Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   108 / 117

321K to 324K   out of 348.6K words

ya leko yana kallon Captain yayi masa alamar ya taho, captain ya mike ya shiga dakin gabansa na faduwa, jawo jakarta dake makale gefenta yayi ya bude zip din ya ciro wayar, ajiye wayar yayi ya hau bincika jakar, panties ya gani, da toothpaste and brush, with turarruka, sai kuma Rubber irin wanda ya gani a dakinta har biyu" Juyawa yayi ya kalli Ahmad dake tsaye yana kallon ikon Allah shi kam, Abuturrab ya dinga kallonta da wani expression, sai kuma ya mayar da kayan gaba daya cikin jakan ya kulle, ya dawo wayarta ya kamo hannunta a hankali ya manna finger print dinta a jiki, nan da nan wayar ya budu, sai da ya fara shiga settings yayi adding nasa finger print din yayi saving sannan yana kallon Ahmad yace "Mu je" Fita suka yi dakin xuwa cikin motar Ahmad, tun Abuturrab bai shiga wayar ba yaji xufa na keto masa all over, he don't even get why, ga gabansa da ya dinga faduwa babu kakkautawa, WhatsApp dinta ya fara shiga, Ahmad dai na xaune a maxaunin driver, shi kuma Abuturrab na xaune a kujera me xaman banxa. Alhaji Mukhtar ya fara cin karo as wanda suka yi chatting last, ya shiga chat din ya dinga scrolling yana karanta content din with mouth agape, magana ne a kan inda xa su hadu ya shigo kaduna state from Adamawa, take ce masa mai gidanta is around sai dai next week idan ya koma aiki, tunani Abuturrab ya dinga yi, su hadu su yi me? Wani business din take wanda bai sani bane, iyakar chat din kenan sai kuma dubu ashirin da tace ya tura mata, kuma ya tura mata din don ga receipt, wani chat din Barrister Ismail ya shiga, first abinda ya fara cin karo da shi shine compliment da yake mata a kan darensu na jiya how awesome it was, lkci daya jikin Abuturrab yayi sanyi qlau, ya duba date din chat din ya ga just 3 days ago ne, jinginar da kansa yayi da kujeran mota yana jin xuciyarsa na bugawa da karfi, Ahmad dai sai kallonsa yake kuma bai bukaci ya nuna masa komai a wayar ba cause it's more like his privacy, Abuturrab ya daure ya ci gaba da scrolling chat din, wanda duk erotic talks ne, wani video ya gani na minti daya da some seconds wanda tayi ma iya private part dinta ta tura masa, Abuturrab couldn't hold it any more ya fita chat din ya sauka Whatsapp din gaba daya, without looking at Ahmad a hankali yace "Na gama duba abinda xan duba Ahmad" Ahmad could sense how hurt he is from d way he sound, Ahmad ya kasa ce masa komai, Abuturrab ya kara jinginar da kansa jikin kujera ya runtse idonsa jin kansa yayi masa wani nauyi, Ahmad ya sauka motar yace "Mu Shiga ciki" Da kyar Abuturrab ya bude idonsa ya sauka daga motar, ganin abun yake kamar a mafarki, is this for real?? Ahmad ya xagayo yayi patting shoulder dinsa a hankali yace "It's well bro..." Abuturrab bai iya yace masa komai ba suka shiga gidan yana tafiya slowly. Parlor ya xauna yana kallon Ahmad alamar ya ma rasa abinda xai ce masa, Nafisah da ta shigo parlon xata tafi dakin Hajja ya bi da kallo yace "Ba ni takarda da biro" Ahmad yayi kasa da murya yace "I won't tell u no Aliyu.... Idan baka mance ba farkon aurenku na ta6a gaya maka in har mace ta saba biye biyen maxa a waje in har tayi aure idan ba wani ikon Allah ba it's hard ta iya bari, she is already used to different men, so daya baxai ta6a iya gamsar da ita ba, she can neva be contented with her husband, sai in Allah ya so ta da Rahama wllh, ban ce fa babu wa enda basu dainawa, but gaskiya sune wa enda Allah ya so da Rahamarsa kamar yanda na fada maka, don haka before coming to ur final decision, talk to Ummi first, convince her, and you can even go ahead and show her all this evidence, ba wani xancen jin kunya a issue din nan" Abuturrab ya kasa ce masa komai, duk jikinsa yayi sanyi ba kadan ba, this is the worst thing dat have happened to him