Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   113 / 117

336K to 339K   out of 348.6K words

ci dadin apple na dibansa yana kakkanne ido, ni kuma sai gani na taho a guje ta bayanta kafin ta turasa ni nayi maxa na turata cikin ruwan sai ruwa ya tafi da ita ta dinga kurma ihu da karfi, ni dai na kamo hannun yaro na muka dawo gida" murmushi kawai Abuturrab ke yi Hajja ta fice daga dakin, Abuturrab ya mike ya dau shayin Jiddah da warmer din masa da miya yace "Tashi mu je" Ta xaro ido tace "Ina?" Ya sha kunu yana kallonta, mikewa tayi ya fita ta bi bayansa, bedroom dinsa ya tafi da ita bayan sun shiga ya kulle kofar, ta marairaice masa tace "So kake in ji kunya don Allah?" Yace "Ehh shi nake so ki ji" Xaunawa tayi saman carpet din dakin ta rasa ma me xata ce masa, ya ajiye mata shayinta da waina yace "Eat now" Abincin ta fara ci yana kallonta, taji ya kira sunanta, ta kallesa, yace "Tell me how everything happen pls" Ta ajiye wainan hannunta tace "Me yasa baxa ka cire wannan abun a ranka ba and move on pls?" Yace "Na cire wife, just that i am still wondering what happened all of a sudden on that day, tunda lafiya muka rabu da ke ai, and i even escorted you to the gate" Sai kuma ya jinginar da kansa da gado a hankali yace "I wish na raka ki har cikin gidan may be hakan da bai faru ba" cikin sanyin murya tace "Ko da kai ko babu kai dole hakan xai faru tunda Allah ya rubuta hakan" Yace "But pls tell me how it happen" Tayi shiru kamar baxata ce komai ba, ganin yanda yake kallonta a hankali tace "I saw someone just like my father...." Abuturrab yace "Ur father?" Ta gyada masa kai, yace "Where?" Ta sauke idonta tace "Gidan mama" Da mamaki yake ta kallonta yace "U mean ur father?" lkci daya hawaye ya kawo idonta tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Yes, i saw someone just like him" Abuturrab yayi kasa da murya da damuwa yace "Amma ai baba ya rasu Jiddah, wani baban kuma kike nufi" Ta fashe da kuka a hankali tace "Eh na san ya rasu, but they look so much alike, ni nasan abinda nake fada ai, i saw my father's duplicate" Abuturrab yace "Ikon Allah, bak'o su maman suka yi ne?" Tace "Nima ban sani ba, ina xaune parlon ya shigo and i was shock sbda nayi tunanin Abbana ne a lkcn at first, kallon Abba na kawai nayi masa...." Abuturrab ya dinga kallonta a bit confuse, knocking din kofar dakin aka yi, ya mike ya bude kofar, Jiddah ta goge idonta da sauri, Umma ya gani tsaye bakin kofar ya gaisheta ta amsa ta shiga dakin tana kallon Jiddah tace "Ya jikin?" Jiddah ta gaisheta ita ma sannan tace "Na ji sauki Umma" Umma tace "Toh maa sha Allah, sannu" juyawa tayi ta fita Abuturrab ya bi bayanta cause he need to talk to her about this. Karfe sha biyu saura na safiyar Hajiya Fatima ta iso gidan da Rahama bayan sun kira Abuturrab ya tura masu address din gidan, a lkcn da suka iso gidan Jiddah na bacci a dakin Abuturrab, Hajja na kyalla ido taga Rahama da Hajiya Fatima ta bi su har parlon Ummi, Umma sai wani hararanta take, Hajja na washe baki tana kallon Rahama tace "Ashe uwarki ce wannan mata me kirki haka?" Rahama na murmushi tace "Ehh" Hajiya Fatima suka kara gaisawa da Hajja cikin fara'a, Hajja tace "Ai ni na haifi Uban Aliyun, da yake dai ni ba mai shige shigen gidan yara bace shi sa tun ranan da aka yi wannan yakin a gidan baki sake ganina ba, balle an saki fitinanniyar gidan, kinsan fa halin banxa aka kamata tana yi dumu dumu, toh dai ba ruwana gwara ka rufa ma wani asiri kai ma Allah ya rufa maka naka" Hajiya Fatima tace "Haka ne kam Baaba, kinga rashin xuwan da baki yi ne yasa bamu sake haduwa ba don kuwa ina yawan leka masu duk bayan sati" Hajja tace "Oh oh dama nace Jiddah na murmurewa idan ta koma gidan mijinta nima sai in tattara in koma can din in sa mata ido da kyau don kada aje a samu wani cikin ya lalace a banxa, ai ba abu bane mai kyau er yarinya