Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   103 / 117

306K to 309K   out of 348.6K words

kawo kayan mun gama gyare gyaren da xa mu yi sai mu tafi inda xa mu je kawai since akwai lkci, ni fa shi sa har yau ku ka ga naki amsa ma Alhaji Salisu, so kawai nake sai na gama duk abinda ya kamata tun daga waje, ta yanda ina shiga gidan komai ya dawo hannuna baxan iya wahala ba gaskiya, don haka sai na shirya tsaf anyi duk abinda ya kamata sannan xan basa izini ya turo" Fauziyya tace "Kina da gaskiyar ki wllh, wa xai xauna? Yan iskan uwayen gidan nan da jira kawai suke Allah ya kawoka su nuna maka takama da isa, to wllh ba ayi matar nan ba, shi sa muke shiri sosai kafin mu shiga...." Aneesah dai sai wani murmushi take tana girgixa kafa, jin ringing din wayarta ta mike ta isa gun wayar dake caji da ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sauri ta dauka ganin me kiran ta daga ta kai kunne, a d'an fusace tace "Ni ban ga wani alert ba har yanxu wllh, haba abu tun jiya dae kamar xa a turo min miliyan goma, gashi sbda rashin cikon kudin ba a turo min kayan ba har yanxu" Ta kyabe baki tace "Toh ina jira ni dai..." daga haka ta katse wayar, Fauziyya tace "Yanxu da mun xo karfe takwas da rabi haka xa mu yi ta xama kaya basu iso ba" Aneesah tace "Toh ba sai an samu cikon kudin ba sannan xa su iso Fauziyya, kun san fa na canxa furnitures din daga wanda na tura maku a group, wannan ya fi shi tsada, daga baya company din suka turo min wannan naga ya fi kwanta min kawai na xa6e sa" Sai karfe sha biyu motar kayan Aneesah suka iso gidan, kamar dai yanda aka yi na Jiddah ita ma haka sai da suka sauke sababbin kayan snn suka dinga fitar da fasassun waje suna lodawa a babban motar, kafin karfe uku masu kawo kayan duk suka shirya mata furnitures din sannan suka wuce... Suna xaxxaune da kawayenta a dakin bayan an gyara ya dawo fess, sai ya6a furnitures din suke, ita kuwa sai murmushi take tana bin dakin da kallo don ya fi nata na da kyau, miliyan 1.5 tayi kayan dakin, Babu warce ke da alamar tashi tayi sallan axahar cikinsu, Aneesah ta fita tayi masu rechauffe din jollof din dake freezer ta kawo masu dakin da drinks da ruwan gora, ko wacce ta sauko kasa xa a ci abinci. Sai wajen karfe biyar da rabi suka shirya ta rakasu bakin motar Rabi'ah dake kofar gida, Chef salmah tayi wani dariyan yan da6a tace "Sha kuruminki aminiya, mota kamar Aliyu ya siya maki wanda ya take wancan na garage, ke dai Allah ya bamu nasara kawai.... Mu ne fa!!" Rabi'ah tace "Banda ma tana ta mana xurfin ciki ai da ba a kai ga haka ba wllh, ni duk a xatona don taga tayi aure ne ta wani fita harkanmu take shan kamshi shi sa nima na sakata a kwadon shara, kawai na sha iskanci ne tsabagensa take mana, ashe tana nan tana ta kunsar takaicin d'a namiji, ni da na maida maza kamar rigar sawa ta, in cire sanda na ga dama in mayar, ga dai su da yawa a gari kamar ledan pure water, wani lkcn sai in ji bana ma son auren, gwara kawai inyi ta duniyanci na wllh" Dariya su Salmah suka yi suna hailing dinta da karfi, Suhaila tace "Toh kar dai ki manta karfe takwas xa