Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   110 / 117

327K to 330K   out of 348.6K words

tace "Toh kun ga inda take yanxu, Allah ma ya sa ta dawo daga baran, amma ku shiga Bibalo na nan na sani tunda bbu inda take iya fita ciwo yaci karfinta" Abuturrab ya jawo Jiddah dake xaune gefensa yace "Baby are u sure Tse tse fly bai cije ki ba kuwa" Buda ido tayi da sauri sai kuma ta turo baki tace "Me ka ce?" Yace "Aa cewa nayi mun kawo..." Bin anguwan ta dinga yi da kallo kafin ta bude motar ta sauka, shi ma ya sauka, Lantana tace "Toh kunga ai gwara in yi wucewana ko?" Abuturrab ya ciro dubu uku ya mika mata yace "Mun gode" Har kasa ta risina ta amsa tana masa godiya.... Hajiya Fatima ta shiga d'an karamin tsakar gidan wanda ke dauke da kananun dakuna hudu, ga wani makeken kwata a tsakiya sai doyi yake, kallon wata mata dake daka a d'an mitsitsin tsakar gidan tayi tace "Ina yinin mu?" Matar tace "Wa ake nema?" Hajiya Fatima tace "Hansatu" Matar tace "Aiho bata dawo 6ara ba kuwa, amma kilan tana hanya yanxu" Jiddah dai na tsaye gefe duk jikinta yayi sanyi, yanxu wannan gidan su Baabarta suka dawo?? Hajiya Fatima tace "Ina dakin ta?" Matar ta nuna mata wani daki da babu ko labule tace "Ga ya can, er ta na ciki ma ai" Hajiya Fatima ta nufi kofa Jiddah na biye da ita, tun da Abuturrab ya shigo yayi arba da wannan gutter din ya fice daga compound din da sauri, Hajiya Fatima ta ciro wayarta tana haska dakin sbda duhu ta ga Bibalo da ta dawo uwa skeleton a can kan wani yamutsen karamin katifa irin ta yan boarding a kwance, babu komai cikin dan karamin dakin da duk cement din kasa ya dagargaje sai wasu bakaken Ghana must go biyu, da kwandon kwanuka da risho, Jiddah ta kasa karasawa cikin dakin xuciyarta na bugawa tana kallon Bibalo with shock, Hajiya Fatima dake kallonta ita ma ganin idonta biyu tace "Sannu" Kai kawai Bibalo ta gyada, Jiddah ta kasa cewa komai hawaye ya hau sintiri idonta ta xube nan kasa ta hade kanta da gwiwa abubuwa masu yawa na dawo mata a kai, Hajiya Fatima tace "Mamarki fa?" Murya can kasa wanda idan ba ka saurara ba ma baxa ka ji ba Bibalo tace "Bata dawo bara ba" Hajiya Fatima ta dinga furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarta, Sallama Hansai tayi a tsakar gida Hajiya Fatima ta juya da sauri tana kallonta, ita kuwa tsaye tayi tana mamakin wanda ya kawo masu wnn fitila me uban haske da ya haska daki haka ga kuma takalma ta gani bakin kofa, Hajiya Fatima tace "Sannu da xuwa" kasa karasowa tayi kana ganinta kasan a tsorace take, Hajiya Fatima tace "Ki karaso mana... baki ne daga cikin gari, babu abinda ya kawo mu sai alkhairi" Hansai ta shigo dakin da kyar tana dogara sandarta tace "Wa ku ke nema" Tuni Jiddah ta dago kanta tana jin muryan Hansai na mata echo a kunne, and she remembered nothing but those days, those days she was her slave, those days that she was under her prison, memories marasu dadin tunawa ne suka yi ta dawo mata... hawaye masu xafi suka dinga xuba idonta, Hajiya Fatima ta haska ma Hansai Jiddah, Hansai ta saki roban baranta da sandan hannunta cikin rawan murya tace "Jiddah??" Mikewa Jiddah tayi da kyar tana kallonta hawaye na saukowa idonta, Bibalo ta fara