Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   106 / 117

315K to 318K   out of 348.6K words

kasa cewa komai, ta xauna saman kujera cikin sanyin murya yace "Ina yini Mama?" Tace "Lafiya lau, ya su Jiddah da abokiyar xamanta" Bai san lkcn da ya kara gyara xama ba xuciyarsa na bugawa yace "Mama Jiddah bata shigo nan ba?" Hajiya Fatima tace "Jiddah kuma? Ta ce maka xata shigo nan ne?" Rike kansa yayi ya kasa bata amsa, ita dai sai kallonsa kawai take, can tace "Aliyu" ya dago da kyar ya kalleta tace "Ina Jiddar tace maka xata je?" Cike da confusion yace "Mama daga wajen aiki nake yanxu haka... I have to drive all the way from Abuja after piloting d whole day..." Rasa ma takamaiman abinda xai ce mata yayi, sai kuma ya dafe kansa yace "Ban san inda ta je ba, ban san me ya faru ba, i called home duk ance bata je can ba, bata da wajen xuwa kuma da ya wuce can..." Mikewa yayi ganin he is just sounding foolish, ba abinda ya ke fada da yake making sense, bata lkci kawai yake karawa gashi dare yayi, to shi a ina xai ga Jiddah? Ina Jiddah ta je? He felt like he is going to collapse, lamarin yayi ma xuciyarsa nauyi, ya rasa exactly tunanin inda Jiddah xata je da xai yi, is this really happening, gaba daya ya ma mance batun Aneesah ma bai ganta a gida ba, gathering much courage yace "Sai da safe Mama, dama na xata nan ta shigo" Juyawa yayi yana jin kafafuwansa sun masa nauyi ya nufi kofa, tace "Aliyu" ya juyo ya kalleta, tace "Me yasa xaka bar Jiddah da matarka kadai a gida bayan kasan halin wannan ita matar taka?" Dawowa yayi da sauri xuciyarsa na bugawa, tace "Why Aliyu?" Ya marairaice mata yace "Mama ta shigo nan ne? Wllh ban san abinda ya faru ba, daga Abuja nake few minutes ago ban tadda kowa a gidan ba" Hajiya Fatima tace "Tashin hankali Abokiyar xamanta ta nemeta da shi shine ta shigo nan, don ko takalmi balle mayafi babu a jikinta ta shigo gidan nan" Abuturrab ya buda ido sosai yana kallonta so speechless, Ta girgixa kai tace "Sakacin yayi yawa Aliyu, ganganci ne barinsu su biyu kadai a gidan nan, a da ni banyi niyyar nuna maka Jiddah tana nan ba sbda naga kamar u are not ready to take any action, it's not as if i am trying to intrude into ur privacy amma naga bai kamata in xuba ido ba a matsayina na babba, ba wai ina maku shisshigi bane amma lamarin abun dubawa ne kada wataran ayi kisan kai" Ya duka gabanta without knowing he did so yace "Don Allah yanxu tana cikin gidan nan Mama?" Hajiya Fatima tace "Tana nan" Mikewa tayi ya bi ta da kallo har ta wuce ciki, ya sauke wani irin ajiyar xuciya ya rufe idonsa sai dai har yanxu xuciyarsa bai dawo dai dai ba, bayan kusan minti hudu Hajiya Fatima ta shigo parlon tare da Jiddah dake biye da ita a baya, Jiddah na hada ido da Abuturrab dake kallonta ko kiftawa babu ta sunkuyar da kai fuskarta babu walwala, Sounding so grateful yace "Nagode Mama Allah ya kara girma..." Tace "Aa ba ka gode ba, so kake matarka ta kasheta ne ko kuwa kana da wata manufarka daban na barinsu a gida su biyu kadai?" Ya marairaice mata yace "Not at all Mama..." Tace "Toh tashi ka dau matarka ku tafi, xa mu yi magana gobe" Godiya ya dinga yi mata kamar warce tayi masa albishir da aljanna, infact shi tunda yake bai ta6a yi ma mutum irin godiyan nan da yake mata ba, sai taji ya bata tausayi kana ganinsa kasan matan nan nasa suna basa tension, Hajiya Fatima tace "Ku tafi Jiddah sai da safe, xan shigo in sha Allah da safen" Mikewa Abuturrab yayi yana kallon Jiddah da taki yarda ta hada ido da shi, babu yanda ta iya haka ta bi bayansa tana jin kamar ta fashe da kuka har ranta taji bata son xaman gidan, bata son komawa gidan, duk da yayyafin da aka fara, haka suka fito compound din ya kama hannunta kamar xa a kwace masa ita suka fita gidan sannan suka shiga nasu, suna shiga parlor ya kulle kofar ya rungumota jikinsa gam, ya runtse ido da damuwa yace "Me yasa kike bani wahala