Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   104 / 117

309K to 312K   out of 348.6K words

07087865788... Thank you


_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Jiddah tayi shiru, daga daya bangaren ta ji muryar Aneesah kasa kasa tace "Hello My captain..." ta fadi hakan yayi sau uku, jin shiru Aneesah ta katse wayar ta sake kira, Jiddah ta dinga kallon screen din kamar baxata daga ba, har ya kusa katsewa sai kuma ta daga a takaice tace "Dama kawai ce maki xanyi ya dawo tun daxu..." Aneesah ta xabura lokaci daya tace "Captain din?" Jiddah bata ce mata komai ba ta katse wayar, Ta ajiye masa kan kujera sannan ta fito ta wuce dakinta.. Abuturrab na dawowa masallaci bayan magrib ya dinga kallon motar da yayi parking kofar gidansa, sai ga Rabi'ah ta sauko daga maxaunin driver ta bude back seat ta riko Aneesah ta fito da ita, Banda nishi babu abinda Aneesah take tana tafiya da kyar Rabi'ah na rirrike da ita tana mata sannu, ya dinga kallonsu sai kuma ya shige gate kawai, yana xaune parlor suka shigo bayan minti goma irin da kyar Aneesah ke tafiya din nan, Aneesah ta kwanta saman kujera tana sauke numfashi da kyar tace "Ka dawo ne Captain? Hope all is well?" Shiru yayi yana kallon tv, Rabi'ah tace "Haba dai Captain, kai da ya kamata ka fara tambayar lafiya ka dawo gida baka sameta ba kuma daga ina take? Sai kuma kayi shiru? To daga asibiti muke" Ko kallonta Abuturrab bai yi ba, Aneesah ta mike xaune ta jingina da kujera tana nishi tace "Ban yi bacci ba kwata kwata jiya da daddare captain wani xaxxabi me xafi ya rufeni na rasa yanda xanyi, ga shi drugs da aka min prescribing a hospital kamar shi ya sake triggering xaxxabin da ciwon kai, na daure da sassafe na fita na kwankwasa ma matarka kofa tana ji ta ki budewa, har ce mata nayi bani da lafiya ne, wllh sai ce min tayi ita baxata iya fitowa ba bacci take, ban ta6a xaton haka ba wllh, na dai koma dakina ina son sake shan drugs din nawa amma ban ci komai ba, sai na daure na sauko downstairs wajen karfe sha biyu tana xaune tana kallo tana cin abincin da ta girka, jin kamshin girkin ya sa naji amai ya taho min, wllh captain a nan parlon na gama amai na, na gyara wajen Jiddah ko sannu balle Allah ya sauwake, shine na koma daki nayi ta kiran layin Aunty Safara'u taki dauka kuma nasan fushi take da ni har yanxu, da na rasa yanda xanyi kai kuma ina tunanin kana bakin aiki sai na kira Rabi'ah ta xo ta kai ni asibiti, shine sai yanxu fa" Rabi'ah ta ajiye mata ledan magungunan hannunta tace "Sai da safe Aneesah, Allah ya sauwake ya kara lafiya, ciwo kuma na kan kowa ai...." Daga haka ta nufi kofa ta fita, Abuturrab ya dinga kallon Aneesah dake sauke numfashi da kyar, yace "Wani asibitin ku ka je?" Tace "Nima ban sani ba, sai dai a tambayeta, i almost lost conscious a hanya" Bai kuma ce mata komai ba ya mike ya wuce sama, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, ta tashi ta tafi dakinta da sauri ta kwanta ta lulluba da bargo, bayan isha Abuturrab ya shigo dakin nata, duk da idonta biyu taki nuna hakan, ya karasa ya xauna gefen gadon yana kallonta yace "Ya jikin?" Ta bude ido da kyar tace "Da sauki" yace "Me xa