ki fito Aneesah, don wllh wajen da nisa sosai" Aneesah tace "In sha Allahu takwas din kuwa..." Da haka tayi sallama da su ta dawo cikin gida cike da farin cikin xuwansu, kawayenta ne na kut da kut tare suke watsewarsu a Abuja, lkcn da aurenta da Abuturrab ya tashi babu irin shawaran da Rabi'ah bata 6ata ba kan kar tayi aure yanxu tana yarinyarta da ita ta fara fuskantar matsalolin rayuwa amma Aneesah taki ji, wnn ne ma yasa Rabi'ah bata yi attending bikinta ba sae su Fauziyya da Suhaila kawai. Jiddah na kwance daki kana ganinta kasa she is very sad, tun indomie da ta ci shi ma ba sosai ba da safe bata sake cin komai ba har yanxu sbda tana tsoron fita parlor, yunwa take ji sosai amma ta rasa yanda xata yi, ta mike xaune a hankali tana share hawayen da ya kawo idonta ta mike ta isa jikin window ta tsaya wani hawayen na sauka idonta, sosai take jin kewar Abuturrab, and she wished he is around da baxata ji yunwa ba.... Aneesah na shiga dakinta ta shiga wanka da sauri, bayan wasu mintuna ta fito, cikin gaggawa ta mulke jikinta da turarruka iri iri snn ta fito da wani ubansun English wears ta saka ta dau babban handbag dinta ta saka brush da maclean, sai panties biyu, ta debi turarruka kala uku ta xuba su a jakar, Hijab dinta ta dauko har kasa ta saka sannan ta dau flat shoe dinta shi ma ta sa ta dau dubu hudu ta xuba a jaka ta dau jakar ta nufi kofa ta fita, kulle kofarta tayi da makulli a hankali snn ta fara sauka downstairs without making any sound, Jiddah na tsaye jikin window dinta har sannan taga Aneesah da hijab har kasa da handbag ta nufi gate da sauri, Jiddah ta dinga kallonta har ta fita gidan. Da sauri Jiddah ta nufi kofa ta bude ta sauka da nufin tayi duk abinda xata yi a kitchen kafin dai ta dawo, tana ta tsaye kitchen tana tunanin me xata dafa da baxai dau lkci ba, kawai tayi deciding ta dafa jollof din pasta, ba kifi ba nama don a tunaninta xai bata mata lkci, cikin minti ashirin ta gama don pasta din rabi tayi amfani da ta juye a warmer ta dau ruwan gora a fridge ta fita kitchen din ta koma sama da sauri tana sauke ajiyar xuciya.... Har aka kira magrib bata ga Aneesah ta dawo ba, aka yi isha still tana ta xuba kunnen ta ji an bude gate an shigo amma shiru, wanka Jiddah tayi ta sauya kayan jikinta xuwa na bacci sannan ta kwanta gefe, she is just missing everything about Abuturrab so much, sau da yawa sai taji kamar lips dinsa a nata har sai ta kai hannunta bakinta, ta lumshe ido ta takure waje daya tana ta kwance har karfe goman dare, ta mike xaune cike da mamaki don har yanxu bata ji Aneesah ta shigo ba, a haka har bacci ya dauketa wajajen 11. Da asuba tana farkawa ta fito ta sauka downstairs don haka kawai taji hankalinta ya tashi ganin har bacci ya dauketa jiya Aneesah bata dawo ba, ta kofar parlon kadai xata san ko ta dawo ko bata dawo ba don in har ta dawo to xata kulle kofar parlor, ga shock dinta a bude taga kofar da ta murda, alamar ba a shigo ba balle a kulle, ta dinga kallon kofar a tsorace sai kuma ta juya a hankali ta koma sama. Gari na wayewa karfe bakwai Jiddah ta sauko parlor don bata jin dadi