Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   111 / 117

330K to 333K   out of 348.6K words

shawarma da tace tana so ya hada har da ice cream sannan suka dau hanyar gida... A hankali yake tafiya a motar ganin kamar Aneesah a kofar gidansa, ai ko yana isa dai dai gate din nasa ya ga ita ce, horn yayi mai gadi ya leko ganin motarsa ya bude gate din, Aneesah ta taso ta nufo motar da sauri, yayi zooming off into the compound, mai gadi na hanata ta hankade sa ta shige cikin gidan, Abuturrab yayi parking a parking space ya bude motar ya sauka, kasa karasawa kusa da shi Aneesah tayi hawaye na sauka idonta ta durkusa tace "Don girman Allah ka tsaya ka saurareni ko na minti biyu ne Aliyu" Abuturrab ya nufi mai gadi yana kwala masa kira a fusace, mai gadin ya taho da gudu bayan ya rufe gate din yana amsa kiran, Abuturrab na huci yace "Me nace maka a kan matar nan Salisu?" Mai gadin yace "Wllh wllh bude maka gate da nayi ne ya bata daman shigowa ciki amma kusan kullum sai ta xo kofar gidan nan har ma ta yini, ko da wasa ban ta6a bude mata gate din ba yallabai" Abuturrab ya juya yana kallon Aneesah dake durkushe tana hawaye da white bandage a hannunta, strictly yace "Look Madam.. i will assume ban ta6a sanin ki ba a rayuwata, and i think i have to report you to the police to stay away from my house because i don't know who u are, i don't know what u are up to, this my take on you... don haka tun muna mu biyu tashi ki fitar min daga gida kada in nuna maki the other bad side of me.... About ur luggages or whatever xan fito da su nan tsakar gida kusa da parking space a rufe su da sheath and anytime aka ganki da babban mota sai a bude maku gate ku kwashi kayan ku" kuka kawai take tana girgixa masa kai tace "Aliyu ka bani minti biyu don darajan iyayenka ka saurareni" Fiercely yace "Get.. out... Of my house" Ta ki tashi tana rusa kuka tana kallon Jiddah tace "Don Allah ki sa baki ya saurareni Jiddah...." a guje ta mike ganin ya nufota, tayi gate da gudu ta fita mai gadi ya kulle gate din, juyawa Abuturrab yayi yaga Jiddah tsaye, ta juya a hankali ta nufi entrance din gidan, ya bude motar ya dau abubuwan da ya siyo sannan ya bi bayanta. Bayan isha Jiddah na kwance jikin Abuturrab dake kallon wrestling a parlor, bata dade da tashi daga baccin da take tun yamma ba, ya dago kanta da damuwa yace "Baby duk yau fa baki ci komai ba, nace ki gaya min me kike son ci kada dare yayi in fita in samo maki plss" Tace "Bayan shawarman da na ci?" Yace "Noo u ate just a bite..." tace "Hakan da na ci ya isheni" Yace "I'm beginning to think if u are really okay..." Tace "Toh kasan me xan ci?" Ya xaunar da ita da kyau yace "Tell me wife, ko kano ne xan je yanxu in samo maki abinda kike so in dawo" Murmushi tayi, tayi lamo jikinsa tace "Indomie nake so with plenty Scotch bonnet pepper, with onion" Yace "Ohk xa mu iya samu a restaurant ai, bari inje in nemo maki in dawo yanxu" Ta dago kanta tayi masa wani kallo tace "Ni dai kai nake so ka dafa min, idan aka siyo a waje baxan iya ci ba" Ya d'an buda ido da mamaki yace "Really" Ta marairaice masa, ya lumshe ido ya bude yace "But idan bai yi dadi ba fa kinsan ni ba girki na iya ba baby, ba gwara in je in samo maki me dadi a duk inda yake ba yanxu" Kwanciya tayi kan kujera ta turo baki tace "Baxan ci ba" Yayi shiru yana kallonta, sai kuma a hankali yace "Ohk... But I don't know all the ingredients u listed..." tace "I will show u" tashi yayi ya nufi kitchen ta mike ta bi bayansa, tana tsaye ta jingina da cabinet ya dauko indomie din a store, ta nuna masa albasa da uban tarugun da take son yayi mata amfani da, yayi ta kallonsu yace "Are they not too much, anyway ya xan yi masu yanxu?" Tace "Wankesu xaka yi" Da wani expression yace "With gloves or what?" Tace "Ka ta6a ganin an wanke pepper da gloves?" Innocently yace "But it's harmful for the bare hands, ba yaji garesa ba? Ba shine tattasai