Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   107 / 117

318K to 321K   out of 348.6K words

har asibiti ya kai ni, Na rantse babu abinda nake iya yi da kai na Ummi, shi kuma muna ta waya da shi ban san ashe yana gidan ba, kuma bai nuna min ya dawo ba, don Allah Ummi ki ce masa s gidan nan na kwana" Kuka take kamar ranta xai fita ta kife kanta da kujera tana kukan da karfi, Ummi tace "Wannan wani irin shashanci ne ki bar gidan mijinki ki tafi gidan kawa ki xauna wai baki da lafiya Aneesah, Jiddah bata gidan ne da baxa ta taimaka maki ba idan baki da lafiya?" Aneesah ta dago cikin kuka tace "Ummi har amai na sha yi a gabanta ko sannu bata ce min ba, ko ruwa xan sha dole haka xan lallaba in sauka kasa da kaina, har gida Rabi'ah ta xo ta daukeni ba wai da kaina na tafi can din ba Ummi" Ummi dai ta rasa abinda ma xata ce, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah ya kyauta, xan kirasa amma gaskiya baxan ce a nan kika kwana ba, menene amfanin karya a rayuwa? Maimakon ya gyara maka lamarinka ma sae dai ya cakudesa, don haka xance gidan kawarki kika kwana kuma xan basa hakuri..." cikin rawan murya Aneesah tace "Nagode Ummi" Rabi'ah bata dade a gidan ba ta wuce.... throughout ranan Aneesah a kwance ta yini kamar mara lafiyar ta lulluba da uban bargo a dakin Ummi, she wish xa a gama issue din nan a wuce wajen ta samu rest of mind, da taji an Shigo parlorn Ummi sae ta kasa kunne ta ji ko captain ne. Abuturrab na kallon Hajiya Fatima bayan ta gama jawabin da take, a hankali yace "Allah ya kara girma Mama, mun gode kwarai da wannan effort din naki, in sha Allah xa mu je can din gaba daya xuwa goben da kika ce in sha Allah" Tace "Madallah da fahimtata da kayi Aliyu, su kuma iyalanka ina ga idan da hali da ka raba masu gida, amma ka fara shawartar iyayenka yanda ku ka yi da su, in my thought hakan kadai ne xai sa kai ma hankalinka ya kwanta kayi concentrating a aikin ka...." Yayi Murmushin karfin hali yace "Haka ne Mama, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" Ta mayar masa da murmushin tace "Ameen my son" Mikewa yayi jin an tada sallan azahar ya mata sallama yace "Xan shiga masallaci" Tace "To shkkn Aliyu, a gaida Jiddar" Yace "Xata ji in sha Allah Mama, bacci take ne shi yasa bamu shigo tare ba" Tace "Toh maa sha Allah" Fita yayi daga gidan ya shiga masallacin dake layin, bayan an idar ya koma gidansa, makullin main entrance din gidan ya ciro a aljihunsa ya bude kofar ya shiga, sama ya haura ya shiga bangarensa xuwa bedroom, bacci Jiddah ke yi har sannan, ya xauna gefen gadon yana shafa fuskarta a hankali ta bude idanuwanta, ya hade goshinsa da nata yayi kasa da murya yace "Sallah... My lazy wife" ta lumshe idonta bata ce komai ba, yayi kissing lips dinta yace "Wa ya koya maki shagwaba haka?" Ita dai bata bude idonta ba, ya juya yana kallon wayarsa dake ring ya mike ya tafi gun wayar ita kuma ta tashi xaune ta sauka daga saman gadon ta shiga bandaki, Abuturrab ya daga wayar ya kai kunne ganin Ummi ke kiransa ya xauna gefen gado yayi mata sallama sannan ya gaisheta, ta amsa tace "Kana gari ne?" Ya d'an yi jim, sai kuma yace "Eh na shigo jiya da daddare" Tace "To ina nemanka yanxu" yace "Toh Ummi, hope all is well?" Tace "Alhmdlh" yace "In sha Allah xan shigo nan da some minutes" Tace "Maa sha Allah" daga haka ta katse wayar, yana xaune dakin har Jiddah ta idar da sallah sannan ya kalleta yace "Ki shirya xa mu je can gida" Tace "Toh" tashi tayi ta nufi kofa xata tafi dakinta, ya bi ta da kallo har ta fita, ya lumshe ido ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ya kwanta saman gadon yana jin wani sonta na musamman na ratsa can kasan xuciyarsa, she is just the perfect wife a man can pray for, both on bed and vice versa.... Karfe biyu da minti sha biyar Abuturrab ya bar gidan tare da Jiddah xuwa gidansu, lkci lkci yake murxa hannunta a cikin motar har suka isa gidan,, parking yyi a waje suka shiga compound din, tana biye da shi suka shiga parlon Umminsa bayan Jiddah ta gaisa da Ummi ta mike ta fita xuwa dakin Hajja, Ummi tace "Me ya hadaku da Aneesah Aliyu?" Da mamaki yace "Aneesah kuma? Tace wani abu ya hada mu ne?" Ummi tace "Ehh ce min tayi ta maka laifi koh" Yace "Ohh ohk, kawai tasan abinda tayi bata kyauta bane shi yasa ta damu kanta, ae ni