa nata yajawota tashigo ciki ta zauna kusa dashi.,fuska bbu walwala yacewa driver din muje ka kaini kadawo da ita""
Da sauri driver din yace to y'allab'ai "
Bbu Wanda yyi mgn sunata tafiya ,can murya k'asa k'asa yace baby pls banason kina damuwa haka ,nima hankali na bazai kwantaba harnayi abinda nazoyi tunda kema kina cikin damuwa!
"Ahankali tace to yaya " amma kada ka kula wannan Sumyn...murmushi yyi yace hmmm baby kenan haryanxun bakison koni waneneba "aibatakai matsayin dazan kulataba ma " amma miyasa bakison na kulata?"
Da sauri ta ce bbu komai...
Parking driver yyi ,yah Suleiman Yakama hannun baby "ahankali yana murzawa sannan yafito da wayarsa yyimusu pics 2suna murmushi, sannan yyimata rad'a akunne yafice dg motar.
Murmushi kawai naga tanayi dan banji meyace mata"
Cike da kewar yah Suleiman baby ta koma gd ta karbe wayarta tana latsa..
************
Washe gari gurin karfe 8am mm zulai ce tsaye a dining area itada su zubaida sunajera break fast.
Fuska bbu walwala mm zulai ta kalli zubaida tace, anya yaron nan lfy tun dg jiya da na dawo har yau babushi bbu alamarsa ,yana qlau?"
Tabe baki zubaida tayi tace ohon masa mudai rabonmu dashi tun shekaran jiya,mm zulai ta ce kwana2 fa gsky abincika...Rukayya tace hmmmm wai mama meye naki na damuwa da d'an da besan darajarkiba?"
Girgiza kai mm zulai ta yi tace hakane ,amma ai Nina azasa akan gurbatacciyar tarbiyya ko?"
Kafin Rukayya tayi mgn wasu mutane sunyi sallama ,a parlourn suna cewa me gidan na nan?
Mm zulai ta nufi part d'in Abba,bbu jimawa suka fito atare,adede k'ofar parlourn Abba yatsaya ganin yan C I D ,hannu yabasu suka gaisa ,byn sun gama gaisa daya yace Sunana mahamood Ahmed da abokin aikina Mustapha lawal dg hukumar binkice ankama danka yaseer acikin yara3da ake zargin sunyiwa yar deputy Governor fyad'e sun kuma kasheta gudun to non asirinsu agurin wani bath day party da akayi a shekaran jiya da misalin karfe10:00 pm.
Dan haka yana hannunmu zamu cigaba da binkice harzuwa karshen wata dg nan amik'a case din zuwa kotu...
Zaka iya zuwa office dinmu sbd wasu tambayoyi daza miyimaka zuwa anjima.....
Salati kawai da anbaton ALLAH abbu kawai yakeyi had'e da zufa ,nan sukayi sallama suka wuce Yakoma ciki cikin bakin ciki dan yana ganin yaseer yagama bata musu suna ga icon jama'a ,sannan ya yarda tabbas yyiwa yarinyar fyade sbd tunawar da yyi lokacin da yyi kokarin yiwa baby fyade....
Su mm zulai yasamu suna salati itada yaranta ,alamar sunji komai.
Tsaki yyi had'e da barin parlourn, azuciyar sa yana ganin duk laifin mm zulai ne itace ta bata yaronta...
Da misalin karfe 9:30am baby ce apart din yah Suleiman tanata gyara masa dakin,harta idar.
Wasu kayansane dke shanye a toilet ta fito dasu ta bude wadrop ta Jere su har zata rufe taga album dan karami me hotuna ,tsintar kanta tayi da daukar album din.
Budewa tayi....zaro ido tayi waje sakamakon ganinta datayi tana yarinya, zaune atsakkiyar cinyoyin yah Suleiman suna murmushi anmusu hota ahaka.
Sake ware idonta tayi dan tabbatarwa.....
๐ณ๐ณ๐ฑ๐ฑ
๐๐. mmn fareesa ceโโ
[6/29, 6:11 PM] Mmn fareesa: AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(Palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written
by
mmn
fareesa
Wannan page nakune shukra novels&ina tare da ita fans club kuyi yadda kukeso da shi comments dinku yafi na kowa"ku nada banne azuciyar mmn fareesa ina mugun yinku irin totally d'in nanโค๐๐ป๐ป
Inajin dad'in comment naku..
Aysha aliyu
Mmn Bilkisu
Samira yahaya
Fatima
Habeeba Muhamma
Aishatou
Fatimatou
Rims
๐
ฟ85&86
"Sake ware idonta tayi dan tabbatarwa kanta " mafarkine ko gaske?"
