Author : Maman Fareesa Category : Romance
tayi ganin zubaida dasu Fatima sun nufota hakan yasa da sauri ta zura aguje had'e da fadawa jikin su tana kuka.
Hannunta suka ja ,kasancewar su ummi sun tsaya agefe suka kaita gun ummin.kama hannunta Ummi ta yi tace muje kinji y'ata amma dan ALLAH kada kisake yunkurun guduwa....da sauri yah Suleiman yace yo tama sake mana" d'agowa baby ta yi cikin SAA suka hada ido da shi wata uwar harara ta gallamasa,mamaki sosai tabasa baki sake yake kallonta har suka fara tafiya itada Ummi jamaa na binsu ,yyinda ko wanne saurayi da partner d'in sa, yaseer ne kawai baya ciki ...
Kwafa yyi afili yace wlh zan kamakine yarinya....
Bayan sun dawo Ummi da abbu suka bata hakuri akan kada tasake irin hakan tace to had'e da basu hkri itama.
Shikuwa gogan lunch yadiba yanufi part d'in sa, yyinda Yusuf zubaida ta manne masa har Ummi na mamakinsu dan tasan basa shiru ,amma data tuna ikon ALLAH saitadaina mamaki..
********
da misalin karfe 7:40 pm ummice tare da abbu zaune awaiting parlou byn yagama cin abin dare .
Kallonta yyi had'e da cewa dazunfa munyi waya da mutanenki!tace kai dan ALLAH "yace eh saura 7days sudawo Nigeria dan haka kinga da jibi abdullahi zasuie garinsu yarinyar nan nemawa Suleiman auren ta ko?" Tace eh"
Yace to na fasa sai dadynsa yadawo suje da shi atare,shima kuma haka yace dan kansa zai nemawa dan lelen nasa aure..
Murmushi Ummi ta yi tace oh ikon ALLAH to ALLAH yamaidosu lfy yasa kuma alkhairi "
Abbu yace ameen yah rabbi, kinga nima da angama maganar auren yaran nan nima zan angwance๐
Harara Ummi ta masa had'e da cewa kai mijin mace dayane rak....da sauri yace maida wukar Rabin ran ina ni ina wani aure haka natsufa...sallamar yah Suleiman ce ta sa abbu yyi shiru ,gaidasu yyi had'e da cewa Ummi baby fah?"
Harara ta bankomasa tace kafini sanin inda take dg nan tabi abbu part din sa tabar yah Suleiman zaune shi daya..
Motsinsu yaji adakin yara ,tashi yyi had'e da tamke fuska yanufi k'ofar dakin...baby nagaban mirror tana cire yan kunne kanta bbu Dan kwali gyaran gashinta yyi kyau gwanin sha'awa gashi bak'i kirin tayi parking dinsa..yyinda su Fatima da Habiba sai santin gashin suke .....tsaya wa yyi dg bakin k'ofar yakafeta da firgitattun idanunsa yana ta kallon gyaran kan da aka mata yana tunanin yaushe taje aka mata shi...
"" kamshin turaren sa dataji ,yasa tagane ko zaishigo dakin ne ko kuma yana ciki,da sauri ta juyo sukayi 4eyes da shi,ashagwabe tanufi gunsa ...
Yyinda su Fatima suka bar dakin byn sun gaidashi..
Ayadda yaso yyimata masifa ,amme me besan meyasaba sai yakasace mata komai yanadai ta kallonta....cikin dire dire had'e da shagwaba ta ce ni yanxun ice cream zansha da fura,kaji yayaaaaa?"
Ta fad'a had'e da kukan shagwaba, aigaba daya jinsa yake wani daban ga kasala da mutuwar jiki sun tasanmasa be shiryaba.
Ahankali yace naji iya dama abinda kikema rigimar kenan?"
Da sauri ta ce to sai kuma irin biscuit d'ina nadazun Dana bari a office naka shima kabiyani abuna....ta fad'a had'e da murguda baki.
Murmushi yyi yace ah ah bazan cigaba sai kin fadamun miyasa kika gudo dg office dina nayita nemanki kika d'agamun hankali,yanxun baby kin kyauta nama lura kinfison kirik'a batan rai ko?"
Cikin sanyin murya tace to yaya dan ALLAH ka yi hkri bazan komaba ,amma gsky bazan koma zuwa office nakaba"
"Da sauri yace meyasa?"
"Tace sbd wannan me kirar samudawan tasaka kazamar k'afarta aciki"
Murmushi yyi wai Sumy ce me kirar samudawa,Ahankali yace ban yardaba to nida gobema tare zamuje nakaiki amiki lalle ma dg nan .
