Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   109 / 117

324K to 327K   out of 348.6K words

yayi gaban Jiddah dake kwance yanda ya bar ta, ya dagota yana jijjigata yana kiran sunanta a rikice.... karfe sha daya da few minutes Abuturrab ya rako Ahmad bakin motarsa, gaba daya he isn't himself, Ahmad ya juya yana kallonsa yayi patting shoulder dinsa yace "She will be fine in sha Allah, u need not to worry Bro..." Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya kawai bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Xan shigo gobe da safe idan Allah ya kai mu" Cikin sanyin murya Abuturrab yace "Ohk... Thank you Ahmad" Yana tsaye har Ahmad yayi reverse ya bar anguwan, sannan ya juya ya koma cikin gate din gidan ya kulle, yana shiga parlor ya kulle gidan ya haura sama, dakinsa ya nufa ya xauna gefen gado yana kallon Jiddah dake bacci, ya kai hannu goshinta a hankali yana kallonta with pity, bayan kusan minti goma ya jinginar da kansa jikin gadon ya lumshe idonsa. Cikin dare ya bude ido da sauri jin tana motsi don har bacci ya daukesa, ya gyara xamansa yace Jiddah, ta bude ido da kyar ya kamo hannunta yace "How are you feeling now?" Kanta kawai ta nuna masa, ganin mikewa xaune take son yi ya dagota da damuwa yace "Xai daina in sha Allah, should i make u tea or anything?" Ta girgixa masa kai da kyar tace "I want to ease my sef" Ya mike ya dagota ya kai ta har bathroom din suka fito tare, kuka ta sakar masa sbda ko ina na jikinta ciwo yake mata sosai, ya dauketa ya kwantar gefen gado ya durkusa gabanta yana kallonta cike da tausayinta yace "Kiyi hakuri plss wife, i caused u all this..." Throughout daren haka ya dinga lallabata bai yi bacci ba yana mata tausa a hankali, a haka har ta koma bacci wajen karfe hudu.... Ana idar da sallan asuba ya kawo mata shayi ya lallabata ta sha sannan ya bata magungunan da Ahmad ya taho da shi jiya bayan alluran da yayi mata, tana shan maganin babu dadewa bacci me nauyi ya dauketa, sai a sannan Abuturrab ya samu ya kwanta gefenta shi ma yayi baccin da bai yi ba daren jiya. Da rana ya dawo daga gidan Umma bayan ta kirasa yaje ya amsar ma Jiddah abinci don Ahmad ya bata labarin abinda ya faru, har da ta shirya xata taho yace mata ai da sauki ba sai ta je ba kawai tsorata Jiddan tayi but she is getting better, yana isa kofar gidansa ya tuna fa bai sake shiga gidan Hajiya Fatima yace da ita komai a kan xuwansu hayi ba, and that's very bad, sauka yyi motar bayan yayi parking a waje ya shiga gidan nata, bayan sun gaisa ya sanar mata jiddah ce bata ji dadi ba amma idan taji dama ko xuwa la'asar ne sai su fito su je can din, Hajiya Fatima tace "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, kun je asibiti kuwa?" Yace "Cousin dina ya xo ya dubata kuma ya bata magunguna" Tace "Toh Alhmdlh, duk sanda taji saukin sai muje babu damuwa, kila xuwa magrib ma in shigo in dubata, Allah ya bata lafiya" Yace "Ameen na gode Mama, Allah ya kai mu" da haka yayi mata sallama ya fita gidan, motarsa ya shiga mai gadi ya bude masa gate ya shiga ciki yayi parking sannan ya sauka ya dau warmers din abincin ya wuce ciki, mamaki ne ya cikasa jin kamshi me dadi na turaren wuta dake tashi a each and every angle of the parlor, ya dinga bin parlon da kallo don an goge ko ina, murmushi yayi ya karasa tsakar parlon ya ajiye warmer din abincin ya haura sama, dakinta ya fara shiga nan ma