Author : Maman Fareesa Category : Romance
yyi yace ban hanaki guduna!
Cikin yarinta tace to aibansan kahananiba sai yanxun ,amma nadena.
Yace yanxun ina zaki?
Tace baby,dama kaina hango nazo inma oyoyo, murmushi yasubuce masa yace hmmm abinda ke sannu d zuwan nan baki iyaba balle gaisuwa sai rashin kunya ni munbata dake..
Cikin shagwaba ta ce to ai zandunga gaidakai,kuma bakaine ke tsokanata ba ,amma bazan koma yimaka rashin kunyaba!
Yatsina fuska yyi yace hmmm kima sake kiga yadda zanyi dke oya muje kinwani tsaya haka!
Batace komai ba sukajera suna tafiya "murya qasa qasa tace yaya ina wayarka?"
Beyi mgn ba yafito da ita dg aljihu yace gata.
Murmushi tayi had'e da karba tace game zaka sa mun nayi!
Kallon ta yyi yace ina kika kiyi game ?"tace yo yah Abbas yanada waya yana samun nayi tun....katseta yyi da Jan doguwar tsuka dan besan daliliba inta ambaci Abbas yakejin haushi.
Fuska daure yace bani wayata"sannan kika koma fadar Abbas gabana wlh xanbaki mamaki.....yafada yana huci.
Ita kuwa harta fara hawaye ,cikin kuka tace to ga wayarka kuma insha ALLAH bazan koma cewa kabaniba ,tana fadin hakan da sauri ta tafi tabarsa tsaye gurin.
Gaba daya saiyaji tabasa tausayi wato fushi tayi da shi kenan.
Duk sai yaji bbu dadi danko ifti baya bari tayi fushi da shi,gashi harda kuka take ALLH yasa kada ta fadawa su ummi
.
Part din sa yanufa ransa fal da damuwa sbd baby nafushi dashi .,
Bangaren mm zulai kuwa...
Share..
๐๐ mmn fareesa ceโ๐ปโ๐ป
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by mmn fareesa
Wannan page din nakune mmn fareesa fans Page kuyi yadda kukeso dashi.kuna raina duk rintsi nagode sosae da kulawarku gareni๐ค๐
NOT EDITED
๐
ฟ61&62
"" bangaren mm zulai kuwa haka ta kashe yan kudin mutane dke kanta gun jinyar yaseer."
Kuma bbu laifi cikin kwana 2 yawarke sosai."
Gashi basu shiri da Abba balle tasamu gunsa ga rufe dakinsa yake balle ta d'auko be saniba."
Ayanxun haka zaune mm zulai take tana tunani Dan Laure (wacce da ita aka batar da iftihal) ta mata waya tace zata zo yau karban kudin dashen mutane."
Tasan halin Laure indai kan kudine bata da mutunci...sallamar zubaida ce ta katse mata tunani ,zama tayi fuska bbu walwala tace Ashe mama yarinyar nan ta warke har angano iyayenta !yanxun haka ubanta yana gidan nan sashen baki",,,kuma maganar auren ta da Yah Suleiman tana nan."
Mm zulai ta yi tsaki had'e da cewa matsalarsu ce ni yanxun abinda ke damuna daban ma wlh ,amma ke waye yagaya miki?"
Zubaida tace Rukayya mana kinsan tana lik'e dasu Fatima nima ai naganta daxun suna mgn da yah Suleiman k'ila ma sonta yake!
Mm zulai ta ce ni wlh har banason ganin yarinyar nan sbd Dana ganta gabana ke fad'uwa bansan daliliba....
Zubaida tace nima haka ,amma mama wai yanxun bari zakiyi a aura mun yah Yusuf yaje yyita azubtar dani ,muna gd ma wacce aka cika ,balle ya aureni dg ni sai shi a gd .ta fad'a kamar zatayi kuka....kafin mm zulai ta yi mgn Laure tayi sallama.... Ji mm zulai ta yi kamar ta yi layar zana ta b'ata ga tsoron rashin mutuncin Laure tanayi....cikin fad'uwar gaba ta amsa sallamar had'e da cewa zubaida ke bamu guri "bbu musu ta fice tabarsu.
Bayan sun gama gaisawa Laure tace hjy zulai bani kigani na wuce ko yamma nayi" mm zulai tayi fuska kalar tausayi tace dan ALLAH Laure kiyi hkri wlh yaseer ne bbu lfy na ari kudin nasiya masa ma... Bata bari ta idaba Laure tace kutumar uba !
