Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   114 / 117

339K to 342K   out of 348.6K words

ba mijin ne baban Jiddan ba, kawai dai yayi guduwansa ya dawo cikin gari yayi aurensa sbda wahalan duniya ya ishesa, ita kuma ina jin mijinta ya mutu ya bar ta da narka narkan 'ya ya da uban dukiya" Abuturrab ya dakatar da ita so pissed off yace "Menene haka don Allah?" Hajja tace "Aa kar ka min tsawa daga na fadi gaskiya xaka hayayyako min, ko kai baka ga yanda jikinta yayi sanyi qlau ba? Ai taga mijin nata ne a hoton, nan kuma bata san ya ta6a aure har da ya ya ba..." Umma tace "Kin ga mu ba abinda ya kawo mu gidan nan ba kenan Hajja, ya xaki dinga irin wannan maganganun a gidan mutane?" Hajja tace "Toh ba sai in ji duka ba, daga fadan gaskiya sai ai min caaa, ko gabanta ance maku baxan fada hakan ba tunda ba tsoron wani d'an banxa nake ba" Ita dai Jiddah ta kasa dago kanta, Abuturrab yace "Umma wai wa yace ta biyo mu ne?" Hajja tace "Uwarka Ramlah tace in biyoku don bana xagi Hauwa ko Usman ba tunda basu min komai ba..." Saukowan Alhaji Ishaq da Hajiya Fatima ya sa Hajja tayi shiru, Ya karaso parlon ya gaida Hajja, Abuturrab ya gaishesa, sannan suka gaisa da Umma, ya xauna a one sitter yana kallon Jiddah da ta ki dago kanta gabanta na faduwa yace "Ya jikin naki?" Jiddah ta dago da kyar lokaci daya hawaye ya kawo idonta jin muryar tasa kamar Abbanta ne yayi magana, cikin sanyin murya tace "Na ji sauki" Yace "Allah ya kara afuwa" Hajja tace "Ameen dai, ka dai ga hotunan da aka kai maka, ince kai ne a jikin hoton ko?" Ya girgixa kai yace "Ba ni bane Hajiya, amma nasan ina da alaka da koma waye a hoton, nasan wanda ke jikin hoton nan jinina ne..." Hajja tace "Yo ai ya rasu aka ce tun tale tale, ga er tasa dai can a xaune...." Alhaji Ishaq ya kara kallon Jiddah yace "Ya sunan baban naki?" A hankali Jiddah tace "Yusuf" Alhaji Ishaq ya jinginar da kansa da kujera yayi shiru, sai kuma ya kalli Hajiya Fatima bayan few seconds yace "Ina khaleesat?" Mikewa Hajiya Fatima wanda kana ganinta kasan gaba daya a sanyaye take ta tafi dakin khaleesat, sai ga su sun dawo tare, Hajja na ganin Khaleesat ta bude baki tace "Lahhh kaga wllh suna yanayi da Jiddan er kace wannan din?" Yace "Ya ta ce, don a shekaranjiya da na shigo parlon ma nayi tunanin wannan ce a xaune" Hajja ta saki salati tace "Ikon Allah ya fi gaban haka, toh yanxu kai baka da wani d'an uwa da ya 6ata ko ya shiga duniya shekaru aru aru ba a gansa" Alhaji Ishaq ya d'an yi murmushi yace "Ina dai neman Alfarma a bamu ita wannan yarinya mu tafi can garinmu gun mahaifiyata da ita, xa aji komai daga bakin ita mahaifiyar tawa idan munje" Hajja tace "Yanxu mahaifiyarka na nan da ranta?" Yace "Tana nan Hajiya" Hajja tace "Huhuhu, to ko gobe kace mu tafi ba sai mu tafi ba d'an nan, idan ya so a bamu daki kawai mu kwana a nan gidan" Umma ta kalli Hajja haka ma Abuturrab, Hajiya Fatima tayi murmushi tace "An baku Baaba, Allah ya kai mu goben lfya" Umma ta d'an yi murmushi tace "Amma da dai a bari jikinta ya d'an kara kwari ko xuwa jibi ina ga xai fi ko..." Hajja ta kalleta da sauri, sai