Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   100 / 117

297K to 300K   out of 348.6K words

wanyewa da duniya lafiya" Abuturrab ya sunkuyar da kansa yace "In sha Allah" Tace "That's all i have to say, Allah ya hade kanku, ya kauda duk wata fitina a tsakaninku, idan ma kaga da wata matsalar i am always around kafin dae ayi involving close ones" Da haka suka yi sallama da Hajiya fatima yana kara yi mata godiya, Aneesah ta mike ta bi bayan Abuturrab, sannan Jiddah ma ta tashi tayi masu sai anjima ta nufi kofa, Hajiya Fatima ta bi ta da kallo... Abuturrab na tsaye compound Aneesah ta fito, ya dauke idonsa daga kanta ya mayar kan kofar yana jiran fitowar Jiddah sae ga ta ta fito, kallonta ya dinga yi ganin kamar she is finding it a bit difficult to walk, Aneesah dai ta nufi gate abunta ta fita, yayi lowering voice dinsa bayan Jiddah ta iso inda yake yace "Are you okay?" Bata ce masa komai ba, ya kama hannunta suka fita daga gidan. Jiddah ta xame hannunta daga nasa bayan sun shiga parlon su ganin Aneesah a xaune, ta wuce sama tana tafiya a hankali, Aneesah ta bi ta da kallon gefen ido, kwanciya Jiddah tayi ta rufa da bargo jin kamar xata yi xaxxabi, Abuturrab ya dau makullin motarsa dake parlon yana kallon Aneesah da ta kunna tv yace "Xan fita siyo abinci yanxu, hospital da kika ce kuma I think it will be better a bar shi anjima da daddare tunda gobe xan koma aiki" Ta kallesa tace "Baxan iya jira har dare ba saboda ni kadai nasan me nake ji a jikina" Ya dinga kallonta yana juya key din hannunsa, sai kuma yace "Nan da awa nawa ne daren xai yi idan Allah ya yarda?" Tace "Kaga Captain.... ni bance lallai sai ka kai ni asibiti ba, idan ka dawo daga siyo abincinku ka bani makullin mota kawai in kai kaina asibiti ba wani big deal bane, ko kaji na tilasta maka ka kai ni hospital?" ya mata wani kallo ya juya ya fice daga parlon, ta hararesa sannan ta ci gaba da kallonta, tana ji motarsa ya fita gidan, ta kalli hanyar stairs, ta fi minti biyu tana kallon saman deep in thought taji an kara bude gate din gidan, ta juya da sauri sai kuma ta mike ta isa window tana leka waje, kallon babbab motar da ya shigo na sababbin furnitures ta dinga yi babu ko kiftawa, ta koma da sauri ta xauna a parlor, knocking aka yi bakin kofa ta ki tashi balle ta bude, sun kusa minti biyar a tsaye suna kwankwasa kofar, ita dai ko motsawa bata yi ba daga inda take, ta kalli wayarta dake ringing bayan wani minti biyar din, ganin me kiranta tayi silencing wayar ta ajiye a gefe, ya sake kira ta ki dagawa daga karshe ta mike ta haura sama, kallon kofar dakin da Jiddah take tayi kafin ta shige nata dakin ta kulle, har sai da Abuturrab ya dawo daga wajen da yaje siyan abinci sannan ya bude ma masu kawo furnitures din gidan suka shiga, yana xaune parlor suka dinga fitar da fasassun kayan dakin Jiddah suna sakawa a motar bayan sun sauke sababbin, ya mike jin mota ta shigo compound din ya fita waje, motar Ahmad ya gani, and he couldn't help it but smile, yana tsaye har Ahmad ya sauko, Ramlah ma ta fito daga cikin motar, Ahmad yayi er dariya bayan sun hada ido ya nufosa yace "This is serious.... kaga wani fresh da kayi kuwa Captain?? Meye