Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   112 / 117

333K to 336K   out of 348.6K words

fasa wani kara a tsorace ba, dai dai fitowar Hajiya Fatima, tsaye Dattijon yayi daga inda yake yana kallon Jiddah da mamaki, Hajiya Fatima ta karaso da sauri tana kallon Jiddah tace "Lafiya Jiddah what happened?" Tana isowa dai dai wajen Jiddah taga ta sulale kasa, rikota tayi a raxane tana kiran sunanta tana kallon mai gidan nata, shi dai yana tsaye inda yake bai karaso ba yana ta kallonsu, Hajiya Fatima ta kallesa cikin tashin hankali tace "What just happened Yallabai, me ya faru da ita?" Yace "Shigowata kenan fa, and at first i tot Khadija ce, who is she? She just shouted after seeing me sai kuma tayi collapsing" Hajiya Fatima ta dinga kwala ma first daughter dinta kira, mai aiki dake tsaye gefe ita ma a tsorace ta tafi sama da gudu ta kira Aunty Rahama, Aunty Rahama na shigowa parlon ganin Jiddah kwance kasa a hannun mamanta ta xaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ya faru mama, me ya sameta?" A rikice Hajiya Fatima tace "Ban sani ba wllh Rahama, ki dauko makullin mota mu tafi asibiti, Ali baya nan, quickly get the car key mu tafi asibiti kawai plss" Alhaji Ishaq dai na tsaye yana kallon ikon Allah, gaba daya mamaki ya gama cikasa, Da gudu Rahama ta tafi sama dauko makullin mota sai ga ta ta dawo har da mayafinta jikinta na rawa tace "Na dauko mu tafi Mama" Hajiya Fatima ta mike da sauri tana ce ma mai aiki tayi maxa maza ta dauko mata Hijab dinta, Aunty Rahama na daga Jiddah suka ga jini kwance a kasanta, Da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kin ga mama" Hajiya Fatima ta kwalo ido a tsorace tana kallon jinin tace "Na shiga uku na lalace, meye haka??" sai kuma ta fashe da kuka tana salati tace "Meye haka ni Fatima, me ya sameta" Alhaji Ishaq da shi ma hankalinsa ya tashi ya ajiye jakarsa da sauri yace "Ku fito da ita mu wuce asibiti, hurry pls" Juyawa yayi da sauri ya bar parlon. Hajiya Fatima na xaune a bakin emergency room tayi tagumi, ta dade bata shiga irin wannan tashin hankalin ba, ta ma rasa wani tunanin xata yi in particular, astagfirullah wannan kuma wani irin jarabawa ne a parlonta, sai a parlonta Jiddah xata fara bleeding? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Rahama na jingine da bango ita ma dai duk hankalinta a tashe fatan ta kada ace Jiddah tayi miscarrying cikin nan, Allah kada ya sa hakan, ko don yanda taga Captain ya kwallafa rai a cikin, don time to time ta kan shiga gidan idan ta dawo daga aiki, tunanin miscarriage ya dinga aika mata da wani goosebumps a jiki, she is so afraid, Alhaji Ishaq da Son dinsa Ali na can reception a xaune all disturbed also, bayan kusan minti talatin wata babban likita ta fito tana kallon Hajiya Fatima tace "Kece mahaifiyarta ai?" Hajiya Fatima ta mike da sauri gabanta na faduwa tace "Ni ce doctor, fatan dai babu matsala" Tace "Ki sameni a office" daga haka ta wuce, Rahama na kallon mum dinta sanin ba komai wani lkcn take iya dauka ba a ranta, ta dakatar da ita da sauri tace "Mama ki bari ni in je ko Ali, ke ba sai kin shiga ba ke" Hajiya Fatima tace "Aa babu komai xan je ni..." Daga haka