Jeeddahtulkhair Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   116 / 117

345K to 348K   out of 348.6K words

ganin sun nufi mota ta mike a hankali ta nufesu, da farko Abuturrab bai ma ganeta ba sai da ya sake kallonta da kyau, ta dan yi murmushi tace "Good evening captain" Sosai gaban Jiddah ya fadi ta juya tana kallonta, yana bude ma Jiddah back seat yace "Evening Aneesah how are you doing, longest time" Tace "Alhmdlh" Jiddah ta shiga motar Aneesah na kallonta tace "Kwana da yawa Hajiya Jiddah" Jiddah tace "Alhmdlh" Rufe motar Abuturrab tayi dai sai kallonsu take ta cikin glass, ya bude driver seat yace "Toh ya aka yi Aneesah?" Tace "No dama gaisuwa ne" Yace "Toh nagode, baki da lafiya ne kika xo ganin likita?" Tace "Ehh" Hannu ya sa a aljihu ya ciro kudi masu yawa yace "Ohk take this little token" Ta dinga kallon kudin amma ta ki amsa, sai ta daga kai ta kallesa hawaye cike idonta tace "I just want to ask u for forgiveness..." Yace "Nahh I've done that long ago Aneesah, na yafe maki wholeheartedly, me yake damun ki kika xo gun likita?" Tace "Xaxxabi nake" Yace "Toh Allah ya sauwake... Allah ya kara lafiya, i need to leave now" Kai kawai ta gyada masa ya bude front seat ya shiga ya tada motar suka bar asibitin ta madubi yake kallon Jiddah ya ga yanda ta wani hade rai, yayi kasa da murya yace "Baby" ko kallonsa bata yi ba ta kauda kanta.



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
=?G? 08052466875 via WhatsApp


Jiddah ce xaune dakin bak'i tana yanka fruit din kankana a tray, xaune daga gefe daya kan darduma Hansai ce, Hansai tace "Ina ta son xan maki wata magana Jiddah" Jiddah ta daga kai ta kalleta ta dau tray din watermelon din ta ajiye a gabanta tace "Ina ji Baabarmu" Hansai tayi kasa da murya tace "Shekarun baya da dadewa akwai wata aminiyar mahaifiyarki ana ce mata Sadiya, baabarki tace min tun bata yi aure ba take tare da Sadiya hasalima Uwar sadiya ta san kakarki sosai ina jin kamar sun ma yi kawance, to a da dai Sadiya ta auri wani me rufin asiri a unguwan sanusi, don lkcn da Mahaifiyarki ma ta rasu wllh xuwan Sadiya uku tana son xata daukeki ta rike ki amma duk na hana, a xuwan karshe ma ba ta dadin rai ta bar gidana ba, nace kada ta sake dawo min gida, to wannan dalili ne yasa har yau bata sake waiwayo inda muke ba, to a lkcn har gidanta na sani a can unguwan sanusi don mun je sau uku da Baabarki a lkcn da take da rai, yanxu dai ban san ko tana nan har yanxu ba, ni nasan ko kadan ne Sadiya baxata rasa sanin wani abu a kan mahaifiyarki ko kakarki ba, xai iya yiwuwa ita Baabar sadiya sun ta6a wani hira da kakarki ta fada mata wani abun game da asalinku, shine nace kiyi ma mijin ki magana ko xa mu je gidan Sadiya idan yaga da halin yin hakan" Jiddah dake ta sauraronta tace "Toh Baabarmu xan masa magana in sha Allah" Hansai tace "Toh maa sha Allah...." Xaunawa Jiddah tayi don dama a durkushe take a dakin, Hansai tace "Aa tashi ki tafi gun mijinki ai dare yayi kuma haka" Jiddah tace "Xan jira idan kin gama in kai tray din kitchen" Hansai tace "Xan kai da kaina, ki tashi ki tafi sai da safe" Jiddah tayi mata sai da safe sannan ta mike ta fita... Xaune ta tarda