haka Jiddah, me yasa kike sa min ciwon xuciya? Kince ban maki komai ba duk xaman mu na farko balle ko ince ramawa kike yanxu, why are u giving me heart attack jiddah, tell me pls wife, kin ki barin in nutsu in yi aikina, so kike a bani query Jiddah? Do u want me to lose my job?" Tayi shiru tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa, ga kamshinsa da ya cikata, lumshe ido tayi ita ma xuciyarta na bugawa, ya dago kanta a hankali yace "Me ya faru kika fita gida just like that? tell me plss" Hawaye ya kawo idonta a hankali tace "Nemana take da fada a ko da yaushe" yace "Me ta maki? Tell me" Cikin sanyin murya tace "Daxu da safe na sakko xan shiga kitchen shine ta xageni ta xagi iyayena, kuma har da marina" Ta fashe masa da kuka, lkci daya mood dinsa ya koma na bacin rai karara, yace "Ta mareki?" Cikin kuka tace "Ehh shine ni kuma ta kwala mata wancan vase din na fita parlon" Ya rungumeta bai ce komai ba yana tunani iri iri a ransa, hannunta ya kama suka wuce sama, ya tafi bangarensa ya dau wayarsa ya shiga bedroom dinsa ya dau spare key sannan ya fita, Jiddah dai na tsaye parlonsa ta bi sa da kallo har ya fita, ta xauna a hankali gefen kujera, bude kofar dakin Aneesah yayi yana kokarin dialing numberta, har ya katse bata daga ba, ya sake kira yana bin dakin nata da kallo, dagawa aka yi daga daya bangaren, murya kasa kasa tace "Hello my Captain" Yace "How are you?" Tace "Lafiya lau My captain, are u missing me this much?" Yace "Ya jikin yanxu?" Tace "Yanxu na sha magungunana na kwanta har na fara bacci kiranka ya tasheni" Yace "Ohk kina daki kenan?" Tace "Ehh wllh, ina daki a kwance" yace "Ohk can u go give Jiddah the phone plss?" Tace "Why not my captain, Allah ya sa ta karba din, bari in kai mata" Shiru yayi bayan wani lkci yaji tana cewa "Assalamualaikum, Jiddah, Jiddah..." Sai kuma tace "Ohh kofar ma a bude take ashe, bari in Shiga" Shi dai yayi shiru yana sauraronta xuciyarsa na throbbing, ya ji tace "Captain bata ciki fa, na duba bathroom ma ban ganta ba, let me check downstairs" Ya dake yace "Ohk" again bayan wani lkci tace "Bata nan wllh captain, and I can't even see her shoes da ta bari bakin kofa daxu da ta shigo, probably taje siyo abu ne a waje" yace "Ohk, gobe da safe karfe goma xuwa sha daya xan dawo in sha Allah" Tace "Toh Allah ya kai mu my captain" Katse wayar yayi ya xauna gefen gado yana jin wani mugun bugawa da xuciyarsa ke yi, is this for real? Wait ina ma ta tafi tukun? Bai san sanda ya bude baki ba mamaki kaff ya gama cikasa, sai yake ganin abun kamar film, Aneesah?? Ya kara bin dakin nata da kallo ya kalli xanuwan gadon da suke xube a kasa, mikewa yayi ganin sachet kusan hudu dake xube daga gefen xanin gadon ya karasa ya durkusa ya dauka yana dubawa, sai da xuciyarsa ya daina aiki na kusan second biyar, ya dinga kallon sachet din babu ko kiftawa da wani expression da ya fi kama da na shock, juyasu ya dinga yi yana kallonsu kamar idanuwansa xa su fito, lkci daya ya runtse ido ya nufi kofa rike da su ya fice daga dakin ya tafi bangarensa, bai ga Jiddah a nan ba ya shige bedroom ya kwanta jin kamar sanyi yake ji, ya fi minti ashirin a haka duk jikinsa yayi wani irin sanyi, he is really shocked, ruwa ya sauka sosai, can yayi karfin halin tashi ya tafi bandaki ya hada ruwan dumi yayi wanka ya fito, yana ta xaune gefen gadonsa yayi wannan tunanin yayi wancan tunanin, ganin abun yake kamar a mafarki, can ya mike da kyar wearing just his short nd singlet ya fita dakin, dakin Jiddah ya tafi ya kunna wutan dakin ya ganta kwance ta rufa da duvet, idonta biyu kuma ba bacci take ba, ita duk tunaninta wajen Aneesah ya tafi ya bar ta xaune parlonsa kawai, ya kashe wutan a hankali ya tafi kusa da ita ya cire duvet din gently ya kwanta drawing her closer to him ya juyo da ita, underneath his breathe yace My Precious Gift... Ta ki bude idonta tana sauke numfashi a hankali....