ta bi bayan likitan da sauri xuwa office dinta, Likitan ta cire glasses din idonta tana kallon Mama tace "Ina shi me gidan nata?" Xuciyar Hajiya Fatima na bugawa da karfi tace "Fatan dai babu wata matsala doctor" likitan tace "Da akwai, don ta samu miscarriage, and she is still unconscious...." Da karfi Hajiya Fatima tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, miscarriage likita? Na shiga uku, yanxu cikin ya xube?" Sai kuma ta fashe da kuka, likitan tace "Kamata yayi kiyi fatan tayi gaining conscious Hajiya ba ki karkata kan miscarriage ba... Did she just slouch down, fall accidentally, or an gaya mata wani labari ne da ya girgixa ta ta fadi?" Kuka kawai Hajiya Fatima take ta ma kasa cewa likitan komai, ta furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya fi a kirga, likitan ta ajiye pen din hannunta tace "I need to talk to her husband, a turo min shi yanxu..." Cikin kuka Mama tace "Baya asibitin likita... Yanxu shkkn cikin ya 6are?" Likitan ta buga table din gabanta a hankali tace "Kiyi tunanin halin da er ki ke ciki tukun ba ciki ba Hajiya, kiyi hakuri ki d'an fita ki turo min wanda aka yi komai a gabansa, u aren't answering any of my questions Hajiya" Mama ta mike da kyar tana kuka ta fita, Rahama dake tsaye tana jiran fitowar mahaifiyarta ganin ta fito tana kuka a ranta ta shiga furta Innalillahi, shkkn abinda take ta gudu ya faru, Mama na kuka tace "Tayi miscarriage kuma wai she is still unconscious" Ita ma hawayen ta shiga yi tace "Mama ki kira mijinta kawai muna ta yin abubuwa gaban kanmu, a kirasa mama a sanar masa ya taho" Mama ta nemi waje ta xauna tana rusa kukan miscarriage din nan da aka yi a parlonta, Ali ya kasa cewa komai bayan yayarsa ta sanar masa abinda ke faruwa, Alhaji Ishaq dai na tsaye shi ma he is so Speechless, Rahama na goge idonta tace "Call him immediately Ali" daga haka ta juya ta bar wajen, Ali ya ciro wayarsa ya shiga neman number Abuturrab, ba karamin courage yayi gathering ba kafin yayi dialing number, yana fara ring Abuturrab ya daga, Ali yayi karfin halin cewa "ermm Captain dama Jiddah ce bata ji dadi ba, so we rushed her to the hospital immediately" Abuturrab ya mike tsaye daga xaunen da yake xuciyarsa na bugawa yace "Jiddah????" Ali ya runtse ido ya bude yace "Ehh" daga haka ya sanar masa da asibitin da suke ya katse wayar. Tun bayan da Abuturrab ya iso asibitin aka sanar masa abinda ake ciki, ya kasa cewa kowa komai, he was more than shock, yana xaune kan kujera a reception ya rike kansa ya kasa kallon kowa cikinsu, lkci daya idanuwansa suka kada, he was so hurt namijin kokari kawai yake, Alhaji Ishaq yace "Kayi hakuri, haka Allah ya kaddaro, ita kuma sai mu yi fatan Allah ya tashi kafadunta, ya bata lafiya" Hajiya Fatima dai na can gefe ta kasa kallon Abuturrab, tayi kuka har ta gaji er ta na taya ta, Ali yayi patting Shoulder din Abuturrab cikin kwantar da murya yace "U need to be strong Captain, Allahn da ya baku shi xai sake baku..." Abuturrab yayi karfin halin mikewa da kyar, gathering much courage yace "I want to see her plss" Ali yace "Likitan ta sanar min she is sleeping now, amma mu je office dinta mu ji ko xa a iya