da ake cewa ba" Tace "To da hannun xaka wanke ka cire duk hancin, ka yanka albasan" Ya fi minti daya yana bin tarugun da kallo sai kuma ya dauka yaje sink yana wankewa a hankali, tace "And baka sa ruwan indomie din ba a wuta ai" Yace "Ohk" dawowa yayi ya kunna gas ya daura ruwa a tukunya ya rufe, ya ga ta fita ta ya bi ta da kallo yana mamakin wannan aikin da ta sa shi da bai ta6a yi ba a rayuwarsa, bai ma ta6a tunanin akwai ranan da xai shiga kitchen da sunan ya sarfa abinci ba sai first night dinsu da ya shiga ya soya kwai sannan yau da tace dole shi xai yi mata indomie, ya langwabe kai yace "And i have to make it very delicious for her" Dawowa kitchen din ya ga tayi da kujeran dinning ya dinga kallonta da mamaki, ta ajiye ta xauna tsakiyar kitchen din tana kallonsa, bayan ya wanke pepper din ya juya ya kalleta yace "Toh ya xan yi da shi?" Hannu ta buda alamar bata sani ba, ya ciro wayarsa a aljihu ya shiga google... Sosai Abuturrab ya wahala kafin ya hada wannan indomie na yan gayu da Jiddah ta sa shi, idonsa sai yaji yake masa sbda albasa, ita dai ko uffan bata ce ba sai bin sa take da kallo, duk yayi kaca kaca da waje kamar kwali biyu na indomie ya dafa, ta dinga kallon indomien da ya juye a plate sai uban ruwan da ya cika kamar farfesu ga Indomien har yayi extra done, da liquid soap ya dinga wanke hannunsa a sink sannan ya juya yana kallonta a hankali yace "Na gama baby" ta tashi tace "Toh ka kawo" daga haka ta fita ta tafi parlor ta xauna, ya sauke ajiyar xuciya ya fitar da kujeran da ta shigo da ya mayar dinning sannan ya dawo ya dau indomie bayan ya saka fork a ciki ya fita ya kai mata ya ajiye gabanta, ya koma fridge ya dauko ruwa da lemon five alive ya dawo ya ajiye yana kallonta, daukan fork din tayi ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fara cin indomie din a hankali, ko taste din kirki babu sbda uban ruwan da ya cika, haka tayi ta cin abunta, ya ji dadi sosai ya xauna saman kujera yana kallonta, sai da ta ci rabin indomie din taji xuciyarta ya fara tashi ta jinginar da kanta da kujera yace "Baby what?" Ta kallesa sai kuma ta tashi ta tafi kujeran da yake ta xauna ta kwanta kusa da shi tace "Amai nake ji" Ya rungumeta yana buga bayanta gently yace "Amai kuma baby bai maki dadi bane" Tace "Yayi" haka ya dinga yi mata har taji aman ya daina damunta, ta lumshe ido jikinsa tace "Yayi min dadi sosai" murmushin jin ddi yayi yana shafa gashinta yace "I am happy my baby like it" Da safe Abuturrab ya tashi da farin ciki wanda baya misaltuwa don faduwa ce ta xo mashi dai dai da xama, Jiddah na bacci ya shirya ya tafi gida wajen Umminsa... bayan ya gaisheta ta amsa tana kallonsa ganin how good his mood was, tace "Ina Jiddar?" Yace "Tana gida Ummi" Ummi tace "Toh maa sha Allah, baka koma aiki bane?" Yace "Dama na xo ne in gaya maki aikin da na nema few years back na samu offer dinsu sun turo min ta mail... daxu na gani da asuba" Da mamaki Ummi tace "Wani aiki?" Yace "Piloting also, a private pilot, ko kin mance sanda nayi applying?" Ummi tayi shiru sai kuma tace "License or certificate din fa Aliyu, isn't it cost?" Yace "Nahh, i got that since Ummi, may be u forgot" Tace "So u mean u are tired of being an Airline transport pilot?" A hankali yace "I need more time for my self and family Ummi, i have served them in the sky for long, so xanyi resigning yanxu..." Ummi tace "Toh Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi a gareka" Yace "Ameen Ummi" Wayarta ne ya fara ring ta dauka ganin Umma ke kiranta ta daga ta kai kunne, bayan sun gaisa Umma tace "Toh munyi grandson" Ummi tace "A'a toh Alhmdlh, Alhmdlh, yaushe ta sauka?" Umma tace "Few minutes ago" Ummi tace "Toh Allah ubangiji ya raya mana, Allah yayi masu albarka" Bayan sunyi sallama Ummi ta kalli Abuturrab tace "Ramlah ta haihu" Yace "Maa sha Allah, Allah ya raya, i left my phone at home kilan Ahmad din ma ya kirani" Ummi ta