ɗan shekara ukune, da zaran ya tada rigimar shi, sai ki duba dabi'ar karamin yaro ki gani, da zaran ya fara kuka zan faɗi a kasa yayita shureshure, a lokacin zai baki haushi kaman ki jibgeshi amma idan kika tuna da, cewa kukanshi kara miki zafin kai zaiyi, niman alewa ko wani abu zaki fara dan kurabu lafiya,
Toh namiji ma haka shi bazai faɗi ba, amma zai koma gefe yayita huci idan kina da wayo, a lokacin sai ki saukar da kai ki bashi hakuri, idan kika ga yaki sa shi a gaba kita rarrashinsa, wanda idan kinga zaki iya saka mishi fitinanne kuka shi akawa laifin tuni zai manta da wani rigima ya sauko, toh a lokacin sai kiyi amfani da damar haka ki bashi hakuri dan zai damu shi akawa laifi ke kuma kike kuka, Mata muna da matsala a rayuwarmu sosai bazamu iya rarrashin miji ba amna zamu iya rarrashin mai saida ɗan kunne dan yayi mana sauki,, haba mata ina hikimar tamu take ina kwarewar tamu take, tunda Asiyah ta iya bawa fir'auna shawara ya ɗauka waye ne mijin naki da bazai ɗauka ba,
Ummu Salma an karɓo daga gare a hadisin da buhari da musulin suka rawaito.
Tace manzon Allah yana zama yayi shawari dasu, akan alamuran addini ko, kuma wani yaki, indai manzon Allah zaiyi shawara da matarshi ke wacece da bazaki bawa mijinki lokacinki ba, ina kira gareku mata yan boko karki cr aiki ya hanaki kula da miji, zakiyi kuka nan gaba idan ya auro undergrad, kina ji kina gani zai, mai dake gefe ya saka wancar a gabanshi idan bai yi haka ba toh yar aikin gidanki da kika bar mata gidan ita zai aura, idan mai tunani da tsoron Allah kenan idan kuma aka rasa haka, kina ji kina gani zai na bin yar aikinki suna masha'arsu, ko kuma yaje waje nima, wallahi muji tsoron Allah, wai tsabar rashin daraja a gurin mace mijinta zai raba gurin kwanciya da ita, sabida tanq wari da hamami, wai nikam mi kuke shirin zamane matan arewa, tun a gida zaki koya mata gyaran jiki girki tareraya, iya magana, sabida sha'anin rayuwa baki san inda xata zauna ba, amna ina sai dai ki koya mata shan maganin mata, can yayi kyau amma rayuwarta ba kyau, kwanakin baya naje kasuwar ganye sayar wani ganye da ake amfani dashi gurin taimakawa yaro sabida kurga, sai naga wasu yan mata guda biyu ɗaya take cewa.
"Ita tagaji dashan maganin mata, dan mijinta baya wani sonta sabida bata iya girki ba, inda take samun saukinshi sai gurin jima'i, Ya ilahi wai sabida mi bazamu koya musu girki ba, sai na kasa hakuri na mata magana harna gabatar mata kaina, take kunya ya kamata janta gefe nayi muka tattauna, nasata ta roki mijinta ya sakata a islamiyana, da kuma ajin Hajiya Falmata, na koyar da girki da gyaran jiki, hmm yau sai ga yarinyar da mijinta kafin nazo ɗin nak ta biya min Umrah, tana kuka tace.
"Malama a'a ke ba malama bace ke uwata ce kin bani farin ciki wanda uwar da ta haifeni bata bani ba, malama Mama, ga takardun zuwa umra na baki, zamu je ofishin Alhazai dake a karasa miki aikinki"
Na rasa mi zancewa yarinyar, bawai dan bantaɓa zuwa ɗakin Allah bane a'a sai dan gani nayi ɗan abu kalilan ya janyo min alkhairi, sai nakira mai gidan na faɗa mishi yace jeki na baki izini, Iyaye wallahi bama kyautawa itace tun yana ɗanye ake ɗan kwarashi, anan zan tsayq Amarya zakiya idan gidanki ya lalace babu ruwan Hajiya Iyami, da Hajiya Falmata da ni Hasinah sabida kina cikin ɗaliban Da'awa, idan gidanki yayi kyau abin alfaharinmu ne.