Abuturrab yana operating laptop Little Jiddah na jikinsa tayi bacci, Ta cire Hijab din jikinta ta linke don dama tayi shirin bacci, ta xauna gefensa ta jinginar da kanta da shoulder dinsa tace "Dee" Jawota yyi jikinsa yace "Baby kina stressing kanki da yawa fa, u need housemaid seriously, kullum cikin gyara gidan nn kike ba dare ba rana" Tayi murmushi tace "Sai kace wani aikin duniya?" Kashe laptop din yayi ya kwantar da little Jiddah, ya jawota jikinsa yana kissing lips dinta, bata yi sanya wajen biye masa ba.... bayan an idar da sallan Asuba ya dawo masallaci ta basa d'an labarin da Hansai ta bata, ya d'an yi shiru sai kuma yace "Alright in the evening sai mu tafi tunda tace ta san gidan" Jiddah tace "Allah ya kai mu" A hanxarce Jiddah ta gama wanke few plates da aka 6ata a kitchen ta goge ko ina sannan ta fito tana kallon agogo, Abuturrab na xaune parlorn yana kallon wrestling ta nufesa ta xauna kusa da shi tace "Dee baka kira ayi fill din gas din ba till now" Ya jawota jikinsa yana kallon agogo yace "Sai mun dawo Baby, hope u are done now?" Tace "Eh na gama, ince ta sauko??" Yayi kissing din lips dinta yana murxa hannunta yace "Yeahh Baby" Mikewa tayi ta wuce sama, bude dakin da Hansai take tayi ta shiga ciki, Hansai na xaune kan carpet da Little Jiddah tana daure mata dogon gashinta da colorful ribbons, babu abinda wannan yarinyar ta mance bata dauka ba na ubanta, ko kadan bata kama da Jiddah ta ko ina sai ta beauty point da haskenta da ta dauko... Kyakkyawa ce yarinyar ta karshe, kamar er india, Tana ganin Jiddah ta 6ata fuska xata yi kuka, Hansai tace "Lah ji min yarinya wai ta 6ata fuska daga ganinki, lafiya fa nayi mata wanka na shiryata babu ko tari" Dariya Jiddah tayi tace "Baabarmu wai ki sakko mun gama" Hansai tace "Toh gani nan fitowa, dauketa ku tafi sai ki karasa daure mata gashin tunda ta fara haka baxata yarda ba kuma" Jiddah ta karasa ta dau daughtern nata ta fita daga dakin, dakinta ta fara shiga ta dauko Veil dinta da handbag sannan ta sauka kasa, Little Jiddah na ganin Abuturrab ta fara mika masa hannu tana masa dariya, she looks so happy seeing him, mikewa yayi ya amsheta yayi kissing Cheek dinta affectionately yace "I love u cute Mamina" rungumesa yarinyar da bata wuce shekara daya da wata bakwai ba tayi, Abuturrab ya mika ma Jiddah dake kokarin yafa veil dinta car key yana kallonta, ta xumburo baki tace "Aa ni baxan iya ba, kullum sai ka dinga min wayo kana bari na da tuki" murmushi yayi yace "Toh amshi er ki sai inyi driving din" Little Jiddah ta makalkalesa xata yi kuka, Jiddah ta rike ha6a tace "Dama idan xai koma aiki sai dai ya tafi da ke, baxai bar min ke ba..." Dariya Abuturrab yayi yace "Salon kiyi kuka idan na tafi da ita" Yana fadin haka ya jawota yayi mata side hug yace "Na lura kishi kike yi da Ummi na fa" Jiddah tace "Toh ba gashi baka da time dina yanxu ba sai dai nata" A tare suka fita parlon yana cewa "Ni ko nake da time dinki, during d day dama time din Mami ne, ke kuma throughout the night time dinki ne kinga equation balanced" Jiddah tayi murmushi kawai ta amshi car key din a hannunsa, Hansai ce ta fito daga parlor ganin makulli jikin kofa ta