dai sai kamshi yake tayi tidying ko ina, ya kullo kofar a hankali ya tafi nasa bangaren, lumshe ido yayi ya bude don kamshi ne ya hadu da sanyin ac, daga bedroom din har parlor nasa, yaushe rabo? Murmushi yayi ya juya ya koma downstairs ya shiga kitchen, ta gama wanke wanke tana goge wajen gas ta juya tana kallonsa, English dressing tayi ta daure dogon gashinta da ribbon, ko hulan ma bata sa ba, wanda ko tayi irin dressing din a gidan Umma sai ta sa hijab duk da isu isu ne a gidan, yau kuma kam bata sa hijab din ba, sunkuyar da kanta tayi tace "Sannu da xuwa" Ya shiga kitchen din giving her a hug from d back ya lumshe ido fuskarsa a kan gashinta yayi kasa da murya yace "Duk ke da baki da lafiya kika gyara gidan nan haka Babyna??" Ta rufe idonta a hankali tace "Na ji sauki" Rasa abinda xai ce mata yayi, yana jin sonta a ko da yaushe na komawa sabo a xuciyarsa, anya Jiddah xata bari yayi concentrating a aikinsa kuwa? Anya xai iya tsayawa without her close to him for good 5 days kuwa, da kansa ya ba ma kansa amsa da No a xuciyarsa, juyowa yaga tayi a hankali ta shige jikinsa tana boye fuskarta a kirjinsa, daga nan kuma labari ya canxa ma Abuturrab... Bayan la'asar yana dawowa daga mosque ya tafi bedroom dinsa, xaunawa yayi gefen Jiddah dake bacci yana jan dogon hancinta a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? hankali yana kallonta yace "Sallah plss" Ta bude idonta, ya dagota xaune yace "Kiyi sallah mu ci abinci" ta daure gashinta sannan ta sauka kan gadon ta tafi bandaki, ya mike ya sauka kasa. Da kansa ya dinga bata abincin tana jikinsa, idan ya bata sai shi ma ya ci, ya lura bata son cin abinci da yawa don sai lallabata yake tana ci da kyar, hakan da take kuma narkar masa da xuciya yake, he just can't get enough of her love... Daga karshe ya rufe abincin don wannan abinda take ma ya sa yaji ya koshi kawai, ya manna mata kiss a forehead dinta underneath his breathe yace "Ina sonki matata" tashi tayi xaune daga jikinsa tayi kasa da murya a hankali tace "Ka gaya min sanda xan koma schl pls" Shiru yayi ya ki ce mata komai lkci daya kuma mood dinsa ya canxa, ya dau remote yana changing channel, kallonsa kawai Jiddah take jin ya ki cewa komai, yayi mata side hug yayi kasa da murya yace "What do u need apart from me again in this life Jiddah? Me xa ki yi da wani schl?" Ta gyara xama tana kallonsa da mamaki tace "You mean i won't go to schl again? Ko waec din ma fa ban yi ba" Ya rungumeta ya kai bakinsa kunnenta pleadingly yace "Pls ki cire wani schl a ranki, babu abinda xaki rasa a rayuwar nan ko bayan rai na my wife..." sai kuma yyi shiru, kankameta yayi yace "Gaskiya ina da kishi sosai, bana son a dinga kalle min mata anyhow, don haka baxa ki kara komawa wani schl ba..." Jiddah ta rasa ma me xata ce masa don she is a bit shock, ya girgixa kai yace "Ba ki ga ko farkon xamanki gidana ba naki sa ki schl duk da maganan su Umma, why because ina kishin matata... Ina da kishi sosai, fiye da yanda kike tunani Jiddah, ko me kike son koya ni xan koya maki a gida babu abinda xaki yi da wani kwali bayan mijinki na da rufin asirinsa, idan ma kince salary kike son in dinga baki wllh ni xan raba albashina biyu in dinga baki rabi duk wata, i think that's what we will do plss, idan kina son farin ciki na kada ki sake min maganan boko plss...." Hawaye ya gani a idonta, ya dinga kallonta, sai kuma ya jinginar