Kuka nake sosai Allah sarki Ya tafi yabarni da marayu.
Ganin ɗago kaina nayi naga yanda Nurse ɗin take wani dangware min yara, kamar ranta a ɓace yake dan an tasota ta gyara musu jiki. Basan lokacin da nace.
"Keeee ki bi min yara a hankali idan bazaki gyara su ba, ki bar min su kifita ki kara min Mamana a waje, banza dake kina dungure min yara dan baki da imani, sake min yarana kifita."
Masifa yasa wacce take kula dani tashiga bani hakuri ni kuma nace tabar min yarana dole aks kira Babbansu, ita tazo ta amshi aikin wancar kuma aka ce tafita zasu ji da ita.
Ajiyar xuciya na sauke, lokacin da aka miko min Hassan, karɓanshi nayi na kifashi a kirjina, sannan na amshi hussain na kifashi akan cikina, ina jin sautin bugun zuciyarsu da yar kiriniyar da suke irinta niman abinci.
D'aga Hassana nayi nace.
"Barka da zuwa Mai Nasarama ka dawo min ko."
Ajiyeshi nayi bayan na sumbaci goshinsa. Na ɗaga Hussain nace.
"My Sameer kaima kadawo min ina sonku dayawa sosai ynz zamu cigaba da hiranmu tunda kunzo duniya zan nuna muku hoton daddynku, da Aunty Huda da Aunty Mufeedah da kakaninku."..
Kasake Nurse ɗin sukayi suna mamakina, karɓan yaran sukayi aka sakasu a wani gadon ni kuma aka bani kayana na sauya min wani gadon suka taimaka min na hau aka fita dani.
Ga yarana a gefena, idanuna na cigaba da zubda kwallar kewar mahaifinsu, farin cikin da Mama tashiga ba'a magana zatq kira malam sai gasu tare da Umma, ɗakin da aka kaini suka nufa.
Gyara min kwanciya nurse ɗin sukayi tare da saka min yarana a gadon yara da aka tanadar,
Kallona Umma tayi, tana murmushi, shafa kaina tayi, tace.
"Masha Allah, Uwata har yara biyu."
Daukar ɗaya Mama tayi Malam ya ɗauki ɗaya addu'a suka musu, sannan aka ajiyesu Malam yace.
"Mata nayi ko abokaine?"
Kauda kaina nayi tare da fashewa da kuka, nace.
"Malam Yunus ne da Muh'd, ku gafarceni da rashin ɗa'ar da na muku bani da zaɓine shi yasa har naji na kirasu haka."
Murmushi Malam yayi sannan yace.
"Toh Madalla aikinyi dai dai, uwata amma kafin nan zanbi kasuwa na sayo bulala sabida sun gajiyar min da uwata, kinga yands kika koma kuwa."
Kin juyawa nayi ina dariya, sabida soyayyar da nagani a idanun iyayena suka farawa yarana yasani jin kwarin gwiwa..
Barcine yayi gaba dani......
........"Ai nasan baka mutu ba kana raye kazo ka amshi yaranka..."
Kuyi maneji, saura kirsss.
Akwai uzurin da ya kutso min Insha Allah an kusa zuwa Iyaka nagode.
[4/3, 7:56 PM] Addah Ramlah: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂
*BOOK 2👈*
Page....10
Cikin kuka nake mika mishi yaran, amma ya gaza amsa sabida mawuyacin halin da yake ciki.
Ajiyesu nayi na isa gareshi na zuɓe a jikinshi nace.
"Yunus Yaranka ne fa, kazo ka amshesu."
Kallon yayi cikin tsananin azabtuwa yace.
"Ban chanchanci zama mahaifinsu ba, sabida ɓarnan da nayi Maryam. Hakkinki yaki barina gashi an mana katanga a tsakaninmu, ki rike min amanar kanki da Yarana, karki...."
Rike shi nayi sakamakon ganin ana janshi ina ihu. " kusake min Mijina....."