shiga ward din yanxu" kama hannun Abuturrab yayi xuwa office din likitan, likitan na kallon Abuturrab tace "Kai ne mijin nata?" Kai kawai ya iya gyada mata, tace "Ohk dama da akwai wani abu dake damun matarka ne, or did they break any shocking news to her?" Ya girgixa mata kai a hankali ya kasa cewa komai, tace "Toh Allah ya kiyaye, idan ta samu kanta sosai sai ayi mata wankin ciki, Allah ya kiyaye gaba" Ali yace "Doctor plss xa iya shiga a ganta yanxu?" Likitan tace "Alright shi dai mijin nata ya shiga ya dubata, amma yana dubata ya fito, she need much rest now" Ali yace "Toh mun gode Dr" ta fada masu ward din da Jiddah take, daga haka shi da Abuturrab da ya kasa cewa komai suka fita office din... Shi ya raka Abuturrab har dakin sannan ya xauna kujeran dake ajiye bakin ward din, Abuturrab ya tura kofar a hankali ya shiga ciki, yana isa kusa da gadon ya daura kansa saman pillon, he was really hurt, can ya dago kansa a hankali yana kallonta da idanuwansa da suka kada, cike da karfin hali yace "Get well soon wife, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" Xaunawa yayi kan kujeran dake ward din ya jinginar da kansa yana jin wani xafi da xuciyarsa ke masa bai ta6a xaton haka ba, can ya ciro wayarsa yayi dialing number Ummi, tana dagawa ya gaisheta, jin voice dinsa tace "Lafiya??" A hankali yace "Ummi muna hospital, Jiddah tayi miscarriage" a rikice Ummi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wani hospital din" Ya sanar mata ta katse wayar tana nanata furta Innalillahi a xuciyarta, can tayi dialing number Umma tana dagawa ta sanar mata sannan ta mike ta fita xuwa dakin Hajja, kwalema ta sameta tana yi da su Nafisah wai taga gilmawan kyankyaso a dakinta, Ummi tayi karfin halin cewa "Hajja yanxu Aliyu ya kirani wai Jiddah tayi 6ari suna asibiti" Hajja ta saki Tsintsiyar hannunta da karfi tace "Li eelafi quraysh, meye kuma 6ari?"




*Sorry for the silence yesterday, jiki da jini... Kuma aski in ya xo gaban goshi...*




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Kwanansu daya a hospital aka yi discharging Jiddah bayan an mata Dilation and Curettage, Aunty Rahama na rike da hannun Jiddah suka nufi motar Abuturrab, tuni ya fita da basket na abincin da aka kawo da safe daga gidan Umma, Hajja ta bi Aunty Rahama da kallo sai kuma ta kalli Umma dake yi ma nurses din reception sallama, tayi kasa da murya tace "Ita kuma wannan narkekiyar daga ina? Naga sai wani kai wa take tana komowa, a ina ku ka samo ta?" Umma tace "Makociyarsu ce" Hajja ta rike haba tace "A kasar nan dai naga kamar an maida kiba wata abar ado... Ita Jiddah ina ita ina wannan jigbegiyar mata da ta kusa haihuwanta, wnn ai ta fi ta wayewa da duniyanci, salon taje ta kwace mata miji mu shiga uku? Ai ba wani kiban a xo a gani ne da matar ba balle ace Aliyu baxai iya aurenta ba, tsaff xai aureta su xauna, sannan naga fuskarta na da kyau kamar dai yar yarinya, jikinta kuma luwi luwi alamar hutu ya xauna, to ni dai ba ruwana kilan baku xaunar da Jiddar kun koya mata karatun duniya ba ne ku ka kaita gidan miji, ai ba a yarda da mata yanxu barin irin wa ennan da idanuwansa ya yage har kunne" Umma dai bata