Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   75 / 117

222K to 225K   out of 348.6K words

ya ciro jiya ya sa a aljihunsa sannan ya fita ya kulle dakin, a adaidaita ya isa gidan Ramlah, bayan ya sallamesa ya shiga ciki yana amsa gaisuwan mai gadi, ya wuce parking space, yana tsaye a nan ya shiga kiran Ramlah, bayan ta daga yace "Ki fito min da makullin parking space" tace "Yaya baxa ka shigo ba?" Yace "Ehh" tace "To bari in fito" ba a dau lkci ba ta fito rike da makullin motar, tana murmushi ta nufi parking space din ta risina ta basa tace "Ya hanya yaya?" Yace "Alhmdlh, ba sae kin ce masa na dawo ba" tace "Toh Yaya" bude motar yyi ya shiga yyi warming dinsa ita dai tana tsaye tana kallon sa, har daga karshe ta daga masa hannu ya fita da motar ita kuma ta koma cikin gida... Abuturrab ne xaune kansa a kasa yana sauraron uncle dinsa, Alhaji Lawal dake ta kallonsa da kyau yace "To ko dai kana shan wani abu ne wanda mu bamu sani ba Aliyu?" Shi dai bai ce komai ba, Alhaji Lawal yace "Dago ka kalleni ina maka magana" Ba musu Abuturrab ya dago kansa yana kallon Uncle din nasa, Alhaji Lawal yace "Tell me what exactly is wrong with u? Do we deserve being taking for granted Aliyu?" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aa Abba ku yi hakuri, kuskure ne..." Alhaji Lawal ya dakatar da shi yace "You called this mistake also Aliyu?? Baka tsoron Allah ne da xaka kara kiran wannan ma da mistake??" Sake baki Alhaji Lawal yayi yana kallonsa, Abuturrab bai iya yace komai ba, Alhaji Lawal na jinjina kai yace "Lallai baka da hankali baka da manners, ka kuma mugun raina mutane ka daukemu for granted, ashe dama kai ka haifa kanka bamu sani ba?" Abuturrab yyi kasa da murya with remorse yace "Don Allah ku yi hakuri Abba, i know i wronged u all, but this the only way out for me, Abba baxai saurareni ba, so is Ummi... No one will give me a listening ear" Alhaji Lawal yace "Ohk ni kuma sbda ka yi shegen raina ni yanxu kake tunanin xan baka listening ear?? No... I am not giving u dat, and i am sorry babu wani abu da xan iya yi" Abuturrab ya kasa ce masa komai, Alhaji Lawal yace "I can't do anything about this... ina ce ita wannan yarinya idan ban mance ba babu irin hakuri da ban bakin da bamu baka ba a kan ka xauna da ita, ashe ka maida mu shashashai ne a lkcn ka je ka saketa kuna ta xama tare duk don sbda kana ganin ita ba class dinka bace or whatever, bugu da kari kuma u bluntly admitted baka sonta, to yanxun da ka koma ka aikata shirmen da ka aikata son nata ka fara yi kenan???" Nan ma dai Abuturrab bai ce komai ba, Alhaji Lawal ya daka masa tsawa yace "Bude baki ka bani amsa my frnd.. i am talking to u" A hankali yace "Ina son xama da ita yanxu Abba" Alhaji Lawal yace "U are very stupid, ae ba tambayar da nayi maka ba kenan.." Kasa basa amsa Abuturrab yayi nan ma, Ganin yanda Uncle din nasa ke kallonsa ya sunkuyar da kai, Alhaji Lawal yace "Toh ka saka a ranka cewar kamar yanda muka xaunar da kai kwanaki muka baka takarda da biro ka datse auren naku wannan karon ma hakan ne xai faru, mu ba 'yan banxa bane da xaka dinga controlling dinmu yanda ka so, kana aikata duk abinda ya xo kanka