Cigaba tayi da kallon pics d'in Wanda dukan su ita da shine wasu kuma ita d'aya.
Zuciyar ta ce taitamata sak'e sake had'e da jero mata tambayoyi "
Itadai tasan photon ta Wanda take yarinya yar 6 years abbanta yabata suna kasan akwatunta ak'auye Wanda tana yawan kallon su a time din datake ak'auye to kuma yanxun taganta da ita da yah Suleiman kuma tabbas itace! ba kama bace to dama yasantane tuni ko kuwa?"wata zuciyar tace hmmm keda yatsinta yataimaka "
shiru tayi had'e da Ciro photo guda Wanda suke tare ita dashi,tasaka acikin rigarta had'e da rufe sashen ta nufi part d'in Ummi dan tanason duba wayarta taga in sim card din yahau takira abbanta wato(mlm) danyimasa wasu tambayoyi.""""
******
Abbune da Abba ke tafe cikin mota ,dukkansu fuskarsu cikin damuwa take suna tafe suna jajanta abin.
"Can Abba yace gsky yaya na yarda da fyaden da akace hardashi aka yima yarinyar amma ina zaton gsky bbu hannunsa a kisan"
Abbu yace ah ah abdullahi kada kayi saurin zatonsa k'ila ma bbushi aduka laifukan.....katsesa yyi da cewa hmmmm ko kamanta halinsa na bata y'ayan jama'a?"bacin har yarinyarnan baby yaso yiwa fyad'e ,dan haka halinsane...
Shiru abbu yyi yana nazari har suka iso police station din.
Byn sun gabatar da Kansu ,suka nemi ganin yaseer d'in, nan bbu jimawa aka fito dashi Wanda ko tafiya bayayi saidai kamosa akayi....
Inhar ba farin Sani kayiwa yaseer ba to wlh baza ka ganesaba sbd dukan dasuka masa na fitar hankali akan ya amsa laifinsa "fuskarsa akumbure take da bakinsa da har hakora 2akafitar masa dasu ,idonsa guda akumbure,muryarsa adashe sbd kuka .atake idanun abbu suka cika d kwallah sbd ganin halin da yaseer din yajefa kansa aciki...
" abban ma yatausaya masa amma be nunaba hasalima harararsa yyita yi da aiko masa d mugun kallon ,amma azuciyarsa tausayinsane fal aransa..
Abbune ya matsa ganin yaseer din na kuka da hawaye "ahankali yace yaseer miyasa ka aikata abinda ake zarginka dashi?"
Murya adashe yace wlhy! wlhy!! abbu ban aikata duka laifikan nan 2 da akamun azaba sbd na amsa su.nadai taka sawun barawone kawai "amma nasan kaida Abba kun yarda sbd abinda nayi yunkurin yiwa baby"
dan ALLAH abbu da Abba kuyafemun kuyimun addua nasan alhakin kune wlh natuba nabiku zan kasance da nagari insha ALLAH inna kubuta dan ALLAH abbu kafito da mama kace itama ta yafemun tamun addua nayi nadama....
Yafada had'e da sake fashewa da kuka!
Abbu yadago kai idanunsa sunyi jawur har cikin zuciyarsa ya yarda da yaseer ,sbd tun alokacin dayaso yiwa baby fyade yasaka ido akansa dasawa ayi bibiyarsa ko awaje yana Neman mata yagano bashi aikata hakan ..."ahankali yace kayi hkuri insha ALLAH zaka fito muddin kanada gsky kuma kadage da addua muma zamu tayaka..cikin kuka yace abbu nagode sai dai ko yankan naman jikina zasuyi sbd azaba bazan amsa laifin dabanyiba sbd ni......dan sandan dake tsaye yace to time d'in da aka Baku yyi ....
Abbu yadubi Abba dake kallon waye yace muje ....muryar yaseer yaji yana cewa abbu dan ALLAH ka cewa Habiba ta yafemun tamun addua kuma inasonta....iya nan sukaji suka fice zuciyarsu fal da tausayinsa...
__________________
bayan sun koma gd kowa da kowa yasan halin da yaseer yake ciki ,mm zulai hankalinta ba k'aramin tashi yyiba danma Ummi na tausarta ,sannan gefe guda koda abbu yagayama Habiba sakon yaseer bata wani ji tausayinsa ba dan ita ta yarda da abinda yyi in aka cire kinsan,hakan yasa tasakejin sabuwar tsanarsa azuciyarta.