Turo baki tayi tace um um Fatima zata kaini,had'e rai yyi yace to goben innace muje kice baki zuwa manah..
Batayi mgn ba ta nufi k'ofar fita.... da sauri yarik'e hannunta had'e da cewa wai miyasa kike son batamun rai ne?"bacin yanxun kikaban hkri amma gashi kin koma..
*cikin sanyin murya tace nadena muje kaci abinci tukum"ahankali yace to kokefa amma bbu kodan murmushin nan,kallon sa tayi suka hada ido state sukayi murmushi ..
Zama yyi kan carpet tayi serving dinsa da ruwan semonvita miyar kubewa busassa.
Ta aje masa hade da zama kusa da shi yyi bissimilla yafara ci..
Ahankali yace baby bara nakira k'asim(yaronsa ne) yakarbomiki ice cream dinko?" Ko nikeso nasiyo miki?"
Cikin sanyin murya tace bazanso Yayana yawahalaba katurasa yakarbomin.
Cikin jin dad'in maganarta yakira kasim yasanardashi abinda zai karbi,kafin ya idar da cin abincin yakawo ,nan tasha komai awadace ,anan take ta basa labarin taje saloon da kanta,Wanda yyi mamaki sosai, harda dungure mata kai yyi wai aita wahalardashi gun nemanta.
Cikin wayo itama ta kai hannunta kan karan hancinsa taja da gudu tabar parlourn bbu shiri tana masa gwalo....dan yyi kokarin kamata ta gudu..
Wayarsa yadauka yana murmushi had'e da cewa hmmm baby mejan fada zan kamaki gobe..
Washe gari tun karfe 7:00amm yah Yusuf ya had'a kudin hannunsa 30k yanufi station din.
Byn yaje yasanar dasu gun wacce yazo ,anan Wanda case din ke hannunsa ,yabukaci akawo dubu 20 din na ba shin sannan yyi signing bbu musu Yusuf yyi ,dg karshe akace sai yabiya dubu goma na ciyarda ita da bata magani dasukayi,bbu musu yabiya dama 30 k ne yazo dasu..
Anan akaje aka cewa mm zulai ta fito ansallameta,wani farin ciki ta ji da murna tasan yaseer ne yazo yyi beling nata.
Fitowa tayi jiki asanyaye duk tayi baki ta rame acikin kwana biyun.
Tana fitowa dg cel sukayi 4eyes da yah Yusuf....
Bana bukatar tanx ko stickers dawasu surutai comments kawai nake bukata inna ga ruwan comments acigaba inkunji shiru to kadama kuyi jaje ..
๐๐. Mmn fareesa ceโโ
[6/24, 2:16 PM] Mmn fareesa: AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
story & written by
Mmn fareesa
Inajin dad'in comments naku sosai da sosai kamarsu...
Salma l y ,Maryam
Musa ,mmn samha,
Miss fatisah,mmn
Ibrahim,
meenal mohd,
Fatimatou,khadeejart,
Aysha aliyu,ummu
Amra,
Maimuna,mmn mashkur,
Haima mmn Abdul,
Aishatou, hjy faty
Khady,mmn zannur.
Ummi dentiest,
Mom iman&h...
Zainab s Usman
Amina ay.....
Da duk wacce bataji sunanta ba ngd sosae๐ป๐ป
๐
ฟ79&80
NOT EDITED
Tana fitowa dg cel sukayi 4 eyes da yah Yusuf! "
Sake ware idonta tayi dan tagane shin shida wani yazone ko kuwa gizone idonta ke mata?"
Amma me ?shidai din ne yana mata kallon tausayi..
Mamakine kwance afuskarta had'e da tambayoyi aranta!
Koda yalura da yanayinta matsawa yyi gunta yana cewa mama sannu!mutafi ko"ahankali tace Yusuf wayazo beling nawa?"dukar da kai yyi yace NINE!
Da sauri ta d'ago kai had'e da cewa Kaine Yusuf?" Yace eh mama muje gd ki huta ko"jiki bbu lakka tabisa yabude mata mota ta shiga, shima yashige had'e da Barin gurin.
Tafiya suke bbu mai mgn ,can mm zulai dketa mamakin waye yasanar da Yusuf har yatausaya mata yazo dubata yyi belling nata Wanda ko y'ayan cikinta basuzo dubata ba!ahankali tace dan ALLAH Yusuf waye yasanar dakai halin danike ciki?
Kallon gefenta yyi yace ZUBAIDA ce!