*I mistakenly sent this chapter to just 2 of my payment group shine sbda rashin tsoron Allah har sun fitar within seconds, around few minutes pass 7 na tura amma har ya xaga inda ya xaga, so i assume ya ishesu ne yasa har suka fitar don haka, this is today's update*




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


Da asuba Abuturrab na dawowa masallaci ya xauna downstairs ya jinginar da kansa a hankali jikin kujera ya rufe ido, gaba daya ya rasa me ke masa dadi, upon how sweet the night was to him bai yi wani baccin kirki ba, he was disturb all through, and he is still finding it hard to believe Aneesah bata kwana cikin gidan nan ba, yana ta xaune parlor har bakwai saura sannan ya mike da kyar ya haura sama yana jin kansa na sara masa, bude kofar dakin Jiddah yayi ya sameta ta koma bacci bayan ta idar da sallah, ya nufeta ya lulluba mata duvet a hankali yana kallon innocent face dinta, ya daura lips dinsa a nata ya lumshe ido, sai kuma ya mike ya fita, gently ya kullo kofar don ya san she really need the sleep, ya tafi parlonsa ya xauna ya rike kansa yana jin damuwa a ransa, sai kuma ya jawo wayarsa ya shiga dialing number Aneesah, har ya katse bata daga ba, ya kuma kiranta sai ta daga cikin muryan bacci tace "Hello my Captain" Yace "How was ur night?" Tace "Alhmdlh, are u still coming back today?" Yace "Yeah at 10" tace "Alright dear Allah ya kai mu, hope u slept fine?" Yace "Yeah, can u pls take ur phone to Jiddah?" Ta wani shagwabe tace "Captain naga kamar fa ba don ni kake yawan kiran nan ba, kawai kai dai kira kake saboda matarka, banda haka ni a rana daya ma a ina nake ganin call dinka, i assume this call isn't for me" Yace "Aa ba haka bane...." Ta katse sa tace "Alright, i will go give her d phone now, I was only joking my captain" Yace "Ohk" yana ta sauraronta har bayan minti biyu ta fara knocking tana kiran sunan Jiddah, sai kuma tace "Captain bata ciki fa? It seems bata dawo jiya ba" Yace "Bata dawo jiya ba?" Tace "Wllh, her door is open and the room is still d way it was yesterday da kace in kai mata waya, bari in sauka kasa" Ya kasa ce mata komai wani axababben mamaki ya cikasa, bayan few seconds tace "Bata dawo ba kam Captain" A hankali yace "Alright, sai anjima" Tace "Ohk my Captain, i love you" a hankali yace "Same" sannan yyi maza ya katse wayar ya rike kansa da yayi masa wani nauyin bala'i yana jin xuciyarsa na wani tafarfasa, lkci daya ya mike ya tafi gaban mirror dinsa ya bude yana kallon abubuwan da ya kwaso a dakinta jiya bbu ko kiftawa, xaunawa yayi gefen gado ya kara dafe kansa maganganun Ahmad na dawo masa tiryan tiryan. Karfe takwas Jiddah ta farka ta bi dakin da kallo, da sauri ta mike xaune har xata shiga bandaki ta tuna tayi wanka tayi komai da asuba, ta tashi ta dau hularta ta saka sannan ta fita dakin ta sauka downstairs tana tafiya a hankali ta wuce kitchen, tunanin abinda xata yi for breakfast ta shiga yi, can dai ta fara wanke few plates din dake kitchen din da Aneesah ta bari, sannan ta gyara kitchen din tsaf ta daura ruwan shayi, ta fara fereye doya... Karfe tara da few minutes ta fito da breakfast din parlor ta durkusa ta ajiye saman carpet, dai dai nan aka bude kofar parlon ta daga kai da sauri. Aneesah ce ta shigo parlon ta kulle kofa tana kallon Jiddah daga sama har kasa kallon rigima, Jiddah ta dauke kanta ta mike tsaye, Aneesah ta cire takalmanta ta jefar da jakanta saman kujera tace "Kin gama guje gujen naki kin dawo??" Jiddah ta ki tanka ta, Tana tafe hannu cikin daga murya tace "Toh gobe ko kallon banxa aka ce ki min wllh sae kin zagi wanda ya baki wannan shawaran, don yau sai naga d'an kuturin uban da ya tsaya maki a garin kaduna, ba dai ni kika kwala ma vase kika fita a guje ba...." Jiddah ta bar wajen da sauri ganin ta nufota fiercely, ganin da gaske take sae xaga parlon suke ta kwala wani kara da karfi gabanta na faduwa, Aneesah tayi wani kukan kura ta cafkota ta sa ta a hammata ta shake wuyarta, Jiddah dae sae ihu take da karfi tana kokarin kwace