kuma tace "Toh ai ba wasan yara bane wannan da xa a bari har jibi Ramlah, yanxu dai ki tashi Aliyu ya maida ku gida ni da Jiddah mu kwana nan din kin ji dai an bamu daki, idan ya so idan kinga xa aje garin dake tunda ke ce uwar rikonta sai ki fito da sassafe ki riske mu sannan a kama hanya, amma ba batun da xa a bari har jibi bane wannan kinji Ramlah" Abuturrab ya dinga kallon Hajja kamar ya shaketa, Umma tace "Allah ya kai mu goben, Hajiya bari mu kama hanya dare na yi" Hajja na kallon Aliyu tace "Sai ka amshi makullin daki na wajen Hauwa ka debo min kayana kala biyar, ita ma Jiddah ka bamu makulli mu bude gidanka mu shiga ta debi kayanta" daga haka ta mike tana kallon Jiddah tace "Tashi mu tafi sama a nuna mana dakin, Allah ya kai mu goben lafiya" Hajiya Fatima ta mike tana murmushi tace "Mu je a kai ku dakin" Jiddah sai kallon Abuturrab da ya hade rai take, Hajja tace "Toh ki taso mana ina maki magana" Tashi tayi a hankali ta bi bayansu Hajja, Alhaji Ishaq dai murmushi kawai yake, Umma ta mike tace "Toh Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya Alhaji, sai da safe" Yace "Ameen, Allah ya tashe mu lafiya, mun gode kwarai" Abuturrab ma yayi masa sallama sannan suka fita da Umma. Bayan Hajja ta ci tayi nakk wajen karfe sha daya, tana xaune kan katon gadon dake dakin da aka basu daga kasa kuma shinkafa ne da miya da coslow ga soyayyen kaji sai farfesun kifi da aka masu sharp sharp, tana kallon Jiddah da duk bata da walwala tayi kasa da murya tace "Ke baki ga wani kankanban da Ramlah keyi a gaban shi me kama da baban nan naki ba, to ko sonsa ta ji ta fara yi wa ya sani, kinsan mijinta xai shekara goma sha daya da rasuwa kuma ta ki aure, to idan ba sonsa take ba meye na wani make murya tace a bari sai jibi aje garin, ina ruwanta?? Wllh ban ta6a ganin haka ba tunda aka haifeni, idan ma sonsa take matar gidan nan dai ta fi karfinta" Murmushi kawai Jiddah tayi Hajja ta gyara kwanciya tace "Atoh, ni ba ruwana wllh" Washegari karfe takwas Alhaji Ishaq suka dau hanyar garin gombe, Ali ne ke driving din Abban nasa na xaune kujera me xaman banxa, Hajja da Jiddah sai Hajiya Fatima na xaune back seat.... Da yamma suka iso cikin garin gombe, Ali yayi parking a kofar gidan kakarsa, shi da Abbansa suka shiga masallaci yin sallan La'asar Hajiya Fatima tayi leading din su Hajja xuwa cikin gidan har parlon Hajiya Dada warce ita ce mahaifiyar Alhaji Ishaq, Hajiya Dada ta dinga masu sannu da xuwa baxa ka ta6a cewa ta kusa dari ba don da sauran kwarinta, sauran yaran nata duk suna gidan suna jiran isowar Alhaji Ishaq, wanda shine babban yayansu, su ma dai suka dinga welcoming dinsu... Bayan kusan minti ashirin Alhaji Ishaq ya shigo ciki tare da Ali don sai da ya tsaya gaisawa da 'yan anguwan da suka dinga kawo masa gaisuwa wanda hakan kadai xai sa ka fahimci yana siyasa ne. Hajja na kallon Jiddah bayan ta idar da sallah ta rike ha6a tace "Ke kiga kantamemen gidan da suka gina ma tsohuwar nan kamar baxata mutu ba..." Jin Jiddah bata tanka ta ba ta kyabe baki ta jawo warmers da aka tula masu a dakin, Hajiya Fatima ce ta shigo duk