Yaciga da cewa wlh mama suntayar da hankalinsu sosai itada Rukayya ,Nina bansaniba sai jiya da marece tasanar dani...mamaki ne aran mm zulai, shin sun manta abinda ta musu?wata zuciyar tace hmmm danma basu San cewa kece silar batan iftihal ba.
Jitayi gabanta ya fad'i.... Amma har cikin zuciyar ta ta ji dad'in yadda su zubaida suka damu da ita, saidai tayi mamakin rashin zuwan yaseer yyi belling nata,kuma bataji yace yaseer din yadamuba.
"Ahankali tace YUSUF !
Be kalletaba yace na'am tace nagode sosae ALLAH yyimaka albarka yasa kagama da duniya lfy ..
Cikin jin dad'in addu ar ta yace ameen yah Allah.
Cikin kuka tace dan ALLAH kuyafemin kuskeren danayi abaya sbd son zuciya da zugar muguwar k'awa nayi nadama dan ALLAH Yusuf kaso zubaida ka kulamun da ita ,duk da nasan kana kokari gurin tarbiyyarta.
Ajiyar zuciya yyi yace bbu komai mama indai dan nine kuma insha ALLAH zancigaba da kulawa da ita..
Ahaka yyi parking kasancewar sun shigo gd.
Tana fitowa dg mota saiga zubaida da gudu itada Rukayya suna kuka suka rungumeta,itama kukan take ,yyinda Yusuf ke tsaye yana kallon su cike da kula wa hade da tausayi.
Sakinsu tayi had'e da cewa su koma ciki ita gurin Ummi zataje.
Zubaida gun yah Yusuf ta nufa, Rukayya tayi part din su,yyinda mm zulai ta wuce part din Ummi..
Zazzaune suke kan dinning suna break Ummi da abbu na k'asa bisa carpet suna break fast.
Sallama ta yi jikinta asanyaye koda tagansu ,itama sai ta tuna dafa haka suke zama itada abba! Ummi ta amsa sallamar fuska asake sbd tabata tausayi ganin yadda ta koma akwana2.
" sannan taga alamar nadama afuskarta"
Dukawa tayi tagaishe da abbu sannan suka gaisa da Ummi,nan suka mata jaje, su Fatima ma sun gaida ita sukabar parlourn.
Suna fita tafashe da kuka had'e da rike hannun Ummi ta na Neman yafiyarsu had'e da abbu,nan suka ce sun yafemata,atake tanemi alfarmar yakira Abba yazo sutayata bashi hkuri.
Haka kuwa akayi ,byn yazo yana ganinta yadaure fuska ya jiya dan komawa ,abbu yadakatar dashi yazo yazauna.
Nan cikin kuka mm zulai ta nemi gafararsa had'e da yimasa alk'awarin gyara halinta kuma tarabu da Laure..
Bbu yabo bbu fallasa yace ya yafe mata ,yafice dg sashen.
Ummi ta hada mata tea mai kauri had'e da sinasir da niyar taushe tace taci,bbu musu ta hau ci sbd tsohowar yunwar datakeji.
Byn ta idar tayi godiya had'e da komawa sashensu.
Wanka ta yi had'e da brush ta shirya tasake yin wani break din nan take tambayar wai ina yaseer.?
Nan su zubaida suka sanar da ita yadda sukayi dashi aranar da aka kaita ceel.
Salati tayi had'e da cewa lallai yaseer abinda zai zakamun dashi kenan.
Hmmmm aidama abin ALLAH haka yake wadanda nak'i su suka fito dani....ALLAH ya isa tsakanina da Laure! Itace tasami hanyar banza amma kibarni da yaseer wlh zai Sani zaigane uwa tanada mahimmanci ga d'an ta..
Zubaida tace wlh mama yah Yusuf yagama mun komai arayuwa da ALLAH yasa yafito da ke dan gsky bazan iya rayuwaba inbbu shi ina mugun k'aunarsa..
Mm zulai ta ce wlh har abada bazan mance hallaccin yaron nanba wlh ,tunda yamun abinda d'an cikina yakasa yimun.
Hakafa sukayi ta jajen abun had'e dayima Kansu alk'awarin zama da kowa lfy agdn,sai dai mm zulai data tuna itace tabayar da iftihal hankankalinta na mugun tashi..
Yah sulaiman ne acikin mota shida baby...
Kuyi hkuri da Wannan bnida caji...
๐๐mmn fareesa ceโโ
[6/24, 7:05 PM] Mmn fareesa: AWESOME WRITER'S ASSO..๐ฎ
(palace of excitation and pleasant writer's)
INA TARE DA ITA!