taga gidan so dirty, tunda ita dai ba me kiwiya bace, ga shi Aneesah da bakinta na jiya sun yi kaca kaca da parlon kamar yan yara, duk cake ne kan tiles da goran drink da ruwa, tana cikin sharan parlon aka bude kofa, daga kai tayi da sauri, Aneesah na ganinta ta hade rai taki yarda ta sake kallon inda take har ta haura sama, Jiddah ta bi ta da kallo tana ci gaba da sharanta a hankali, bayan ta gama tayi mopping xata kai bokitin waje sai ga Aneesah ta sauko daga sama da saurin ta again, atamfa ne a jikinta da mayafi sai handbag dinta sai xuba kamshi take, nan ma ko kallon Jiddah bata yi ba ta fice daga parlon tana picking call dinta tace "Kai Rabi'ah gani na fito yanxu, wllh na makara ne" Jiddah dai ta bi ta da ido don a bude ta bar kofar.... Bayan la'asar Jiddah ta fito kitchen kenan bayan ta wanke plate din da ta ci abinci, har sannan Aneesah bata dawo gidan ba, xata tafi sama ta ji an bude kofa ta juyo da sauri, Hajja ce ta shigo parlon ba ko sallama, Jiddah da ta ji dadin ganinta ta dawo parlon da sauri tana murmushi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Bari Jiddah ba wannan ne gabana ba, Ina mijin naki?" Jiddah ta girgixa kai tace "Ya tafi aiki ai" Hajja ta rike kai tace "Kashh, wai nan na shirya ne ya kai ni gidan kyauta ance min shi kadai ya san gidan a Barnawa tunda a lkcn da ya maida Hafsah uwarsa da ubansa kusan duk kwana biyu sai sun je gidan da shi da ita, yanda yake xuwa gidan ma ko gidan Ramlah bai xuwa... Amma wllh ban ji dadin wannan shegen aikin da ya tafi ba, wai fa daga na d'an kishingida in huta yanxu kawai sae nayi mafarki an kwama ma bakina katon kwado bana um bana um um, kuma ni kadai ke ganin kwadon babu me gani wllh, su Usman da Hauwa sun tsaya kai na suna ta hajja lafiya, Hajja lafiya, amma ina ba baki an garkame sae kallonsu kawai nake kamar bebiye, to shi yasa ban ga ta xama ba a xo a kaini gidan Kyauta ayi min iyaka da Hafsah, wllh da kyar idan baxan kai wannan xancen kotu gobe ba, don ya gigita ni shiga bandakina biyar kafin in xo gidan nan, yanxu haka xancen da nake maki sae na kara xagawa a gidan nan, ai ko dabba ba a kulle ma baki ba balle mutum" Jiddah dake ta kallonta tace "Hajja ai ana kulle na doki" Hajja ta saki baki tace "Toh ni doki ce? Ina ruwana da doki xaki ce min ana kulle na doki, ana maganar mutane me ya kawo na dabba kuma Jiddah? Kawai mata matsiyaciya ki nemi garkame min baki ban maki komai ba, wllh baki ga ba ko abincin kirki ban iya ci a kan wannan xancen yau kwana hudu kenan, kwatsam sai ga mummunan mafarkin nan daxu, kin ga kuwa ai ba lafiya, to tun kan a cuceni a mayar dani Bebiye gwara a xo a biya min tikiti in koma Masar bakina alekum" Jiddah dai sauraronta kawai take, Hajja tace "Shi kuma yaushe xai dawo daga gararin samaniyar tasa?" Jiddah tace "Kilan juma'ah ko asabar, Hajja ki xauna in kawo maki ruwa" Hajja tace "Wani ruwa bayan abinci ma wannan na kasa ci, meye kuma ruwa, naga alama kun dau wannan kess din karamin kess, wllh da a Masar ne sai an bata kwadon gaske ace ta kulle bakin nawa a gani, Allah sai an mata zindir an xane shegiya sannan