haka Jiddah ke baka?" Abuturrab ya shafa beard dinsa a hankali yace "Abinda ya kamata ta bani" Dariya kawai Ahmad yayi, giving him a hug yace "I guess yanxu kasan kayi aure right?" Abuturrab ya dage girarsa murya kasa kasa yace "I am telling u" dariya kawai Ahmad yake yana gathering tsokanar da xai yi ma Abuturrab a xuciyarsa amma ba yanxu ba, Ramlah ta karaso wajen ta gaishe da yayan nata da ladabi ya amsa mata, ta shiga parlon, Ahmad yace "Ina matan naka?" Murmushi Abuturrab yayi ya juya ya shiga ciki Ahmad na biye da shi, stairs Abuturrab ya haura ya fara bude dakin Jiddah ya ganta kwance tana bacci, ya karasa ya duka kusa da ita yana shafa hancinta ta bude ido a hankali, turo baki tayi ganinsa xata juya masa baya ya dagota yace "Baccin ya isa haka, yamma yayi..." Kamar xata masa kuka tace "My legs are aching" ya cire duvet din yana massaging kafar ta hade rai ta rike hannunsa gabanta na faduwa tace "Bana so" ya kalleta da lumsassun idonsa yayi kasa da murya yace "Baki son me?" Bata san lkcn da ta fashe da kuka ba cause it started just exactly like this daxu, ya saketa da sauri, a rikice yace "Toh yi hakuri plss..." Ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, bai ta6a ta ba ya marairaice yace "Na fa ce kiyi hakuri wife, don Allah kiyi hakuri" ta dago kanta taba goge idonta a hankali, ya langwabar da kai yace "To taso ki gaisa da su Ahmad, they are around" ta bude ido sosai tace "Da gaske?" a hankali yace "Yea wife..." Mikewa yayi ya dagota tsaye, kamar xata sakar masa kuka tace "Ni wllh bana jin dadi" Ya xaunar da ita gefen gado da damuwa yace "Toh ko mu tafi asibiti yanxu?" Ita dai tayi shiru ya rungumeta tayi lamo jikinsa yana patting bayanta, ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace "Toh baxan kuma ba, till u are healed...." Ta lumshe idonta tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa a kirjinta, murya can kasa yace "I love u with every breath of mine Wife" Ta kara shigewa jikinsa amma taki cewa komai kuma bata bude idonta ba, shi haka kadai ma ya ishesa ko bata mayar masa i love u din ba, narkar masa da xuciya da tunani gaba daya Jiddah take, she is the best thing that have ever happened to him, he felt complete with her, kamar me rada yace "Mu tafi asibitin a dubaki?" Ta make masa kafada, yace "Toh kin ce baxa ki iya tashi ba, ko in kira Ramlan ta shigo ku gaisa a nan kawai su tafi?" Da sauri ta bude ido tace "Aa xan je" Ya dago kanta ya shiga yi mata single lip kiss... Vibration din wayarsa ne ya dawo da shi ya mike xaune da sauri sannan ya dau wayar ya duba yaga Ahmad ne, buda ido yayi sosai sai kuma ya kalleta ganin yanda ta kulle idonta ya ja hancinta ya mike ya fita daga dakin, Yana sauka downstairs Ahmad yace "Captain da sai kace mana mu tafi kawai da dai shanya mu da kayi a parlor haka" Abuturrab ya kasa kallonsu yana shafa kansa yace "Ohk... I was suppose, ohhh sorry..." Sai kuma ya juya da sauri ya koma sama, dakin Aneesah ya shiga yana kallonta yace "Ki sauko ku gaisa da su Ramlah" ya juya ya fita ya koma downstairs yana kallonsu yace "Jiddah bacci take, she is having headache since morning, so Aneesah will be coming down now" Yana fadin