Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   105 / 117

312K to 315K   out of 348.6K words

ya fi damunki, ni damuwata ta yaya xa ace mutum bashi da dangin uwa bashi da dangin uba kamar daga sama ya fado? Ai idan tana son samun 'yan cin kanta dole sai ta san su waye danginta, idan ba haka ba no matter kwanciyar hankalin da xata samu dole sai an mata gorin dangi, kishiyarta baxata ta6a daina mata wannan gorin ba, kai har shi wataran wllh sai ya mata gori, ki kyale maxan nan kawai" Rahama tace "Gaskiya ne kuma, to yanxu ya xa ayi kenan mama?" Tace "Ni nasan yanda xanyi in sha Allah" Aneesah na xaune parlor da kawayenta su hudu tun bayan da ta kirasu ta sanar masu abinda ya faru suka yo xuga xuwa gidan, labarin yanda captain ya ji da ita daren jiya ta dinga basu, da irin yanda suka rabu yau da asuba, Fauziyya da Rabi'ah suka yi wani shewa suka ce "Gaba da gabanta, ba kin tsaya sanya ba da, kin xauna kina ta hauka da fashe fashe da dambe a asibiti, to ai yanxu kin fara ganin aiki da cikawa" ita dai sai wani blushing take, Wayarta ne ya fara ring tayi masu alama duk suyi shiru daga surutun da suke, lkci daya suka yi tsit, ta daga ta kai kunne a hankali ta rausaya murya tace "My Captain" Yace "How are you feeling?" Tayi fari da ido tace "Alhmdlh, da sauki, sai dai ciwon kan ne kawai bai tafi gaba daya ba" Yace "Toh Allah ya kara lafiya" Tana wani murmushi tace "Ameen, na ga sakon da ka turo daxu, nagode My captain" yace "You are wlcm" tace "Kana lagos ne?" Yace "Yeah... Kai ma Jiddah waya" Ta d'an yatsine fuska tace "Ai kam daxu na ga ta shirya ta ci kwalliya ta fita, bata ce min komai ba nima ban ce mata ba gaskiya, don abinda ta min jiya yayi min ciwo" Yace "Ta fita?? To where?" Tace "Aa ban sani ba karya haramun, na dai ji tana waya wai ga ta nan fitowa yanxun nan, har nake tunanin ashe tana da waya don ni ban ta6a ganinta da waya ba sai yau" Shiru yayi bayan few seconds yace "Sai anjima" Tace "Alright my captain" Daga haka ya katse wayar, ta fashe da dariya tana kallon kawayenta da suka hau hailing dinta, tayi kasa da murya tace "Kun ga anjima sai in ce masa an kawota an ajiye a mota naje raka Rabi'ah da ta xo dubani na gani da idona" Abuturrab na gama waya da Aneesah ya shiga kiran Maimoon, Maimoon na dagawa bayan ta gaishesa yace "Kina ina?" Tana magana kasa kasa tace "Islamiyya" Katse wayar yayi, ya ma rasa tunanin da xai yi, sai kuma ya hau kiran Umma, bayan sun gaisa tace "Ya su Jiddah?" He was s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hort of word at first, sai kuma yace "Alhmdlh Umma" Tace "Ahmad ya gaya maka sun koma makaranta ko bai gaya maka ba" Yace "Ya gaya min" Tace "Toh yayi kyau" sallama yayi mata yace "Dama na kira ne in gaisheku" Tace "To madallah, Allah yayi albarka" ya amsa da Ameen ya katse wayar, Ummi ya kira nan ma sai da ta tambayesa Jiddah da Aneesah hakan ya nuna masa Jiddah bata gidan, yayi mata sallama ya katse wayar....