tayi serving dinsu abincin sannan ta fita, Hajja ta kara rike ha6a tace "Lallai manyan mutane ne, sai kace ina gidan kabiru don ma dai wahala bai isheni ba ai da babu uban da xai sa in bar gidan Kabiru yanda kika ga haka fa haka ake min a fadar nan ta Bauchi, to amma ni din ce wahalalliya inyi ta rabe rabe a kaduna ana hantara ta" Wajen karfe biyar Hajiya Fatima ta yi ma Hajja da Jiddah iso xuwa babban parlon Hajiya Dada, yaranta biyar a duniya kuma duk suna xaune parlon, maxa biyu mata uku, ko wannensu kana gani kasan nera ta xauna ne kawai, Jiddah ta sunkuyar da kanta bayan ta gaishesu gaba daya, su kuma suka dinga gaida Hajja ana tambayarta ya gajiyan hanya, bayan an gama gaishe gaishe Alhaji Ishaq ya mike ya isa gun mahaifiyarsu ya durkusa ya mika mata hotunan hannunsa yace "Dada kin gane waye wannan a hoton nan?" Hajiya Dada ta dau gilashinta ta saka tana kallon hotunan da kyau, wani murmushin takaici tayi tace "Wannan ai Yusif dina ne, bana ce maku yana nan raye ba babu wanda yake yarda dani ana ganin kamar xaucewa nayi, nasan yusif bai mutu ba, to ina yake yanxu? A ina yake?" Hajja ta daga hannu tace "Aa mu dai ya rasu kusan shekaru biyar kenan, sai dai ga er cikinsa nan a kusa da ni..." Hajiya Dada tayi shiru tana kallon Jiddah, sai ta fashe da kuka tana girgixa kai, duk kowa yayi shiru a parlon, a hankali ta fara magana tace "A shekaru kusan hamsin da suka wuce a kasar nan ina jin babu wanda ya kai mu shiga tsananin rayuwa da rashi da muke ciki da ni da mai gidana da abokiyar xamana, mai gidan namu ba shi da komai sai gona daya tak shi ma gadon mahaifinsa ne da ya ci, Yusuf shine d'a na na uku, ita kuma kishiyata Kulu a lkcn tana da ya ya biyu ita ma duk maza, duk da rashi irin na mai gidanmu Malam Sunusi haka ya dau son duniya ya daura ma Yusif don duk cikin yaran nasa ma ya fi kama da shi, babu abinda ya raga ma Yusif komai yi masa yake toh ashe hakan na kona ma ita kishiyata kulu rai ni duk ban sani ba, mai gidanmu ya sha siyan karamin dabba idan ya d'an samu kudi ya kawo gida yace a kiwata ma yusif, komai na gidan nan yace yusif, kwatsam watarana muka wayi gari babu Yusif babu dalilinsa a cikin gida, neman duniya dai a garin nan na gombe anyi amma ba a ga yusif ba, a lkcn yana da shekaru 4 kacal a duniya, na shiga tashin hankali da baya faduwa yanxu haka, wato mahaifinsa ma ya fi ni shiga tashin hankalin, ita kanta kishiyar tawa kullum cikin tayani kuka take, amma ya muka iya da wannan kaddara? Bayan shekaru biyu babu wani labari na ganin yarona muka tabbatar baxa mu sake ganin Yusif ba ya 6ata ne na har abada, amma ni dai ban cire rai ba kullum addu'a nake Allah ya bayyana min shi, kusan duk dare sai nayi kukan 6atan yusif dina, bayan shekara 49 da 6atan Yusif wato ina maganan shekaru biyu da suka wuce kenan, bayan shi mahaifin Yusif ya ma rasu da kusan shekara goma kenN, Kishiyata Kulu ta dinga ciwo kamar dai ba na tashi ba, tun bayan haihuwar nan nata biyu dama kuma bata sake haihuwa ba, daya yaron nata rasu, dayan kuwa na garin Legas ko waiwayarta baya yi shekaranmu takwas kenan rabonmu da shi, komai dai na