ki ci?" Tayi kasa da murya tace "Shayi kawai xan sha kar in yi amai" mikewa yayi ya sauka kasa ya shiga kitchen, yana making cup of tea Jiddah ta shigo kitchen din, ya kalleta sau daya ya ci gaba da abinda yake, ta wanke plate din hannunta ta ajiye xata fita ta ji yace "Me yasa da Aneesah ta ce maki bata da lafiya kika yi shunning din ta?" Kallonsa Jiddah take with confusion, ya juya ya kalleta yana jiran amsanta, jin tayi shiru yace "Just like that?" Tace "Ehh, haka nayi niyya" tana fadin haka ta juya ta fita ya bi ta da kallo, lkcn da Aneesah ta fada masa he find it hard to believe ya dai ji ta kawai, amma yanxu ya tabbatar hakan ne, ya dau shayin ya fita ya kai ma Aneesah daki, Jiddah ta xauna gefen gadonta tambayar da Abuturrab ya mata na rotating a kanta, wai me yasa tayi shunning Aneesah, a ina ta ganta balle tayi shunning dinta?? Karfe hudu da rabi na asuba Abuturrab ya gama shiryawansa a dakin Aneesah, ita ce ma ta tashesa don yace mata he will be leaving very early kafin sallan asuba sbda karfe takwas xa su yi piloting jirgi xuwa PH, ta hada masa ruwan wanka ta dauko masa kayan da xai saka daga bangarensa har hakan ya basa mamaki don duk xamansu bata ta6a yi masa haka ba, da damuwa tace "To breakfast fa? Haka xaka tafi baka karya ba?" Yace "I will... At the airport, how are you feeling now?" Tace "Aa na ji sauki sosai" Yace "Alright, Allah ya sauwake" Tace "Ameen My Captain, yaushe xaka dawo?" Yace "Friday in sha Allah" tace "Toh wai me ya dawo da kai jiya, ko dai ka ji a jikinka bani da lfya ne?" Yayi murmushi kawai ya dau jakar laptop dinsa yace "Probably.... Take care, sae na dawo" tace "Toh xa ma ka samu motar da xai je Abuja this early kuwa?" Yace "Aa i will drive" daga haka ya nufi kofa tace "But ina son magana na minti daya captain" ya juyo ya kalleta, tayi kasa da murya cike da damuwa tace "I don't know why Jiddah bata son mu xauna as one Captain, ko don sbda abubuwan da na dinga yi a baya ne ya sa ta ki sakin jiki da ni ban sani ba, dama shi mutum baya canxawa Allah baya canxa sa? Wllh nayi nadaman abubuwan da na aikata a baya, naga ba shi da amfani ba shi da fa'ida, i was just behaving like an illiterate a lokacin, baya bayan nan na gane babu abinda ya kai xaman lafiya dadi, balle ita da nake mata kallon warce bata da hayaniya xa mu xauna lafiyan, amma wai bani da lafiya Jiddah tayi kamar bata sani ba a gidan nan alhalin a gabanta nayi amai ta kauda kai, rashin lafiya ae ya fi gaban komai... da bata min haka ba wllh" Yace "Sai na dawo" fita yayi dakin, ya nufi dakin Jiddah ya murda kofar ya bude ya shiga, bude kofar ya farkar da ita, ya kunna wutan dakin yana kallonta yace "Lend me the car key" Sauke ido tayi daga kallonsa ta sauka kan gadon ta tafi gaban madubi ta dau makullin ta ba sa, har ya nufi kofa ya dawo yana kallonta yace "Ke yanxu abinda kika yi jiya kin kyauta Jiddah? Komin abinda mutum yayi maki kika ga bashi da lafiya ai xaki yi masa abinda ya kamata a matsayin ki na musulma, Did u know what it means to have a forgiving heart kuwa?" kallonsa kawai Jiddah take ta ma rasa abinda xata ce don bata san a kan me yake maganan ba ma, a xuciyarta kuwa tunani