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Aneesah na ta shiryawa a dakinta bayan magariba, ta dau duk wani abinda ta san xata bukata a er jakarta bata da yanda xata yi ne kawai amma yau kam bata yi niyyar fitar ba ma, wayarta ne ya fara ring, ta xaro ido ganin Abuturrab ne ke kiranta, ta dauka ta xauna gefen gado tayi kasa da murya tace "Hello my Captain" Yace "How are u doing?" Ta langwabar da murya tace "Alhmdlh wllh" yace "Ya jikin?" Tace "Aa naji sauki Alhamdulillah yanxu" Yace "Ohk, ta dawo gidan?" Tace "Ehh fa, Rabi'ah just left few minutes ago na fita in rakata motarta naga ita kuma an dawo da ita ta sauka daga wata mota" Yace "Motar??" Tace "That was what i saw, dama da baka tambaya ba ba ruwana ai tunda ban san wa ya sauketa ba, xai yiwu ko d'an uwansu ne" Yayi shirun kusan second ashirin, har sai da tace "Hello" Yace "Alright, sai mun yi magana" Tace "Ohk my captain" Katse wayar tayi, ta ajiye tayi shiru, anya ya kamata ta fita yau kuwa, kar ta fita ya dawo unexpected fah, but his schedules tomorrow are so tight don karfe bakwai da rabi take jin xa su yi piloting xuwa lagos, tana ta tunane tunane wayarta ya fara ring kuma, ta duba da sauri taga shi ne, ta daga ta kai kunne tace "Hello my Captain" Yace "Can u pls go give her d phone?" Sosai hankalinta ya d'an kwanta, which means baxai dawo din ba kenan, mikewa tayi sai kuma ta tuna fa bata ji shigowar Jiddah ba har yanxu, har kawayenta suka gama jiranta suka bar gidan bata dawo ba, kilan ma gidan Umma ta tafi, da sauri tace "Kana ganin babu matsala captain, kar in kai mata kuma fa ta xageni, kaga ni bana son fitina wllh" Yace "Ki kai mata" mikewa tayi tace "Toh" daga haka ta fita daga dakin ta nufi dakin Jiddah ta bude kofar a hankali ta leka ciki taga babu ita babu alamarta, kulle kofar tayi ta fara knocking ta yanda xai ji... tana cewa "Assalamualaikum, Jiddah xa ayi maki magana a waya, Jiddah, Jiddah..." Ta kira sunanta yayi sau biyar, sai kuma ta juya tace "Ka dai ga... Tana ji wllh taki cewa komai Captain, kofar ma ta sa key" Yace "Ohk, sai da safe" Tace "Toh Allah ya kai mu captain, goben xaka dawo ne?" Yace "No, sai friday da safe in sha Allah, i will be piloting all throughout" Tace "Toh shkkn Captain Allah ya kai mu Friday din, Allah ya tsare min kai, sai mun yi magana gobe" Yace "Ameen... In sha Allah" Daga haka ya katse wayar, tayi wani murmushi tana jujjuya wayar hannunta ta koma dakinta ta karasa shirinta a hanxarce, wardrobe dinta inda take ajiye bedsheets ta bude ta daga squeezed bedsheeta din nata ta dau wani sealed abu a leda ta cusa cikin handbag din nata, tana ganin xanuwan gadon suka xubo kasa ko bin ta kansu bata yi ba ta dau Hijab dogo ta saka ta boye handbag din ta cikin hijab din ta bude dakin ta fito ta kulle da makulli ta sauka downstairs, ta daga wayarta da ya fara ring tace "Gani nan tahowa na fito yanxu" daga haka ta katse wayar ta fito compound, sosai taji dadin ganin mai gadi yana sallah a compound din yayi backing dinta, ta lallaba tana tafiya a hankali ta nufi gate, ta bude ta fice daga gidan. Jiddah na xaune parlon Hajiya Fatima sanye da Hijab din Khaleesat, Hajiya Fatima ta gama waya da mai gidanta da baya kasar bayan ta nemi izininsa na cewa xata fita, ajiye