kulle sannan ta cire makullin ta nufi motar ita ma, duk da ba da sanda take tafiya ba amma har lkcn bata tafiya dai dai... Abuturrab na kallon Hansai ta madubi yace "Wani anguwan ma kika ce?" Hansai tace "Unguwan Sanusi" Suna isa gidan luckily har lkcn Sadiya bata tashi ba don gidan mijin nata ne, wanda shi ma ya rasu ya bar mata 'ya ya, duk da Sadiya bata ganesu ba, haka ta shimfida masu tabarma a tsakar gida tana bin su da kallo tace "Sannunku da xuwa" Hansai na murmushi tace "Hansai ce fa Sadiya naga kamar baki gane ni ba" Sadiya tayi shiru tana kallon Hansai, sai kuma ta mike da sauri tace "Hansan Amina?" Hansai na murmushin karfin hali tace "Ni ce Sadiya, kinga ga Jiddah nan" Sadiya ta saki wani salati tace "Jiddah er wajen Marigayiya Amina?" Sai kuma ta fashe da kuka ta dago Jiddah ta rungumeta tace "Allah sarki rayuwa, sannunku da xuwa Jiddah, ashe da rabon xamu sake ganawa Hansai, sannunku da xuwa, Allah sarki rayuwa" Hansai dai sai kirkiro murmushi take, Sadiya tace "Toh ina bibalo?" A hankali Hansai tace "Allah yayi mata rasuwa" Sadiya ta saki salati ta nemi waje ta xauna tace "Yaushe ni Halima?" Hansai tace "Yau kusan shekara uku kenan da rasuwanta" Sadiya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya gafarta mata Hansai, Allah ya ji kanta, wayyo rayuwa" Hansai dai ta sunkuyar da kanta, Sadiya tayi tagumi tana jimamin mutuwan Bibalo, Hansai ta dago tace "Dama mun xo gunki ne Sadiya tare da fatan Allah dai ya sa kinsan wani abu game da kakar Jiddah da mahaifiyarta" Sadiya tayi shiru, sai kuma tace "Toh, amma dai duk abinda ni na sani baxai kai wanda mahaifiyata ta sani ba, idan kun ga babu damuwa to mu tashi mu tafi gidan Mamanmu yanxu, tana nan anguwan ita ma" Hansai tace "Wannan ba damuwa bane" Fita suka yi gidan gaba daya suka shiga motar Abuturrab, Abuturrab ya gaida Sadiya dake gaishesa a back seat sannan ya nufi hanyar da tace masa ya bi, bai yi niyyar shiga gidan ba amma haka Sadiya ta matsa ya shiga ayi komai a gabansa kawai, babu yanda ya iya haka ya sauka ya kulle motar yana rungume da little Jiddah, duk da ba wani tsufa mahaifiyar Sadiya tayi ba amma yanayi na rashi da halin rayuwa ya sa duk ta wani yakune kamar warce ta shekara tamanin a duniya, bayan sun gaisa Sadiya ta gaya ma mahaifiyar tata abinda ke tafe da su, Mahaifiyarta ta dinga kallon Jiddah tace "Yanxu kuna nufin jikar Maijiddah ce wannan Sadiya?" Sadiya tace "Ita ce Inna" Inna ta girgixa kai tace "Allah me iko, ikon Allah ya fi gaban haka, Allah sarki rayuwa, Allah ya gafarta ma maijidda, Allah ya Rahama mata, Allah ya raya xuri'ar da ta bari" Duk suka amsa da Ameen, kamar yanda Hansai ta sanar ma Sadiya abinda ke tafe da su a can gidanta haka ta sanar ma Mahaifiyarta abinda ya kawo su, Inna tayi shiru sai kuma a hankali tace "Toh, ita dai Maijiddah nasanta a lkcn tana aikatau a gidan Alhaji Labaran, tace min asalinsu yan kasar Nijar ne, amma bata ce min ga garinsu a Nijar ba gaskiya, ni kuma bata ta6a ce min ai ga abinda ya kawo ita da er ta Amina Nigeria ba, sai amsa daya da ta bani a lkcn da nayi mata tambayar, tace min ita kawai tana son nisa da yan uwanta da garinsu ne ta rike er ta har Allah