without our consent, we birth u..." Abuturrab ya marairaice masa yace "Abba don girman Allah ku yi hakuri, wllh ban koma na aureta da nufin in cuceta bane wannan karan, wancan lokacin ma kuskure aka samu, don Allah Abba kayi hakuri, i mean no harm to her..." Alhaji Lawal yace "Da nufin me ka koma ka aureta yanxu? Bani amsar tambayar nan" Abuturrab yace "Ina son xama da ita ne na har abada" Alhaji Lawal ya girgixa kai yace "Kamar dai yanda na fada you are very stupid, kawai ka koma ka aurota saboda kana son ku xauna tare har abada, wait!! are u mad??" Abuturrab yace "Abba ni dama fa ban ta6a buda baki nace bana sonta ba, kawai sharrin shaidan ne da kuma yanda kowa baya son auren shi yasa na aikata abinda na aikata, amma wllh ban ta6a cewa bana sonta ba" on a serious note Alhaji Lawal yace "Daga Hajja a rashin alkibla sai kai, anyway... I am so dedicated today, don haka idan Allah ya amince mana gobe xan shiga kadunan, xaka iya tafiyar ka sae na xo goben..." A hankali Abuturrab yace "Xan jira mu tafi tare goben in sha Allah" Alhaji Lawal yace "Allah ya kai mu" Godiya Abuturrab yayi ma uncle din nasa sanan ya mike ya nufi kofa hoping this will be the only challenge he is to face till end, Alhaji Lawal ya bi sa da kallo har ya fita yana mamakin karfin hali da taurin xuciya irin na Abuturrab, kiri kiri yayi ta abu ba tsoro. Abuturrab ya fi minti daya tsaye kofar parlon Abbansa ya kasa bude kofan, bai ta6a jin mugun shakkan Abbansa irin na lkcn ba, bai san me ya sa wnn karan ko Aunty baya jin ta kamar yanda yake jin Abbansa, ga bugun xuciyarsa da ya tsananta, it's been long da ya shiga yanayin nan da yake ciki yanxu, muryan Umma yaji a bayansa ta rike ha6a tace "Kai kuma yaushe a gari??" Ya juya da sauri, yyi feigning smile yace "Good evening Umma" tace "Saukan yaushe?" Ya d'an fara kame kame kafin yace "Jiya" tace "Ikon Allah, to sannu da dawowa..." Bude kofar parlon tayi, lkci daya fara'ar da ke fuskarta ya bace, ta wani sha kunu ta shiga parlon, tunda aka kirata aka ce ta xo gidan tayi tunanin xancen baxai wuce na auren da suke shirin laka6a ma Jiddah ba, kuma ta sha alwashin yau kam sae inda strength dinta ya kare, dai dai take da kowa, ganin Hajja xaune parlon ta wani kara daure fuska ta nemi waje ta xauna, Abuturrab ya shiga parlon kansa a kasa gabansa na mugun faduwa, xaunawa yyi saman carpet ya kasa kallon kowa, a hankali ya fara gaida Hajja kafin sauran occupant din parlon, Hajja dae fuskar nan nata babu ya6o bbu fallasa, Umma ma babu yabo babu fallasan tace "Ina yini Hajja" Hajja ta rike kanta tace "huhuhu wllh tun da naje Masar na samu saukin gaishe gaishen jaraban nan, yo kowa na ta kansa ina batun wani gaisuwa, su basa haka a can wllh, duk wayayyu ne, a kasar nan kowa sae yace sae ya gaisheka alhalin wani gaisuwar ma bai kai ciki ba, to ni dai na yafe, ko Usman ma ban amsa gaisuwarsa ba balle wani...." Ko kallonta Umma bata sake yi ba tana jan counter dinta... Alhaji Umar ne ya bude wajen da addu'a, sannan bbu 6ata lkci kuma babu boye boye in Brief Alhaji Lawal ya maimaita masu duk abinda Abuturrab ya sanar masa jiya a Zaria, Babu wanda bai girgixa ba a parlon, Abba dai kallon ceiling