wayar tayi ta kalli er ta Rahama tace "Toh yanxu ita haka xa a fita da ita babu izinin shi mijin nata?" Aunty Rahama tace "Atohh ai komai kamawa yake Mama, ba kuma fitar shiririta xa ayi ba, da ma dai ana son yasan tana nan ne sai ki amshi numbersa a wajenta ki kirasa, amma ni wllh bana son ma yasan tana gidan nan" Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ko dai a amshi number tasa a wajenta sai a kirasa kar ma aje ayi ta nemanta mun ajiyeta a nan" Aunty Rahama tace "Mama don Allah mu je mu dawo, ayi ta nemanta din, yasan baya son ya nemeta me yasa xai barta da wnn rikakkiyar matar su biyu kadai a gida, ai shima yayi kuskure wllh, bai yi tunanin abinda xai je ya dawo ba" Mikewa tayi ya fita, mahaifiyarta ta bi bayanta, Jiddah dai kanta na kasa, Hajiya Fatima tace "Kina da number Aliyun ai ko?" Jiddah ta girgixa kai tace "Aa bani da shi" Tace "Toh tashi mu je" Mikewa tayi ta nufi kofa suka bi bayanta, Aliyu dake xaune parlor yana jiran fitowarsu tun daxu ya mike ya fita yana rike da makullin motarsa, Jiddah da Hajiya Fatima suka xauna back seat, Aunty Rahama kuma ta xauna a gaba, cikin minti ashirin suka isa hayin rigasa, Jiddah ta nuna masu hanyar gidan nasu, bayan Aliyu yayi parking ya juya yana kallon Mum dinsa, Hajiya Fatima na kallon Jiddah tace "Xa mu shiga ciki ke ki xauna a mota kin ji" a hankali Jiddah tace "Toh" Duk suka sauka motar har Aliyu suka bar ta ita kadai, Aunty Rahama ce tayi sallama kofar xauren gidan, wani d'an tsoho ya fito yana kallonsu yace "Wa ku ke nema?" Hajiya Fatima ta gaishesa tace "Sannu baba, matar gidan fa?" Ya d'an buda ido yace "Wai matata?" Sake lekowa waje yayi yana xaro ido ganin katuwar motar dake parke a firgice yace "Bayin Allah lafiya kuwa?" Hajiya Fatima tayi murmushi tace "lafiya lau baba, kar ka wani samu damuwa" Tsohon da ya ji hankalinsa ya kwanta yace "Toh bari ayi kiranta..." Juyawa yayi ya koma ciki sai gasu sun dawo tare da matar tasa, ita ma a tsorace take kallonsu tace "Lafiya??" cikin kwantar da murya Hajiya Fatima tace "Ba ke ce Malama Hafsatu ba" Da sauri matar tace "Aa bani bace ba wllh...." Tsohon yace "Hajiya siyan gidan muka yi, ko wata uku bamu yi da dawowa nan ba..." Matar tace "Kuma tunda muka dawo nan yan bashi ke xuwa neman matar nan da kika ambata, kusan kullum sai an xo mana nan... idan ku ma bashin ya kawo ku to kuwa ance bata ma garin ta gudu, ta cinye ma jama'a kudi ta tsere" Hajiya Fatima tace "Hasbunallah, yanxu bata garin nan kuma?" Matar ta tafe hannu tace "Wllh kuwa, wannan gidan ma da ta siyar ance ko dubu hamsin bata tsira da shi ba sbda duk bashin lapo ta biya, kuma har yanxu da nake maki wannan magana mutane sun fi ashirin da take bi bashi a hayin nan, ta tsallake kawai ta bar garin, an dai ce hakkin er marigayin mijinta ke bibiyarta, mu ma haka muka ji, wllh babu wanda yasan inda take" Hajiya Fatima tace "Toh Allah ya kiyaye Allah ya kyauta" Suka amsa da "Ameen" Hajiya Fatima da su Aunty Rahama suka juya suka koma gun motarsu, Jiddah dake cikin motar sai kallon wasu mutane da suka fito daga gidansu a maimakon babarta da