a mika ma yara su yi ta jifa, me na mata xata min haka??" Tana kai wa nan ta nemi waje ta xauna tana fiffita xufar da tayi da mayafinta, Jiddah ta nufi kitchen dauko mata ruwa da lemo ta ajiye gabanta, Hajja ta dau goran ruwa daya sai da ta kwankwadesa tass, sannan ta ajiye tace "Rabona da shan ruwa tun kan inji wannan mummunan batun" Bude kofar parlon aka yi duk suka daga kai, sosai gaban Jiddah ya fadi ganin Abuturrab ya shigo parlon, suna hada ido ya dauke idonsa fuskar nan tasa a daure, ta sunkuyar da kai, Hajja ta kalli Jiddah tace "Kika ce min ya tafi aiki?" Kafin Jiddah tace komai yace "Ehh daga can nake" Hajja ta mike tace "Abinda Allah ya ga xuciyata ko daga sararin samaniyar ne ai sai a hankado min kai kawai, wllh ina cikin garari Aliyu, gidan Kyauta yayar Hafsah xaka kai ni a Barnawa don girman Allah" Abuturrab yace "Daga Abuja fa nake yanxu ko hutawa ban yi ba Hajja" Hajja tace "Oh oh Allah, Aliyu mafarki nayi an kulle min baki da kwado fa? Wa xai xauna da wannan mugun mafarkin idan ba gantalalle ba" Yace "Toh ki bari in huta na gaji, bayan nayi aiki kuma na sake shiga mota na taho kaduna" Hajja ta koma ta xauna tace "Toh tafi ka huta ko na minti sha biyar ne, ai ni ba bakuwar xafi bace, banda Ramlah ma bata san gidan ba ai ita nayi niyyar ta rakani don naga ita dai dai take da ko wani d'an banxa a duniya" Abuturrab bai ce mata komai ba ya nufi sama, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja tayi kasa da murya tace "Ina gantallaliyar abokiyar xamar ta ki?" Jiddah tace "Kila tana daki ban sani ba" Hajja tace "Atoh, ina ruwanki da ita da xaki san inda take dama" Mikewa Jiddah tayi tace "Ina xuwa Hajja" Hajja tace "Toh ni dai kar a shanya ni, ba ruwana da iskanci da rana tsaka" stairs Jiddah ta nufa, tana haurawa sama ta tsaya corridor tana tunanin ta je ko kar taje side din nasa, haka kawai ta ji tana shakkarsa sosai, bayan few seconds kawai ta nufi bangaren nasa tana tafiya a hankali, bude kofar parlon tayi kamar munafuka ta shiga ciki ta gansa xaune, ta karasa ciki ta d'an durkusa kasa daga gefensa ta ki yarda su hada ido tace "Sannu da dawowa" Ba tare da ya kalleta ba yace "Thank you" Kallonsa tayi a hankali, jin bai sake cewa komai ba ta mike ta nufi kofa ta fita ta koma wajen Hajja. Bayan minti ashirin Abuturrab ya sauko parlor kafin nan sai da ya bude kofar dakin Aneesah ya ji sa a kulle, kallon Jiddah yayi yace "Lend me ur car key" Ta mike tana kallonsa don babu yabo babu fallasa yayi maganar, ta wuce sama ta dauko masa makullin a dakinta ta risina ta basa, ya amsa yace "Tashi mu je Hajja" Hajja ta mike tace "Allah yayi maka albarka, mu je in ji ba'asin kulle min bakina" Kofa ya nufa tana biye da shi ko sallama bata tuna tayi ma Jiddah ba har suka fita, Jiddah ta bi su ta tsaya bakin kofa tana kallon Abuturrab, ya ki yarda ya kalleta, nan da nan hawaye ya kawo idonta, kamar ance ya juya ya ga hawaye a idonta, ya jefa mata wani kallo, turo masa baki tayi ta juya ta koma parlon da sauri. Abuturrab na ajiye Hajja kofar gidan Kyauta ya ciro dubu biyar ya mika mata yace "Hajja gashi idan xaki