Abbu da Abba da mm zulai sundage da addua dg karshe abbu sukayi shawara akan zasuje gun shugaban yan C I D sbd abokin abbune kozai taimaka musu sbd ansanar dasu nanda 7days zaa Shiga kotu...koda akwai taimakon dazaimusu dan bbu maganar nuns duniya a wannan tannin sbd yarinyar y'ar deputy governor ce..,,,,,,,
Bangaren baby kuwa kanta yyi zafi dan takira Fatima asiyasance kasancewarta me ilimin addini,ta tambayeta dan ALLAH ta nuns mata photon IFTIHAL, bbu musu ta nuna mata saidai me ?itadai ce din a pic din ,bata nunama Fatima kobai ba tace oh ALLAH yabayyanata,tace ameen..
Bayan Fatima ta fice ,tunani ta fada dan duk pics din ba a k'auyeneba a birnine akayisu to bama wannan ba ance wai IFTIHAL ce !to wai meke faruwa ne?"sannan gashi yah Suleiman baya gd balle ta tambayesa wani abu"wata zuciyar tace kidai kira mlm kawai ko kije k'auyen sbd ki fita aduhu...
Wayarta ta duba taga sim card din yahau ,ajiyar zuciya tayi ta tahi ta nufi parlour gun Ummi dan karbo number mlm da tasaka awayar ummin..
"Koda taje byn tasaka number din sai da Ummi tace mata aiko baby dazun babana yakira da Ku gaisa bakya kusa ,sannan hankulama ba a kwanceba sbd halin da Dan gidan nan yake ciki wato yaseer" sauna kashe wayarma yanxun na budeta..
nan ta sanar da ita lbrin".
Salati tayi had'e da jajanta mata da adduar nemar masa kubuta.
Sannan tace ai dama sim card dina ne dabe hauba amma zankirasa yanzun ,ta fad'a had'e da sunne kai" cikin jin kunya. murmushi Ummi ta yi dan tanajin dad'in yadda baby keda kawaici.;;;
dakin yara ta koma taduba contact kawai taga ansa yaya nah!murmushi tayi dan tanazaton number dinsace.
Seving number din mlm tayi takira amma akashe tsaki tayi ta saka kira a number din yah Suleiman...
Harta tsinke be d'agaba "kafintasake kira ,kiransa yashigo.
Sai gab da zata tsinke ta da'aga cikin shagwaba tace yaya gsky bakayi missing d'ina ba"
"Ahankali yace oh baby sarkin korafi " wayace banyi missing nakiba?"
To ai baka kiraniba nice na kiraka ko"yer dariya yyi yace to ai nakira Ummi dazun baki kusa!
"Ahankali tace to ya aikin yanzun ?"
Yace hmm baby yanxunfa muna daji, d'azunma sauka kiris aharbeni akafad'a wlh dannayi saurin kaucewa....zaro idanu tayi cikin masifa tace wanne marar imanin ne ze harbemunkai yaya?"
Mamaki yake dama baby ta iya masifa haka....muryarta yaji tana cewa wlh dama inagun amma to miyasama yake son yaharbeka?"
Cikin jin dad'in yadda tadamu dashi yace ai kinsan yan fashine basaso Muka masu to yanxundai cikin mu 20ankashe mutum5"
Zaro ido tayi had'e da cewa ankashe mutum fa 5kace pls yaya dan ALLAH,ka dawo wlh banaso nida iftihal murasaka !ta fad'a hade da sakamarmasa kuka.....
Gaba daya yarude musamman data anbacci itfi dakuma yadda tadamu tsoronsa kada ta d'agawa Ummi hankali ta sanar da ita gashi dama hankulansu ba akwanceba sbd yaseer dan dazun abbu yasanardashi..
"Cikin rarrashi yace my baby kada muyi haka dake dan ALLAH ki kwantar mun da hankalinki kimun addua kefa malama ce ko addini yamana nuni da muceci ran musulmi wlh ko ankasheni muddin mun kamasu munkashe nakashewa alhmdllh Burina yacika ,sannan inbanida Rabon mutuwa a can xandawo pls kimun addua kinji Tawan?"
"" sannan dan ALLAH kiyi shiru kada kisanar da Ummi kinjiko?"ahankali tayi ajiyar zuciya dan ta gamsu da bayaninsa tace to yaya dan ALLAH ka kulamun da kanka ,kuma insha ALLAH zandage da maka addua..
Murmushi yyi yace yauwa ko kefa ,kinga inharmunci nassara har girma zaa karamin..
"Ahankali tace to ALLAH yataimaka nan sukayi sallama dukda taso tamasa tambaya game da pics din data gani,amma dataga ayanayin aikinsa sai ta bari har yadawo..
Number din mlm tasaka calling atake tashiga ringing 3 tayi mlm yad'aga hade dayin sallama."
Cikin murna ta amsa...
share..
๐๐ mmn fareesa ceโโ
[7/2, 3:12 PM] Mmn fareesa: AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
story & written