kawai yake, gaba daya sauran mutanan parlon kallon Abuturrab suke irin kallon tsoro, babu ko kiftawa, shi ko kansa na sunkuye xuciyarsa na bugawa, Hajja dae sae wani murmushi take me sauti irin na bosawa tana girgixa kafa da kai, Bayan shirun kusan minti biyu da ya ziyarci parlon, Aunty ta mike duk ta hada xufa daga sama har kasa tana girgixa kai tayi wani murmushin takaici tana nuna Abuturrab tace "Wllh karya kake Aliyu, karya kake baka isa ka kunyata ni ka toxarta ni, ka walakanta ni a idon duniya ba wllh... Karyanka ta sha karya wllh" kofa ta nufa ta fice daga parlon da sauri, Umma da Ummi har sannan hangame baki suka yi suna kallon Abuturrab, Hajja na kallon Abba a hankali tace "Yau da ace a Masar ne idan ba a garkame d'an ka a kurkuku ba shegiya nake Usman, ae wannan shine ta'addanci mafi muni da mutum xai yi a hukuntasa a kasar Masar, kai ba a ma ta6a haka a can ba wllh, Aliyu dai ya fita sahun mutanen kwarai, Aliyu mutumin banxa ne... Kiri kiri ya nuna ma d'an uwansa na jini bakin ciki, da hassada, ba fa son yarinyar yake ba kawai bakin ciki ya mayar da shi gun danginta ya sake aurota a gantale, su ma dai dangin nata matsiyata ne, kawai sun mayar da 'ya kaza don yaje yyi masu fafan yana tukin jirgin sama, to meye kuma tukin jirgin sama Allah na tuba abinda matsayinsa da d'an acaba da d'an taxi daya a idon duniya, wato sbda hassada sai ya ga ta yanda yarima zai aureta ko??" Cije yatsa Hajja tayi sae kuma ta rushe da kuka tace "Wllh mun fi awa biyu da mutumin nan muna garari a hayin rigasa, katon ya gilla min karya wai an rushe gidansu Jiddah daga karshe ma gaya maka ne kawai ban yi ba Usman wllh a tsakiyar titi ya yasar dani yyi wucewarsa kamar mara galihu duk na hada xufa, har ya kai ya kawo mutane suka xata almajira ce idan an xo wucewa sae a mika min ashirin, goma...." Sosai Hajja take kuka tace "Ni a tarihin duniya ma ban ta6a jin an haifi me hali irin na Aliyu ba, kuma a bisa dokan Masar duk wanda xai iya aikata abinda ya aikata to xae iya kashe rai babu ko darrr, shi yasa ma ake garkamesa a gidan gyaran hali, ni dae xan xuba ido kawai in ga hukuncin da xaka dauka a kan wannan d'a naka Usman, dalilin abun nan da Aliyu ya aikata sae zumunci ya tarwatse ya daidaice ya lalace wllh, don ba Yarima kadai ba.. hatta mutan Bauchi sae sun kullaci Aliyu, daga nan kuma sae a fara gaba tsakanin Bauchi da kaduna, to wa xai so haka??" Ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kwance ha6ar xaninta tana salallami, ta mike ta fice daga parlon tace "Tirrrrrr" A karo na farko Abba ya kalli Abuturrab da har sannan ya ki raising kansa, Abba ya gyara xama speaking calmly yace "Yanxu kai ka tabbatar ka koma an sake daura maku aure da yarinyar nan Aliyu? Are u very sure about this" Sai a sannan Abuturrab ya daga kansa ya kalli Abbansa amma ya kasa cewa komai, Abba yace "I'm asking you...." A hankali yace "Ehh Abba" Abba yace "To da yaushe kaje aka mayar da auren?" Cikin sanyin murya Abuturrab yace "Before i got married to my recent wife..." Abba ya gyada kai yace "Ohkk that's good, wani sadakin ka kai kenan?" Abuturrab ya sunkuyar da kansa yace "Ehh" Abba yace "Nawa ka kai?" Abuturrab