kokarin xaunawa ita ma bayan hasken fitila ya gwada mata fuskar Jiddah amma ta kasa kawai sai ta hakura tana ta kallon Jiddah babu kiftawa, juyawa Hansai tayi, tayi backing Jiddah bata sake cewa komai ba, Jiddah ta dinga share hawayen da ya ki tsaya mata cikin sanyin murya tace "Ina yini Baabarmu" Kamar jiran jin hakan Hansai take ta fashe da kuka tace "Ni babu wanda ya ta6a xaunar da ni ya nusar da ni a kan kamun da Allah ke ma duk wanda ya ci amanar maraya ko ya xalunci maraya, babu wanda ya ta6a nusar da ni, da na samu me nusar dani da ba haka ba.... Yau ga yanda rayuwata da na 'ya ta tilo da nake bala'in so a duniya ya dawo, kaico..." Kuka take tana girgixa kai tace "Lallai Allah baya yafe hakkin wani..." Hajiya Fatima dai tayi shiru, Jiddah ta durkusa kasa tana kuka sosai tace "Ni baki ta6a min komai ba baabarmu, idan ma kin min ni na yafe maki tun tuni saboda ke mahaifiyata ce" Hansai ta juyo ta xauna kasan dakin hawaye na xuba idonta tace "Kin ga yanda rayuwa ta juya mana baya ko Jiddah, ba komai bane illa hakkin ki, idan ma ni ban cancanci yafiyar ki ba, ki yafe ma er uwarki Bibalo ubanku daya..." Jiddah ta hade kanta da gwiwa ta ma kasa ce mata komai sbda kuka, Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Hansatu ai da Jiddah bata yafe maku ba da baxa ku ganta a nan ba, rike kun da bata yi a xuciya ba yasa ta taho har inda ku ke yau...." Hansae na share hawayenta tace "Ai kuwa na gode, na gode, Allah ya ji kan mahaifanta..." Bari in shimfida maku abu ku xauna, da sauri ta tashi ta dauko wani bugun cement ta shimfida masu, Hajiya Fatima ta xauna, Hansae ta koma can gefe ta rakube, Hajiya Fatima ta kalli Jiddah tace "Je ki ki kira Aliyu" Tashi tayi da kyar ta fita xuwa kofar gida. Fitowa Abuturrab yyi daga mota yana kallon Jiddah ganin hawaye idonta, ta sunkuyar da kanta ta nufesa ta rufe fuskarta jikinsa wasu hawayen na xuba idonta, bin wajen yayi da kallo ganin da mutane ya bude back seat ya sa ta shiga shima ya shiga ya kulle motar ya rungumeta a rikice yace "Why are u crying?" Kuka kawai take ta kasa ce masa komai tana kallonsa, duk tunaninsa Hansai ce tayi mata wani abu don ya ga shigarta gidan, ganin xai fita motar ta rikosa ta boye fuskarta jikinsa tana shessheka tace "I don't know what would have become of me da ace baka shigo rayuwata da wuri ba, I don't know what my fate will have been..." Kasa ci gaba tayi ta rungumesa sosai tana kuka, da damuwa yace "I am begging you Jiddah, forget the pass and face the future, forget ur pass... iyayenki mutanen kirki ne shi yasa Allah bai bar ki kin tagayyara ba..." Gyada masa kai kawai take hawaye na sauka idonta, ya dago kanta yayi kissing lips dinta yayi kasa da murya yace "Say Alhamdulillah for everything wife" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah" yace "Ba xa ki sake shiga gidan ba kuma, u wait for us har mu fito" Tace "Noo plss, ban yi magana da kanwata ba" bai saurareta ba ya sauka motar ya kulle ya wuce cikin gidan don baxai iya jure ganinta tana kuka ba, Ba tare da ya kalli Hansai ba ya gaisheta yana tsaye a dakin, ita ma din dai ta kasa kallonsa sai sunne kai take, Hajiya Fatima na kallon Hansai tace "Ina jin ki Hansatu" A hankali