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
(bansan ita bace)
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
Story & written by
Mmn fareesa
wannan shafin nakine maman feenat kiyi yadda kikeso dashi sbd ke akayisa ina mugun jidake over๐ป๐ป
๐
ฟ 81&82
Yah Suleiman ne acikin mota shida baby "ahankali yace baby yau zanyi tfiya zuwa Lagos.....katsesa tayi da cewa amma tare da ni zakaje ko?"murmushi yyi ganin kuruciya ce atare da ita, yace ah ah nima yau da safe akasanar da ni sbd tafiyar gaggawace ,kuma kinga koda akwai aure atsakanunmu bazanje dakeba duk da kwana5zanyi acan, to balle bbu sbd had'arin gurin kiyi hkri kinji baby nah" batace komai ba ta sharesa"
Shiru sukayi har yagaji yyimata mgn wai baby meye haka? "Yakikeso nayi da raina ne wai?" kanta tad'ago saiga hawaye sharr afuskarta a time din kuma yyi parking.
Kallon ta yyi "ahankali yace pls kidena kukan kinji?"
kishare hawayenki nida nikeso kik'aramin karfin gwiwa saiki kuma Sani acikin tunani"yafada had'e da Ciro hand chief mai kamshi yafara share mata hawayen.
Saiso yake su hada ido amma taki yarda"ahankali yace baby bazakimun mgn ba kenan?"
Ahankali tace ah ah yaya ALLAH yatsare yabada SAA kuma insha ALLAH ko byn katafi zan dunga maka addua ai,murmushi yyi had'e da Jan hancinta yace yauwa wana kama? "kingama yimun gwalon " marairaicewa tayi had'e da shagwabewa wai yyi hkri kadaa yyi latti anajiransa,girgiza kai yyi yace hmmmm aizandawo zankamaki ai ,yanxun bara mufita asamu Yaro yamun mgn da meyin lallen sai insanar da ita tamiki bazan jimaba zan dawo"
Fitowa sukayi dg cikin motar adedenan wasu yara zasu wuce nan yaturasu sukira meyin lallen dan dama acan ne akema angel insa lalle kafin ta bata!
Kallon ta yyi byn yatura yaran yace mekikeso na siyamki?"murmushi tayi tace bakomai yaya nagode sosae da yadda kake kulawa dani....katseta yyi da cewa nikuwa da waya zansiyamiki domin inkiraki inji yaya yan gd da abinda gidan yake ciki kinsan su mommy wato mahaifiyar my angel d'ina sun kusa dawowa wlh amma sai sundawo da kwana1 zandawo insha ALLAH..
Wani fad'uwar gaba taji hakan jin yace sunkusa dawowa,amma afili sai tayi y'ar dariya tace to masha ALLAH gsky ina tayaka murna ALLAH yadawo dasu lfy"cikin jin dadi yace ameen "sannan yace to amma tunda kince bbu komai nafasa siyan wayar....be ida karasawaba tasaki ihu..har saida yatoshe kunnensa ,tana dire dire... Anan kuma me lalle tayi musu sallama dan ita azatonta anga ifti sbd kamarsu datagani d baby"
Byn sun gaisa tace oh ranka yadade' rabonka da gidan nan tun kafin abin nan yafaru ,amma natayaka murna Ashe anganta?"sai asannan yah Suleiman yafahimci Rana zaton angantane ,girgiza kai yyi atakaice yace ah ah ba ita bace...
Sannan yace pls kimata lalle yyi kyau nanda awa1da Rabi zandawo,amma ki kula da ita kada ta fito ko ina,matar tace to ai kasan itama waccen ina kulawa da ita alokacin, bece komai ba yafito da kudi yabata had'e da duban baby dke turo baki gaba yace oya kuje amiki yanxun kinaso Kisa nayi latti zaki tsiro da wata rigima taki..
Itadai mai lalle gaba tayi dan azatonta matarsace,"ahankali baby tace pls yaya wayar....katseta yyi da kinasone?"tace eh" to shikenan naji oya shige kuje...
Bai bar gurinba said a ta shiga gidan..
Kai tsaye barrack dinsu ya wuce yaje suka gudanar da meeting akan tafiyar tasu ,sannan yawuce office din cpt salim (babban amininsa)
Samunsa yyi yana harhada papers yazauna sukayi musabiha ,yah Suleiman yace to mayen sumayya harda kai zaa naga bakaje meeting bako?"