ya share xufar forehead dinsa yace "150k" Abba ya gyada kai cike da gamsuwa yace "Ohkk that's fine" Ummi ta rike ha6a tana kallon Aliyu da abinda ya fi mamaki, Umma kam dariya ma abun ya fara bata sai taji kamar film, hakan yasa bata san sanda ta dinga murmushi ba tana gyada kai, Mikewa Abba yayi Abuturrab ya bi sa da kallo kamar idanuwansa xa su fito ganin ya nufi bedroom dinsa, kallon Ummi yayi ya marairaice mata amma ya kasa cewa komai, gaba daya hankalinsa ya tashi sosai, ita kuwa sai kallonsa take har sannan tana rike da ha6a, Abba ya fito daga dakinsa rike da paper and pen, Alhaji Lawal ya dakatar da shi yace "Let's talk first Alhaji Usman" Abba ya ajiye takardan hannunsa gaban Abuturrab kafin yace komai Abuturrab ya hade hannayensa cikin breaking voice yace "I am sorry Abba, wllh i can't, i can't plsss...." Ai bai jira mai Abba xai kuma cewa ba ya mike ya fice daga parlon, duk suka bi sa da kallo. Babu yanda Alhaji Lawal bai yi kokarin ganin yayi convincing Abba yayi hakuri da abinda Abuturrab ya aikata ba, he should calm down before making any decision... but all his effort prove abortive, har Alhaji Umar ya sa baki don ganin Abba ya janye wannan kudirin da ya dauka amma Abba ya ki sauraron kowa, kana ganinsa kasan ya hau sama sosai, Ummi dai sai kallonsa take haka ma Umma dake parlon har sannan, Alhaji Umar yace "Ka fahimce ni Alhaji Usman ba don muna tsoronsa ya sa xa mu saurara masa ba, akwai abubuwan dubawa da yawa...." Abba ya dakatar dashi yana girgixa kai yace "Kasan Allah Umar?? Wllh wllh sai ya saketa, wllh baxai xauna da ita ba, xan nuna masa i birth him...." Yana kai wa nan ya mike ya fice daga parlon......



*Masu neman littafin Jiddatul Khair complete sae ku yi payment ku xo ku sameni da evidence* =?G?
Wa.me/+2347087865788



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Allah ubangiji ya maimaita mana=??




Jiddah ce ta fara dauke idonta ta ci gaba da wankin da take a hankali, har ya wuceta sannan ta bi sa da kallo ta durkusa tana ci gaba da daurayan hijabs dinta, bayan minti goma ta gama ta shanya su sannan ta dauraye hannunta ta wuce cikin gidan, Xaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, su Maimoon na daki Umma ma na bedroom dinta, Huraira kuma na kitchen tana girkin lunch, ta karasa cikin parlon tana kallonsa a hankali tace "Sannu da xuwa..." Kallonta shi ma yake yace "Kema sannu" Xata tafi dakin Umma taji yace "I will be back later" Ta juya tana kallonsa, mikewa yayi ya nufi kofa ita dai tana tsaye har ya fita parlon. A hankali ta nufi dakin Umma ta yi sallama sannan ta bude, Umma na xaune tana waya, Jiddah ta xauna saman carpet ta jira har ta gama ta ajiye wayar, Umma na kallonta tace "Ya aka yi Jiddah?" Tace "Aa dama xan tambayeki sanda xa ayi awaran da kika ce ne" Umma tace "Au kinga ma na mance ni, duk sanda kika shirya ba matsala ki xo ki amshi kudin ingredients din, ke da Huraira ko Maimoon ku tafi kasuwa" Jiddah tace "Toh Umma" Daga haka ta mike ta fita daga dakin. Abuturrab na isa gidansa ya sauka daga d'an sahun da ya kawo sa, sai a sannan ya tuna ba shi da currency din kasar a tare da shi, ya nufi gun Mai gadinsa da ya taso yana