Bibalo take, nan da nan taji gabanta ya fadi, Hajiya Fatima ta bude bayan motar tana kallonta, sai kuma tayi kasa da murya tace "Babu wani naku a unguwar nan bayan stepmum din taki Jiddah?" A sanyaye Jiddah tace "Basa gidan kuma ko Mama?" Hajiya Fatima tayi shiru tana kallonta, sai kuma a hankali tace "Ta siyar da gidan, ta bar garin" Jiddah bata san lkcn da ta fashe da kuka ba, Hajiya Fatima ta hade rai tace "Meye haka kuma? Meye na kuka? Kukan naki ne xai dawo da ita" Jiddah ta girgixa mata kai tana share idonta wasu hawayen na xubo mata tana tausayin rayuwarta kuma, Hajiya Fatima da duk jikinta yayi sanyi tace "Wa kike tunanin a unguwar nan gaba daya xai iya sanin inda ta tafi ko inda ta koma?" Jiddah na share idonta da kyar tace "Kila Iyah, ga gidanta can" Hajiya Fatima ta sa ta sauko daga motar suka nufi gidan Iyah gaba dayansu, banda Aliyu dake jingine jikin motarsa, sosai shi ma yake tausayin Jiddah... her story is heartbreaking, no relatives, no siblings, no parent, nothing nothing, what a life, Jiddah ta rungume Iyah bayan sun shiga gidan, Iyah ta kasa boye farin cikinta ta rasa inda xata sa Jiddah tsabar murnan ganinta sai ta fara hawaye, Hajiya Fatima dai kallonsu kawai take tana tsaye daga gefe da Aunty Rahama, Iyah ta farga da su ta dauko tabarma da sauri bakinta har kunne ta shimfida masu tace "Sannunku da xuwa, kun xo bamu da wutan nepa, fitina kuma batur yayi sanyi, ku xauna don Allah" Hajiya Fatima ta xauna, Aunty Rahama ma ta xauna sannan suka kara gaisawa, Iyah na kallon Jiddah dake xaune ita ma tayi nisa tunanin da take tace "Jiddah Hansai dai ta siyar da gida ta bar garin..." Jiddah ta sauke idonta kasa wasu hawayen na taruwa idonta, A Hankali Hajiya Fatima tace "Haka muka samu labari kaka, domin can muka fara xuwa kafin nan, yanxu kaka baki da masaniyar inda ta koma" Iyah tace "Ai babu wanda yasan inda wannan mata dai ta koma, duniya tayi mata xafi, kowa ya juya mata baya, er ta kuma Bibalo ta dauko mata abun kunya, ko kafin su bar anguwan nan bibalo Haihuwa yau ko gobe, abun dai babu dadin fadi, Hansai na cikin gararin rayuwa yanxu..." Hajiya Fatima tace "Ya salam, Allah ubangiji ya bamu dacewa..." Iyah tace "Ameen, alhakin Jiddah kadai ya isa hanata xaman lafiya a duniya duk inda xata je kuwa, haba ai Allah ba axxalumin bawansa bane, ta xalunci yar nan da kike gani, ta xalunci uwarta... Duniya kam ta juya ma Hansai baya, ita kanta kawarta me xuxxugata tana can ciwon kafa ya sa ta gaba ana tunanin yanke kafar ma xa ayi, bata iya xuwa ko ina, Zulai ba" Jiddah dai sai kallon Iyah take hawaye na sauka idonta, Hajiya Fatima tace "Toh ita zulan yanxu bata san inda Hansatun take ba?" Iyah tace "To sai dai ko gobe in shirya inje in jiyo maku, amma babu tabbas ta sani, in sha Allah ni dai xan je" Hajiya Fatima tace "Mun ko gode kaka Allah ya kara girma" Dubu uku Hajiya Fatima ta ajiye ma Iyah daga haka suka yi mata sallama da xummar gobe xa su dawo su ji yanda suka yi da Zulai a kan whereabout din Hansai, har suka koma gida Jiddah jikinta a sanyaye yake sai goge hawaye take a idonta, Hajiya fatima ta