Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   115 / 117

342K to 345K   out of 348.6K words

rabata da ita.





*Wannan littafi dai ya ki karewa bayan nagaji da shi shima ya gaji dani9&? ko da yake nasan me xanyi* =??


_4 years later_..... >???



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Parking Aunty Rahama tayi a kofar gidan Abba, Hajja dake bayan motar tana washe baki tace "Allah ya maki albarka, in sha Allahu nan da kwana biyu xan dawo anguwan naku gaba daya kin ji?" Aunty Rahama na murmushi tace "Toh Allah ya kawo ki lafiya kaka" Jiddah dake gaban mota tace "Mun gode Aunty" Aunty Rahama na mata murmushi tace "In kun shiga ki gaida su mama kin ji" Hajja tace "Au ni da nake xaton xaki shigo ku gaisa" Aunty Rahama tace "Aiki xan tafi kaka, na makara wllh" Hajja tace "Aa kin makara gaskiya gashi har tara saura, to ke mijin naki ba a kasan yake bane?" Tayi murmushi tace "Allah ya mashi rasuwa kaka" Hajja ta saki wani salati tayi tagumi cike da damuwa tace "Allah sarki, Allah ubangiji ya gafarta masa, to baki da 'ya ya da shi ne?" Tace "Ina da, su biyu ne, suna gun yayansa a Abuja, sai hutu ake kawo min su" da sauri Hajja tace "Aa ki amshe yaranki, ce masu kika yi baxa ki iya kula da su ba ko salon kar yaran su ji kanki su san ciwonki" Ita dai murmushi kawai take, Hajja tace "Wllh amshe abin ki, ni ban yarda da rikon d'a ba..." Daga haka ta bude motar ta sauka, Jiddah ma ta sauka tana kara yi ma Aunty Rahama sallama suka shiga gidan da Hajja, tun daga parlor Hajja ke kwala ma Ummi kira, Ummi na fitowa tace "Toh dai Jiddah ba yar matsiyata bace, kuma kakarta na nan da ranta sai kin ga abun arzikin da aka mana a wannan gari na gombe, mutanen kirki mutanen arxiki suka cika garin, sun karrama mu sun daraja mu sun mutunta ba, wllh basu so mu taho ba amma wannan yayan baban nata Alhaji Sani naji ana ce masa ko wa? Wannan dai da ya mana jagora xuwa garin shi ya axalxala mu taho, in don ta nine da bamu dawo ba wllh, jiya da daddare muka dawo to yau naga wnn yarinya Jiddah sai wani nukurci take taki kulani nace to ko kewan mijinta take shine dai nace su maido mu gida da safe, amma wllh dangin ubanta en arxiki ne babu talaka ko kwaya daya a cikinsu, ke kin ga gidan ma kuwa, wllh yayi biyar din wannan, kuma kinsan gidan waye, gidan uwarsu ne, su suka gina mata gwanin ban sha'awa, ai ita kam ta more rayuwa wllh...." Ummi tace "Toh Alhmdlh, nayi murna sosai, Allah ya bayyana dangin mahaifiyarta haka" Hajja tace "Allah gidan yayi ukun wannan kuma tsohuwar kadai ke rayuwa a ciki, duka duka fa bai fi ta girmeni da shekara uku ko hudu ba, amma sai kin ga abinda yaranta suka kera mata, tana xaxxaune ta mike kafa sai dai ayi mata komai" Ummi ta amsa gaisuwar Jiddah da ta duka kasa ta gaisheta, Ummi tace "Ya hanya, fatan kun dawo lfya, ya kuma ku ka bar mutanen can din" Hajja ta amshe tace "Alhmdlh, babu abinda basu mana ba, yanxun ma fitowa muka yi ba shiri ita kuma warce ta kawo mu tana ta sauri xata aiki, banda haka in gaya maki ai tsarabanmu da yanxu haka ba a gama shigowa da su ba, to sunce anjima da yamma xa a taho mana da shi, ke dai ki bari kawai Hauwa, karramawa da mutunci na inda yake, ni kam bani da abinda xance ma mutanen nan" Daga haka ta wuce dakinta, Ummi da ta bi ta da kallo tace "A kawo maki kumallo Hajja" Hajja tace "Meye kuma kumallo? Aa mu mun yi lafiyayyen kari, kawai a bani makullin d'an kuturun dakina" Ummi ta tafi dauko mata makullinta ta kai mata, ta bude ta shige ciki tana kyabe baki, Ummi ta dawo parlor ta xauna tana kallon Jiddah tana murmushi tace "Kin je kin ga kaka da kawunnanki ko?" Murmushi Jiddah tayi ta gyada mata kai, Ummi tace "Toh Alhmdlh, Alhmdlh, i am so happy for you daughter" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta kawai, Tashi Ummi tayi ta tafi parlon Abba, Jiddah ta dinga kallon hanyar dakin Abuturrab amma ta kasa