Jin ana danne ni yasani buɗe idanuna ashe tun fara mafarkin aka kira likita, mikewa zanyi suka tsira min alluran barci tuni na koma sabida karfinshi.
Karfe uku na farka naga ɗakin ya cika da mutane, dafe goshina nayi ina kallonsu. Hajiyarsu Daddy tace.
"Sannu Maryam, Barka da arziki Allah yabaki lafiya, su kuma ya rayasu tafarkin Sunnah."
Lumshe idanuna nayi na kalli Mama Amarya nace.
"Mama ina son gyara jikina."
Ita da Aunty Hamdiya suka zo kaina, ɗagani sukayi Mama ta samin Hijab, na sauka a hankali a jingina nayi da jikin Aunty Hamdiya, ta rungume ni sosai muka shige ban ɗakin. Kafin su fito Rahimah ta cire zanin gadon ta shimfiɗa wanda Umma tabawa Matar Yayanmu.
Dake Asibitin na kuɗine har da room heater, ruwan wanka Mama ta haɗa min nayi da kaina, kallona tayi cikin tausayawa tace.
"An miki ɗinki ne."
"A'a"
Fita tayi bayan tace na shiga cikin ruwan idan nagama. Watsa ruwan yayi min daɗi nusaman da na shiga ciki, saka kunne nayi naji yaran na kuka, da sauri na watsa ruwan, riga da zanin da aka kawo min nasaka tare da hijab ɗina nafito.
Raba idanuna nake, ina kallon waye ke kuka a cikinsu.
" Zauna mana Maryam! Wannan mai gidan da alamu bazai iya azumi ba, dubi yanda yake niman abinci kamar wanda aka masa yasa a cikinshi."
Zama nayi bakin gado, Mama ta miko min katon Cup da Tea, kasa karɓa nayi sai da ta sake mika min na amsa zuciyata na gurin Yarona.
Kurɓa nayi naji yaron ya callara kara, irinta jarirai. Bansan lokacin da na haɗiye tea ɗinba har da kwarewana. Sannu suka min, burina su bani Yaran amma na lura bazasu bani ba,
Ni kuma kunya tasa naki kallon inda yaran suke, kaɗan nasha tea ɗin na ajiye filet ɗin farfesun kayan ciki Mama ta mika min kamar magani haka nake ci. Shima banci dayawa ba na ajiye.
Sai a lokacin Hajiyarshi ta mike ta kawo min Yaron da yake rigiman ta ɗaura min akan cinyata, kallonta nayi idanuna cike da kwalla nace.
"Hajiya ya zanyi dashi."
Murmushi tayi sannan ta gyara min rikon yaron tace.
"Yanzun ki ciro mamar ki bashi da bismillah."
Sake kallonta nayi zan tambayeta an musu huɗuba ne, tare da basu dabino.
"Ki shayar dasu an gama komi."
A hankali na mai dashi cikin hijab ɗina, na ciro nono ta kasar rigar jikina nasaka mishi a baki. Sai naji kunya ta kamani naki kallon kowa.
Kama nono da yaron yayi yasani cewa.
"Ya Salam."
Da ɗan karfi, sannu suka ce min. Tare da karfafa min gwiwa. Gaskiya shayarwan farko ba daɗi. Dariya Rahilah tai min tace.
"Sannu Uwar two, akwai zafi ko."
Tura baki nayi cikin rigima nace.
"Mama kinjita ko."
"Eh mana don Allah ki ɗaga hijab ɗin nan dan ba mamaki iska yaron yake ja,nd ki kalli yaronki for first time."
Inji Aunty Hamdiya dakyar na zare hijab ɗin, na kalle yanda yake tsotson nono. Haka kawai sai tausayinsu ya kamani, da kuma tuno mafarkina.
"Hajiya Daddy yana raye fa."
Shiru suka min tare da zuba min ido,
Ganin zasu maidani mahaukaciya nace musu.
"Yana raye bai mutu ba, wallahi da gaske nake faɗa muku, ku tsananta addu'a yana bukatar addu'armu."
"A ina kika ganshi?"