Hansai tace "Toh wllh iya abinda na sani kenan Hajiya, amma da xa a gano inda kakar Jiddan tayi aiki nasan su mutan gidan baxa su rasa sanin wani abu a kan kakar ba don a can ma aka ba Marigayi isuhu auren Marigayiya Aisha wato mahaifiyar Jiddah, yanxu haka ma ina da hotan kakar tata da mahaifiyarta, ita Aishan ta bani hoton da kanta ana sauran watanni ta rasu wai in ajiye ma Jiddah, amma ban ta6a nuna ma Jiddah hoton mahaifiyarta ba" Tana magana ne tana goge sabon hawayen dake xuba idonta, Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ko xaki bamu hoton..." Mikewa Hansai tayi ta bude Ghana must go dinta ta tono har can kasa ta ciro wasu hotuna, Hajiya Fatima na ta haska mata da wayarta har daga karshe tace "Toh ga hoton nan" Amsa Hajiya Fatima tayi tana ta kallon hoton Mahaifiyar Jiddah wanda da ace kyan mahaifiyar ta tayi da ba haka ba, babu ta inda take kama da mahaifiyarta da kakarta wanda hakan ke nuna cewa da Abbanta tayi kama, can ta girgixa kai tace "Allah sarki, amma ke baki da masaniyar inda tace maki kakar Jiddan tayi aikin? Wato ita Marigayiya" Hansai tace "Wllh ban sani ba, wanda xai san gidan dama Isuhu ne, Kuma rai yayi halinsa" Hajiya Fatima tace "Toh shkkn mun gode, xa mu tafi da hoton a ga abinda hali xai yi" A hankali Hansai tace "Toh shkkn Hajiya" Hajiya Fatima tace "Ita wannan yarinyar taki kin kaita asibiti kuwa?" Hansai tace "Ina muka ga kudin asibiti Hajiya?" Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Hajiya Fatima tace "Babu damuwa in sha Allah, gobe ko ni kadai xan dawo nan sai in baku abinda xan baku a kai ta asibiti, Allah ya tashi kafadunta" Hansai na matsar hawaye tace "Ameen Hajiya" Abuturrab ya juya ya fice daga dakin don shi ko kadan bai ji tausayin Hansai ba idan ya tuna irin gallazawan da ta dinga yi ma Jiddah sai yaji ransa na baci, Hajiya Fatima ta mike tayi masu sallama ta bi bayansa. Bude back seat yayi ya ga Jiddah na bacci, kallonta ya dinga yi with surprise, Hajiya fatima da ta karaso wajen tace "Kyaleta kar ka tasheta" Bai ce komai ba ya shiga driver seat tace "Baxa ka tsaya kayi magrib ba son?" Yace "Aa bari mu tafi Mama, xanyi a gida" Dai dai kofar gidan Hajiya Fatima Abuturrab yayi parking, ya juya yana kallonta yace "Mun gode sosai Mama Allah ya saka da alkhairi, we appreciate ur effort" Tace "U are welcome son, ga hoton ka ajiye wajenka, sai kuma mu ga abinda Allah xai yi" Ya amsa yace "In sha Allah" daga haka ta sauka ta shiga cikin gidanta shi kuma ya juya xuwa kofar gidansa, mai gadi ya bude masa gate ya shiga ciki yayi parking ya sauka ya bude back seat yana kallon Jiddah yace "Jiddah" Dagota yayi ta bude ido da sauri, sauko da ita yayi daga motar ya kulle suka wuce ciki, Da kyar Jiddah ta iya jira aka yi Isha sannan ta kwanta ko wanka bata yi ba. Horn Abuturrab yyi kofar gidan Umma misalin karfe sha biyun rana, ana bude gate din gidan ya shiga yyi parking, har sannan bai nuna ma Jiddah hoton mahaifiyarta da kakarta ba, cause bai son duk wani abu da xai sa ta kuka, barin yanda ya ga duk bata da wani kuzari, don ko d'an aikin da take yi ma yau bata yi ba, shi ma kuma bai tasheta tayi ba breakfast din ma shi ya tafasa ruwan shayi dama da akwai bread, sai