karama kamar ta cikin fari ace ya lalace, kwata kwata ba kyau haka idan ba a saka ido a kanta ba tayi ta samun ciki yana xubewa kenan, amma dai ni nasan da akwai wani abu a kasa ba banxa ba, da kyar idan wannan kishiyar tata ta barta a haka, don kaf xuri'armu babu wanda ya ta6a 6ari mu dai" Hajiya Fatima na murmushi tace "Toh Allah dai yayi mana mai kyau, ita kuma Allah ya bata wanda xai tsaya" Hajja tace "Ameen dai, to a kawo masu abinci mana, me lemo da ruwa xai yi ma mutum???" Ganin su Mama xasu wuce bayan Azahar Umma ta tafi dakin Abuturrab ta taso Jiddah ta fito su gaisa, Jiddah ta shigo parlon Ummi ta gaida su da murmushi fuskarta, Hajiya Fatima tace "Ya jikin Jiddah?" Jiddah tace "Na ji sauki Mama" Hajiya Fatima tace "Alhmdlh, Allah ya kara maki lafiya" Ummi na kallon Jiddah da ta rakube waje daya tace "Shiga ciki ki kwanta to..." mikewa tayi ta shiga dakin Ummi, Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Tsautsayi dai kawai, ni fa na shiga gidan nasu da safe yace tana bacci..." Da sauri Ummi ta dakatar da ita don kada ma Hajja ta ji kan xancen tace "Allah sarki, Allah shi yasan dai dai ai Hajiya" Hajiya Fatima tace "Wllh abun ya tsaya min har yanxu a rai, ji nayi ta kwala ihu kawai..." Hajja ta gyara xama tace "Ta kwala ihu a ina?" Hajiya Fatima tace "A parlor na" Hajja ta hangame baki tace "Wai a parlonki cikin ya lalace dama?" Hajiya Fatima tace "Ehh wllh Baaba shi yasa abun ya dameni" Umma tayi saurin cewa "Aa babu xancen saka damuwa a rai Hajiya, sai kace ba musulmai ba, Aa mu kam mun yarda da kaddara wllh, ai ko ba a parlon ki ba tunda Allah ya kaddara sai cikin nan ya xube dole xai xube ko ma a ina ne, in ma dakina, dakin Ummi, ko ma dakin Hajja" Hajja dai aka rasa abun cewa, sai kallon kowa take ta gefen ido, Hajiya Fatima tace "Haka ne kam, Allah yayi mana me kyau" Umma tace "Amma kun yi wani bako a ranan da ya sameta a parlon naki ko?" Hajiya Fatima tayi shiru, sai kuma ta kalli Umma tace "Mai gidana ne, dawowarsa kenan ma daga Abuja" Umma tace "Ikon Allah... To ce ma Aliyun tayi taga yana kama da babanta ne...." Hajiya Fatima ta gwalo ido tace "Babanta, amma ai tace min babanta ya rasu" Umma tace "Kwarai ya rasu, amma tace wai suna kama sosai" Hajiya Fatima ta kalli Rahama da ta saki baki ita ma, Hajja tace "Me kama da babanta kuma??" Hajiya Fatima tace "Toh ni kam na rasa ma me xance kuma" Ummi tayi murmushi tace "Ai kam abun da mamaki, kuma dama irin haka na faruwa ai sai ka ga wani wanda ke kama da wani naka da ka sani" Hajja tace "Aa to ko dai uban nata mutuwan karya yayi masu, wato ya gaji da wahalan su da talauci a hayi" Umma da ta bude baki ta kalli Hajja tace "Toh sai kuma aka yi yaya?" Hajja tace "Atoh, ya gudu mana, so nawa muke samun irin wannan labarin daga karshe ace ai ya gudu birni ya auri wata mai kudi sun hayayyafa, ku ka san ko haka yayi shi ma" Salati Ummi ta dinga yi a ranta, Umma kuma ta dinga ma Hajja wani irin kallo, ita kam Hajiya Fatima sai kirkiran murmushi take, Hajja tace "Xancen gaskiya fa, idan kuwa har sun tabbata ya mutu din to duk yanda aka yi wanda ta gani din d'an uwan ubanta ne, tunda ba daga sama ta fado ba... ayi mutum ace bai da dangi ko daya" Hajiya Fatima da kanta ya ga???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ma daurewa don ita dai a iya saninta duk familyn mijinta ta sansu na kauye na birni da ma wa enda suke wasu kasashen, ta dinga kallon Hajja ta ma rasa abun cewa, Hajja tace "Da xa a samu hoton shi uban nata da aka ce ya rasu sai a kai ma mijin ki ya gani kawai" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina ga hakan xai fi, idan anyi hakan kilan Jiddan xata fi samun nutsuwa ta kara sakawa a ranta cewar ba mahaifinta bane kawai me kama da shi ne" Hajja tace "Toh ba shkkn ba, amma idan nayi magana a dinga min kallon ta6a66iya, kawai abinda xa ayi kenan yanxu a samo hoton ubanta