Muryan Sulaiman yayi min bazata,
Janyo hijab ɗina nayi na kalli cikin idanunshi nace.
"Mafarkinshi nayi, kuma jikina na bani yana raye."
"Ki daina damun kanki ki kula da Yaranki, har Allah ya kawo miki miji nagari, kiyi aure."
"Wannan kuma ai zance banzane babu auren da zanyi ina nan ina jiran mijina ko shekara dubu zaiyi zan jirashi, duk wanda zamana ya takura mishi sai yasan nayi dani Amma ni matar Yunus ne."
Ina gama faɗar haka na fashe da kuka. Mi yasa komi sai nice na rasa cikina a farko, Yanzun narasa mijina, "Ya Allah na tuba indan laifi nayi Ubangiji ka yafe min, ka sassauta min Ina son Uban Y'ayana"
Shiru ɗakin yayi aka rasa mai magani, jikin Sulaiman yayi matuƙar sanyi, fita yayi daga asibitin yana kalubalantar kanshi da rashin adalci.
Wani irin son kai da zuciya ne suka kaishi da aikata abinda bazai yafewa kanshi ba.
Kifa kanshi yayi da a cikin mota ya fashe da kuka, sosai dan yana hango. Rashin amincewa da buƙatarshi kawai yake,
Haka yayi kukan mai isarshi, ga wutar kaunarta dake kararu mishi zuciyarshi tare da shaiɗanin zuciyarshi dake bashi shawaran banza.
....... Bayan awa shida aka sallame mu, su hajiya suka koma zaria.
Tunda muka koma gida, Umma da kula da yaran Mama kuma dani, wanka sau biyu muke samu. Ga abinci mai kyau wanda sulaiman ya kawo ya jibge.
Ga hidimar da Fareeda take kullum tana hanya, itace kawai bana iya ɗaga ido na kalli yaran a hannunta, amma ko wanka umma ce ke musu wanka sai nace ummana abi a hankali kar su fasa auren.
Zan iya cewa wani mahaukacin son Yarana ya rufe min ido ko barshi nake naji ɗan kukansu a gigice nake farkawa. Sune abu mafiya soyuwa da nasamu bayan rasa mahaifinsu shi yasa ko tari sukayi bana iya hakuri akan haka.
Iyayena sun min uzuri basu taɓa jin zafina ba asalima sake koya min yanda zan kara son Yarana.
Duk wani al'adar bahaushe sai da Familyn Daddy sukayi min, abinda ya matuƙar sani zubda kwalla kenan domin ji nake ina da yana tare damu da munga zallar so da kulawa.
Haka zan zauna ina tausayin yarana, sabida bansan mi zance musu ba idan sun girma, ajiyar zuciya na sauke idan na tuna amsar a bayyane take.
Yan uwana sun zage sosai gurin hidimar suna, wanda baya cikin lissafina. Sai da Mams tayi min faɗa sannan na yarda aka wanke min kaina inda suka kawo kayan gyaran gashin har gida, ana jibi suna Aunty Asma'u tazo daga Abia.
Washi garin zuwanta suka shiga aiki dan buhu uku Ahmad ya kawo na fulawa da Mangyaɗa, da duk wani abin bukata na kayan suya, Aman kuwa ya ajiye mana kayan abincine suna, Alhajinsu Daddy Raguna biyu ya kawona sai gana Fareeda da akwatinta guda uku, tsabar sonkai nawa ne karami, duk sauran na yaran ne,
Ta ɓangaren Sulaiman kuwa duk abinda Uba yakeyi yayi mana, komi har pampers laida sha biyu ne, duk wannan hidimar da yake mana ni haushinsa nake ji, wallahi dan haka kawai zuciyata ke sani jin zafinshi. .
Balkisu akwatina biyu tayi mana.
Banda nasu Hajiya da kanen Yunus, da sauran dangi sai da Umma tayi ta faɗa, Yaseen ko a jikinsu.
Anzo za'a min lalle nace ni bana so, Rahilah tace.
"Baki isa ba Maryam wallahi sai anyi miki."