mike tace "Bari in sanar ma Hajja" Daga haka ta fita daga parlon. A ranan kamar yanda Abuturrab ya fada da rana ya kira masu fitar da kayan Aneesah ya sa aka ajiye mata su kusa da parking space sannan aka lullube da Sheath din, Jiddah dai na xaune parlor don ya sa ta shirya xa su fita amma bai ce mata ga inda xa su ba, tana ta kallon yanda ake fitar da kayan Aneesah, har lkcn she is speechless she don't even know what to say to Aliyu, she don't know why she felt bad about everything that have happen, duk da bai gaya mata abinda ya sa shi sakin Aneesah ba amma har ranta bata ji dadi ba, bayan yan fitar da kayan sun gama ya sallamesu sun wuce ya dau makullin motarsa ya sauko downstairs yana kallon Jiddah ya nufeta, yana jan hancinta yace "Mu je ki ga baby" Tace "Wani baby?" Ya kashe mata ido yace "Ramlah ta haihu" tashi tayi da sauri tana wara ido tace "Don Allah da gaske?" Yace "Yea" kasa boye farin cikinta tayi tace "Shine baka gaya min tun daxu ba... Ni dai don Allah mu je ka kai ni" ya kama hannunta suka fita daga gidan, da yake an sallamesu asibiti gidan Umma suka wuce, Jiddah ta wuce dakin Umma direct bayan Maimoon ta sanar mata Ramlah na ciki, Hajja na rike da jaririn tana shiryasa bayan ta gama masa wanka ta kankance ido tana cewa "Mata ki dinga abu isa isa da gadara kamar ni bare ce wajen Ramlar, toh dai ni na haifi uban Ramlah don haka ban ga ta inda kika fi ni kusanci da ita ba, kuma in don ta kece ma baxa ki gan ni gidan nan ba, to ina ruwana da wani Ahmad, ni sabida jikata na xo, daga nace a hada ma yaro gulucodi a fida sai ki kama min fitina, aa ni baxan biyeki ba aniyarki ta bi ki...." Ko kallonta Umma bata yi ba tana ta gyara sabon siff din baby, Ramlah kuma na kwance tana bacci kan gadon Umma, Hajja na ganin Jiddah tace "Xan dai ga uban da xai ce min haka xanyi ko ba haka xanyi ba idan matar Aliyu ta haihu... Ko ita Hauwan sai in tsine mata albarka idan tace xata min shisshigi a lkcn balle ke" kwafa tayi tace "Allah dai ya bamu lafiya ai kamar gobe ne, xan nuna ma kowa ni er banxa ce a lkcn" Jiddah ta durkusa ta gaida Hajja tana kallon kyakkyawan yaron hannunta, Hajja tace "Ga can jakata ki budu ki jera min kayana a kambodin Ramlah, atamfa a gefe, leshi a gefe, mayafan kuma ki saka su a tsakiya, basu fi kala ashirin ba kayan" Jiddah ta juya tana kallon katon jakan da Hajja ke nuna mata.




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Jiddah dake xaune gefen gado rike da Babyn Ramlah a hannunta ta kauda kanta da sauri ganin abinda ke hannun Huraira me aikin Umma, Huraira ta karaso ta ajiye plate din tuwo da miyar agushi a kusa da Hajja, Hajja ta kalli Umma dake hada ma Ramlah shayi tace "Toh kin ga rashin d'a'an maimakon a bani girmana a xubo min abincin a cooler na tuwo da miya amma an kawo min tuwo a plate kamar almajira miya kuma na galantoyi a plate, to dai ya fi babu wai d'an agwai da bak'in da" Umma dai bata ce komai ba ta gama kada shayin ta mika ma Ramlah, Hajja ta kalli Jiddah da ke kallon wani side din daban aroma din miyan na damunta tace "Ki ajiye masu yaronsu kiyi ta kanki ki xo mu ci abinci, yaron da ake ta nuna mana fin karfi kamar d'an gwal..." Jiddah ta kasa juyowa ga amai dake taho mata, Kafin Hajja ta sake cewa komai ta kwantar da jaririn da sauri ta ajiye gyalenta xata fita Umma dake lura da ita ta nuna mata bandakinta tace "Shiga nan" Dawowa tayi ta shiga bandakin Umma da sauri ta hau kwarara amai, Hajja da ta bi ta da kallo ta saki baki har sai da Jiddah ta fito bayan minti biyar, kwanciya tayi saman carpet din dakin tana maida numfashi, Hajja tace "Sai dai da kika bari ya kai ki ya baro kenan er nan?" Jiddah ta daga kai a hankali tana kallon Hajja, Umma na kallon Jiddah tace "Ta shi ki dawo nan" Jiddah ta kalli gadon da Umma ke nuna mata sannan ta tashi da kyar ta hau ta kwanta Ramlah na mata sannu, Hajja ta kyabe baki tace "Toh ai shkkn kuma"

4months later...