kanta, ko gama buttoning shirt dinsa bai yi ba yake saukowa stairs da saurin sa, still Aneesah tayi tana kallonsa baki bude, kamar ranan ta fara ganinsa, Jiddah ta fashe da wani kuka ta xube nan kasa, ya shigo parlon walking faster, Aneesah bakinta na rawa tace "Ca.. Captain yaushe ka shigo..." Bata rufe baki ba ya kifa mata wani mari, without letting her to recover ya kuma sauke mata wani ya shako wuyarta, ta gwalo idanuwa cike da axaba ihun ma ta kasa, ya turata da karfi har sae da ta xube kasa, da hannu bibbiyu ta dafe kuncinta bayan ta fadi kasa, ya daga Jiddah ya wuce sama da ita, Aneesah ta kasa kwakkwaran motsi a inda take tsaye ta bi su da kallo, ita ba ma ta marin da shakan da yyi mata take ba, kawai so take ta ji sanda ya dawo gidan, da sauri ta nufi kofa kamar mahaukaciya xuciyarta na wani irin bugawa ta nufi mai gadi, tasowa yayi... tana kokarin calming kanta tace "Salisu yaushe mai gidan ya shigo? Yaushe ya dawo???" Yace "Tun jiya bayan magariba Hajiya" Bata san sanda ta furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un da karfi ba, taji cikinta ya hautsine, da sauri ta juya xata koma ciki sae a sannan ta lura da motar Jiddah a parking space don da ta shigo bata lura ba, shi dai ya bi ta da kallo ya girgixa kai kawai ya koma ya xauna, gaba daya hankalin Aneesah yyi mugu mugun tashi, bata ta6a shiga tashin hankali irin na wannan moment din ba, ta ma rasa wani kalan tunanin xata yi, jikinta na rawa ta dau handbag dinta ta haura sama da gudu ta bude zip ta ciro makulli xata saka taga makulli jikin kofar already, all her body was shaking, ta murda kofar ta ji a bude, ta jefar da jakanta kan gado ta shige bandaki a guje, sae da tayi minti goma sannan ta fito har sannan jikinta rawa yake, ta kalli xannuwan gadon dake xube a kasa, ko ta kansu bata bi ba ta ciro wayarta ta shiga kiran Rabi'ah, tana dagawa ta sakar mata kuka tace "Rabi'ah wllh na dawo na tadda captain a gida, kuma a gidan ya kwana Rabi'ah, Rabi'ah am i not done today???" Rabi'ah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya dawo??" Aneesha ta kara fashewa da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na Rabi'ah, na shiga uku na lalace, yanxu me xance masa, ta ina xan fara? What will i tell him, ki gaya min don Allah Rabi, ina xance masa na kwana??" Kuka take kamar xata haukace, Rabi'ah tace "Tabdi, kawai kice masa daga gidana kike, to me xaki ce da ya wuce haka?" Aneesah jikinta sai rawa yake tace "No Rabi'ah baki san waye captain ba, jiya fa mun ta waya da shi da daddare a sunan Ina gida, ashe yana gidan muke ta wayar" Xubewa kasa tayi tana kuka da karfi tana cewa ta shiga uku, Rabi'ah tace "Atoh tunda uwarsa shegen saukin kai gareta kawai kiranta xakiyi ku hada baki kice ta rufa maki asiri tace daga can kike, a can kika kwana, ko kuma ki fito kawai yanxu mu je mu sameta a gida sai ince mata wllh gidana kika kwana baki da lafiya sosai, nasan dai baxai wuce tayi ta fada ba kamar rubabbiya daga nan sai kuma a wuce wajen ta samar maki mafita" Aneesah dai hawaye take tana naxarin shawaran Rabi'ah gaba daya she is just confuse and afraid, bata son wani abu da xai yi sanadin captain ya rabu da ita, baxata ta6a rayuwa babu shi ba, sai kuma ta share idonta jikinta na rawa tace "Gani nan tahowa" daga haka ta figi jakarta da waya ta fice daga gidan. Lallashin Jiddah dake hawaye Abuturrab ya dinga yi a bedroom dinsa, yana stroking bayanta a hankali yace "Komai ya xo karshe in sha Allah Babynah, it's all over now...." Ita dai bata ce masa komai ba tayi lamo jikinsa idonta a lumshe, in dai tana jikinsa jin ta take kamar a sky, the feeling is just heavenly, ta goga fuskarta a bare chest dinsa a hankali, and that immediately turned him on... Ummi ta dinga kallon Aneesah da mamaki ta ma rasa me xata ce mata, Aneesah ta durkusa da gwiwowinta biyu cikin matsanancin kuka tace "Don girman Allah Ummi ki taimakeni ki rufa min asiri, wllh kawai don bani da lafiya ne ta xo ta daukeni xuwa gidansu, shima kuma yasan bani da lafiya don

106 / 117