Yau akeyinta kuwa ai wlh bazata sab'u ba ko kudi ko nakaiki police station dan ni inkan kudine bbu sani babu sabo...
Mm zulai tace oh Laure Ashe ke y'ar akuyace ?"butulu!
Dariya Laure tasheke da ita tace hmmmmmm dad'ina da yau da gobe saurin zuwa ke in har ana maganar masu bulci to kece kan gaba sbd tsabar rashin godiya da butulci kika salwantar da yarinyar da bbu abinda iyayenta basa miki dake da y'ayanki,kinga kuwa kece shugabar masu butulci .
Sannan in bakiyi wasaba to wlh zan FASA kwan komai zai faru yafaru sai me?"
Sassauta murya mm zulai tayi had'e da cewa jibi zata kama ta kudin...shiru Laure tayi tana nazari..can tace in har namiki waya baki dagaba alamar bbu kudi kenan zaki ganni da jami'an tsaro wlh...ko sallama basuyiba Laure ta fice rai bace...
Zama mm zulai ta yi duk abin duniya yadameta...
***** ***** ******
Baby nah nah tunda suka rabu da yah Suleiman take bbu walwala ,Ummi ta tambayeta lfy ?"meke damunta? amsar guda ce bbu komai "sai ummun ta yi tunanin kodan mlm zai tafi ne ,yabarta nan saita rabu da ita..
Har marece yayi bataga sake saka yah Suleiman ba jitake kamar taje sashenshi ta duba amma tana gudun ya yarfata..
Shima anasa bangaren yad'an damu azuciyar sa amma ko a fuska be nunama asalima Barin gidan yyi bayan sunvrabu da baby,suna wani k'auye bincike aka kece da ruwan sama kasan Cesar cikin damuna ne ,duk ruwa yadakesu kafin sukai gun motar.
Bedawo gd babu sai bayan isha'i jikinsa ringis da zafi ,amma dayake jarumine inba tabasa kayiba bazaka San yana zazzabiba saidai ko inkaji yanayin muryarsa nagane..
part din sa yanufa yake yyi wanka da ruwan dumi yasha magani had'e da kiran Ummi awaya yace bazaiyi diner ba ,yadawo agajiye!koda taji muryarsa taji kamar baya lfy kafin tayi mgn yakashe kiran ...baby dke saurarensu ,kasan cewar ummin na a parlourn suke wayar,jitake kamar ta karbe suyi mgn amma yanajin nauyi ,gashi dama sabida tana tunanin k'ila yashigo yasa ta zauna a parlourn.
Tashi tayi taje tayiwa mlm sallama tazo suka kwanta itasu Fatima amma ranta da tunanin ta ma gun yah Suleiman Wanda ita batasan dalilin yin tunaninba..
Washe gari tun karfe 8:00am mlm yashirya inyafita yake gun ayuba suyi sallama ya wuce gd.
Da kanta baby taka mass break fast yyi sun Dade Suns mgn wacce nasihace da shawara acikinta yaketa basa nah nah akan zama da mutane had'e da yima ta alk'awarin sati mai zuwa zasudawo su duka su ganta..
Bayan mlm yagama kimtsawa abbu yazo yyi mass godiya had'e da sha Tara na arziki akace driver yakaisa inda zashi da tasha ..
Nah nah kuwa sai waige waige take kota ga Yah Suleiman amma bbu alamarsa".
Abbu dasuke tsaye Wanda shima yanaso ace yah Suleiman d'in yazo yyiwa sirikinsa sallama.
Yusuf yahango yakirasa had'e da cewa jeka dubamun yayanku kace yazo suyi sallama da Mlm!yah Yusuf have to had'e da tafiya.
Baby dke tsaye kusada mlm tana jin ance akirasa saitaji dadi amma tayi alk'awarin ko yazo zata nuna bata damu dashi ba !
Abbu nata zolayar nah nah yana cewa aike yatakin zama y'ar gd ko?"
Cikin. Jin kunya tace eh "
Yah Yusuf da gudu ya nufo su had'e da cewa ,abbu wlh yayan bashida lfy zazzabi yake da amai ,yanxun haka aman yake yacemun wai kada na fadawa kowa bashida lfy...
Abbu yace ikon ALLAH har yanxundai baidaina wannan halin na boye abu ba ko?"