welcoming dinsa da fara'a, yace "Ka basa dari biyar idan kana da shi" Mai gadin ya taho gun Mai adaidaitan da sauri xai basa kudin Abuturrab ya shiga cikin gidan, the compound looks so neat saboda yayi employing masu shara da gyaran flowers da ba su ruwa, yana isa entrance din shiga parlon ya murda kofar gently ya shiga ciki, kida ne ke tashi an kure sa har kusan karshe a parlon, ya dinga bin parlon that looks very untidy and unkept da kallo, ga plates sun fi kala biyar a kan carpet da duk ya baci da shinkafa da kwallin le???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?mo, kayan kallon da suka yi uban k'ura ya dinga kallo, ya kalli dining area can ma duk plates da cups ne da breads ko kulle ledan ba ayi ba, calmly yake tafiya ya nufi stairs, shi ma duk yana jin yana taka k'ura kasan tiles din, bangarensa ya tafi ya bude kofa, sun fi su bakwai xaune parlonsa nan din ma dai plates ne da kwalaye na ciye ciyen da aka yi, suna ta labari ga kida na tashi a parlon ma amma bai kai na parlor ba, Duk suka juya jin an bude kofa, Aneesah dake xaune kan carpet sanye da zani da ves a jikinta ta mike da mugun mamaki tana kallonsa tace "My Captain saukan yaushe babu notice? Mun fa yi waya jiya baka ce min kana tasowa ba" Bai sake kallonta ba balle ta sa ran amsa ya bude kofar bedroom dinsa, Safara'u dake parlon ita ma da daurin kirjin ta mike da sauri tana cewa "In ji dai bai gan ni ba??" Bata jira an bata amsa ba ta fice da sauri daga parlon, Kawayen Aneesah duk biyar din su ma suka mike suka bi bayanta suka bar Aneesah tana xaxxare ido tana bin parlon da yayi kaca kaca da kallo, gashi takasa bin sa cikin bedroom din, Abuturrab ya fi minti biyu tsaye yana bin bedroom din nasa da kallo, kaya ne ta ko ina a xube tun daga kan gado har kasan tiles da carpet, bayan kaya har da takalma, ga farin bedsheet din saman gadon har ya fara fita hayyacinsa duk ya yamutse, sababbin jakunkuna na kayan sa wa har uku ya gani jere a dakin su ma duk a wangale, tun da yake bai ta6a sanin bedroom na iya xama haka ba sai ranan, wannan ya wuce untidy ko unkept, har wani tsami tsami mara dadi yaji bedroom din ke yi, ga kofar bandaki a hangame, ya lumshe ido ya juya ya bude kofar
ya fita, har sannan Aneesah na tsaye sai wuwwurga idanuwa take, bai kalli direction dinta ba ya fice, wani dakin daban ya tafi ya bude ya ga Safara'u xaune saman gado wanda shi ma din duk a yamutse yake, har lkcn daurin kirji tayi, ganin sun hada ido ya gaisheta, bai jira amsa dogon gaisuwan da take jere masa ba bayan ta jawo zanin gado ta yafa, yace "Alhmdlh mun gode Allah" Daga haka ya fice ya kulle mata kofa, wani dakin ya bude ya ga kawayen Aneesah sun yi dai dai a dakin ya kullo kofar ba tare da ya amsa gaisuwansu ba, bai sake bude wani dakin ba ya sauka downstairs ya fice daga gidan gaba daya, Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kofar gida gashi babu cash a jikinsa babu Atm card, luggages dinsa kuma bai dauko daga airport ba, wayarsa ya ciro daga karshe ya shiga kiran layin Maimoon, tana dagawa bayan sun gaisa yace "Give the phone to ur frnd" Maimoon ta mika ma Jiddah dake gefenta waya, Jiddah ta amsa tana duba

75 / 117