haka ya nemi waje ya xauna, Ahmad dae kallonsa kawai yake yana murmushi ganin duk a birkice yake, masu gyara sababbin kayan dakin Jiddah dai na ta faman gyara a sama, Aneesah taji wani abu ya tokareta a makogwaro bayan ta fito, kallo daya tayi ma dakin Jiddah ta sauka kasa da sauri, babu yabo babu fallasa ta gaida Ahmad sannan ta amsa gaisuwan da Ramlah tayi mata, Shi dai Abuturrab fa gaba daya hankalinsa yayi sama, soul dinsa kawai ne a parlon amma spirit dinsa na can sama, can dai ya kalli Aneesah yace "Baki basu ko ruwa ba" ya mike ya dau abincin da ya siyo ya ajiye masu ya dau daya xai kai ma Jiddah sama, A stairs ya ganta tana saukowa a hankali, hakan ya sa ya ajiye ledan, har ta shigo parlon taki yarda ta hada ido da su Ahmad ta xauna kan kujera ta gaishesu cikin sanyin muryarta tana murmushi, Ahmad dake kallonta yace "Duk kewan Umma ne yasa kika rame haka Jiddoh" Ita dai murmushi kawai take ta d'an kalli Ramlah tace "Yaushe ku ka xo?" Ramlah dake ta kallonta ganin yanda ta kara haske tayi kyau amma kuma ta rame kamar yanda Ahmad ya fada, ta sakar mata murmushi tace "Yau da safe muka xo Aunty Jiddah, ya gida?" A hankali Jiddah tace "Alhmdlh, ya jiki?" Ramlah tace "Mun gode Allah" Tun da Aneesah ta shiga kitchen kmr xata dauko ruwa ta ki fitowa, Ahmad ya lura how uncomfortable Jiddah is a parlon kamar dai bata jin dadi, shi kuma ogan da ya xo wajensa sai kallonta yake kamar xae cinyeta, it's just as if he is obsessed with her... Ahmad yayi wani murmushi yana mamaki iri iri, sai kuma yace "Dama nace bari mu xo mu duba amarya Jiddah, yanxu kuma xa mu je can gida wajen Ummi, sae kuma wani lkcn in sha Allah" Abuturrab ya kallesa da sauri yace "So early, naga baku ci abincin ba fa...." Ahmad yace "Aa sae yanxu nayi reason, ba a wannan lkcn ya kamata mu kawo ziyara ba, in sha Allah xa mu dawo lkcn da ya kamata, but before then yaushe xaka barta ta koma makaranta Captain? cause satinsu biyu kenan da resumption" Abuturrab ya shafa kansa yace "Makaranta kuma?? Wani makaranta?" Ba Ahmad ba har Jiddah kallonsa take da mamaki, Ahmad yace "Ohh baka san ma wani makaranta ba ko, to Umma xata maka bayani da kyau" daga haka ya mike yace "Mu xa mu koma" Abuturrab yace "Shkkn sai mun yi waya" tare suka nufi kofa suka fita yana son gaya ma Ahmad abubuwa da yawa, bayan sun fita Ahmad bai basa daman magana ba yayi patting shoulder dinsa yace "Kar dai kayi ma er mutane ciki da wuri, kaga she is still very young...." Abuturrab ya d'an 6ata fuska yace "Ciki kuma? Aneesah bata dau ciki ba sai ita?" Dariya Ahmad yayi sosai ya ma kasa ce masa komai, wato Aneesah da suke yi for long bata dau ciki ba sai wata Jiddah tunda an gaya masa it's by that, kwafa Ahmad yayi yace "Xaka sha mamaki ka ci gaba da relying a kan haka... Sae kaga cikawar aikin ka" Jiddah na kallon Ramlah da ta mike da kyar, cike da damuwa tace "Baki ci komai ba kuma xa ki tafi, ko in kawo lemo sai ki tafi da shi?" Ramlah tace "Wllh mun ci abinci gidan Umma kar ki damu, Maimoon tace yaya ya siya maki waya da mota, and i saw the car da muka shigo yanxu, a very hearty congratulations dear, Allah ya sanya alkhairi" Da murmushi ta kare maganar, Jiddah dai ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Nagode" Ramlah ta bi parlon da kallo to make sure Aneesah bata nan ta mika mata ledan hannunta murya can kasa tace "Duk na rubuta maki yanda xa ki yi amfani da ko wanne, idan ma baki gane ba ki amshi lambata wajen yaya ki kirani" Jiddah ta amsa tana kallonta cikin sanyin murya tace "Toh nagode, yanxu haka xaku tafi ko ruwa fa baku sha ba" Ramlah tace "Sai kace wata bakuwa, kar ki damu wllh... Sannan maganar makarantarki ki lallaba yaya don naga kamar in don ta shi ne baxai bari ki ci gaba ba, do all u can ya barki ki xana waec dinki kin ji?" Jiddah tace "Toh nagode" Ramlah bata bi ta kan Aneesah da ta walakanta su ba ta nufi kofa, ta juya ta kalli Jiddah dake biye da ita, ganin kamar tafiyar na mata wahala ta dafa ta tace "Ki koma Jiddah, we will talk on phone in sha Allah..." Daga haka ta fita parlon Jiddah ta daga mata hannu ta bi ta da kallo, dai dai nan Aneesah ta fito kitchen tayi wucewarta sama kamar xata yi tsuntsu Jiddah ta bi ta da kallon gefen ido.... Bayan magrib Abuturrab na dawowa mosque ya shiga dakin Aneesah, earpiece ne jone kunnenta tana daga xaune kan duvet da ta kwana jiya, dakin nata dai babu kyan gani kamar anyi yaki a ciki, suna hada ido da shi tayi pausing wakar da take ji amma bata cire earpiece din ba, bai ga alamar tayi sallah ba ma shi ma kuma bai damu yace tayi ba, ya rungume hannunsa yace "Naga u didn't make any food ko baki amshi girkin bane har yanxu?" Tace "Make food for who?" Yace "For the entire house" tace "Ohk let me make this clear captain, ko wacce ta dinga girka abinda xata ci iya cikinta ko ranar girkinta ne ko ba ranan girkinta ba, idan ita ce da girki sae tayi har mijinta, yau da na amshi girki kuma ban yi maka ba ma sbda bani da lafiya!!" Ya dinga kallonta thinking if at all Aneesah xata iya canxawa daga yanda ya santa, duk da fa ba cikin fada take masa maganar ba, yace "Ke kika ajiyeni gidan nan ko ni na ajiyeki da xaki tsara min yanda xa ayi Aneesah?" Ta cire earpiece din kunnenta tace "Baxan kulaka muyi tashin hankali ba Captain, amma dai naga gidaje da yawa haka suke yi, ni idan na amince na ci abinda kishiya ta girka kana tunanin ita kishiyar xata yarda ta ci nawa? So u just have to reason it captain, shi yasa kawai na kawo wannan shawaran amma ba hukunci na yanke maka ba" Yace "Ki shirya in the next five minutes mu tafi asibitin" Daga haka ya juya ya fice daga dakin, ta jawo wayarta da ta ajiye ta danna ma Chef salma kira, murya can kasa tace "Ke ya ake ciki ne wai shiru shiru har yanxu?" Chef Salmah tace "i am almost done my dear, ya xa ayi tahowan da shi kenan?" Aneesah tace "Probably yanxu xa mu fita hospital da shi...." Salmah tace "Tooo har da amaryar xa ku dugunzuma xuwa hospital din?" A takaice Aneesah tace "Akan wani dalili? Shi ma baxai fara wannan haukan ba tunda ai ba girkinta bane" Dariya Salmah tayi tace "Goben dai xai koma aikin ko?" Aneesah tace "Eh" Salmah tace "Yana tafiya xan shigo in Allah ya yarda, akwai magananganu da yawa ke dai" Aneesah na kyabe baki tace "Wai ki ji shigowa yayi yanxu wai ina abinci, ni kuwa nace kowa yayi nasa" Salmah tace "Kika gaya masa haka??" Aneesah tace "Eh mana" Salmah tace "Amma wani lkcn idan kin yi wani abun kamar warce bata ta6a shiga aji ba wllh Aneesah, ta ya xaki gaya masa haka bayan ga chatting da mu ka yi dake daxu?" Aneesah ta xaro ido tace "OMG na mance wllh..." Tsaki Chef Salmah tayi tace "Sai ki nemi yanda xaki gyara tunda kika bata, haba a gama magana dake kawai ki shigo da wani salon da xai 6ata, ni dai gaya min inda xa a bar maki abubuwan idan kun fita" Aneesah ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Kawai idan an kawo a xagaya a kai min ta kofar baya kawai a ajiye i will stock dem all in the freezer idan mun dawo daga hospital din cikin dare" Chef salmah tace "Ohk to, sai dai na shigo goben" Aneesah tace "Toh ki shigo da wuri don Allah gobe xa a kawo min furnitures, i have to borrow ontop of wanda kika ara min fa wllh..." Chef salmah tace "Sai dai na shigo din, kar ki wani damu" Daga haka suka yi sallama, Aneesah ta mike a hankali bayan ta ajiye wayar, wani kayan ta sauya ta cika turare ta dau karamin veil dinta da handbag ta fito ta kulle rubabben dakin nata da makulli tana ma kofar dakin Jiddah wani kallo, tun bayan da aka gama jera mata furnitures din ta koma dakin, sauka downstairs tayi taga Abuturrab xaune alamar ita yake jira, bayan ta shigo parlon ya mike ya wuce sama ta bi sa da kallo, dakin Jiddah ya bude ya ganta xaune saman darduma, ya xauna gefen gado yana kallonta yace "Me xaki ci Baby?" Wani iri ta ji sunan, ta dai daga manyan idonta ta kallesa, yyi mata murmushi yace "Yes tell me duk abinda kike so" a hankali tace "Anything" Ya d'an shafa kansa yace "Ohkk xan je in siyo yanxu in dawo" a hankali tace "Allah ya tsare" Ya sakar mata murmushi yace "Ameen" Sannan ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta kwantar da kanta jikin gadonta a hankali, Aneesah na ganin saukowarsa parlor ta koma sama, ya bi ta da wani kallo yace "Kin san kina bata min lkci kuwa?" Tace "One minute" tana haurawa sama dakin Jiddah ta bude ta shiga dakin tana tsaye daga bakin kofa tana kalle kalle, Jiddah tayi mata kallon mamaki, Aneesah na murmushi tace "Pls ki d'an ara min body spray dinki i couldn't get access to mine sbda yanayin dakin..." Jiddah ta nuna mata gaban mirror dinta, ta tafi ta dau kala uku ta feshe jikinta da shi sannan ta juya ta kalleta ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ce "Thank you dear" Daga haka ta fita Jiddah ta bi ta da kallo, Bayan few seconds ta mike ta nufi jikin window tana kallon waje, sai ga Abuturrab ya nufi parking space din Aneesah na biye da shi a baya, yana shiga driver seat ta bude gaba ta shiga, kallonsu take ko kiftawa babu har ya ja motar suka fita compound din, sauke idonta tayi ta nufi kofa ta sa makulli ta bar makullin a jiki ta tafi ta kwanta gefen gado ta rufe har kanta da duvet. Sai da Abuturrab suka 6ata kusan 2 and a half hour a hospital din sbda series of test da aka yi ma Aneesah, ya so su wuce gobe ko ita ta koma ta amshi result din ta ki yarda wai ita gwara a tsaya ya fito a bata magunguna ko xata iya bacci yau, gaba daya hankalinsa na kan Jiddah sai kallon agogo yake, har karfe tara ya gota... wani kallo ya jefa ma Aneesah da ko ajikinta

100 / 117