da kansa da kujera yace "Shkkn ki shirya ki koma schl din" daga haka ya mike ya wuce sama ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta. Har aka kira magrib bai sauko ba ita ma bata je saman ba, mamaki kawai take wai baxata sake xuwa schl ba, da ta tuna wannan furucin nasa sai taji hawaye ya taho mata, saukowa yayi ya fita parlon without looking at her ta bi sa da kallo, da kyar ta iya tashi ta tafi dakinta ta je tayi alwala. Da kayan shayi Abuturrab ya dawo gidan duk da ba wai na gidan ya kare bane, ya kai su kitchen ya ajiye ya dawo parlor ya xauna, bai kai minti goma xaune ba aka danna bell, ya juya ya kalli kofar sannan ya mike ya karasa can, yana bude kofar ya ga Hajiya Fatima ce, murmushi yayi ya bata hanya yace "Sannu da xuwa mama" ta shigo parlon tace "Yauwa sannu Aliyu, ya mai jikin" yace "Alhmdlh, bari in kirata" Sama ya wuce, Hajiya Fatima ta xauna parlon tana yaba wannan turaren wuta me shegen dadin kamshi da aka sa a parlon a ranta, don ya kama ko ina and the scent is so heavenly, Abuturrab ya fara saukowa kasa sannan Jiddah, da murmushi ta xauna ta gaida Hajiya Fatima, Hajiya Fatima tace "Lafiya lau Jiddah, ya kika kara ji?" Ta sunkuyar da kanta tace "Na ji sauki Mama....." Hajiya Fatima tace "Toh Allah ya kara afuwa, dama daxu da ya shigo yace min baki ji dadi ba shine nace bari in leko in duba ki, kuma naga kam jiki Alhmdlh" Jiddah tace "Nagode mama Allah ya kara girma" Hajiya Fatima tace "Ameen, amma wannan turaren wutan naki a ina kika siya kuwa" Jiddah tayi murmushi tana jan fingers dinta tace "Umman mu ce tayi order wajen S.SQuare Collection" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah a wani kasuwan?" Jiddah tace "Aa a Gombe matar take, amma tana turawa ko ina" Hajiya fatima tace "Toh bani number ta, na jima ina neman turare me kyau haka ban samu ba sai dai a cinye maka kudi kawai" Jiddah na murmushi tace "Xan tambayar maki Umma idan na amshi number sai in kawo maki gida, ni wayata ta fashe" Hajiya Fatima tace "Toh shkkn, ina saurare" Sallama tayi masu Abuturrab yace "In sha Allah gobe xa mu je can hayin Mama" Tace "Allah ya kai mu lfya" Har balcony suka rakata ta wuce, Abuturrab ya haura sama Jiddah ta bi sa da kallo. Washegari da yamma suka wajajen karfe biyar dau hanyar hayin rigasa a motar Abuturrab, Hajiya Fatima na xaune bayan motar, Jiddah kuma na xaune gaban motar, tunda suka kamo hanya take bacci heavily, lkci lkci Abuturrab dake hira da Hajiya Fatima yake kallonta a gefensa, bayan yayi parking kofar gidan Iyah Hajiya Fatima ta bude motar ta sauka, ya jawo Jiddah don motarsa tinted ce ta bude ido a firgice, da damuwa yace "Wani bacci ne wannan kike yi haka throughout Baby?" Ta langwabe masa a hankali tace "Kilan aikin da nayi ne ya sa na gaji sosai" Yace "Toh baxa ki sake wani aiki ba, beside the house is too big for you to clean all alone, xa mu samu house help ko da biyu ne, i don't want my wife to be stressing her self" Girgixa masa kai tayi da sauri tace "Aa ni bana son wasu house help, xan iya yi da kai na...." Xaro ido tayi tana bin anguwan da kallo tace "Lahh har mun kawo ashe" sai kuma ta kalli bayan motar tana xaro ido don gaba daya ta mance tare da Hajiya Fatima suke, sai taga bata motar, bude side dinta tayi ta xame hannunta daga nasa a hankali, ta sauka... shi ma ya sauka ya kulle motar suka shiga cikin gidan don tuni Hajiya Fatima ta shiga.