Mlm tace subhanallahi!
Aje akira likita ko alhj sai yadubasa ,kafin abbu yyi mgn sunga baby ta zura aguje zuwa part din su yah Suleiman..
Da Mlm d abbu sukayi murmushi baki daya ,mlm yace agaidashi da jiki ,number ta nagun nah nah saimu karba Marika gaisawa ...
Abbu tace baza ka jira tazoba ?"
Mlm yace ah ah akyalesu ,ALLAH yabashi lfy .
Abbu yace ameen sukayi sallama.
Shikuwa yah Yusuf waya yyiwa family doctor dinsu yazo yaduba yah Suleiman.
Yana ida wayar yahango zubaida ta fita da gyale ajikinta ...afili yace kutumar uba!
Da sauri yabi bayanta ,yana fita get yaganta tsaye itada wani saurayinta course mate d'inta ne"
Yawanku da kananun kaya ga suma irin wacce samarin zamani ke bari yabari tasha gyara..
Rungume hannuwansa yyi a kirjinsa yasamusu ido,Wanda bazaka iya gane shin cikin damuwa yake ko bacin rai?"
Zubaida bbu laifi tana son guy d'in dan a skul yana wasata yana k'od'ata wai ita kyakkyawa ce gashi yana mata Barin kudi..
Zubaida dasuke gaisawa da guy d'in tana mass fari da ido tana wani yatsina had'e da kashe murya Lamar ance tad'ago kanta!
Wazata gani?"
Yah Yusuf tsaye yana kallon su idanunsa sunyi jajir.,,,,
Wai mugun fad'uwa gabanta yyi da wani tsoro yashigeta ,arazane tace oh ni zubaida nashiga ukku !
D'agowa guy din yyi yace lfy?"numa masa yah Yusuf tayi,tana cewa yayane wlh yahani tsayawa da kowa shikenan kajamun wlh...
Bata jira jin amsarsaba da gudu yabar gun ,yyinda yah Yusuf yyi kamar bashiba ,atunaninta biyota zaiyi saitaga be biyotaba kuma yyi hanyar part dinsu na maza..
Duk da ta tsorata, amma ranta yabata k'ila ma anjima zai hukuntata,jiki bbu kwari tayi part dinsu ,dama anguwa r yazo gun abokinsa ,shine yakirata away a yace tazo su gaisa ,ita kuma ganin da safe ne ta d'auka k'ila ma be tashiba tunda tasan bayan sallar asuba yana komawa baccin safe..
Baby kuwa da Dan gudunta tana hawaye ,sbd akwaita da tausayinta,ta iso Dede k'ofar dakinsa .
Ta murd'a k'ofar had'e da kuta kai ....
Share
๐๐mmn fareesa ceโ๐ปโ๐ป
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story&written by mmn fareesa
๐
ฟ63&64
NOT EDITED
Ta murd'a k'ofar had'e da kutsa kai cikin parlourn, adedenan yah Suleiman ya murd'o k'ofar bed room yafito dan yazauna a parlourn yajira Dr."kamar dg sama yaga baby na nufosa,awahalce had'e da dauriya ya zauna kan 3 seeter sbd jirin dake dibarsa...
Kafeta yyi da ido ganin hawayen dake xuba a kumatunta....tambayar kansa yake meyasa take kuka?"
Muryarta ta katsesa gun cewa yah eleeee!yajikin?"yanxun meke maka ciwo?"
Aransan yace oh my God! afili yace hmmmm baby ke da kike fushi dani "
Kuma kike tambayar yajikina ,ko kin manta mun bata?"
Batayi mgn ba ta sunkuyar da kanta "shikuwa so yake tasake kiransa da yah eleee dan yaji dad'in sunan"
Ahankali yace oh dama ba jinyata kikazo yiba?"
Turo baki tayi tace ai jinyanka nazo yi kuma kanamun wannan abun ni bara natafima ,ta fad'a cikin yarinta...
Dan tari yyi yana cewa ruwa !ruwa!da gudu ta je ta kama sa had'e da zuba masa a cup ,ta mika masa sai hawaye take tana kallon sa da alamar tausayi afuskarta."
Bayan yasha ruwan yakalleta ganinta ta duk'a gab da kujerar dayake tana kuka tana kallon sa.
Cikin muryar marasa lfy yace pls baby kidena kukan banaso kinji?"
Ahankali tace yah ileee! Yajikin?"
