Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   102 / 117

303K to 306K   out of 348.6K words

Har aka kira magrib bata ga Aneesah ta dawo ba, aka yi isha still tana ta xuba kunnen ta ji an bude gate an shigo amma shiru, wanka Jiddah tayi ta sauya kayan jikinta xuwa na bacci sannan ta kwanta gefe, she is just missing everything about Abuturrab so much, sau da yawa sai taji kamar lips dinsa a nata har sai ta kai hannunta bakinta, ta lumshe ido ta takure waje daya tana ta kwance har karfe goman dare, ta mike xaune cike da mamaki don har yanxu bata ji Aneesah ta shigo ba, a haka har bacci ya dauketa wajajen 11. Da asuba tana farkawa ta fito ta sauka downstairs don haka kawai taji hankalinta ya tashi ganin har bacci ya dauketa jiya Aneesah bata dawo ba, ta kofar parlon kadai xata san ko ta dawo ko bata dawo ba don in har ta dawo to xata kulle kofar parlor, ga shock dinta a bude taga kofar da ta murda, alamar ba a shigo ba balle a kulle, ta dinga kallon kofar a tsorace sai kuma ta juya a hankali ta koma sama. Gari na wayewa karfe bakwai Jiddah ta sauko parlor don bata jin dadi taga gidan so dirty, tunda ita dai ba me kiwiya bace, ga shi Aneesah da bakinta na jiya sun yi kaca kaca da parlon kamar yan yara, duk cake ne kan tiles da goran drink da ruwa, tana cikin sharan parlon aka bude kofa, daga kai tayi da sauri, Aneesah na ganinta ta hade rai taki yarda ta sake kallon inda take har ta haura sama, Jiddah ta bi ta da kallo tana ci gaba da sharanta a hankali, bayan ta gama tayi mopping xata kai bokitin waje sai ga Aneesah ta sauko daga sama da saurin ta again, atamfa ne a jikinta da mayafi sai handbag dinta sai xuba kamshi take, nan ma ko kallon Jiddah bata yi ba ta fice daga parlon tana picking call dinta tace "Kai Rabi'ah gani na fito yanxu, wllh na makara ne" Jiddah dai ta bi ta da ido don a bude ta bar kofar.... Bayan la'asar Jiddah ta fito kitchen kenan bayan ta wanke plate din da ta ci abinci, har sannan Aneesah bata dawo gidan ba, xata tafi sama ta ji an bude kofa ta juyo da sauri, Hajja ce ta shigo parlon ba ko sallama, Jiddah da ta ji dadin ganinta ta dawo parlon da sauri tana murmushi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Bari Jiddah ba wannan ne gabana ba, Ina mijin naki?" Jiddah ta girgixa kai tace "Ya tafi aiki ai" Hajja ta rike kai tace "Kashh, wai nan na shirya ne ya kai ni gidan kyauta ance min shi kadai ya san gidan a Barnawa tunda a lkcn da ya maida Hafsah uwarsa da ubansa kusan duk kwana biyu sai sun je gidan da shi da ita, yanda yake xuwa gidan ma ko gidan Ramlah bai xuwa... Amma wllh ban ji dadin wannan shegen aikin da ya tafi ba, wai fa daga na d'an kishingida in huta yanxu kawai sae nayi mafarki an kwama ma bakina katon kwado bana um bana um um, kuma ni kadai ke ganin kwadon babu me gani wllh, su Usman da Hauwa sun tsaya kai na suna ta hajja lafiya, Hajja lafiya, amma ina ba baki an garkame sae kallonsu kawai nake kamar bebiye, to shi yasa ban ga ta xama ba a xo a kaini gidan Kyauta ayi min iyaka da Hafsah, wllh da kyar idan baxan kai wannan xancen kotu gobe ba, don ya gigita ni shiga bandakina biyar kafin in xo gidan nan, yanxu haka xancen da nake maki sae na kara xagawa a gidan nan, ai ko dabba ba a kulle ma baki ba balle mutum" Jiddah dake ta kallonta tace "Hajja ai ana kulle na doki" Hajja ta saki baki tace "Toh ni doki ce? Ina ruwana da doki xaki ce min ana kulle na doki, ana maganar mutane me ya kawo na dabba kuma Jiddah? Kawai mata matsiyaciya ki nemi garkame min baki ban maki komai ba, wllh baki ga ba ko abincin kirki ban iya ci a kan wannan xancen yau kwana hudu kenan, kwatsam sai ga mummunan mafarkin nan daxu, kin ga kuwa ai ba lafiya, to tun kan a cuceni a mayar dani Bebiye gwara a xo a biya min tikiti in koma Masar bakina alekum" Jiddah dai sauraronta kawai take, Hajja tace "Shi kuma yaushe xai dawo daga gararin samaniyar tasa?" Jiddah tace "Kilan juma'ah ko asabar, Hajja ki xauna in kawo maki ruwa" Hajja tace "Wani ruwa bayan abinci ma wannan na kasa ci, meye kuma ruwa, naga alama kun dau wannan kess din karamin kess, wllh da a Masar ne sai an bata kwadon gaske ace ta kulle bakin nawa a gani, Allah sai an mata zindir an xane shegiya sannan a mika ma yara su yi ta jifa, me na mata xata min haka??" Tana kai wa nan ta nemi waje ta xauna tana fiffita xufar da tayi da mayafinta, Jiddah ta nufi kitchen dauko mata ruwa da lemo ta ajiye gabanta, Hajja ta dau goran ruwa daya sai da ta kwankwadesa tass, sannan ta ajiye tace "Rabona da shan ruwa tun kan inji wannan mummunan batun" Bude kofar parlon aka yi duk suka daga kai, sosai gaban Jiddah ya fadi ganin Abuturrab ya shigo parlon, suna hada ido ya dauke idonsa fuskar nan tasa a daure, ta sunkuyar da kai, Hajja ta kalli Jiddah tace "Kika ce min ya tafi aiki?" Kafin Jiddah tace komai yace "Ehh daga can nake" Hajja ta mike tace "Abinda Allah ya ga xuciyata ko daga sararin samaniyar ne ai sai a hankado min kai kawai, wllh ina cikin garari Aliyu, gidan Kyauta yayar Hafsah xaka kai ni a Barnawa don girman Allah" Abuturrab yace "Daga Abuja fa nake yanxu ko hutawa ban yi ba Hajja" Hajja tace "Oh oh Allah, Aliyu mafarki nayi an kulle min baki da kwado fa? Wa xai xauna da wannan mugun mafarkin idan ba gantalalle ba" Yace "Toh ki bari in huta na gaji, bayan nayi aiki kuma na sake shiga mota na taho kaduna" Hajja ta koma ta xauna tace "Toh tafi ka huta ko na minti sha biyar ne, ai ni ba bakuwar xafi bace, banda Ramlah ma bata san gidan ba ai ita nayi niyyar ta rakani don naga ita dai dai take da ko wani d'an banxa a duniya" Abuturrab bai ce mata komai ba ya nufi sama, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja tayi kasa da murya tace "Ina gantallaliyar abokiyar xamar ta ki?" Jiddah tace "Kila tana daki ban sani ba" Hajja tace "Atoh, ina ruwanki da ita da xaki san inda take dama" Mikewa Jiddah tayi tace "Ina xuwa Hajja" Hajja tace "Toh ni dai kar a shanya ni, ba ruwana da iskanci da rana tsaka" stairs Jiddah ta nufa, tana haurawa sama ta tsaya corridor tana tunanin ta je ko kar taje side din nasa, haka kawai ta ji tana shakkarsa sosai, bayan few seconds kawai ta nufi bangaren nasa tana tafiya a hankali, bude kofar parlon tayi kamar munafuka ta shiga ciki ta gansa xaune, ta karasa ciki ta d'an durkusa kasa daga gefensa ta ki yarda su hada ido tace "Sannu da dawowa" Ba tare da ya kalleta ba yace "Thank you" Kallonsa tayi a hankali, jin bai sake cewa komai ba ta mike ta nufi kofa ta fita ta koma wajen Hajja. Bayan minti ashirin Abuturrab ya sauko parlor kafin nan sai da ya bude kofar dakin Aneesah ya ji sa a kulle, kallon Jiddah yayi yace "Lend me ur car key" Ta mike tana kallonsa don babu yabo babu fallasa yayi maganar, ta wuce sama ta dauko masa makullin a dakinta ta risina ta basa, ya amsa yace "Tashi mu je Hajja" Hajja ta mike tace "Allah yayi maka albarka, mu je in ji ba'asin kulle min bakina" Kofa ya nufa tana biye da shi ko sallama bata tuna tayi ma Jiddah ba har suka fita, Jiddah ta bi su ta tsaya bakin kofa tana kallon Abuturrab, ya ki yarda ya kalleta, nan da nan hawaye ya kawo idonta, kamar ance ya juya ya ga hawaye a idonta, ya jefa mata wani kallo, turo masa baki tayi ta juya ta koma parlon da sauri. Abuturrab na ajiye Hajja kofar gidan Kyauta ya ciro dubu biyar ya mika mata yace "Hajja gashi idan xaki koma sai ki samu adaidaita sahu, ni yanxu xan koma aiki ne, nayi mantuwa ne yasa na dawo" cike da masifa Hajja tace "Yau naga jalala, dama ba da kai xa mu shiga ba ni kadai raina xan shiga?" Yace "Toh ni macece da xan bi ki mu shiga Hajja, excuse na dauka wajen aiki, jirgi na can a airport din Abuja xan daga xuwa kano" Hajja tace "Toh na fi