mu kai ma mijinki shi kuma mu ji me xai ce, sannan idan kin lura er ki na da wannan nakasan na gefen kumatu ita ma jiddah na da shi, wannan lotsewan nan" Hajiya Fatima dai tayi shiru, Hajja tace "kawai abinda xa ayi kenan" Sai wajen karfe biyu da rabi Hajiya Fatima da er ta suka bar gidan, amma gaba daya a sanyaye take da wannan lamari har Allah Allah take ta tafi ta sanar ma mijinta dake gari har lkcn. Abuturrab na kallon Umma yace "Xan gane gidan, wancan lkcn ma ai da Hajiya Fatimar muka je" Umma tayi shiru, sai kuma tace "Toh Allah ya kyauta, xuwa bayan la'asar sai mu tafi can din, nasan ita matar uban ai baxata rasa hoton marigayin mijin nata ba" Abuturrab yace "Haka ne, amma fa tana fita bara sai dare ake samunta a gida" Umma ta rike ha6a tace "Bara kuma? Allah me hikima, bara take yi?" Yace "Ehh" Umma tayi shiru sai kuma tace "Kar a biye halinta Aliyu, idan da taimakon da muka ga xa mu iya rendering mata we should do so, ta ci albarkacin Jiddah" Abuturrab ya girgixa kai yace "Bani da wannan halin Umma" Umma bata kuma ce masa komai ba, ya mike yace "In kina nan har magrib din sai mu tafi can gidan, idan kin koma gida kuma sai in je in daukeki a can gidan mu tafi" Tace "Shkkn" Bayan magrib Abuturrab ya tafi can gidan Umma ya dauketa xuwa can gidan Hansai, yau kam bai yi mistake din xuwa anguwan ba nose mask ba, tunda yayi parking Umma ke kallon layin da gidan yake, suka sauka daga motar ya nuna mata gidan, Umma ta shiga ciki ya tsaya daga waje ya ki shiga, da ya tuna irin abubuwan da Hansai ta dinga ma Jiddah a hayi da irin axabar da ta dinga gana mata tana amfani da ita tana making kudi shi kansa dubi irin karyan da ta dinga lafta masa ya bata kudinsa yayi dubu dari biyar sai yaji wani bacin rai ya xo masa, and he believes the situation she is right now serves her right, don haka ko digon tausayinta baya ji wllh, Umma na shiga dakin ta rasa wajen xama ga wani doyi da dakin yake, Hansai dake xaune kan darduma da wani rubabben fitila da ya d'an haske dakin ta amsa sallamarta cikin sanyin murya sai kuma ta mike ta shimfida mata buhun cement a kasa tace "Sannu" Umma ta daure ta xauna tace "Yauwa nagode... ya gida?" A hankali tace "Lafiya lau" Umma ta kunna wayarta ta ajiye sai kallon Hansai take ganin yanda idanuwanta suka wani kumbura tace "Amma in ji dai lafiya baiwar Allah" Kamar jira take ta fashe da kuka tace "Yau kwana uku Allah yayi ma 'ya ta rasuwa..." Sai ta dinga rusa kuka, Umma tace "Hasbunallah, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya gafarta mata" cikin kuka Hansai tace "Ameen" Umma ta girgixa kai tace "Nasan baki san ni ba, ni ce uwar rikon Jiddah sannan kuma kanwar uwar mijinta" Hansai ta dinga kallon Umma sai kuma ta sunkuyar da kai, Umma tace "Na xo neman wata alfarma ne a wajenki" Cikin rawar murya Hansai tace "Ina jin ki Hajiya, Allah ya sa bai fi karfina ba, ni ma kuma ina son rokon wata alfarka a gareki" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "In sha Allah" a hankali Hansai tace "Toh wacce alfarman kike so wajena Hajiya?" Umma tace "Hoton mahaifin Jiddah xaki bamu idan har kina da shi don Allah" Hansai ta goge idonta tace "Baxa a rasa ba" Tana fadin haka ta mike ta bude Ghana must go da ta ciro hoton kakar Jiddah da mahaifiyarta, ta dubo hoton mahaifin Jiddah wajen kala shidda ta ajiye ma Umma har da wanda yake saurayi, Umma ta dau hotunan tace "Toh nagode kwarai da gaske, ki fadi ta ki alfarman..." Hansai ta xauna a sanyaye tace "Alfarma daya nake so Hajiya don Allah a bar ni inyi xumunci da Jiddah, ko da sau daya ne a shekara in dinga ganinta xanyi farin ciki wllh, nasan na xalunceta na ci amanarta da na mahaifanta amma na roketa yafiya kuma tace ta yafe min yau wata hudu kenan tun xuwansu gidan nan, in ci albarkacin ubanta kada a rabani da ita don girman Allah" Hawaye kawai take tana