Murmushi salim yyi yace hmmm naji koma meye zakace kasan kuwa sbd ita nak'i zuwa meeting sbd kawai naga wucewarta..tsaki yah Suleiman yyi yace wlh kai anyi dan iska!kana bada maza wlh ....murmushi cpt salim yyi yace eh naji tunda nibakai bane mata nacewa suna sonsa amma yanak'i,Ima ni nasamu damarka,yanzun yarinyar nan sumayya Dana kwallafa raina akanta tuni Nagano kai takeso kana tozartata amma ta na nunamaka k'auna,nikuwa ko ganina tayi saita canza hanya sbd tsana da kiyayyar datakemun,amma kullum sonta k'aruwa yake araina,WHY.....yafada had'e da dafe saitin zuciyarsa.
dariya cpt Suleiman yafashe da ita daya tuna baby tacewa Sumy basamudiyya!shikuwa salim yakule da haushin yah Suleiman "ahankali yah Suleiman yashe wlh shawarar dazanbaka kadena wahalar da kanka gun basamudiyyar yarin yar nan wlh ka kama kanka mlm kaja ajinka , gaka da kyawunka da komai amma kana bada maza...akule cpt salim yace mlm ya isa haka sbd rashin k'auna har suna kama rad'a mata !
Dariya yah Suleiman yyi yace ah ah banina saka mata ba ,watace tasamata!tsaki yyi yace hmmmm dasanta Dana fasa mata baki....Harar da yah Suleiman ya aikomasa dashi yasa yyi shiru.
Rage kafad'a yah Suleiman yyi yace inkaji shawara ta fine k'ila ma hakan yasa tasoka ,inzaka tafi muje karakani nasiyawa my baby waya nakuma Dakota gdn meyin lalle..
Da mamaki cpt salim yace oh abokina ka kamu kenan?" Tunda gashi kana fadin my baby....katsesa yyi da cewa look mlm dan nace my baby shine yake nufin sonta nike?"
Baka fahimci soba ,nidai nasan nashaku da ita ,sannan maganar so kuwa IFTIHAL nake yiwa SO d'aya aduniya,yanafadin hakan yamike had'e da cewa inxaka muje inbazakajeba kaga tafiya.
Murmushi cpt salim yyi yace hmmm intayi wari maji kada kamanta anan kake cemun kagaji same tabin hankalin nan gashi harta warke,to kadaiyi rainonta in anyi auren dukda bansan taba nasan tama karanta bazata iya daukar kaba.....tsaki yah Suleiman yyi yace aidayake aka cemaka ni Kaine mayen mata,inma kayi Wannan tunanin kacanza dan ANGEl dina natanadarwa kaina insha ALLAH...
Yana fadin hakan yafice ,cpt salim yabisa yana murmushi dan yasan halin aminin nashi inya botsare...
********
Gurin siyar da waya yatsaya yazaba had'e da darjewa me tsadar gske yasiyawa baby da sabon sim card da memory, shidai cpt salim na kallonsa yanaso yyi mgn ganin yasiya mata wayar dubu dari da sittin, kuma natafi 15 years ba yana ganin tamata tsada ,ganin yadda yahad'e girar sama da k'asa yasa yashare kawai..
Sai da yasiya mata ice cream tukum suka nufi gidan kunshin.
Sunayin parking tana fitowa dg gidan Dan hartagaji, da jiransa,aita na ganin motarsa da sauri ta nufo gun motar.
Shikuwa cpt salim tasbihi yake sbd ganin baiwar kyawu nata ,aransa yace wlh abokina yakamu da son yarinyar nan be auneba yaga cpt Suleiman yafito...
Lamar zata fada jikinsa ta je gunsa tana shagwaba r tagaji da jiransa harta fito,girgiza kai yyi yace oh baby wlh yau kinason samun ciwon kai sbd rigimarki ,yanxun banadawoba,shine kika fito salon ki koma guduwa ko?"yafada had'e da tsareta da idanunsa masu kashe mata jiki yana kallon lallen da aka mata ,tsintar kansa yyi da jin haushin cpt salim yasan kilama yafito yana kallonta....
Da sauri ya waigo aiko yaganshi jingine da mota yana kallon su kamal TV ,shikuwa cpt salim da ma soyake yagano wani abu kuma yagano sbd kishin daya gani k'arara a icon cpt Suleiman..
Juyawa yyi dan komawa cikin motar ,yah Suleiman yace baby ga aminina nan kugayyasa cpt salim,cikin sakin fuska had'e da jin kunya tace ina wuni!"dan Batman tare sukeba said a yyi mgn tukum .
"Ahankali yace lfy lau amaryarmu