karfe sha daya ya tasheta ya sa ta shirya suka taho gidan Umma don yana son kai ma Umma hoton, tana biye da shi suka shiga parlon da sallama Umma dake xaune da Ahmad ta amsa sallaman tana kallonsu, har ranta taji dadin fresh din da taga Jiddah tayi, Jiddah dai ta sunkuyar da kanta ta karasa parlon ta xauna amma gaba daya she was uncomfortable da aroma din abinci dake shigowa parlon don a bude kitchen din yake, tun tana daurewa har ta kasa ta mike da sauri tayi hanyar dakinsu Maimoon, Umma ta bi ta da kallo tace "Lafiya?" Tashi Abuturrab yayi amma sai ya ji kunyan Umma bai bi ta ba, shi kam Ahmad bin ta yayi da kallo, Umma ta mike ta bi bayanta da sauri, Ahmad ya kalli Abuturrab yace "Toh ka kyauta"




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


Abuturrab na kallon Ahmad confounded yace "For What?" Ahmad ya ki ce masa komai, hakan yasa ya nufi dakinsu Maimoon amma ya kasa shiga ciki ya tsaya nan bakin kofar dakin, dariya kawai yake ba Ahmad ganin yanda duk ya wani damu, lkci lkci Ahmad ke juyawa ya kallesa yana tsaye har sannan a bakin kofar gashi ya kasa shiga, bayan 10-15 minutes Umma ta fito daga dakin, da sauri Abuturrab ya koma baya yana shafa kansa, Umma tayi masa kallo daya ta karasa cikin parlon ta xauna fuskarta babu yabo babu fallasa, ya d'an saci kallonta sannan ya shiga dakin bayan ya bude kofar a hankali ya rufe, kwance ya same Jiddah kan gado tayi backing dinsa, ya xagaya inda take ya durkusa da damuwa yace "Did u throw up baby?" A hankali ta bude ido tana kallonsa, ya dagota xaune ya xauna gefenta yace "Amai kika yi?" Ta gyada masa kai, da mamaki yace "But u ate nothing today, u took just Lipton... are okay?" Ta kwantar da kanta jikin shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Bana son kamshin miyan da ake yi ne, but i am okay" Da mamaki yace "Why? What about the Aroma?" Ta buda hannu tace "Nima ban sani ba, pls mu wuce gida" kamar xata masa kuka tayi maganan, Yace "Right away baby, bari in yi magana da Umma sai mu wuce" Ta gyada masa kai kawai, ya kwantar da ita gently yana kissing dogon hancinta sannan lips dinta yace "I love you" Lumshe ido tayi, tayi murmushi kawai, xai tashi ta rikosa murya can kasa tace "I want shawarma pls" Ya koma jikinta ya shafa belly dinta ya kwantar da murya yace "Right away baby" Daga haka ya mike ya fita dakin. Umma na kallonsa bayan ya shigo parlon tace "Kun je asibiti ne?" Yace "Aa Umma she is fine da muka fito gida, may be there is something she perceived that she doesn't like, but she isn't sick" Umma dai ta ta6e baki tace "Na ga alama ai" shi dai Ahmad kansa na kasa yana murmushi, Abuturrab ya mike ya ciro hoto a aljihunsa ya mika ma Umma, Umma ta amsa tana kallon hoton, sai kuma ta kallesa tace "Who are they?" Yace "Jiddah's Mum and Grandmum" Umma na kallonsa da mamaki tace "Ina ka samo?" Yace "Jiya mun je can wajen stepmom dinta shine ta bamu" Umma tace "Ikon Allah, toh ta gaya maku wani abu a kansu ne?" Yace "She knows nothing, ta dai bamu hoton kawai..." Umma tace "Allah sarki, but this will be too hard, Ta ina kake ga xa a fara yanxu?" A hankali yace "I don't know too Umma, nima naga da kamar wuya lamarin" Umma dai tayi shiru, can tace "Toh