ya raya mata ita, wato Amina kenan, ko a lkcn da kudinsu na Nijar da yawa a jikinta tayi ta ajiya bata komai da su wllh, ni idan ban manta ba har zinarai maijidda na da su a jaka, ni kuma ban gaya maku dalilin haduwarmu da kawancen mu ba, to a lkcn nima ina aikatau a gidan aminin shi Alhaji Labaran din wato Alhaji Sama'ila, don haka wani lkcn na kan yi ma matarsa Hajiya Kande rakiya xuwa wajen matar Labaran ita kuma ana ce mata Hajiya Bilki, to kun ji dalilin sabawar da muka yi da Maijidda kenan har muka dawo kamar yan uwa, ni kuma a lkcn aurena ne ya mutu, mata me kirki da gaskiya da amana, wnn dalili yasa Hajiya Bilki ta rike ta da kyau, don su suka aurar mata da er ta Amina ga Isuhu, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a gidan kuma Allah yayi mata rasuwa don tana ta ciwon da ba a san daga ina ba, sun kashe mata kudin asibiti bayin Allahn nn ba na wasa ba, amma har ta koma ga mahaliccinta ba a gano kan ciwon nata ba, Allah sarki yanxu xancen da nake maku daga matar har mijin babu su suma duk sun rasu, sai dai ya 'yansu da jikoki, basa ma garin kaduna ynxu gidan ma na samu labarin sun siyar, to ni shkkn iya abinda na sani a kan Maijidda kenan, er mutan Nijar ce dai" Hansai ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh mun gode sosai Inna, Allah ya saka da alkhairi" Tace "Allah ya maku albarka" Jiddah dai duk jikinta yayi sanyi sosai, Inna tace "Kawai ku je kuyi ta addu'a in da rabon Jiddah xata gana da dangin uwarta xata gana da su wataran, Allah kadae yasan dalilin da Maijidda ta baro kasarsu da yar ta da bata wuce shekara goma ba ta dawo Nigeria" Godiya Abuturrab ya kara yi ma Inna ya ciro dubu biyar ya ajiyeta mata, sannan suka bar gidan nata, bayan sun ajiye Sadiya a gidanta suka koma gida. Da daddare Jiddah na kwance jikin Abuturrab tayi lamo, tun bayan dawowarsu ya lura she is moody ya shafa fuskarta a hankali yace "Not again wife, akwai wani abu da kika nema kika rasa ne a rayuwa yanxu? U have ur fathers relative that are firmly there for u always, tunda gashi sun canxa min ra'ayi ba wai don na so ba, u will be starting ur higher institution next month in sha Allah, non of my penny was used, they paid for everything, isn't that for the sake of the love they have for u?" Kasa ce masa komai tayi wasu hawaye masu xafi na sauka idonta, ya rungumeta sosai yace "bana son haka Wife, kina daga min hankali sosai" Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" Yace "Definitely one day, one time, u will meet with ur Maternal relatives in sha Allah, xa mu tafi Umra soon sai ni dake muyi wannan addu'an a can, sai ki ga Allah ya amsa.... In sha Allah" Cikin sanyin murya tace "In sha Allah" Washegari Karfe goma saura Jiddah ta gama duk abinda take, bayan Hansai tayi breakfast ta shiga gidansu Hajiya Fatima, ita kuma Jiddah suka fita tare da Abuturrab, shi ke driving din, tana xaune front seat rike da Little Jiddah a kafarta, motoci ne sun kai biyar anyi parking kofar gidansu Abuturrab, Abuturrab ya nemi waje shi ma yayi parking ya sauka, Jiddah ma ta sauka, ya amshi little Jiddah a hannunta suka shiga cikin gidan, ganin guards din palace din bauchi ya gane uncle