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Jiddah ta tafi kusa da Iya tana murmushi ta gaisheta, Iyah ta amsa tana washe baki tace "Sannunku da xuwa Jiddah..." Abuturrab ya xauna saman tabarman dake shimfide yace "Ina yini Baaba" Da fara'a tace "Lafiya lau Alhmdlh... Sannunku da xuwa" Hajiya Fatima tace "Ina saurarenki Mama" Iyah tace "Shine nace ko xa ku je wajen Jibirilun a gwada sa'a tunda Zulan tace babu tantama yasan inda take, mu dai nan yayi ta rantsewa bai san ina Hansai ta nufa ba... Zulai kam na can tana fama da kanta duk babu kafafuwan wai yanke su xa ayi, ita kanta Hansan ta gudu da dubu ashirin dinta tace min.. " Hajiya Fatima tace "Toh Allah ya kiyaye, mun gode kwarai mama Allah ya saka da alkhairi, yanxu wa xai kai mu can gidan wan nata?" Iyah ta kalli Jiddah tace "Ba kin san gidan Jibirilu ba?" Jiddah tace "Na sani" Hajiya Fatima tace "Au to shkkn, ashe ma ta san gidan" Abuturrab na kallon Iyah yace "Kiyi hakuri Baaba har yanxu ban kai ki can inda muke ba kamar yanda nayi alkawari, in sha Allah xan sa lkci in xo in dauke ki, ina sane, yanayin aikina ne ya sa bana samun lkci" Iyah tace "Allah ubangiji ya dafa maka, babu komai wllh, ai ka gama mana komai tunda ka rike Jiddah da amana, Allah ya saka maka da alkhairi ya dafa maka a lamuranka" Yace "Ameen nagode" Dubu goma ya ajiye mata, ta dinga godiya kamar xata ari baki, ta rakosu har bakin mota tana daga masu hannu har suka bar layin, tana murmushi tace "Allah sarki Isuhu, kyawun halinka kadai ma ya ishi a rike maka er ka da amana har abada kuwa" Parking Abuturrab yayi kofar d'an kuturun gidan Kawu Jibiril, Hajiya Fatima da Jiddah na tsaye daga gefe Abuturrab yayi sallama bakin kofar Zauren, Wata yarinya ce da baxata wuce Jiddah ba ta leko tana tambayar waye, kallon Jiddah ta dinga yi irin kallon sani, Hajiya Fatima tace "Babanki fa?" Tace "Baya nan, Hajiya Fatima tace "Yaushe xai dawo?" Tace "Ya tafi kauye duba gonarsa" Hajiya Fatima tace "Mamarki fa?" Tace "Tana ciki" Hajiya Fatima tace "Kice ana sallama da ita" Juyawa tayi ta koma ciki, sai ga ta sun dawo da uwarta, Lantana na gyara daurin kirjinta a d'an tsorace tace "Lafiya wa ku ke nema?" Hajiya Fatima na murmushi tace "Maganar ba ta tsayuwa bace, kar ki wani damu alkhairi ne ya kawo mu" Lantana ta hangame baki tana kallon Jiddah tace "Wacece wannan kamar Jiddar Hansai?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Hajiya Fatima tace "Ita ce" wani salati lantana ta rafka tace "Ku shigo ku shigo, tsakar gidan ne dai babu shara, Bismillan ku" Da sauri ta koma ciki ta fito da wani bak'in tabarma ta shimfida masu, tana yi tana kallon Jiddah har sannan ta kasa rufe bakinta, Jiddah ce ta fara xama tace "Ina yini Maman Jummai" Lantana ta kasa amsawa sbda mamaki tace "Yanxu Jiddah kece kika dawo haka