jirgi ne? Ko ina ruwana da shegen jirgin naku? Sbda ba bakin uwarka aka yi niyyar garkamewa ba shi sa baxa ka bi ni mu shiga ba ko??" Dariya ta basa amma ya cije yace "Toh sai in bar aikina in shiga ayi ta xancen garkame baki da ni?" Hajja tace "Toh Allah ya isa, ai sbda kai da uwarka aka yi niyyar kulle min bakin nawa Allah ya toni asiri, kuma wllh daga yau ko kasheku naga xa ayi kai da uwarka shiru xanyi abina in koma gefe tunda gashi ta dalilinku aka nemi hallaka min bakin da nake salati nake ba Allah gaskiya" Daga haka ta fixge dubu biyar din ta shige gidan tana rafka wani uban sallama, dariya yayi ya juya kan motarsa ya dau hanyar gida. Yana komawa gida bayan ya haura sama dakin Aneesah ya bude ya ji a kulle har sannan, ya d'an tsaya sai kuma ya nufi dakin Jiddah ya bude, kwance ya ganta tayi kukanta ta koshi, ta mike xaune tana kallonsa ya wani hade rai, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" yace "Ban yi ba" Tura masa baki tayi ta juya masa baya, ya shafa kansa yana kallonta, sai kuma yace "Ina Aneesah?" Ta kallesa a hankali tace "Nima ban sani ba" ya karasa dakin ya rungume hannunsa yana kallonta, lkci daya ya dauke idonsa daga kanta, yyi kasa da murya yace "Make me a cup of tea" daga haka ya juya ya fita, ta mike a hankali ta fita ita ma ta sauka downstairs. Bangarensa ya tafi ya dauko spare key ya bude dakin Aneesah thinking ko kulle kanta tayi a ciki, amma babu kowa dakin haka ma bathroom din... A ranan Abuturrab xai koma Abuja don ko awa biyu bai yi niyyar yi ba a gidan, but ya kasa tafiya yana ta xaune parlor downstairs yana jiran ya ga sanda Aneesah xata shigo gidan, Jiddah ta fito daga kitchen tana kallonsa tace "Na gama in xubo maka yanxu?" Ya daga kai ya kalleta yace "Tun yaushe Aneesah ta fita gidan nan?" Ta d'an buda hannunta tace "Nima ban sani ba ina daki" Yayi shiru, ta koma kitchen ta xubo masa girkin da tayi ta fito ta ajiye masa kusa da shi, kallon kirjinta kawai yake da ta durkusa ajiye abincin, ya lumshe idonsa ya jinginar da kansa jikin kujera, don ba karamin nesa yake kai xuciyarsa ba a kanta tun daxu, barin da ya shiga dakinta ya ga tana kuka he wish he can hug her tightly and tell her he isn't angry and he is back all because of her, ta mike tana kallonsa ta wuce sama ta shiga dakinta ta xauna tana tunanin yanda xata yi Aneesah ta san ya dawo gidan, mikewa tayi ta tafi bangarensa tana kallon wayarsa da ya bari kan kujera, dauka tayi ta kulle kofar parlon, ta shiga call logs dinsa amma bata san yanda yayi saving number Aneesah ba, Blossom ta gani can kasa nan da nan ta tuna ta ta6a ganin sunan a phone dinsa da dadewa tayi dialing number, yana fara ringing aka daga.....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Karfe goma saura Jiddah ta bude kofar dakinta a hankali ta dalilin yunwan da taji ya dameta, tun da taga fitan Abuturrab daxu da sassafe ta tsorata da gidan kuma, material ne a jikinta na doguwa riga sai hulan da ta rufe gashinta da shi, ta fito daga dakin ta kulle kofar without making any sound tana satan kallon kofar dakin Aneesah dake can karshe duk tunaninta tana ciki, ta fara sauka downstairs shi ma bata yarda tayi making any sound ba, sosai gabanta ya fadi ganin Aneesah xaune parlon tana sanye da rigar bacci har sannan, ta daura kafa daya kan daya tana cin cake tana danna wayarta, xuciyar Jiddah ya dinga bugawa ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, duk da yanda ta dinga avoiding su hada ido sai da suka hada idon da ita, daburcewa tayi, bata san lkcn da tace "Ina kwana" Aneesah tayi mata wani kallon daga sama har kasa, ta ja wani tsaki ta ci gaba da cin cake din hannunta tana danna waya, Jiddah ta sauke idonta ta nufi kitchen duk jikinta yayi sanyi, kulle kitchen din tayi ta turo baki ta jingina da kofar, sai taji haushin kanta gaisheta da