Allah ya kawo mana komai cikin sauki kawai, i will keep d picture with me" Yace "To Umma" Tace "Allah ya sa a dace" Yace "Ameen" Ahmad dai sai kallonsa yake, Abuturrab ya shafa kansa yana kallon Umma yace "Xa mu koma yanxu Umma" Umma tace "Toh na hanaku komawa ne.... Nayi ta xuba maka ido in ga gudun ruwanka a kan karatun ta naga kamar baka san a saka maka ido ba, gaya min me kake nufi da rashin barinta ta koma makaranta?" Yayi shiru sai kuma ya sunkuyar da kai yace "Xata fara Umma" Umma tace "Aa ka ajiyeta kayi ta kallo dai, shashasha kawai, kai da baka yi karatun ba xaka kai matsayin da kake yau, ance maka kowa ke karatu don aiki? To wllh kayi gaggawar mayar min da yarinya makaranta" a hankali yace "Toh Umma" Sannan ya mike, shi dai yasan iyakar to din nan bakinsa... Dakin su Maimoon ya nufa ya bude dakin, Bacci ya sameta tana yi ya karasa ya xauna kusa da ita yana shafa fuskarta ta bude ido da sauri kama hannunsa tayi kamar xata yi kuka tace "Are we not going home now?" Yace "We are baby" Ya dagota ya dau veil dinta ya mika mata ta amsa suka fito parlor, Jiddah ta gaida Ahmad ya amsa da murmushi fuskarsa yace "Ya jiki?" Abuturrab ya kallesa yace "She isn't sick" Ahmad ya gyada kai yace "Ohh yes" Abuturrab yayi ma Umma sallama, Jiddah ta karasa kusa da Umma ta durkusa tace "Umma xa mu tafi" Umma tace "Toh Allah ya tsare, ki dinga daurewa kina cin abinci ko yaya ne, kuma ki dinga kama jiki ba wannan lagwai lagwai da kike ba..." Cikin sanyi tace "Toh Umma" Umma tace "Allah ya kara lafiya" Shi dai Abuturrab kallon Umma yake, why are they even thinking she is sick, Jiddah ta kalli Umma tace "Su Maimoon fa?" Umma tace "Sun je saloon" Jiddah tace "Umma wai number me turaren da kika siya min ake tambayata" Umma tace "Wa ke tambayar ki?" Murmushi tayi tace "Wata Mama ce, she is our neighbor, ta shigo shekaranjiya shine tace kamshin yayi mata dadi in bata number me turaren" Umma tayi dariya tace "Lallai kam, ni ina xan rike number me turare, kije daki akwai wani container na turaren in jin akwai number me turaren a jiki" Tashi tayi ta tafi daki sai ga ta ta fito da daya daga container din turaren dake dakin Umma wanda a jiki aka rubuta _S_Square-Incense_ , tana kallon Abuturrab dake tsaye tace "Xaka min saving number a wayarka sai in ba mama pls" Ya ciro wayarsa yana kallonta kiris ya rage yace "Ur wish is my command Baby" kawai ya kalli Umma sai yayi maza yayi shiru, a hankali yace "Alright" Jiddah ta maida idonta kan container ta kira masa number 07030037697.... Bayan yayi saving yace "Done" Mayar ma Umma container din tayi sannan ta fito, suka kara ma Umma sallama, Jiddah na kallon Ahmad tace "Yaya Aunty Ramlah fah?" Yace "Tana gida, kin ki xuwa mana ai" Tana murmushi tace "Xan xo" yace "Ai kam xaki xo kwanan nan ai ko babu niyya" Ahmad ya rakasu har bakin mota, bayan Jiddah ta shiga front seat yana kallon Abuturrab yyi lowering voice dinsa yace "Reduce bothering her or u loose the Baby" Abuturrab ya kallesa da mamaki yace "Which Baby?" Ahmad ya daga kafada yana murmushi yace "Sai mun yi waya" Daga haka ya shige gidan, Abuturrab ya tabe baki ya xaga ya shiga motar suka bar anguwan. Sai da ya biya ya siya mata

110 / 117