kamar wata er sarki?? Allah mai iko" Hajiya Fatima ta xauna kusa da Jiddah tana bin tsakar gidan da kallo, Abuturrab kuma ya ki xama saman tabarman, Hajiya Fatima na kallon Lantana tace "Mun wuni lafiya?" Da sauri Lantana ta xube kasa ta fara jero masu gaisuwa, Hajiya Fatima tace "Alhmdlh, fatan mun sameku lafiya" Lantana tace "Lafiya lau wllh, Wai yanxu Jiddah ce haka Jama'a" sai kuma ta rike kai tace "A gaskiya wanda bai ji tsoron Allah ba yayi asara a rayuwar nan" Jiddah dai kanta na kasa, Hajiya Fatima tace "Yau dai shine nace bari mu shirya ta xo ta gaida Baabarta, sai kuma da muka je anguwan muka samu labarin ai ta tashi gidan" Lantana ta rike ha6a tace "Cabdi, wannan ai tsohon xance ne, tun yaushe en lapun suka xo suka siyar da gidan suka cire kudinsu suka bata sauran canjinta, ai ko dai Hansai bata Hayi yanxu, bashin da ke kanta na jama'a ya fi dubu dari biyu.... Nemanta ake ido rufe" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah, to yanxu ina ta koma?" Lantana ta dinga bin su da kallo daddaya da daddaya, Hajiya Fatima tace "Kar ki ji komai wllh, mu alkhairi ne ya kawo mu ba sharri ba, mun xo sada xumunci ne kawai, idan da wani taimakon da xa mu yi kuma sai mu yi..." Lantana tayi kasa da murya tace "Sai dai in kai ku a boye mu dawo a boye don ban ma son mai gidana ya sani, abun sirri ne, sannan Hansai dai bara take a Kana rad, er ta kuma fama take da cutan xamani, shegun da ta haifa ma Allah yayi masu rasuwa, kun san yan biyu ne, to ance dai cutar ce ta kashesu satinsu 3 a duniya, ni ko yaran ban gani ba don ba a hayi ta haihu ba, Iliya ne dai yayi mata cikin ya goga mata kanjamau" Hajiya Fatima ta bude jakarta da sauri ta fiddo en dari biyar biyar tace "Mun kuwa gode wllh, ki kai mu ko da taimakon da xa mu iya mata..." Ajiye mata kudin tayi a gabanta, Lantana ta mike da sauri tana kallon kudin tace "Bari in saka riga, Allah ya so mai gidan nawa baya nan, ina nuna maku inda ta koma xan juyo ni kuma" Da sauri ta shiga ciki sai ga ta ta fito sanye da riga ta yafa mayafi tace "Ku taso mu yi maxa kafin magariba yayi" shi dai Abuturrab sai kallon Jiddah da ta jingina da bango idonta a lumshe yake, Hajiya Fatima ta mike without noticing baccin da jiddah take, Xagawa yayi ya d'an ta6a shoulder dinta ta bude ido da sauri sai kuma ta mike tsaye ganin su Hajiya Fatima sun nufi xaure da Lantana, yayi kasa da murya yace "Baby are you okay?" Ta langwabe tace "Bacci nake ji" Kama hannunta yayi ta xame a hankali suka fita daga gidan... Can cikin Kabala lantana ta kai su, Abuturrab ba abinda ya damesa sai irin portholes da ya dinga shiga da motarsa a anguwan, parking yyi dai dai inda lantana ta nuna masa yana kallon gidan, wanda gidansu na hayi ya fi sa mutunci da daraja sau 100, Hajiya Fatima ta sauka motar Lantana ma ta sauka

109 / 117