tayi, to amma ai bata ma san sanda ta gaisheta ba, bin kitchen din ta dinga yi da kallo, duk da babu wani plate da aka bata amma kitchen din na bukatar gyara, rabon da ayi masa komai tun jiya da safe da ta yi, ta ta6e baki ta shiga store ta dau indomie guda daya a kwalli sannan ta fito, sai da ta fara daura kwai a kan wuta, tana tsaye har ya dahu, sannan ta fara girka indomie din, bata jima a kitchen din ba ta gama, ta juye indomie din a plate sannan ta rufe da wani plate ta dau fork ta bude kofar kitchen din ta fito, sosai gabanta ya fadi ganin wasu manyan mata har hudu a parlon tare da Aneesah duk sun cika parlon da muryarsu kamar ganga, da yake ta rufe kofar kitchen din shi yasa bata jiyo su ba tun daxu, tana fitowa parlor duk suka yi shiru, duk da ba kallonsu take ba amma jikinta ya bata duk ita suke kallo, har wani hardewa take tana tafiya da sauri, Chef salmah ce da Rabi'ah sai Suhaila da Fauziyya, duk kawayen Aneesah ne kuma sa'aninta da suka yi karatu tare a Abuja kana ganinsu ka ga gogaggun yan matan Abuja, Aneesah kadai ce ta dace tayi aure cikinsu, sauran duk gantalinsu kawai suke, kuma yawanci duk babu warce iyayenta ke nan kaduna kawai xamansu suke a garin, Chef Salmah da Rabi'ah ma su biyu kadai ke xaune gidan iyayen Rabi'ah dake Unguwan sarki, dukkansu suka bi Jiddah da kallo, Rabi'ah ta kalli Aneesah da wani expression tace "Wait... wai wannan er yarinyar ce kishiyar taki?" Aneesah ta kyabe baki tace "Wai ba" Wani dariya suka yi gaba daya har da kyakyatawa, Chef salmah tace "Kuturin uba!!! Yo ai wannam karamar alhaki ce Aneesah, ni wllh duk tunanina sa'ar mu ce aka kawo maki xa ku gwabza, yanxu da wannan er cikin naki aka hada ki kishi? To kiyi kishi da ita kice kinyi kishi da wa Aneesah?? Wllh ni duk sai naji raina ya baci, me aka yi aka yi wnn yarinyar, dubeta fa duk a tsorace kamar zomo...." Jiddah dake jin su ta nufi stairs ko juyowa bata yi ba tana jin kamar xata fadi sbda hardewar da take, Suhaila ta rike ha6a tace "Ikon Allah, yo minti nawa xa a 6ata wajen gamawa da wnn er yarinyar? Ni har kin ban kunya wllh Aneesah, ni fa na xata wata uwar mata ce ashe wai wnn kwailar aka kawo maki gida kika bi kika daga hankali kika bi kika ishemu a group" wani tsaki ta ja, Fauziyya ma ta ja tsakin tace "Wllh kwana uku yayi kadan idan ban sa xaman gidana ya gagareta ba shegiya nake, look how meek she is, wannan ai kamar kin samu er wanke wanke ne da share share, ya wuce ma ki aiketa ta amso maki kati ko cingam a kofar gida??" Duk suka kyalkyale da dariya, Rabi'ah tace "Toh ke yanxu Aneesah fasa kayan daki shine iya abinda xaki iya yi ki burge kenan? Is that all u can do? Haba wannan ai karamar alhaki ce" Aneesah tayi wani dariya tana jinjina kai tace "You guys are only being faster than ur shadows" Jiddah dai tuni ta shiga dakinta ta saka key, gaba daya ta tsorata da su, on a serious note Chef salmah tace "Kinsan Allah Aneesah lamarinki ya kunyata ni wllh, na xata xan xo in ga er 35 ne, wai ashe a kan wnn da kilan bata wuce 18 ba kika daga hankalinki haka" Aneesah tayi kasa da murya tace "I think i told u all yanda abubuwa suka dinga faruwa tun ma kafin ta tare, da rashin mutuncin da na dinga yi, yanxu abu kadan captain yake jira inyi shi yasa ku ka gan ni a yanda ku ka gan ni, shi yasa ku ka ga nayi shiru, wllh ba don mahaifiyarsa fa ranan da nayi ma kayanta aika aikan nan saki na yayi niyyar yi don har ya dauko takardan ta hanasa, banda haka ni dai kunsan ba kanwar lasa bace, kawai ku bar ni in ci gaba da bin su da ido for the mean time, ko kun ta6a ganin mutumin da bai kama dahir ba yana iskanci? Ai yanxu sai dai kawai in bi komai a hankali, domin kuwa a wuyar captain nake yanxu, nasan kuma babu wanda yake jin haushi sama da ni a duniyar nan, sarai na sani" Rabi'ah tace "Toh Allah ya kyauta, idan an

102 / 117