shessheka, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh in sha Allah, xa ku yi xumunci" Godiya Hansai ta dinga yi ma Umma kamar xata ari baki, Umma ta bude jakarta ta ciro dubu biyar tace "Kiyi hakuri da wannan sai mun sake dawowa, duk da gobe ko jibi xa mu xo din tare da Jiddah ta yi maki gaisuwar yar uwarta in sha Allah" Har bakin mota Hansai ta raka Umma duk jikinta a sanyaye, har ranta take son rayuwa tare da Jiddah gatan da bata gwada mata ba tun ubanta na da rai har ya rasu tana son ta gwada mata yanxu duk da bata da komai, so take kawai ta ja ta a jiki tamkar bibalonta, tana ganin Abuturrab ta duka tana gaishesa, ya amsa a takaice ya xaga ya shiga driver seat ta bi sa da ido, Umma ta bude gaba ta xauna tana daga ma Hansai hannu har suka bar anguwar, sosai taji tausayin matar, lallai kam ita taga kamun Allah tun a duniya. Suna komawa gida da hoton Abban Jiddah Hajja tace Inaaa ai hoton baxai kwana ba aje a nuna ma mijin Hajiya Fatima kawai, haka suka shirya da ita da Umma, da Jiddah da Abuturrab xuwa gidan Hajiya Fatima bayan isha.....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Tun da suka shiga compound din gidan Hajiya Fatima Hajja ke washe baki tace "Toh kun ga dai, ai basu wani nuna su masu kudi bane da suka je can gida duba Jiddah, to haka ake son mutum wanda bai da burga ko fafa, kuma da irinsu ya kamata ayi xumunci, naji dadin yanda suka tsaya kan jiddah har ta ji sauki, ji yanda babbar er nan tata me mota ta dinga kula da Jiddah a asibiti tana nan nan da ita, to kuwa idan ma ku baxa ku yi xumunci da su ba ni dai xan yi" Abuturrab dake ta kallonta yace "An ce maki suna xumunci da mutan Masar ne?" Hajja ta juya da sauri baki bude ta kallesa tace "Meye da Masar din?" Bai sake tanka ta ba har suka shiga parlon Hajiya Fatima, sosai Hajiya Fatima tayi welcoming dinsu ta kawo masu fruits iri iri a tray da bottle water ta ajiye masu, Hajja sai wani murmushi take tana kallonta tace "Kinga yanda kika yi din nan? Wllh haka suke yi a Masar.... Kya ga kayan marmari iri iri a tray an ajiye ma baki, ko jarkan madara da cinyoyin kaji" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah..." Hajja tace "Wllh, kin san daga Masar nake, daga xuwa bikin jikana shine na rashe a Najeriya, suna can suna ta kewana kullum sai sun kirani kira me motsi ta waya mun gaisa" Hajiya Fatima tace "Allah sarki, da kawai kiyi xamanki tunda kin dawo Baaba" Hajja tace "Inaaa xan iya kirga maki sau nawa na ci kaza tun Dawowata kasar nan, can kuwa gasu nan baja baja har sai ka ture, ke dai kawai ayi harka er nan" Hajiya Fatima ta dinga murmushi, Umma ta kalli agogo tace "Hajiya sai kika gan mu da daddare ba notice" Hajja ta amshe tace "Wllh kuwa ni na takura a taho ko min dare don ba a wasa da lamari me muhimmanci irin wannan, na lura in dan ta su ne sai dai a shashantar da xancen a hau wata sabgar can, kinga kenan yarinya bata da makubuli, sannan idan aka samo danginta ai babu wanda xai ta gadara da ita babu gaira ba dalili, to in gaya maki shine na basu shawaran aje duk inda matar uban Jiddah take a amso hotunan uban nata sai mu taho mu nuna maki, amma dai ina shi mai gidan naki yake tukun?" Hajiya Fatima tace "Yana sama Hajiya" Hajja ta kalli Umma tace "Mika mata hotunan ta gani, idan mu bamu san fuskar mijinta ba ai ita ta sani" Umma ta xuge zip din jaka ta ciro hotunan Baban Jiddah, Hajiya Fatima ta taso ta amsa tana kallo with much interest, waje ta nema ta xauna ba tare da ta shirya yin hakan ba tana ta maimaita kallon hotunan guda hudu dake hannunta babu ko kiftawa, Hajja tace "Toh kinyi shiru, gaya mana ai xaki yi ko yana kama da mijin ki ko baya yi" Hajiya Fatima ta dago ta kalli Hajja, tayi shirun kusan 5 seconds sai kuma ta sauke ajiyar xuciya tace "Bari in kai masa Hajja...." Daga haka ta mike ta wuce sama, Hajja ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Da kyar idan

113 / 117