ta shiga yi waye ba lafiya? Ganin taki ce masa komai ya nufi kofa ya fice daga dakin. Da safe karfe tara Jiddah ta sauko ta ga Aneesah xaune parlor tana kallo da plate din samosa da spring rolls a hannunta tana ci, aikin kenan ta ci tayi kallo... Tana ganin Jiddah ta dinga mata wani kallon raini daga sama har kasa, Jiddah dai bata kalleta ba har ta wuceta, ta ja wani dogon tsaki tace "Shi dan talaka dama idan ya samu waje ya fi kowa gogewa da girman kai, banxa kawai er matsiyata" Jiddah ta tsaya ta juya tana kallonta, Mikewa Aneesah tayi ta nufeta a fusace tace "Ko xa ki rama ne da kika tsaya kallona haka?" Jiddah ta girgixa kanta tace "Not my home training" Ta juya xata wuce Aneesah ta fixgota da karfi tace "Home training din waye kenan?" Duk da yanda gaban Jiddah ya dinga bugawa haka ta hade rai tace "Cika ni..." Aneesah ta dunguri kanta tace "Anki a cika ki don ubanki, kiyi abinda xa kiyi" Jiddah tace "Babu abinda xanyi tunda ni ba mahaukaciya ba..." Bata rufe baki ba Aneesah ta sauke mata mari sannan ta hankadeta da karfi tace "Uwarki ce mahaukaciyar, ehh uwarki da ba a san ko cikin shege tayi ta haifeki ba tunda har yau ba a ga dalilin asalinki ba..." Jiddah ta dafe kuncinta tana kallonta, Bata san lkcn da ta figi flower vase dake saman center table ba ta buga mata shi a kai, duk da Aneesah ta kauce sai da abun ya sameta, wani ihu ta fasa ta dafe kanta lkci daya idonta ya fara juya mata sai dai kan nata bai fashe ba, ta nufi kitchen da gudu kamar mahaukaciya, Jiddah na ganin haka tayi hanyar kofar fita, kan kace me sai ga ta a bakin gate, gaba daya ta tsorata, mai gadi na tambayarta lafiya ko kallonsa bata yi ba ta fice ta shige gidan Hajiya Fatima, da gudu Mai gadin ya nufi entrance din gidan don ganin abinda ya faru.... Babu kowa parlon gidan, Jiddah ta xauna saman kujera a hankali tana bin parlon da kallo, lkci daya ta rufe fuskarta da kujera ta fashe da kuka a hankali, ji tayi ta gaji da komai na rayuwan, ta rasa me ke mata dadi, ta ma rasa wani tunanin xata yi, kuka tayi sosai a parlon daga karshe ta goge hawayenta a hankali ta jinginar da kanta da kujera tana tunanin rayuwarta, she wish she have another place to go apart from Umma's house, she wish tana da yan uwanta na jini da ta sani, she wish her father is alive today, kilan da gorin da xa a dinga yi mata bai kai haka ba, wasu hawayen masu xafi suka sauko idonta tunawa da maganganun da Abuturrab yayi mata daxu bata san hawa ba bata san sauka ba, Rahama ce ta shigo parlon daga kitchen, da mamaki ta tsaya take kallon Jiddah, tace "Aa Jiddah? Yaushe kika shigo?" Jiddah ta daga kai a hankali tana kallonta ta kasa ce mata komai, tace "Bari in sanar ma Hajiya" juyawa tayi ta koma sama ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da mum dinta, Hajiya fatima na kallon Jiddah ganin hula ne kawai a kanta ga shi doguwar riga ta saka, ta nufota tace "Lafiya Jiddah? Daga ina haka?" Jiddah bata san sanda ta fashe da kuka ba cikin sanyin murya tace "Nemana take da fada mama" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah, amma wannan yarinya dai ina ga ta hada iri da maguzawa, bata da mafada ne ko hankali ne