tashi, ta fi minti biyar sai ta kalli dakin sai ta dauke kai, can dai ta mike a hankali ta nufi dakin kamar munafuka muryan Ummi taji tace "Ai bai nan ya koma aiki Jiddah" kunya ta ji kamar ta nutse, ta kasa juyowa ta kalli Ummi, jin shiru sai kuma ta juyo a hankali, gani tayi Ummi bata ma wajen, da sauri ta wuce dakin Hajja. Washegari da safe Jiddah na dakin Hajja, Hajja na cewa "Kin ga ai ni bana kai kaina inda Allah bai kaini ba kuma bana takura ma yarana ince sai sun min abu dole, da wata ce yanxu duk sai ta kwarzabi yaranta tace sai fa an mata gini irin na wannan kakar taki, amma ni kam Allah ya kiyaye inyi haka sai kace wata er banxa, ni ko burgeni gidan bai yi ba balle inji sha'awa ince a min irinsa" Jiddah dai kallonta kawai take amma bata ma san me take cewa ba, kewan Abuturrab kawai take, ji take kamar ta fi wata daya rabon da ta gansa, she's a kind of sad, gaba daya ta ji gidan ya isheta, gashi bata san sanda xai dawo ba, ga surutun Hajja dake sa mata ciwon kai, tayi mata xancen gidan Dada ya fi sau ashirin daga jiya xuwa yau, har Umma da ta xo jiya ta bata labari, Hajja ta ta6e baki tace "Ba ruwana da sa ma wani ido wllh, nagode Allah da inda ya ajiyeni, shege ne kawai xai dinga hangen abun wasu" Bude kofar dakin aka yi Ummi ta shigo tayi ma Hajja sannu, tana kallon, Jiddah tace "Ur husband said he will be back in the evening of today, so get ready after Zuhur, i will instruct the driver to drop u home" Tace "Toh Ummi" Juyawa Ummi tayi ta fita, Hajja ta ta6e baki tace "To ko matansa ma basa hanasa ya min kantamemen gini ba don bakin ciki, ai kai dai kawai ka haifar ma mace yaro kawai, bayan haka baka da sauran martaba a wajensa" Tun da Ummi ta fita Jiddah ke counting agogo sai taga baya sauri, wai karfe goma da rabi, har bacci tayi ta tashi wai karfe sha daya, kawai daga karshe ta mike ta fita daga dakin Hajja ta tafi part din Ummi... Ummi ta ajiye littafin hannunta tana kallonta tace "Ya aka yi Jiddah?" Kunya taji ya rufeta, Ummi tace "Ko har kin shirya?" Tayi karfin halin cewa "Ehh Ummi ina son xanje inyi girki ne" Ummi tace "Eh gaskiya kam, bari in kira driver din, shiga ki dauko jakarki to" Kanta a kasa ta shiga dakin Ummi ta dau jakarta ta fito dama da Hijab dinta a jikinta, bayan Ummi ta kira driver ta mike ta tafi daki ta dauko mata makullin gidan nasu, tana mika mata tace "ki je ki ma Hajja sallama kice mata xaki gidan Umma ne" Jiddah tace "Toh" Ummi tace "Idan kin mata sallaman ki samu driver din yana waje" Jiddah tace "Ummi ina son in siya wasu abu a kasuwa ne..." Ummi tace "Kina da kudi wajen ki ne?" Girgixa mata kai tayi, Ummi tace "Toh bari in baki Atm card, idan ya dawo sai ya maido min da card din nawa" Atm card din ta dauko ta mika ma Jiddah ta gaya mata pin din tana kara nanata mata kar ta manta, Jiddah ta risina ta amsa tayi mata godiya ta fita, kallonta Hajja ta dinga yi sai kuma tace "Me ake yi a gidan Umman?" Jiddah tace "Kawai xan je ne" Hajja tace "Toh sai mijin naki ya dawo xamu koma can gidan kin dai ji abinda nace ma dangin ubanki kar su daukeni makaryaciya idan basu gan ni ba" Jiddah tace "Ehh sai ya dawo" Hajja tace "Toh ki gaida Ramlan" Jiddah ta juya ta fita, sai da driver ya fara ajiyeta kasuwa ta siya ingredients din fried rice da zobo drink, tunda suna da nama a deep freezer bata siyi komai ba banda liver, daga nan driver ya ajiyeta gida tayi masa godiya ta shiga ciki bayan ta gaida mai gadi. Tana shiga cikin gidan ta kai kayan girkin kitchen ta tafi sama ta canxa kaya xuwa kanana sannan ta fara gyaran gidan, ta tsaftace ko ina tayi mopping da goge goge ta kunna turare a burner, sai da tayi azahar sannan ta shiga kitchen.... Kafin la'asar ta gama hada lafiyayyen fried rice dinta with zobo drink, ta soya kajin tayi pepper chicken da shi, sai farfesun offals da tayi kadan, duk ta jera abincin a dinning, ta koma ta tsaftace kitchen din kamar