Cikin karfin hali yace da sauki ,yanxun Dana sha mgani zan wartsake kinji ,kigoge hawayen nan !ai munshirya ko?"
daga kanta tayi alamar eh !
Murmushi yyi yace to zoki zauna kiji wata mgn .
Bbu musu ta zauna dab dashi....ahankali yace miyasa kike cemun yah elee?
Bacin asanina mutum daya ce ke kirana da hakan ,inkuma kinkirani dasunan kina tunamun da ita! Dan shiru tayi...can tace oh nidai kawai hakanan naji na kiraka da hakan,san
nan wacece ke kiranka da hakan?"
Lumshe ido yyi had'e da dafe saitin zuciyarsa ,yace IFTIHAL ce !
wani abu taji yadaki zuciyarta,amma saita daure tace ko wacce su Fatima sukacemun ta bata ne?batare da yakalleta ba yace eh yana girgiza kai,jiyake kamar yanxun akace masa ta b'ata"
Ahankali tace bacin yan uwantaka akwai soyayya ne atsakanunku?"
Atsawace yace eh kuma itace zabina bakeba !kuma ko an lik'amunke naganta zan aureta kota auri wani ,shikuma nasa bindiga na harbesa....yafad'a yana huci had'e da dafe kansa da ke Sarawa....har cikin ranta bataji dad'in kalamansa ,amma saita tuna da giyyarso na dibarsa dakuma nasihar abbanta ,akan taso abinda mijinta keso koda aranta bataso afili ta nuna masa tanaso..
Ahankali tace ikon ALLAH wlh har naji tausayinta had'e da kaunarta ALLAH yabaiyanata !kayita addua ALLAH yana tare da mai gsky insha ALLAH tana hannu na gari ,nima zantayaka addua insha ALLAH ,kaga inkaganta kobayan aurenmu saika rabu dani tunda ita kakeso ,nima saina auri yah Abbas ..,,,,
Shiru yah Suleiman yyi yana sauraren kalamanta wadanda bbu rashin kunya aciki sai ilimi da gsky had'e da ita shirya zance tamkar babba,azuciyarsa yace gsky yarinyar nan dg gani tanada ilimi gsky... amma wani gefen na zuciyarsa yaga kamar be kyautaba daya gayamata mgn haka ,yasandai ita bata da laifi kuma tanada Wanda take so,amma tayi biyayya zata auresa gsky be kyautaba ,ga wani dad'i dayaji jin tace tana kaunar angel insa kuma zata tayasa addua ALLAH yasa aganta"
Aiko in watace bazata damuba kodan sbd maganar da yaga yamata yanxun...muryarta ta katsesa gun cewa yah elee natafi tunda bazaka kulani ba nasan zakace nafiya shishshigi,ALLAH yabaka lfy ameen.....
Da sauri yabude idonsa dayyi jajir yace baby pls kada kitafi..
Ki zauna insanardake lbrin angel dina ko bakison ji ne?"
Ahankali tace inajinka ,amma azuciyar ta cata ke gsky yanama yarinyar nan kurman SO"
gyaran murya yyi had'e da ba baby lbrin ifti tun dg shakuwarsu da batanta da halayenta da shakwabarta da duk abinda take masa insuna wasa ta tsokanesa duk yabata labari dg karshe yace yanxun inna ce banason ko wace mace zakiga laifina?"
"Cikin tausayinsu tace ah ah "
Yace to inhar mgn ta tamiki ciwo ki manta da ita dan ko mummy mahaifiyarta inta batawa angel d'ina rai ina yin fushi da ita!
Baby tayi ajiyar zuciya afili tace ikon ALLAH naso inganta ita iftihal din..
Ahankali yace inkinaso ki ganta zan nuna miki pic nata Wanda tana karama ,amma ai nasan yanxun tazama babba dan yanxun shekarunta 15 years ..
Kafin baby tayi mgn Dr yyi sallama yashigo ..da sauri baby ta fice.
Dubasa yyi had'e da yimasa allurai ya rubuta masa mgni,had'e da kiran Yusuf yabashi takardar mgnin yace asiyo yasha in yaci abinci.
"Bayan Yusuf yatafi siyan mgnin sukayi sallama da Dr yatafi.
Yananan zaune yanata tunanin angel d'insa har Yusuf yadawo ,yahad'a masa tea mai kauri yasha ,sannan yasha magani.
Bbu jimawa bacci Yy gaba dashi..