na bacin rai da shock, matarsa ta sunna take harka da wasu mazan a waje, shi da yake namiji me yawo gari gari ya iya rike kansa... Ohh This is so sad, ya rike kansa with so many thoughts running his mind, can ya mike ya tafi dakin Hajja don Ummi na ciki, tun da ya shigo Ummi ke kallonsa ganin yanayinsa, Jiddah ma kallonsa take, Hajja kam dama shiru tayi ta hade rai taki kallonsa irin haushinsa take ji har sannan, Abuturrab ya shiga Whatsapp din ya mika ma Ummi, cike da karfin hali yace "Ki d'an duba Ummi" Daga haka ya juya ya fice daga dakin, Hajja ta dago da sauri tace "Ki duba me?" ummi dai sai kallon What'sapp din take bata ma san chat din wa xata shiga ba, kuma taga wayar kaman na Aneesah, Hajja ta mike a rikice tace "Ya xa ki min shiru Hauwa, matsala ya samu wajen aikin ne?" Ummi ta kalleta tace "Aa Hajja, magana ce ya bani in duba" Daga haka ta mike ta fita dakin ta koma parlonta, kamar hadin baki da Abuturrab iya chats din da ya shiga ita ma ta shiga a lkcn, and she couldn't scroll further, har ta fi sa shiga shock din ta kasa rufe baki, dai dai kan video din ita ma ta sauka what'sapp din gaba daya ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Abuturrab ya shigo parlon nata rike da paper da pen, Kasa kallonsa tayi, duk jikinta yayi sanyi qlau, ya xauna saman kujera yana kallonta yace "And i just have to do this Ummi, ni ba mazinaci bane, don haka baxa a so in ci gaba da rayuwa da mazinaciya ba...." Kai kawai Ummi ta iya gyada masa, ta ji tausayin d'an nata ya ratsata, Aneesah ta ci amanar aure, Cikin few minutes Abuturrab ya rubuta abinda xai rubuta a takardan ya mike yayi folding dinsa neatly ya shiga dakin ya ajiye mata a dai dai inda tana juyawa xata ga takardan sannan ya juya ya fita daga dakin, mika masa wayar Ummi da ta ma rasa abinda xata ce tayi, ya amsa yace "Xan tafi da wayar idan Abba ya dawo anjima xan dawo in basa shi ma..." Ummi tace "Aa, xan sanar masa da baki ba sai ka nuna masa wata waya ba" sae kuma kawai ya ajiye ma Ummi wayar yayi mata sallama ya fita ta bi sa da kallo. Abuturrab bai kara minti goma a gidan ba ya dau Jiddah Ahmad yayi dropping dinsu a gida, Ahmad na kallonsa bayan sun sauka yace "We will talk on phone Captain" Abuturrab ya gyada masa kai kawai, ko magana bai son yi, Ahmad yayi reverse ya bar anguwan, Tun da suka shiga parlor Jiddah ke kallon Abuturrab ganin bata ta6a ganinsa a wannan yanayin da yake ciki ba, gashi ya ki ce mata komai, har xata wuce sama ta kasa, ta dawo ta xauna dab da shi tana kallonsa a hankali tace "Are you okay?" Ya dinga kallonta bai ce komai ba ya sauke idonsa, da damuwa tace "You are not saying anything" Ya jawota jikinsa cikin sanyin murya yace "I am fully okay Jiddah, ki je ki huta probably anjima xa mu fita da su Mama" Kallonsa ta dinga yi, can ta mike ta wuce sama ya bi ta da kallo, kwanciya yayi kan 3 seater din yana jin kamar xaxxabi xai rufesa ya runtse idonsa. Kiran Magrib ya sa Abuturrab mikewa duk da ba bacci yayi ba, ya shiga bandakin dake downstairs ya fito ya tafi masallaci. Ana idarwa bayan ya dawo gida yayi minti goma xaune parlor still thinking, sai kuma ya tashi ya tafi dakin Jiddah, yana shiga dakin ya ji kamar an yaye masa damuwar da ta cika masa xuciya, xaune ya ganta can karshen gado ita ma ta yi sallan, tana ganinsa kuma ta dauke kai, ya karasa ya xauna kusa da ita yana murmushi ya kamo hannunta yace "U are sulking" xata kauda kai ya rike kanta giving her a deep kiss, don kansa ya gaji ya kyaleta, yana kallon fuskarta with much love yace "Tell me fushin me kike?" Tayi shiru bata ce komai ba, ya jawota jikinsa yace "I love you Jiddah, and I won't halt saying I am sorry over and over again, i am sorry wife...." Ta turo baki tana kallonsa tace "You are sorry for what?" Yayi kasa da murya yana murxa hannunta yace "For everything i have done to you