Dole suka min, aka zana min lalle ja da baki, ina gamawa na kalli yatsin hannuna, yarrrr naji tsigar jikina ya mike.
"Yunus"
Zuba min ido sukayi dan bani mantawa ranar da nayi lalle ja a hannu, kamar ya cinye hannun tsabar abinsun mishi. Kuka nasa musu sosai.
Sam yanzun bani da juriya da hakuri dan na lura kamar Yunus ya tafi min dasune, yabar fanko mara juriya.
......Ranar suna anyi hidima sosai wanda sai da akayi da gaske dani na iya sake jikina, yan zaria kuwa kamar su ɗauke Hassan da Hussain. Haka aka bar musu bayan hassan yaci sunan Yunus Hussain kuma Sameer.
Bayan an watse Yan uwana suka shiga duba kayan da aka mana, cike da mamaki. Suna faɗa min, murmushi nayi dan fitowana kenan daga wanka na samesu sun baza kayan.
"Yanda ya tafi da fatan nasake samun wani cikin da yana nan, ai wannan wasane dan nafi kowa sanin waye Yunus ko Matanshi da nasamu basu sanshi kamar yanda nasanshi ba."
Duka Rahilah ta kaimin cikin tsokana tace.
"Yarinya taji Yaren novel,"
Tsaki na mata, dan nasan fassarani tayi ta other sider.
.....Haka suka gama ganin kayan, har kowacce mijinta yazo ya ɗauketa.
****
A hankali komi yake tafiya, musaman kwanakinmu kafin kace mi har munyi arba'in. Shiryamu Umma tayi Yayanmu ya kaini na musu kwana biyu. Na dawo,
Al'amarin Ubangiji tare ds niman yardanshi Ummana tasani a gaba da addu'ar dangana da hakuri, dama niɗin ba ma'abociyar kwaranniya ba sai wani nutsuwa ya shigeni da kamala.
Gashi dai ban cika ashirin ba amma, nakoyi wani dattako a gurin Ummana, hakuri yayinda aka zaluncika. Shanye ɓacin rai yayinda aka zageka. Sadaukarwa ga abinda kafi so da bukata.
Jajjarcewa ga niman nasara a rayuwa, wanda haka ce ta faru dani, a cikin shekaru ɗaya da watani nake zaune a gida, dan yarana yanzun suke da shekaransu ɗaya kenan. Masha Allah gasu nan kaman wasu zakuna.
Ga kiriniya da kujiba kujiba,.
A yanzun da Yayanmu ya nima min, N.C E,
Dan shi nace zanyi dukda kowa bai so ba na zaɓi abuna haka dan bana son dogon karatu.
****
"Sun guy, kana nufin wani aikin ne ya faɗo daga sama."
"Zanci kaiii, kaji min shege. Kana wasa da Sunguy ne, nifa ba karamin kwaro bane, dan haka an bani turamol da Emzlin nasaka a jakar Yar gidan Minister tsaro zata tsallaka saudiya."
"Kutt nawa aka biyaka."
Mikewa yayi yace.
"Uwani bata ce jeka ka gani ba."
Tafiya yayi yabar abokin da cizon yatsa.
*****
A cikin yan kwanakin nan Sulaiman ya takura min, sosai dan sakonshi yafi sama da ɗari a wayata, gashi ya shigewa yan gidanmu alkhairi yake musu kamar wani sauna.
Ranar jumma'a na dawo daga makaranta naga baki a cikin falon baki dake kana iya hangosu ra glass ɗin window. Ga takalmansu a zube.
Shiga gida nayi na sami Umma na a ɗakinta zama nayi sai ga H² sun ɗibo jiki da tafiyarsu da bata wani kwari ba, suka zuɓe min a jiki.
"Wash mazaje zaku karyani, ku barni na huta mana."
Dariya Umma tayi mana, musaman yanda taga, Hussain yana tura baki alamun zai sha nono, tasan yanzun zan gudu. Dan yaran suna shan nono sosai ni kaina kamar zan faɗi idan suka zuke ni.