kawai yayi gardama? ina shi mai gidan naku?" Cikin rawar murya Jiddah tace "Ya koma aiki" Hajiya Fatima tace "Wannan wace irin fitinanniya ce kuwa? Taso mu je sama, shi ma yasan mara tarbiyar da ya ajiye gida ya xa ayi ya dinga barin ku ku biyu kadai a gida? Haba wannan ai ba dubara bane, yaushe aka gama wancan case din ina jin ko sati ba ayi ba, shi tunaninsa bai basa cewar bai kamata ya bar ku a gida tare ba tunda yasan matar tasa yar tasha ce? Wani bala'i ne wannan ke cin ta kamar jahila?" Dago Jiddah Hajiya Fatima tayi ta wuce sama da ita xuwa parlonta, Rahama ta bi bayansu ita ma ta ji ranta ya baci sosai, tace "Yarinyar nan na bukatar wa enda xa su koya mata hankali wllh, tana bukatar a koya mata lesson, ita ko kunya bata ji ba da er cikinta take tashin hankali kullum? Ko dai bata da saiti ne?" Hajiya fatima ta xauna bayan ta xaunar da Jiddah saman kujera, Rahama ma ta xauna, duk ranta ya gama baci, cikin fada tace "Allah Mama wannan ba karamin issue bane wllh, ya kamata ayi masu iyaka me karfi ko kuma a raba masu gida kada wataran ta illata ta tun da ba sa'arta bace karfinsu ba daya ba, yanxu me ya hadaku?" Jiddah ta share hawayen dake xubo mata tace "Kawai na sauko kasa shine ta fara xagina har da iyayena tana dungurina, kuma take tambayata ko xan rama ne nace mata ai ni ba mahaukaciya bace shine fa ta mareni" Kuka sosai Jiddah take tana kallonsu, Rahama tace "Kan bala'i, ta mareki? Sai kika yi me?" A hankali tace "Ni kuma na dau vase na kwala mata a kai na fito" Rahama tace "Good!!! Dai dai kenan da fuskarta kika saita kika maka mata vase din a kai tunda ita yar matsiyata ce bata san mutunci ba, banda jahili wa ke irin wannan kishin en kauyen da take? Ai kai ya waye yanxu matured kishi ake na kwalliya da kamshi da iya tarairayan miji, sai kuma kayi takama da kwallinka, wa ke irin wannan kishin na hauka a yanzu dai? Aa wllh babu sai a kauye" Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "A wani anguwan iyayenki suke Jiddah?" Jiddah ta d'an yi shiru, lkci daya wasu sabbin hawayen suka kawo idonta ta ma rasa abinda xata ce, Hajiya Fatima tace "Ko ba a kaduna suke ba?" Hawaye na sauka idonta cikin sanyin murya tace "Iyayena duk sun rasu" Hajiya Fatima tace "Hasbunallah!!" Allah ubangiji ya gafarta masu yayi masu Rahama" A hankali Jiddah tace "Ameen" Hajiya Fatima tace "Toh ina relatives dinki kuma suke?" Jiddah ta goge idonta cike da karfin hali tace "Wajen stepmom dita na taso" Rahama sai kallon Jiddah cike da tausayinta cause ta yanda tayi maganar xaka san she is hurt, a hankali Hajiya Fatima tace "Toh dangin mahaifiyarki da Mahaifinki fa?" Jiddah ta kalleta, bata san sanda wani kuka ya taho mata ba ta fashe da kuka sosai tace "Ban san su, i only know my step mum, ita kawai na sani, wajenta na taso" Duk suka yi shiru suna kallonta cike da tausayi, Hajiya Fatima tace "Ina ita stepmom din taki take?" Cikin rauni Jiddah tace "Hayin rigasa" Hajiya fatima tace "A can din Aliyun ya auro ki?" Jiddah ta kasa ce mata komai hawaye wani na bin wani a idonta, Hajiya Fatima tace "Ki daina kukan nan kiyi min magana Jiddah" Tayi kokarin daina kukan da take, cikin sanyin murya tace "Ina yi mata awara a bakin titi ya gan ni, a hayin rigasa...." Daga Hajiya Fatima har 'er ta where a bit shock, don dai a class din Abuturrab da kyansa, da kudinsa, da kuma profession dinsa, infact Abuturrab bai yi kama da wanda xai yi stooping kansa that low ba at all, Rahama a ranta ta dinga tunani to kyanta ne ya tafi da shi, ko haskenta? Ko da yake babu yanda Allah baya ikonsa, l Hajiya Fatima tace "Ikon Allah, a can ya auro ki kenan?" Jiddah ta girgixa kai tace "Ya dai taimakeni, kuma ba wai don ya aureni ya taimake ni ba, ya taimakeni ne saboda halin da ya ga nake ciki wajen stepmom dita" Hajiya Fatima tace "Kamar yaya kenan?" Cikin sanyin murya Jiddah ta fara basu labarin tun daga farkon haduwarta da Abuturrab har xuwa yanxu da ya sake aurenta for the second time ya hadasu da Aneesah, Rahama dai sai hmm take cause she is speechless, Hajiya Fatima kuwa tagumi tayi tana ta kallon Jiddah don labarinta ya sanyaya mata jiki, wani tausayinta ta dinga ji har kasan ranta, Rahama ta kara sauke ajiyar xuciya for the third time sannan tace "Yanxu na gano dalilin da ya sa ta sako ki gaba, na farko tana ganin baki da kowa baki da wani me tsaya maki banda dangin Aliyun, ta yanda idan ta tafka tsiyarta a kanki sai ace family issue ne kamar yanda aka yi last week ta lalata maki furnitures, na biyu kuma tana ganin ke ba class din kishinta bane, ta raina wacece ke, ta raina personality dinki, tana ganin ta fi ki komai ta fi ki gata, but she is mistaken, she is deceiving her self don ko nayi rantsuwa baxan yi kaffara ba kin fita value a wajen mijinku from the way i saw things..." Hajiya Fatima da tayi nisa a tunanin da take ta kalli Jiddah bayan ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina gidanku yake a hayi Jiddah?" A hankali Jiddah ta gaya mata, Hajiya Fatima tace "Tashi ki sauka downstairs akwai breakfast a dining ki deba ki karya tukun" Jiddah ta mike a hankali ta juya ta fita daga parlon duk suka bi ta da kallo, Rahama tace "Mama don Allah kar ma ki nuna tana gidan nan, ki bar ta tayi xamanta a nan ta samu nutsuwa, kalli fa duk a firgice take kana ganinta kasan bata da rest of mind a gidan miji? For what reason? She is too young to be experiencing this bull shit, Wllh kawai don kin hanani shiga abinda babu ruwana ne banda haka sai na nuna ma kishiyarta karamin hauka take, Allah sai na rama mata marin" Hajiya Fatima tace "Aa bbu ruwanki, ki bar komai a hannu na kawai..." Rahama tace "Allah ya sa mai gadinsu bai ga shigowarta nan ba, a barta ta huta na kwana biyu wllh, shi ma banda dama ya so a cuceta ne ai yasan mahaukaciya ya ajiye a gida, ta yaya xai tafi ya barsu su biyu kadai, wato ya ba kura nama kenan, ko kanninsa baxai kawo gidan ba su xauna saboda Jiddan, haba tayi kankanta da yawa da fara fuskarta matsalan gidan aure, kamarta yanxu ai ya kamata ace karatu take ba wai facing marital crisis ba, gaskiya banji dadin wannan labarin ba, na tsani in ga ana walakanta 'ya mace, macen ma karama, idan bata samu kwanciyar hankali a gidan aure ba albarkacin shekarunta ai baxa a dinga musguna mata haka ba, no plss this is too bad..." Hajiya Fatima tace "Ke wannan ne

104 / 117