ce da Hajja komai ba tana ta tafiyarta, Hajja ta ta6e baki tace "Ni dai bata min ba wllh, wa ya sani ma ko mayya ce ita ta lashe d'an a ciki? banda haka mu kaff xuri'armu babu wanda ya ta6a barin ciki yana karaminsa wllh, kana samun cikinka sai ka haifesa lafiya da izinin Allah, toh sai kuma a fara 6ari a kan matar Aliyu? Aa wllh ni dai na dasa ayar tambaya a kan wnn mata dake shisshige masu, to naga mata tun jiya tana ta sintiri cikinmu kamar wata er uwarmu, wa xai yarda da haka banda ku da baku san ciwon kanku ba, ni don dai kada ace ban kyauta bane na cika fitina, banda haka wllh da na koreta nace imu imu ya isa ta koma gida kawai" A haka har suka isa mota Umma uffan bata ce mata ba, Hajja na kallon Rahama da murmushi tace "Toh mun gode yarinya Allah ya saka da alkhairi, yanxu tafiya xaki yi daga nan dai ko? Don mu gidan ubansa muka nufa" Rahama tace "Ehh Kaka ga motata can, nima gida xan wuce" Hajja ta juya ta kalli motar da ta nuna mata tace "Au haba, toh Allah ya saka da alkhairi, dama don naga ba can anguwan naku xa mu bane shi sa nace bari dai in gaya maki inda xa mu... Naka ma ya samu me kula da shi idan bai da lafiya a wannan xamanin ai abun farin ciki ne, don gaskiya yanxu ba a ba ma makotaka hakkinsa kamar xamaninmu" Aunty Rahama dai murmushi kawai take, can ta kalli Jiddah tace "Toh Allah ya kara lafiya Jiddah, sai na kawo mama can gidan in sha Allah, Allah ya kara afuwa" Jiddah tayi murmushi tace "Ameen Nagode Aunty" Aunty Rahama ta kara masu sallama ta tafi gun motarta, shi dai Abuturrab na xaune driver seat ya kulle, Hajja ta bude bayan motar tana kallon Jiddah tace "Toh shiga" Jiddah ta shiga motar Hajja ma ta shiga, Umma ta xaga xata shiga ta daya side din murya can kasa Hajja tace "Yanxu xata shigo duk ta matsi mutane malam" Kamar kuwa Umma ta ji abinda Hajja ke cewa ta bude front seat kawai ta shiga, a hankali Hajja tace "Toh Alhamdulillahi" Bayan sun d'an yi nisa Hajja tace "Yanxu ina muka nufa naga kana ta wani xagaye xagaye Aliyu" Umma tace "Can gidana xa mu tafi" Hajja tace "Me?? Aje gidanki a kan me? Anya kina tsoron Allah kuwa Ramlah ga dai gidan uwarsa a kai mata yarinya ta kula da ita tana yi nima ina yi xaki wani ce a tafi gidanki? To ni nace gidan Usman xa mu kai ta, ai matar Aliyu ce ba matar wani ba, mata kawai neman fitina yayi maki katutu, me xaki yi ma Jiddan wanda mu bamu iya ba, ni dai wllh kin cika wahala, to gidan Usman xa a kai ta in ji ni, mata duk kin shanye yayarki sai yanda kika yi da ita kina ta mulkanta yanda ranki ya so? To ni dai ba ruwana" Shi dai Abuturrab driving yake a hankali, Umma tace "Idan kaje can bus stop din ka ajiye ni Aliyu" ya d'an kalleta yayi kasa da murya yace "No Umma u just have to ignore her, don't take this personal, as if u don't know who she is" cike da damuwa Hajja tace "Toh wai meye kake bata baki kamar warce aka yi ma laifi dai daga fadan gaskiya, ni fa ba wani abu nace ba, ko kaji na xageta ne?" Umma tace "I said drop me Aliyu" yace "Then let me drop u home kawai, bai kamata kiyi dropping a hanya ba" Ta kallesa tace "Ba ni nace maka haka ba" parking ya nemi waje yayi ganin how serious she was ya juya yana kallonta