dinsa ma na gidan, Tun daga nesa yake kallon El-Basheer dake tsaye tare da Ahmad, ya karasa suka fara gaisawa da Ahmad sannan ya mika ma El-Basheer hannu yana kallonta, El-Basheer yace "And i am hoping u will be unblocking me this very moment" D'an murmushi kawai Abuturrab yayi yana patting shoulder dinsa yace "I neva did block you brother" Jiddah ta sunkuyar da kai ta gaishe su, El-Basheer na ganin little Jiddah ya wara ido yace "Waow, and at last, my wife is born..." Karasawa tayi ya amshi yarinyar a hannunta yace "Waoow she is so cute" Jiddah na kallon Ahmad tana murmushi tace "Aunty Ramlah fa yaya Ahmad?" Yace "Tana ciki" Juyawa tayi ta karasa cikin gidan, Maimoon ta taso da sauri ganin Jiddah ta rungumeta cike da murnan ganinta tace "Mrs Aliyu" Jiddah na murmushi tace "Mrs Yusuf" Dariya kawai Maimoon tayi, Jiddah ta janye jikinta ganin su Ummi a parlon tace "Bari in gaida su Ummi" xaunawa kasa tayi gefen Ummi ta gaisheta, Ummi ta amsa da fara'a, ta mike ta tafi kusa da Umma tana jin kamar ta rungumeta tana murmushi tana kallonta tace "Umma ina yini" Umma tace "Lafiya lau Daughter, ina Ummin?" Tace "Tana wajen yaya Bashir" Ramlah dake xaune ta daga ma Jiddah hannu tana murmushi, Jiddah ta daga mata hannun ita ma smiling at her, gaida few visitors dake parlon tayi, sai ga Hajja ta fito daga dakinta sanye da kaya na alfarma ta sha gwal a wuya da kunne tana taku dai dai, Akwatunanta uku fal da kaya ana biye da ita da shi.. Wai ashe Masar Hajja xata koma shine yan rakiya xuwa airport suka cika gidan Alhaji Usman, yan kano ne, yan Bauchi ne, har ma da yan zaria, Umma na murmushi tace "Hajja kuma sai Masar" Hajja na daga shoulders ta nufi kofa tana cewa "A bi min akwatuna a hankali kar su yi ko kwarzane a cuce ni, mu a Masar a nutse ake jan akwati" Dariya Maimoon ta dinga yi har da saukowa daga kan dining, Ummi ta mike da su Umma suka bi bayan Hajja suna murmushi, Abba da Mai martaba da sauran brothers dinsu duk suka fito compound jin Hajja ta fito bayan awa daya da ta dauka tana shiri a dakinta, kace wani karamin biki ake yi a compound din gidan saboda mutane, a haka duk suka nufi airport don a private jet xa a kai ta kano sannan ta hau jirgi xuwa Masar..... Waige waige ta dinga yi a airport tana neman Jiddah tana ganinta ta yafito ta, Jiddah ta nufeta Hajja ta jawota kusa da ita tace "Toh Allah ya kaddara saduwan mu Jiddah ni xan koma Masar kuma ban jin xan sake dawowa kasar nan" A hankali Jiddah tace "Aa xaki dawo Hajja" Hajja ta girgixa kai tana kyabe baki tace "Lala, abubuwan kasan nan duk ba tsari, toh me xan dawo yi?? ni dai ina 'ya ta ta ke?" Jiddah tace "Tana hannun Yaya Bashir" Hajja ta d'an waiwaiga ta tabbatar babu idon kowa a kansu ta kamo hannun Jiddah ta saka mata gold na dankunne tace "Gashi ki ajiye ma 'ya ta, tana shekara biyu cif cif ki saka mata kuma kada kice ma ko wani shege ni na bata balle a kullaceni suce ban ba ma yaransu ba to me na hada da su? ko shi gantallalen Aliyun kar ki gaya masa don babu abinda na hada da shi ma din" Rungumeta Jiddah tayi cikin sanyi tace "Mun gode Hajja Allah ya kara girma, Allah ya kai ki lafiya, in Allah ya yarda mu ma muna nan

116 / 117