hitherto...." Tayi murmushi a hankali ta kwanta kirjinsa cikin sanyin murya tace "You did nothing to me than molding me to who i am today, you influence me..." Ya rungumeta sosai yana shakan kamshinta me rikitarsa. Bayan isha Aneesah ta farka daga baccin da take, ta ji kanta yayi mata nauyi sosai, ta dinga bin dakin da kallo, sai kuma ta mike xaune da sauri idonta ya sauka kan farin takardan dake gefenta, dauka tayi tana jujjuya takardan that is folded neatly, haka nan kawai taji gabanta yayi mugun faduwa, sai kuma tayi tunanin ko maganin da Ahmad yayi mata prescribe ne, ta warware takardan da sauri tana kallon content din, "Ni Aliyu Usman na sake ki saki daya, na sake ki saki biyu Aneesah, duk xamanmu idan na ta6a wronging dinki in anyway, forgive me, nima ki je na yafe maki" Wani ihu ta kwala kamar xata tsaga gidan, ta sauka saman gadon dama Hijab dinta na jikinta har sannan, ta fito kamar mahaukaciya parlon Ummi taga babu kowa, main parlor ta fito taga Hajja xaune da Ummi sai Umma a parlon, ta rushe da wani matsanancin kuka ta nufi Ummi ta durkusa tana rike kafarta da karfi take cewa "Me nayi masa ya sakeni, saki ya rubuta min a takarda fa, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga ukuna, don girman Allah Ummi ku rufa min asiri, wllh ina son mijina, me nayi masa ya sakeni kina kallo" Tashi Hajja tayi tana d'an tattaka rawa tace "Rana dubu ta barawo, rana daya ta me kaya...." Haka ta dinga nanatawa tana d'an takawa abinta, Umma dai takaici ma yasa ta kasa kallon Aneesah, she just finish checking all what is on the phone few minutes ago, ita ta ma fi Ummi da Abuturrab shiga wayar deeply, abun yayi muni ainun, Kuka kawai Aneesah take yi tana cewa ta shiga uku a gaya mata me tayi Aliyu ya saketa, Ummi ta girgixa kai cike da takaici tace "Baki kyauta ma kanki ba Aneesah, baki kyauta ba, kin cuci kanki, kin xalunci kanki, kin cuci rayuwar ki, kuma kin ci amanar aurenki, gaya min menene amfanin fornication Aneesah? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aneesah ta dakatar da kukan da take xuciyarta na wani irin bugawa tana xare ido, Umma ta jefa mata wayarta tace "Allah ya shiryeki, ya kuma shirye masu ire iren halinki ya sa su gane, Allah ya rabamu da son xuciya irin naki Aneesah, sai kije kuma kiyi ta istigifari Allah ya gafarta maki...." Sai da Aneesah ta dauke wuta na kusan second goma ta dinga kallon wayarta da Umma ta jefo mata, Hajja ta tafe hannu tace "Allah ya isar ma jikana, Allah ya isar masa wllh...." Sai kuma ta fashe da kuka ta nemi waje ta xauna tayi tagumi tace "Dama duk tsawon lkcn nan da mazinaciya fasika yake xaune a gidansa bai sani ba, bawan Allah yana can yana neman na abinci a sararin samaniya bai rageki da komai ba na bukatar yau da kullum amma kike cin amanarsa haka, ashe dama uwarki bata gasa maki matancinki yanda ya kamata ba Aneesah, mu dai Allah ya isa wllh, na kuma gode Allah da bai sa mun hada xuri'a da mazinaciya ba, wllh da a Masar ne dama katon rami xa a haka a jefa yar iska ciki a bar iya katon kanki a waje, ayi ta jifa har sai kin mutu" Tsam Aneesah ta mike ko ina na jikinta na rawa ta dau wayarta ta fice daga parlon, kamar xata tashi sama ta dinga tafiya har xuwa inda xata samu adaidaita sahu, ta tsayar ta sakar masa kuka tace "Don girman Allah ka taimaka ka ajiye ni nan nan ba nisa bawan Allah, wllh ina cikin tashin hankali babu ko sisi a jikina, ka rufa min asiri bawan Allah" Mai adaidaitan ya tausaya mata yace ta shiga, ya ajiyeta har kofar gidan Abuturrab, ta sauka bakinta na rawa tace "Nagode" a guje ta shiga gidan ta nufi entrance, mai gadi dai ya bi ta da kallo, murda kofar parlon tayi ta shiga kamar an cillota, Abuturrab na xaune parlor kasan carpet Jiddah kuma na xaune opposite dinsa tana yanka masa watermelon ya kafeta da ido ko kiftawa baya yi.... Duk suka daga kai suna kallon Aneesah.