Bata gama dariya ba, na mike zubur ina dariya nace.
"Mazaje tsoro kuke bani, idan kuka fara shan nono baku tuna komi, sai shi. Yawwa ummana nags baki agidan nan lafiya dai ko?"
"Zauna Maryam muyi magana."
Zama nayi a gabanta ina kallonta dan naga babu wasa a fuskarta.
"Dama kakansu H² ne yazo nimawa kanin Yunus aurenki, sai Baban faruq da yazo niman gausiya ta kom.."
Mikewa nayi a kiɗime nace.
"Na shiga uku na lalace, Umma kuna kaunata kuwa, don Allah ku rufa min asiri wallahi bana son Sulaiman, Umma mijina yana raye."
Kuka na saka mata wanda yasa yaran firgita suka fashe da kuka suma,
Sosai nake yi nace.
"Umma ina zan kai Yaran nan, mi zan ce musu? Idan kuma babansu ya dawo a ce nayi hakuri dan na tara wasu Yaran ko Ya-ya kunga gawarshine? Babu wanda yake da yakinin ya mutu akan mi bazaku bani damar kaiwa shekaru huɗu ba."
"Bazamu baki ba, sabida bama kaunarki. Mahaifinshi yace a binneshi a inda ya mutu, wato har kin kai wacce zaki faɗa mana bama kaunarki toh mungode Allah ya shiryeki."
Tana gama faɗar haka ta barnin ɗakin tashin hankalin da na shiga ba iyaka, wani tausayin kaina nake ji,
Gashi abin an saka auren sati biyu, duk na gigice na fita hayyacina sai rama nake.
Aunty gausiya kuwa kanta rawa yake zata koma gidan mijinta.
Matar Sulaiman har sako take turo min na yanda zata wulakantani.
Zafi uku, ga tashin hankalin da nake ciki, ga fushin Umma wanda yake yawo a jinina, ga exam wanda bansan mi nake yi ba.
Nabi umma na bata hakuri taki, kulani sai ma zuba min idanun da tayi, a ɓangaren sulaiman kuwa ya haukace da murna dukda wannan bai taɓa zuwa ba. Sai sako
Ana bikin saura sati guda aka kawo kayan lefe, wanda kallo ɗaya zaka musu kasan aci kaniyar nera, ko kallo basu isheni ba.
.......
A yau kasar saudiya takama wata matashiya ɗauke da muyagun kwayoyi, yar Minister tsaron naija.
Abinda ya ɗauki hankalin ɗinbun alumma, inda akalar duniya ta juya alamarin.
Lokaci guda mahaifinta ya haukace har da yunkurin koran mutane da dama a cikin gidanshi.
Kafin a wani lokaci har an shiga tattaunawa tare da tsanananta bincike, tun daga fitar Yarinyar har zuwa airport.
A nan aka saka idanu akan Cctv nan suka, gano fuskar Sunboy. Da lokacin da ya fakaici jakanta yasaka mata kwayar.
Take akayi copy ɗin hotonshi aka mikawa sojoji da Yan sanda, tun daga abuja har zuwa sauran state ɗin.
Nan aka shiga muhawara, yanayin saka Kwayar irinta Yunus Marafa ne, mi yasa shi ba'yi magana ba kodan an taɓa Yar miniter ai shima mahaifinshi tsohon sakataren gwanatin tarayya ne.
A cikin awa goma sha ɗaya aka kamo Sun boy, wanda kafin akawo shi yaci mugun duka, sabida sojoji ne suka cafke shi a birnin gwari.
Tsabar yaji wahala tun kafin akaisu yace.
"Zan faɗa muku, Nuriya Kishiyar Mamanta ce ta bani kwayar nasaka mata."
Wani soja ya zabga mishi naushi yace.
"Ba yau kasaba ba, zaka faɗa waye da waye kasawa."
..........
Lokacin da Sulaiman Yaji labarin an kama sunboy, haɗa komi nashi yayi yabar garin Zaria baki ɗaya.