ban ce mata komai ba, ta kira ki ne?" Infact tun da ya shiga dakinta yaga bata nan bai sake bin ta kanta ba, Kuma da ya ganta shi kansa yasan hukuncin da xai dauka a kanta ba karami bane, Ummi tace "Tana gidan nan" shiru yyi ya ki cewa komai, Ummi tace "Tace taje gidan kawarta har ta kwana without ur knowledge kuma tayi maka karya tana gida without knowing kana gidan kai ma, is that so?" A hankali yace "Ummi ban dau issue din personal ba ni, it's okay..." Ummi tace "Kayi hakuri Aliyu, i know it's painful ko don karyan da ta maka, shine ma worst part din, bata kyauta ba wllh, amma just over look it, tunda har ta gane kuskurenta and she is remorseful..." Yayi murmushin karfin hali kawai yace "Babu komai Ummi" Ummi tace "Good, but she is still sick tun safe take kwance abincin ma bata iya ci wai, asibitin xaka mayar da ita?" Yace "Toh Ummi" mikewa tayi ta fita, ya jinginar da kansa ransa na wani irin baci, she even have the guts to come to his mother, rike bakinsa yyi cike da mamaki da takaici, can ya ciro wayarsa yyi dialing number Ahmad yana fara ringing Abuturrab yace "Plss tell me u are in kaduna" Daga daya bangaren Ahmad yace "What happened?" Abuturrab yace "Tell me so pls" Ahmad yace "Yeahh i am in..... Abuja" Abuturrab ya hade rai, Ahmad yyi dariya sosai jin Abuturrab yyi shiru don ko ba a gaya masa ba yasan hade rai yyi, Ahmad yace "Toh me ke faruwa kake hoping am in Kaduna?" Abuturrab yyi kasa da murya cike da damuwa yace "It's something very very urgent Ahmad, i have nobody to talk to da ya wuce kai wllh" Ahmad yace "Ba a maganan ta waya ne?" Abuturrab yace "Ya fi karfin ta waya Ahmad" Ahmad yace "So what are you insinuating? In taho kd yau?" Abuturrab yyi kasa da murya yace "Plss" Ahmad yace "Ka ci kai, to matata labor take a tsattsaye, and she just start today, don haka kaga baxan bar ta in taho kd ba" Abuturrab yace "Allah ya raba lafiya, but baxa ka taho tare da ita ba" Ahmad yace "Saboda issue din Captain sae matata ta haihu a titi?" Abuturrab yace "I was thinking sati uku ake dauka ana labor din ae" Dariya Ahmad yayi yace "Aa sae dai wata uku" Shiru Abuturrab yyi, and Ahmad gets that he is so disturbed nd tensed, Ahmad yace "Xa mu yi magana, sae anjima" a hankali Abuturrab yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya dafe kansa. Sae kuma ya mike ya fice daga parlon, Ummi da ke can main parlor tace "Xa ku tafi asibitin ne yanxu?" Yace "Ahmad xae xo dubata yanxu, ae munje asibitin few days ago" Ummi tace "Eh haka ta ce min, Ahmad din na gari ne?" Yyi kasa da murya yace "Ehh" Ummi tace "Ohkk" Dakin Hajja ya nufa yana tafiya slowly ya bude kofar, Hajja na kallon Jiddah tace "Toh kin ga ai baxan biyesa mu raba hali a titi da girmana koh?" Jiddah dake ta kallonta tace "Kuma kin shiga gidan?" Hajja tace "Ka ji ki ke kuma da wata magana kamar ta yan wiwi, idan na shiga ai tarwatsa gidan xan yi in tara masu jama'an anguwa in tona masu asiri, ae abun baxae yi kyau ba wllh, sannan gaskiya a Masar ba a goyon bayan tonon asiri, ke baki ga unguwar ba ma na talakawa birjik duk kutaren gida ne a jere bi da bi..." Abuturrab ya gaisheta tayi banxa da shi tana ci gaba da maganarta, Jiddah tace "Yana gaisheki Hajja" shiru Hajja tayi sai kuma tace "Wa yake gaisheni?" Jiddah tace "Shi" Hajja tace "Shi wa?" Kallon Abuturrab Jiddah tayi kamar yanda yake kallonta shi ma, A hankali Hajja tace "Yanxu ke saboda har kin san dadin miji in gama baki labarin walakanci da cin kashin da bawan Allahn nan yayi min a Barnawa kawai mutumi ya shigo ya gaisheni na ba banxa ajiyarsa sai kice min yana gaisheni? To ya gaisheni a saboda me? Me na hada da shi? Mutumin da ya yasar da ni a Barnawa? Ban fa hada komai da shi ba wllh banda Usman da na haifa shi kuma ya haifesa, xumuncin da Allah yace ayi fa kawai nake dubawa ba don haka ba wllh ban hada komai da shi ba, wato ke me miji ko, iyakarsa fa ya dirka maki ciki ya bar ki da wahala yana gantali da tsuntsaye a sararin samaniya, har ki gama wahalanki ki haihu yana kabu kabunsa sama babu abinda ya sha masa kai, don haka idan xa ki kama kanki ki kama kar ya kai ki ya baro ki" murmushi kawai Abuturrab yake yana kallonta, Jiddah kuma ta sunkuyar da kanta ta ki dagowa, mikewa Hajja tayi tace "Ko a fitar min a daki ko kuma ni in fita kawai" Ya ki fita