sa yayar Khaleesat ta kawo mata dinner don bata ci ba kafin su fita. Karfe tara da yan mintuna that same day Abuturrab yayi horn bakin gate din gidansa, Mai gadi ya taso da sauri ya bude masa gate din ya shiga yayi parking sannan ya sauka, gaba daya a gajiye yake, kwanan nan stressing kansa yake sosai na kai wa da komowa da yake xuwa kaduna, ya shiga ciki yana jin shoulders dinsa na ciwo saboda driving da yayi, sama ya tafi ya bude kofar dakin Jiddah ya shiga ciki, ya dinga bin dakin da kallo kafin ya juya ya fita, dakin Aneesah ya nufa ya murda kofar ya ji sa a kulle, mamaki ne ya cikasa, ya tafi bangarensa ya xauna, bayan minti sha biyar ya mike ya sake komawa dakin Jiddah don a tunaninsa daxu tana bathroom ne, ganin har sannan bata cikin dakin ya karasa ya tura kofar bayin yaga wayam babu kowa ciki, juyawa yayi ya sauka kasa da mamaki, ya shiga kitchen yaga babu kowa ciki nan ma, ya fito yana bin parlon da kallo cike da surprise, Ya kalli agogo dake nuna goma saura ya nufi kofa ya fita, gun mai gadi ya tafi mai gadin ya taso da sauri ya sake gaishesa, bai damu ya amsa ba yace "Babu kowa gidan... Da yaushe suka fita?" Mai gadin yace "Toh ita dai Hajiya daxun nan bayan magriba ina sallah naga fitarta, ita Hajiya karama kuma gaskiya tun da safe naga fitowarta kamar da matsala don hankalinta ma baya jikinta ta fito, ina tambayarta lafiya ma bata saurareni ba ta fita gate, sai na tafi da sauri in ga meke faruwa, to ni dai ban ga kowa a parlon ba ma" Abuturrab ya rasa ma exactly tunanin da xai yi ya dinga kallon mai gadin xuciyarsa na bugawa, juyawa yayi da sauri ya koma ciki ya dau wayarsa ya shiga kiran Maimoon tana dagawa yace "Jiddah tana gidanku ne?" Maimoon tace "Jiddah kuma? Aa yaya bata nan, lafiya?" Strictly yace "I am not joking" Tace "Wllh Allah bata nan yaya" he was shock at that, yace "Look, bance kice da Umma komai ba" Daga haka ya katse wayarsa ya kira Nafisah ita ma tambayar da yayi mata kenan tace bata xo ba, lkci daya ya ji hankalinsa yayi mugun tashi, ya juya da sauri ya fita ya koma gun mai gadi yace "Ita warce ta fita da safen ina kaga ta nufa?" Mai gadin yace "Yallabai ai ina ganin yanda ta fito kamar da matsala cikin gidan sai na yi cikin gidan da sauri, wllh ban san inda tayi ba, kuma ko da na fito babu alamarta" Abuturrab ya ji wani xufa na keto masa duk da yanda garin yayi sanyi don da akwai hadari, he was shock, a xuciyarsa ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya nufi gate ya fice daga gidan direct ya tafi gidan Hajiya Fatima....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Abuturrab na shiga compound din gidan ya tafi entrance din parlon yayi knocking, he is just trying his very best to be calm, mai aikin gidan ta bude kofar, ta gaishesa bai amsa ba yace "Mama na ciki?" Tace "Eh Bismillah" shiga parlon yayi ya xauna saman kujera, sosai ya ji kansa ya masa nauyi dama ga gajiyar da yake tare da shi, Mai aikin ta tafi dakin Hajiya Fatima, bayan kusan minti biyar Hajiya Fatima ta fito parlon ganinsa tace "Aa, ashe kai ne, welcome son" Ya daga kai ya kalleta ya

105 / 117