bata yi komai a ciki ba ya dawo fes fes, sama ta wuce dakinta ta shiga wanka, da alwalanta ta fito sai da tayi salla snn ta fiddo da kayan da xata sa, ta dau kusan minti talatin tana shirya, ta saka wasu ubansun English wears masu daukan hankali, ko ina na jikinta wani sanyayyan kamshi ne ke tashi, tayi packing gashinta da ribbon leaving it that way, she look just like a princess, tayi kyau sosai, bude gate taji anyi ta karasa window tana kallon waje yaga Abuturrab ne ya shigo da motarsa... Sauka tayi downstairs ta tafi bakin kofa ta tsaya, she is just so happy, ta labe a gefe daya har ya bude kofar, wani kara tayi da nufin basa tsoro, ya jawota jikinsa yana kallonta daga sama har kasa yana murmushi, 6ata fuska tayi yayi kasa da murya yace "Jirgi bai bani tsoro ba sai matata?" Dariya tayi ta boye fuskarta jikinsa a hankali tace "Wel??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????come my Man" Ya lumshe ido ya bude yana shafa bayanta yana kare ma dressing dinta kallo yace "U look sexy in this wife..." Sai kuma ya kankameta yace "Wllh i have missed u so much wife, Hajja bata kyauta min" amsar jakan hannunsa tayi tana murmushi tace "I missed u more dear... Abinci ko wanka?" Ya girgixa kai yace "Sallah" Tace "Toh mu je" Sai da yayi sallah sannan yayi wanka bayan ta hada masa ruwan wankan a bedroom dinsa, kafin ya fito ta ciro masa kayan da xai sa, sannan ta sauka downstairs ta dauko girkin da tayi xuwa parlonsa, xata shiga bedroom bayan ta gama hayowa da abincin suka kusa cin karo, sai taga ko kayan da ta ciro masa ma bai sa ba sai short, daukanta yayi kamar baby xuwa bed din dakin, ta marairaice masa tace "Dear ga fa abinci can..." Bai bata daman ta karasa ba, ya dinga ce mata yayi missing dinta so much, kamar yanda ya tara mata gajiya ita ma dai hakan tayi masa, bai ta6a tunanin da akwai sanda jiddah xata sake haka da shi ba balle har ta maida masa martani.... Sai bayan ya dawo magrib ta xuba masa abincin da ta girka masa, yana kallonta ta gefen ido yace "Ke dai fadi gaskiya Baby wannan abincin daga gidan Ummi kika taho da shi ko?" Murmushi tayi tace "Ae wannan ma da na ta6a xuba ma Colleagues dinka da dadewa ka kusa cinyewa baka sani ba... Shi ma ai daga gidan Ummi...." jawota yayi jikinsa ya matseta ya buda idonsa yace "Ni xa ki ma sharri?" Dariya tayi tace "Kai ka fara min sharri ai" ya lumshe ido yana murmushi yana shafa dogon gashinta yace "U are really a good cook wife, i know i am blessed... tun daga wannan ranan da kika xuba ma Colleagues dina abinci na dandana na san haka, i was stunned after tasting ur food that day, how possible i thought to my self many times" Tana murmushi tace "Saboda i am too local then ko?" Ya dago kanta yace "Daga sanda na raba ki da hayi kika bar locality dinki a can, u left that locality behind... Ban ta6a tunanin xaki fahimci abubuwa ki koyi abubuwa lkci daya ba jiddah, u were a fast learner... A iya xamanmu na farko I can't say ko na ta6a maki wani correction kan abubuwan da na koya maki" Ita dai murmushi kawai take, yayi kasa da murya yace "Tun daga sannan kika fara burgeni, when i notice u were always clean" Ta d'an saci kallonsa tace "Ashe ina burgeka" He couldn't help it but laugh, sai kuma ya rike kansa yace "Sosai Jiddah, in dai na barki a gida na tafi aiki bani da sukuni up in the sky sai na dawo gidan nan, i hate seeing u sad or worried hakan na karyar min da xuciya..." Ta kwantar da kanta kan shoulder dinsa tace "Kawai dai so na ne baka yi a lkcn ko??" Jin yayi shiru ta daga kai ta kallesa, kallonta taga yana yi babu ko kiftawa, sai kuma ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Na kan yi sha'awanki a lkcn" Ta d'an buda ido tana kallonsa tace "Wani iri" Ya lumshe ido yana shafa laps dinta yace "Irin wannan but i always try hard to fight it away, i always put in the back of my mind that i am just ur guardian" ita