a dakin, hakan ya sa ta fice a fusace, Ya durkusa kusa da Jiddah ya dago kanta yana kallonta a hankali yace "Kina son cikin?" Kauda kanta tayi da sauri, yayi murmushi yana jawota jikinsa. Abuturrab na fitowa masallaci bayan la'asar wayarsa ya fara ring, yana dubawa yaga Ahmad ne, da sauri ya daga Ahmad yace "To kuma don walakanci sai in xo gida baka nan?" Abuturrab ya buda ido sosai yace "Are u for real?" Ahmad yace "Ban sani ba" Da sauri Abuturrab yace "Pls ka jira ni in few minutes time xan iso yanxu, kar ka bar kofar gidan plss" Katse wayar yayi ya shiga motarsa don dama Makullin motar na aljihunsa ya nufi gidansa, yana isa ya tadda Ahmad xaune cikin motar a kofar gidan, yayi parking ya sauko yana murmushi, Ahmad ma ya sauko yace "Wannan ai kanka ka siya ma sabuwar mota ba Jiddah ba, har Abuja fa naga kaje da motar, dama yaudara ce kawai kayi mana??" Abuturrab couldn't help it but laugh hard, Ahmad dai sai kallonsa yake, Abuturrab yayi patting dinsa yace "Idan ma tace bata son motar nan kuma wllh sai in canxa mata, ai aro nake yi ba komai ba, infact ko gidan nan Jiddah tace tana son in mallaka mata wllh i will do so without second thought, i will give her wholeheartedly, ba gida ko mota ba, ni kai na i belong to her, and her wish is always my command" Sake baki Ahmad yayi yana kallonsa, can ya fashe da dariya yace "Ita murhun? Ita me Awaran?" Lkci daya smile din fuskar Abuturrab yayi fading, Ahmad ya dinga dariya don ba da niyyar ya 6ata masa mood ya fadi haka ba, ya kama hannunsa suka shiga ciki yana cewa "Pulling my brothers leg" har suka shiga ciki kuma gaba daya Abuturrab ba shi da walwala duk yayi wani sanyi, Ahmad yace "I left Abuja all because of u now, don haka cheers and tell me what's up?" Abuturrab ya sauke idonsa sai kuma ya mike ya wuce sama, ba a dau lkci ba ya sauko rike da sachet din jiya da ya gani dakin Aneesah ya mika masa su yace "I need more explanation on this pls" Ahmad ya dinga juya abun a hannunsa da mamaki ya kalli Abuturrab yace "This is a prophylactic for ladies, a ina ka samo wannan?" A hankali Abuturrab yace "Dakin Aneesah" Ahmad ya bude ido sosai yana kallon Abuturrab, Abuturrab yace "Yea, i saw them yesterday" Ahmad yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to me take yi da su" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujera, Ahmad yace "Did she know u saw it?" Abuturrab yace "I don't think so" Ahmad yayi shiru yana naxari, Abuturrab yace "kasan me ya faru?" Ahmad yace "No" A nutse Abuturrab ya shiga narrating masa yanda suka dinga yi da Aneesah har xuwa safiyan yau, da kuma lkcn da ta shigo gidan, Ahmad ya buda baki yana ta kallon Abuturrab da mamaki ko kiftawa baya yi, Abuturrab da yaji xuciyarsa na masa kuna, yayi kasa da murya yace "I'm really shock Ahmad, i couldn't sleep well yesternight, I'm still finding it hard to believe this, but i need more evidence before anything Ahmad, yanxu maganan da nake maka tana gidan Ummi taje ta shirya mata karya da gaskiya wai gidan kawarta ta tafi ta kwana... Ban ta6a sanin da gaske akwai karyan da ke girgixa mutum ba sai jiya, wllh i am shock, but all the same i am happy don duk karyan nan da ta dinga min a kan Jiddah ko sau daya ban fito na nuna ma Jiddah bacin rai na ba, I was super calm all that while, sai gashi tun ba aje ko ina ba...." Ahmad ya girgixa kai shi ma dai lamarin da alama ya girgixa sa yace "So what next Captain?" Abuturrab yace "Ba tace bata da lafiya ba? Dama nace ma Ummi xaka je ka dubata tunda mun riga munje asibiti, yanxu abinda nake so shine kawai mu siya alluran bacci mu je can gidan kayi mata, bayan tayi bacci xan yi unlocking wayarta da finger print dinta sai in binciki wayarta, and i am hoping we will find concrete evidence a wayar nata, yanxu if i should show this stuff to our parent the first thing that will come to der mind shine bata son haihuwa ne kawai, infact kowa ma haka xai yi tunani, kaga kuma ai ni bani da abinda xance..." Ahmad ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Exactly, at first nima na xata haihuwan ne bata so, not until this ur story..." Abuturrab ya mike yace "Mu je" Tashi Ahmad that is just speechless yayi ya bi bayan Abuturrab suka fita, sai da suka fara biyawa Pharmacy ya siya alluran bacci sannan suka tafi can gidan.