Cikin bacci Jiddah ta ji ana jan hancinta a hankali, ta bude ido da kyar tana kallonsa, cikin shagwaba tace "Me yasa baka son ka dinga bari na ina bacci ne?" Ya marairaice mata yace "Baccin ya isa haka, tun safe fa, kin barni ni kadai kamar maraya...." Bai jira cewarta ba ya dagota xaune ta sakar masa kuka cike da shagwaba tana turasa tace "Ni wllh baka bari na inyi bacci" rikicewa yayi ya rungumeta sosai yace "I only want to show u something sai ki dawo ki ci gaba da baccin, i am so eager to show u" Tana kallonsa ta turo baki tace "Oya toh meye shi?" Dagota yayi suka mike tsaye, riga ce iya cinya a jikinta, idan kai ba me lura bane ba ma baxa ka san da wannan cikin na jikinta ba, sosai ta kara kyau tayi fresh, kuma ta d'an murmure kirjinta suka cicciko, da kansa ya daure mata gashinta sannan ya matso mata da takalman da take sa wa a daki ta saka yana rike da hannunta suka fita dakin, dakin Aneesah na da ya bude a hankali yana kallon Jiddah da murmushi fuskarsa, wara ido tayi ganin yanda aka gyara dakin for a new born, kamar dai irin gobe xata haihu din nan, gadon jaririn ciki kadai ma abun kallo ne... Dakin yayi masifaffen kyau, yana rike da hannunta suka shiga ciki ya bude press din kaya taga wasu uban kayan baby iri iri masu tsadan gaske, ya ja ta xuwa bathroom nan ma dai complete set iri biyu na kayan wankan jariri ne a ciki, ta juya ta kallesa tana wara ido, rungumesa tayi ta lumshe ido cikin sanyayyan muryarta tace "Thank you my world" Ya kankameta yace "Anything for u and my little pilot wife" Kissing lips dinsa tayi, sai kuma ta hade rai tace "little Pilot dinka kadai ka sani, don ni bani da kowa ko?" Dariya yayi yace "Ai sai mun gama da shi xa mu fara naki babynah" Turo baki tayi tace "Ka dai nuna yan ubanci tunda pilot din ka fara yi ma...." Yana murmushi yana shafa cikinta yace "Mama ta shigo daxu kina bacci" Tace "Me yasa baka tasheni ba?" Yace "Idan na tashe ki ai na tashi Lil pilot ne" Murmushi tayi tace "Toh in je gidan nata yanxu tunda baccin ya fita idona?" Yace "Ba ki ci abinci ba ai" Tace "Aa ban fara jin yunwa ba" Yace "Are u sure babynah?" Tace "Sure dear" Yayi pecking lips dinta yace "let me get you ur hijab, sai ki tafi amma kar ki dade plss, just 5mins ki gaisheta ki fito" Daga haka ya koma dakinta don dauko mata Hijab, ta dinga bin dakin da kallo tana kara jin son captain a ranta, tun bayan da aikinsa ya dawo twice to 3 times a week take samun kulawa na musamman daga garesa a ko da yaushe yana makale da ita, always there for her, komai shi yake mata, hakan yasa shakuwansu ya karu sosai... Ba a dau lkci ba ya dawo da hijab dinta da wata doguwar rigan, duk shi ya saka mata sannan ya rakata har bakin gate kafin ta fita ta kallesa cike da shagwaba tace "Plss ka dafa min white rice kafin in dawo ina son in ci da mai da ya ji" Yace "Right away baby" Daga haka ta fita shi kuma ya koma gidan ya shiga kitchen kamar Ummi ta sa shi aiki. Kasancewar ranan asabar ne su Khaleesat duk sun tafi makaranta, babu kowa downstairs sai mai aiki, bayan sun gaisa Jiddah ta xauna a parlon, mai aikin kuma ta tafi sama sanar ma Mama xuwanta, Jiddah na ta xaune ita daya parlon har taji shigowar mota compound din gidan, bayan few minutes aka bude kofar parlon ta daga kai, wani Dattijon da baxai wuce shekaru 73 ne ya shigo parlon da sallama hannunsa rike da karamin jaka, kallonsa Jiddah ta dinga yi babu ko kiftawa kamar idanuwanta xa su fito, can ta mike tsaye da sauri, ya karaso parlon shi ma dai yana kallonta, bata san sanda ta

111 / 117