koma sai ki samu adaidaita sahu, ni yanxu xan koma aiki ne, nayi mantuwa ne yasa na dawo" cike da masifa Hajja tace "Yau naga jalala, dama ba da kai xa mu shiga ba ni kadai raina xan shiga?" Yace "Toh ni macece da xan bi ki mu shiga Hajja, excuse na dauka wajen aiki, jirgi na can a airport din Abuja xan daga xuwa kano" Hajja tace "Toh na fi jirgi ne? Ko ina ruwana da shegen jirgin naku? Sbda ba bakin uwarka aka yi niyyar garkamewa ba shi sa baxa ka bi ni mu shiga ba ko??" Dariya ta basa amma ya cije yace "Toh sai in bar aikina in shiga ayi ta xancen garkame baki da ni?" Hajja tace "Toh Allah ya isa, ai sbda kai da uwarka aka yi niyyar kulle min bakin nawa Allah ya toni asiri, kuma wllh daga yau ko kasheku naga xa ayi kai da uwarka shiru xanyi abina in koma gefe tunda gashi ta dalilinku aka nemi hallaka min bakin da nake salati nake ba Allah gaskiya" Daga haka ta fixge dubu biyar din ta shige gidan tana rafka wani uban sallama, dariya yayi ya juya kan motarsa ya dau hanyar gida. Yana komawa gida bayan ya haura sama dakin Aneesah ya bude ya ji a kulle har sannan, ya d'an tsaya sai kuma ya nufi dakin Jiddah ya bude, kwance ya ganta tayi kukanta ta koshi, ta mike xaune tana kallonsa ya wani hade rai, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" yace "Ban yi ba" Tura masa baki tayi ta juya masa baya, ya shafa kansa yana kallonta, sai kuma yace "Ina Aneesah?" Ta kallesa a hankali tace "Nima ban sani ba" ya karasa dakin ya rungume hannunsa yana kallonta, lkci daya ya dauke idonsa daga kanta, yyi kasa da murya yace "Make me a cup of tea" daga haka ya juya ya fita, ta mike a hankali ta fita ita ma ta sauka downstairs. Bangarensa ya tafi ya dauko spare key ya bude dakin Aneesah thinking ko kulle kanta tayi a ciki, amma babu kowa dakin haka ma bathroom din... A ranan Abuturrab xai koma Abuja don ko awa biyu bai yi niyyar yi ba a gidan, but ya kasa tafiya yana ta xaune parlor downstairs yana jiran ya ga sanda Aneesah xata shigo gidan, Jiddah ta fito daga kitchen tana kallonsa tace "Na gama in xubo maka yanxu?" Ya daga kai ya kalleta yace "Tun yaushe Aneesah ta fita gidan nan?" Ta d'an buda hannunta tace "Nima ban sani ba ina daki" Yayi shiru, ta koma kitchen ta xubo masa girkin da tayi ta fito ta ajiye masa kusa da shi, kallon kirjinta kawai yake da ta durkusa ajiye abincin, ya lumshe idonsa ya jinginar da kansa jikin kujera, don ba karamin nesa yake kai xuciyarsa ba a kanta tun daxu, barin da ya shiga dakinta ya ga tana kuka he wish he can hug her tightly and tell her he isn't angry and he is back all because of her, ta mike tana kallonsa ta wuce sama ta shiga dakinta ta xauna tana tunanin yanda xata yi Aneesah ta san ya dawo gidan, mikewa tayi ta tafi bangarensa tana kallon wayarsa da ya bari kan kujera, dauka tayi ta kulle kofar parlon, ta shiga call logs dinsa amma bata san yanda yayi saving number Aneesah ba, Blossom ta gani can kasa nan da nan ta tuna ta ta6a ganin sunan a phone dinsa da dadewa tayi dialing number, yana fara ringing aka daga.....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via

103 / 117