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you







_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Ahmad ya gaisa da Ummi sannan ya shiga hada alluran, Ummi ta mike bar masu parlon nata, Abuturrab dai na xaune har Ahmad ya gama ya mike, leading dinsa yayi xuwa bedroom din Ummi, ta blanket Aneesah ta lekosu a hankali don ganin wa ya shigo, sai da gabanta ya fadi da suka hada ido da Abuturrab sannan Ahmad, wani tsanarta yake ji har ransa, ya dai dake yace "Kince ma Ummi baki da lafiya bayan ni kince min kin ji sauki, so Ahmad is here xai dauraki kan wani treatment din...." Ta mike xaune tana sauke numfashi kamar gaske, cikin rawan murya tace "Wllh bana son inyi ta daga maka hankali ne kana wajen aiki My Captain, shi yasa nake ta ce maka ni naji sauki" hawaye ta fara yi tana kallonsa, Ko sauraron muryarta Abuturrab bai ma son yi, yana kallon Ahmad yace "Yi mata mu fita, i have somewhere to go m" Ta kalli Ahmad haka nan ta ji gabanta ya fadi, ta girgixa kai a hankali tace "Ni ban son wani allura gwara a bani drugs kawai in sha.... Ban son alluran" Ahmad yace "Alluran xai fi maki drugs din kuma ai" tana kara girgixa kai tace "Aa gaskiya gwara min kwaya baxan iya amsan wani allura ba bayan wa enda na amsa a baya" Kallonta kawai Abuturrab yake yi cike da mugun tsanarta, can ya juya ya fice daga dakin, da Ummi ya tafi ya hadata, Ummi ta shigo dakin tare da shi, tana kallon Aneesah tace "Ya haka ana nema maki sauki kuma kina cewa Aa Aneesah, tunda suna ga alluran ya fi sai ki bari ayi maki ai... Meye a cikin allura" Aneesah ta kasa cewa komai ta rasa me yasa gabanta ke faduwa, Ummi tace "Kiyi hakuri ayi maki kawai" Daga haka ta juya ta fita, Abuturrab ya fita shi ma, haka nan hankalinta bai kwanta ba Ahmad yayi mata alluran, sai wani hahhade masa rai take tana hararansa, dama kuma yana sane ko gaishesa bata yi ba, shima din bai ko kalleta ba bayan ya gama alluran ya juya ya fita xai yi disposing din syringe din, a parlor ya tadda Abuturrab xaune, Ahmad ya dage masa gira sannan ya fita, Abuturrab ya shafa kansa a hankali waiting to proceed for the worst, should he really do this? Yana gudun abinda xai daga masa hankali shi kam, ba a dau lkci ba Ahmad ya dawo parlon ya xauna shi ma, a hankali Abuturrab yace "So where did u leave ur wife?" Ahmad yace "Nayi dropping dinta gidan Umma" Yace "Ohk..." Ahmad na murmushi yace "Captain the once upon a time Hygienist.... Not anymore" Abuturrab ya kallesa da sauri yace "Har yanxu ma kuwa" sai kuma a hankali yace "Is just that one have to adapt to every situation he finds himself in life, i still appreciate Cleanliness, and it's still my priority...." Dariya Ahmad yayi yace "Gaskiya ne..." Lkci lkci Ahmad ke kallon agogon wrist dinsa har ya mike daga karshe ya nufi bedroom din Ummi ya tura kofar a hankali yana kallon Aneesah...., karasawa yayi ciki yaga she is already fast asleep,

107 / 117