ta bude motar ta sauka, sai duk Jiddah bata ji dadi ba taji kamar ta sauka motar ta bi Umma, shi dai Abuturrab ya bi Umma da kallo har ta kulle motar tayi gaba, Hajja ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ba shkkn ba... Yanxu da fada nayi mata ai baxata sauka ba, kaga yanxu da nayi mata bayani cikin nutsuwa tayi wucewarta gida abunta baki alekum" Abuturrab bai tanka ta ba ya ci gaba da driving dinsa, Hajja tace "Kai kuma sai wani cika kake kana batsewa kamar dai mu muka kashe maka jariri Aliyu, toh kai arnene da baxa ka dau tawakalli ba, ita kanta warce d'an ya lalace a cikinta ma ta hakura tana ta fara'a abunta tun a asibiti amma kai sai wani nukurci kake yi kana ba ma banxa ajiyar mu, a hakan kake so Allah ya baka wani? Ai ba a ma Allah haka, da kasan xai baka ne?" Wani harara Abuturrab ya watsa mata ta madubi, Jiddah ta d'an yi murmushi ta sunkuyar da kanta. Da daddare Jiddah na kwance kan gadon Hajja bayan tayi wanka tayi shirin kwanciya, bude kofar dakin aka yi ta daga kai Abuturrab ya shigo dakin ya kulle, ta mike xaune tana kallonsa har ya iso ya xauna gefenta ya kamo hannunta yace "How are you feeling now?" Tace "Alhmdlh naji sauki" Gyada mata kai kawai yayi, da damuwa tace "Are u still sad" ya kalleta amma bai ce komai ba, cikin lallashi tace "Kayi hakuri plss, Allah ya rubuta hakan xai faru... And there is a reason for everything..." Ya d'an yi murmushi slowly yace "Sure wife" Ta rungumesa tace "Cheer up pls dear" Ya marairaice mata yace "Xa ki samar mana wani da wuri plss???" Er dariya tayi tana shafa chest dinsa tace "Sai in ka bani da wuri ae, sai in samar mana da wuri" yayi kasa da murya yace "Yanxu fa??" Xaro ido tayi dai dai nan aka bude kofar dakin, ta dinga kokarin kwace kanta amma ya ki saketa, Hajja tace "Kun ga jaraba ko? Ni dama sai da na innata a raina kawai dai na bi son rai ne na laka ma matar mutane maita, amma can kasan xuciyata ina tunanin kilan takuranka ne ma ya sa cikin nan ya lalace, banda haka yarinya daga 6ari ko kwana biyu ba ayi ba ka xo ka sa ta gaba a daki ka makaleta, yanxu meye ma'anar haka Aliyu? Ke kuma kin wani sakar masa jiki kamar kyanwa, ai kya bari ki murmure yanda ya kamata tukunna dai ko" Tashi Abuturrab yayi daga kan gadon ya nufi kofa, Hajja ta bi sa da wani kallon takaici, can tace "Tirrr, wannan ai jaraba ce kawai ba wani abu ba..." Jiddah dai ta koma ta kwanta ta ki yarda su hada ido da Hajja, don sai ta ji kunya sosai... Washegari da safe Hajja na kada mata shayi me kauri Abuturrab ya shigo dakin, ya xauna saman kujera yana kallon Hajja yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, basu baka kumallon bane a can ka yo mana nan?" Yace "Aa, Abba ne ke kiranki" Tace "Usman din?" Yace "Ehh" ta mike da sauri tana cewa "Dama nayi wani mugun mafarki a kansa wllh, shi sa yau da sassafe na fita na ba mai gadi kudi yaje can anguwan da almajirai suke ayi min sadakan kosai na dubu daya" Abuturrab dake kallonta yace "Mafarkin me kika yi?" Tace "Aa sai kace wata jahila xan xauna ina gaya maka mafarkin da nayi bayan naji ance babu kyau, er benue fa nayi mafarki tana kokarin tura mun shi a teku ta basa apple yana

112 / 117