bukatar yau da kullum da ku ka sani kai hatta gidan da take ciki 'ya yana suka siya mata tunda Allah ya hore masu, tana dai cikin rufin asiri amma ciwo dai ya ki ci ya ki cinyewa, wai sai ana gobe Kulu xata mutu naje dubata da yake kullum sai an kai ni gidan a mota, shine take rokona gafara tana kuka, nace gafarar me kuma kulu, me kika min, nace mata ni baki min komai ba wllh kulu, lafiya muka xauna dake har xuwa yanxu... Hajiya Dada ta fashe da kuka tana girgixa kai tace "Wai a nan Kulu ke ce min ai ita ta ba ma kaninta Saleh Yusif ya kai sa garin kano kawai ya bar shi a kan hanya sbda kawai Malam Sanusi na yawan yi masa waka yana cewa ya mallaka masa gonarsa kwaya daya tak... Toh a daren ranan Kulu ta rasu, ni kuwa ya xan yi? Nace na yafe mata, a nan take kuma na sa yan uwan Yusif a buga gidan jaridu a kai labarin gidan radio har ma da talabijin ko Allah xai sa Yusif ya ji ya nemo mu, amma shiru kake ji, har snn kuma ina ji a raina Yusif bai mutu ba, ashe ma rai yayi halinsa...." kuka take sosai, Hajja tayi tagumi tace "Amma Allah ya tsine ma wannan mata kulu, Allah ya kara mata nauyin kasa, Allah ya matse kabarinta" Cikin Kuka Dada tace "Aa na yafe mata wllh, dena fadar haka na yafe mata" Hajja ta bude baki tace "Tabdi, yanxu ashe uban Jiddah da gatansa yayi ta galantoyi tun yana karami a kaduna, to kuwa wllh da yasan da wnn labari da kyar idan ya sa ma Jiddah wannan sunan da ya sa mata, don ita ma kulun ce ai, da yasan matar ubansa ce ta gantalar da rayuwarsa wllh baxai sa ma yar sa kulu, ni har naji na tsani sunan duk da sunan surkata ce dai" Dada na kallon Jiddah cikin kuka tace "Taho kusa da ni Hauwa..." jiddah ta goge idonta a hankali ta mike ta isa kusa da kakar tata ta xauna, Hajiya Dada ta rungumeta tana shessheka tace "Ko ba komai ai xan ganki in ji dadi, ko ba komai xan kalleki in tuna da masoyina Yusif, nayi farin cikin da Allah bai dau raina ba sai da na ga jinin Yusif" Hajja ta fashe da kuka tace "Allah ka tsine ma wnn mata dai kulu, ko ya xata yi da hakkin da da uwa a kabari, ashe tun tale tale ake rashin gaskiya a duniya ban sani ba, tirrrr" Hawaye kawai Jiddah ke yi a jikin Hajiya Dada, Hajiya Fatima ta fi kowa farin ciki a parlon nan, she was so happy Jiddah is closely related to her Husband, tun da ta ga Jiddah dama ta san da wani abu dake boye a kasa, she just like her for no reason, xurfin cikin mai gidanta bai sa ya ta6a bata labarin d'an uwansa da ya 6ata shekaru masu yawa da suka wuce ba, sauran yaran Hajiya Dada sun yi farin ciki sosai su ma da ganin daughter din d'an uwansu da ya bace shekaru hamsin kenan don su kansu ba wai saninsa suka yi ba sai a labarin mahaifiyarsu da take yawan yi masu duk sanda ta tuna da shi, Hajiya Dada ta goge idonta tace "Ina mahaifiyarta?" Hajja tace "Ahau, ance tun tana jaririya uwar ta rasu, a hannun matar uba ta taso tana ta gallaza mata tana bata tallan awara da doya da dankali tana bi layi layi da shi a kai tana siyarwa, shine fa jikana matukin jirgin sama ya ganta cikin mugun yanayi yaji tausayinta ya rabota da wnn anguwa ana kiransa da hayi, in dai kunsan