dai Murmushi kawai take, ganin ya ki daina abinda ya ke mata a kafa ta turo baki tana kallonsa, tuni taga idanuwansa suka canxa, ta marairaice tace "Ni wllh na gaji ko abincin fa ban ci ba..." Wannan fried rice din dai sai wajen karfe sha daya na dare aka ci sa, Abuturrab ne ya fara tafiya sama bayan ya wanke baki ya kwanta cause he is so very exhausted, ta gama wanke duk abubuwan da suka 6ata, ta sa turaren wuta ta jira yayi a parlon sannan ta kashe komai ta wuce sama, bedroom dinta ta tafi ta sake wanka ta wanke baki sannan ta saka kayan baccinta ta kashe wutan dakin ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa, can wajen karfe biyu Abuturrab ya koma dakinta ya kwanta because he can't resist sleeping without her close to him... Haka rayuwarsu ya ci gaba da gudana cike da so da kaunan kamar su maida junansu ciki, in dai yana gari bata da sauran sukuni har ma ta sa6a da kwarzabanta da yake, ya kuma yi programming dinta a yanda yake, ya maidata irinsa, shi yasa bata wani wahala ko gajiya da shi, kusan inda Abuturrab ya tafi wajen aiki ta kan shiga gidansu Hajiya Fatima har ma ta yini, Hajiya Dada kuwa duk bayan 2 days ko ita bata kirata ba ita xata kirata don Abuturrab ya siya mata exactly irin wayar da ya siya mata wanda Aneesah ta hade da kayan daki ta dagargazar, hka sauran Uncles dinta da aunt duk suna gaisawa a family group da aka sakata a ciki, she felt belong now, ko ba komai yanxu tana da wa enda xata nuna tace ai wa ennan dangina ne na jini, kowa a familyn ji yake da ita, sau dayawa idan Alhaji Ishaq ya shigo kaduna komai ya kawo ma su khaleesat sai ya raba dai dai da Jiddah ya bada a kai mata, hakan na yi ma Jiddah dadi sosai, jinsa take kamar mahaifinta na gaskiya, Hansai kuwa ta kusa sati uku yanxu a gombe wajen Hajiya Dada.... Yau duk da tasan Abuturrab na hanya sai duk ta kasa tashi tayi abinda ya kamata a gidan gaba daya wani kasala take ji tun da ya tafi ya bar ta, da ta yunkura xata yi aiki sai taji ta kasa sai dai ta koma ta kwanta, gashi gaba daya appetite dinta na cin abinci babu, ko a waya kuma bata sanar masa yanda take ji ba, ganin dai ya kusa shigowa ta mike da kyar tayi karfin halin shiga bandaki ta hada ruwan wanka tayi wanka sannan ta fito ta saka turare sama sama ta shirya, kwanciya ta koma tayi don taga alamar fa baxata iya ta6uka komai a gidan ba, tana jin shigowar motarsa bayan la'asar, ta daure ta kara mikewa ta sauko downstairs, dai dai nan ya shigo parlon karasawa tayi ta shige jikinsa kamar yanda ta saba in dai ya dawo, rike breathing dinta tayi sbda wani hautsine mata ciki da kamshin turarensa yayi, ta sa hannu ta rufe bakinta da hancinta, da mamaki yake kallonta yace "Baby me ya faru" Ta fara masa alamar amai na taho mata, da sauri ya ja ta xuwa bathroom dake parlorn, ganin yanda take aman yace "Oh my God baby dama baki da lafiya ne?" Ta kasa basa amsa sai sauke numfashi take, fitowa yayi da ita daga bandakin, ko minti biyar basu kara a gidan ba ya tafi da ita hospital, tun da suka shigo Aneesah dake xaune reception ta dinga rurrufe fuskarta tana kallonsu kasa kasa, shi kam ko lura da ita bai yi ba haka jiddah dake fama da kanta, bayan an duba Jiddah Abuturrab ya kasa boye farin cikinsa bayan likitan ya sanar masa tana dauke da ciki na sati uku, he felt like kissing and caressing her in public, he was so very happy, kasa daurewa yayi daga karshe ya rungumeta gam a office din likitan ya dinga sa mata albarka, sai bayan kusan 30 mins suka fito haraban hospital din yana rike da hannunta da few drugs da aka bata sbda amai da kasalan da take, gently yake tafiya da ita don bai son anything that will stress her, don ma cikin mutane ne da daukar abarsa xai yi baxata taka kasa ba, tun shigowarsu asibitin da minti goma aka sallami Aneesah amma ta kasa tafiya ta xauna karkashin bishiya a haraban asibitin tana jiran taga fitowarsu, tana

115 / 117