*******
Bangaren zubaida kuwa duk atsorace take tana dubar kiran yah Yusuf amma shiru har azahar hakan yasa tayi tunanin k'ila sai marece tukum yamata hukuncin..
Baby ce zaune kusada Ummi ,Ummi na cewa oh natura tun dazun se acemun bacci yake Kodai baby kije kiduba kiga ko yatashi....
Kafin baby tace wani abu yah Suleiman yashigo parlourn da sallama ,har yadan fad'a saikuma yyi had'e da yin kyau..
Kafe juna da ido suke suna kallo," ahankali baby tace yah ileee nah sannu!(ta kwaikwayi yadda ifti ke cemasa dayabata lbri)
Murmushi yyi had'e da jin dad'in hakan danshi jiyake tamkar itace sbd Sak muryarta yaji,besan sadda yazauna kusada itaba..
Ummi dketa kallon su tana murmushi tace babana ya jikin?"
Dan Sosa kai yyi yace da sauki dan yama manta daa gabantane.
Ummi tace to Alhmdllh! baby kamasa abinci tunda su Fatima na islamiyya,bbu musu ta tashi ta nufi dining area, ita kuma Ummi ta fice...
Komai da komai baby ta shirya masa kamar yadda ta lura yan gidan nayi haka itama tayi.
Bayan tagama serving nasa tace to yah else oya kaci abinci kasha mgni!
Ahankali yace my angel rigima kixo.....shiru yyi sbd tunawar dayyi Ashe ba ifti bace watace .
Cikin shagwaba ta ce nima fad'a ,sai kayi mgn kayi shiru...
Cikin damuwa yace kixo muci tare!
Mak'e kafada tayi had'e da cewa um um saika fadamun, tafada had'e da ihun kuka tana dire dire Wanda duk shagwaba ce zalla...
Cikin kasalallar murya yace oh baby haka kike da rigima kuyimun shiru ALLAH kada raina yabaci ,dan bazakiji da dadiba !
Batace komai ba sai hawaye take"
Afili yace oh yah salam ke kuka be miki wahala ne ?"
Hannunta ta sa ta share hawayen ta !ahankali yace inkina sakemun kuka zamu bata dake ,amma gayamun meyasaki kuka?
Cikin murguda baki tace bakai bane ,ahankali yace banason surutu in bazakici saniba shikenan.
Koda taga kamar beji dadiba saita zauna suka faraci har suka idar kowa da tunanin dake ransa..
Tashi tsaye yyi bayan ta kwashe kayan "ahankali yace baby muje kirakani ko k'ofar dakina nane sauki dawo ko?
Bbu musu ta bisa ,yyinda Ummi da ta sjigo taji yana cewa Tara kasa ,tayi murmushi afili tace hmmm Yaro Yaro ne dg shi har ita na lura Suna son junansu,to ALLAH yakara daidaitasu..
Bangaren mlm kuwa....
Share
๐๐mmn fareesa ceโ๐ปโ๐ป
AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story &written by mmn fareesa
๐
ฟ65&66
"Bangaren mlm kuwa be iso gd ba sai gurin karfe 2:30pm" tun a cikin farkon shiga k'auyen yake sanar da jama'a anga nah nah"nanfa aka yita masa murna da jaje,da haka yyi sallama agdnsa...
Kuluwa da atine na tsakar gd zaune "bayin ALLAH " kullum suna ta tinanin yaya mlm yake da saa ko bbu??"
Cikin murna suka amsa sallamar had'e da mikewa tsaye sukace ya zauna !ko zaman beyiba yace masha ALLAH anga nah nah.... Ihun murna sukayi tamkar wasu yara,yyinda mlm yyi murmushi ya zauna yasha ruwa suka gaisa had'e da yiwa juna murnar ganin nah nah... Nan mlm yace ina Jidda?"
Kuluwa tace natanan!taje rafi debo ruwa.amma meyasa bakazo da nah nah ba mlm?"
Mlm yyi gyaran murya had'e da zayyane musu komai da komai game da loosing memory da ta yi da auren ta da yabada da alfarmar da suka nema abarta,gunsu dh karshe yace zasuxo Neman auren ta nan sannan Ku kuma karshen satin nan zankaiku Ku ganta!
Kuluwa tace ALLAH Sarki ,ubangiji kenan me yadda yaso da bawansa amma mlm inaga yakamata gsky insunxo Neman auren musanar