kaduna xa ku san hayi, kuma duk wanda ya ji hayi ya san sauran, to a can dai jikina Aliyu ya aurota ya kawota cikinmu, babu abinda muka ragata da shi yau shekaranta biyu kenan tare da mu, kanwar uwarsa ce uwarta da ubanta matar ta rike ta da amana ko er ta sai haka, don isa da gadara kawai take xubawa a kanta tayi ta nuna ta fi kowa sonta" Duk aka dinga kallon Hajja a parlon, Hajiya Dada ta girgixa kai tace "Allah ubangiji yayi maku abinda ku ka mana Hajiya, Ina matar uban nata?" Hajja tace "Wa?? Tana can duniya ta juya mata baya aka ce, idan xa ku ji shawarata ku fita harkarta kawai, don wllh ina da yakinin har da bala'inta ya kashe isuhun naki, duk ita ce ta fitinesa, to me xa ayi da ita kuma?" Hajiya Dada tana hawaye tace "A dai a kawo min ita ko a kai ni inda take Hajiya, duk wani abu da ya shafi Yusif ba abinda xanyi banxa da shi bane" Hajja tace "Atoh, amma dai Jiddah kam yau shekaranta biyu rabonta da matar uban gaskiya" Hajiya Dada tace "Allah ya saka maku da alkhairi Hajiya, Allah ya saka, Allah ya saka, yau na daya daga ranakun farin cikina a rayuwa, Allah ya rubuta baxan bar duniya ba tare da na ga jinin yusif ba, har in koma ga mahaliccina ni da yarana baxa mu mance da wannan halaccin naku ba, Allah ya saka maku da alkhairi Hajiya" Hajja ta dinga wani murmushi tace "Ameen Ameen" Hajiya Zuwaira fourth born din Hajiya Dada ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Toh dangin mahaifiyarta fa?" Hajja ta gwalo ido tace "Ke kin ta6a ganin wanda ba a san asalinsa ba a dau yarinya me asali a basa? To wllh abinda ya faru kenan, ita kanta uwar Jiddan a yanda shi isuhun yake ita ma a haka take, wato dai ba a san asalinta ba, mu ai aiki biyu ne a gabanmu, yanxu munyi daya saura daya, duk inda dangin uwarta suke su ma sai mun nemo su, ko kuma mu bar ku da wahalan ku mu, ai munyi kokari haka" Alhaji Sulaiman yace "Haka ne Mama, wnn kam aikin mu ne in sha Allah duk inda yan uwan mahaifiyarta suke xa mu yi bakin kokarinmu na ganin mun nemo su, da izinin Allah kuwa" Hajja tace "Ina sha Allahu, shine kadai gatan da xa ku yi mata don duk wanda xaku mata ba birgeta xakuyi ba tunda ta samu a wajenmu da wajen jikana Aliyu" cikin sanyi Hajiya Dada tace "Toh shi jikan nawa baxai xo in sa mashi albarka wannan namijin kokari da yayi haka ba" Hajja tace "Huhuhu.... Namijin kokari kuwa, kaff Najeriya babu matukin jirgi bahaushe sai shi, hatta turawa ji suke da shi wllh don ya iya sarfa jirgi, a lkcn da ya auro Jiddah fa wllh ko da kudi aka hadaka da ita baxaka amsheta ba, talaka ma wllh da kyar xai amince ya aureta, wahala tayi wahala, ba arabi ba boko sai talla, fatar nan nata yayi wani dukun dukun malam, kai!!! wllh Aliyu yayi kokarin da ba kowa xai yi ba, amma sbda xuciyarsa irin tawa ce wllh haka ana masa dariya ana xolayarsa ya rufe ido ya aurota ya kawo mana gida, ranan da ya kawota kuwa duk sai da muka girgixa muka fita hayyacinmu, biyar baxaka siyi Jiddah ba wllh wllh, ko da yake dai duk ina Masar aka yi hakan" Hajiya Fatima dai sai murmushi take tana kallon Hajja, Hajiya Dada kuwa ta makalkale Jiddah kamar xa a

114 / 117