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Mikewa Abuturrab yayi ganin ta nufo su yana mata wani kallo furiously ya nuna mata kofa yace "Fitar min daga gida Aneesah, don't make the mistake of coming closer, leave my house immediately Aneesah..." Cikin tsawa ya kare maganar, ta taho kamar mahaukaciya without minding his words ta cakumosa cikin daga murya tace "Ka gaya min abinda na maka ka sakeni Aliyu?" Bai jira ta rufe baki ba ya shaketa sannan ya wurgar da ita kasa da karfi, Jiddah ta mike da sauri ta nufesa ganin yayi kan Aneesah ta rikosa tace "What is this u are doing?" Ko sauraronta bai yi ba ya dago Aneesah da ta kasa motsi bayan ta fadi kasan tiles, wasu tagwayen mari ya kai mata yace "U still have the guts to question me, u still have d guts to walk into my house? who advice u to come after me? Who gave u this deadly advice" Ya sake lafta mata mari, ya jefar da ita kasa yana ball da ita towards d door kamar ya samu kwallo, fixgosa Jiddah tayi cikin tashin hankali tace "Wai don Allah meye haka kake yi? What is this u are doing" Sai kuma ta fashe da kuka still holding onto him tana jijjigasa ganin bai fasa ball da Aneesah ba, ta dinga cewa "Stop this plss Aliyu, me tayi maka haka, do u have the heart of beating a woman this way??? Are u this wicked? Did a lady deserve this from u?" Bai san sanda ya tura Jiddah saman kujera ba, ya tafi xai dau wayan wuta gun kayan kallon da ke parlon gaba daya ransa ya gama baci biyosa da Aneesah tayi, Da Aneesah ta samu ta mike ta xagaye kujeran a guje ta cafko Jiddah ta shaketa da karfi tana cewa "Ke kika rabani da mijina, ke ki sa ya sakeni, ke kika hada komai da ya faru, yau xan ga ko da gawarki xai kare rayuwarsa, wllh sai dai wata ba ke ba" Abuturrab ya nufeta with full speed yana kokarin freeing Jiddah daga rikonta, komawa tayi kamar mahaukaciyar gaske tana gwale ido tana ci gaba da shake Jiddah, duk da dukan da yake kai mata taki sakinta, gaba daya hankalinta da idonta na kan wukar da ke kasa kan tray, kamar dai wancan lkcn da ta rike Jiddah a asibiti yau ma hakan ne tayi, duk karfin Abuturrab he couldn't free jiddah, duka ba na wasa yake mata ba amma taki cika jiddah, idan kuma yace xai yi amfani da force he will definitely hurt Jiddah, wani kukan kura Aneesah tayi ta hankade Jiddah ta fada kanta tana kokarin jawo wukan da take ta kallo da hannunta tana cewa "Wllh sai na kasheta idan ya so nima a kasheni, gwara in kasheta nima a kasheni duk mu bar duniyar babu me xama da kai...." Abuturrab yayi hanxarin sa kafa yayi wani ball da wukan kafin hannunta ya kai kansa, ya duka kasa ferociously ya kama hannun da ta so daukan wukan da shi yayi masa wani mugun murda har sai da yaji hannun yayi wani kara sannan ya sake, lkci daya jikinta ya mutu tayi wani karan axaba ta kasa ci gaba da rike Jiddah, with full strength ya dagota sama daga kan jiddah, ya dinga kifa mata mari yana kai mata kulli, jefar da ita kasa yyi yana haurinta yana tattaketa, ihu kawai take yi ta kasa tashi sbda hannunta da taji kamar baya jikinta gashi ta kasa daga hannun, ya kara dagota da hannu biyu ya bugata da pillar din dinning area, jini ke xuba ta bakinta da hanci, mari kuwa har sai da yaga palm dinsa sun kwanta a fuskarta sannan ya dinga jan ta kamar rago ya nufi kofa da ita, bai tsaya ko ina ba sai bakin gate ya wani cillata waje yana kallon mai gadi da ya ja gefe a tsorace, cikin tsawa yace "Kada ka sake barin ta shigo gidan nan, ka ji me nace maka??" Mai gadin ya gyada kai da sauri yace "Na ji Yallabai..." Aneesah ta mike da kyar ta xube kan gwiwowinta tana son hade hannunta amma ta kasa daga daya hannun nata, gaba daya tayi weak, cikin kuka sosai tana maida numfashi tace "Don girman Allah kar ka min haka Aliyu, wllh ina sonka baxan iya rayuwa babu kai ba, don darajan annabin Rahama kar ka gujeni, wllh xan iya kashe kaina idan na rasaka, I can't continue leaving without you Aliyu, wayyoo na shiga uku na lalace, kar ka rabu da ni Aliyu" Tuni Abuturrab yayi banging gate din ya sa lock ya nufi entrance din gidan da sauri, Xubewa

108 / 117