Da haka nake miki nasiha ki gyara rayuwar aurenki kija mijinki da danginshi a jiki wani sabon salo wai kuna kiran iyayen miji da ulcer ko hawan jini, a'a kuskure ne, ke zaki rushe dangantsrku ke zaki gini, ina da suruka, naki na saka ido akanta da mijinta, ina da yara mata baxan so nimaa cutar min dasu ba, akan Yan ukuna zan kwaɓe hijab da rigar malamta na gurzawa surukina rashin kirki, dan ni nasan abinda na bashi, idan yace min bata da kunya shi xan fara tuhumq kafin na tuhumeta, sabida karfe ɗaya baya amo sai da wani a kusa da shi,"
Daga nan ta,rufe da Addu'a, daɗin abinda tayi sai shi ana ta,tururuwan zama a kusada mu, kafin atashi mun zama celebritys.😂
Haka muka dawo daga gurin, nan umma tace zata koma kirikiri nace zan bita, nan suma rahila suka ce zasu bita, ai nan hajiya falmata tace.
"Yan uku ai zama zakuyi sai jibi zan mai daku."
A gaban mutane bai hanani saka kuka ba, tsakanina da Allah, haka kawai, za'a barmu a bakon guri Mama kilishi da tun dawowarmu take bina da ido murmushi tayi kafin tace.
"Malama anya Yan ukunku zasu zauna a gidajensu kuwa nan da kaduna suna kuka kaman yara, koda yake ai autotine."
"Eh hajiya Rukayya haka nake fama dasu ko gidan yayunsu basa zuwa hutu, idan basa gurina toh suna gurin Malama Atika, gwara ni ina gurxa musu faɗa, daga malam har malama babu ruwansu da faɗa, toh Hajiya ga Amanar yan ukuna, don Allah jibi su dawo da wuri sabida akwai islsmiyan safe kuma sune malaman."
Tana gama faɗar haka, ta mike haka muma muka mike, har gurin motar da zai maida ita gida muka je, muna share kwalla tsabar sakalci, ko irin ta kallemu dan matukar ta kallemu zamu iya karya mata zuciya, haka ta suka tafi muna, kallo sai kuka dariya Rahama tayi ta mana, tace.
"Kutt wallahi kun cika shagwaɓa, ina zaria ina kaduna, da kuke kuka."
Haka hajiya falmata tasamu a gaba muka koma cikin gida, a ɗakin yan matan duk mun taru mun cure, dakyar sukayi ta janmu har muka sake jikinmu....
.......
Da dare, ana ta shirin arabiya night amma banda mu, sabida dukkanmu muna jin kewar gida dakyar muka shirya da faɗar da hajiya Falmata tayi mana sannan ta ɗaura mana da rarrashi, Rahma tayi mana kwalliya dake ta iya, muka yafa abayarmu, su rahmah sun rigamu fita. Duk mutane sun tafi jin muryan Hajiya falmata yasa muka leka ɗakin da take, muka ce.
"Mun shirya Hajiya."
"Toh kuje Yayanku na waje ina zuwa." tace mana,
Muns fita Mahaifiyar Ahmad tace.
"Nifa zan zo kaduna, cikin sati me zuwa, duk yanda kikayi da ita ki faɗa min, babu wanda zaiki haɗs zuri'a da Malama Hasina, kiga irin shakuwar dake tsakaninta ds yaranta ki dube yaran mana da sauran yan matan ko iya kallonka basayi, tsabar tarbiya da Addini ya shige su."
"Toh ke hajiya firdausi, Ahmad ya nuna miki yana da bukatar aurene?" Inji Hajiya Iyami,
Dariya tayi sannan tace.
"Aini ce nake hanashi yanzun kuma nice zan sashi."
Haka sukayitq tattaunawarsu....
***
Muna fitowa muka sameshi sanye da jallaɓiya har da hirami, dake ango duk abokinsune, kafarshi ɗaya na ciki ɗaya na waje, ɗago kai yayi ya kallemu, sannnan ya janye idanunshi yace.
"Maryam Sajida keda Husaina kushiga baya Hassana ta shigo gaba."
Fuska yayi kaman bashi ba, shiga baya mukayi nida Rahimah Rahilah taja kafa zuwa gaban motar ta zauna, shiru motar yayi can ya juya ya kalleta a sace sannan yace.
"Mi ƴasa kika saka turare?"
D'ago kanta tayi kaman zata fasa ihu, sunkuyar da kanta tayi bata ce mishi kome ba, shiru ya biyo tsakaninsu nida Rahimah muna kallon abu, can yace.
"Ba tambayarki nayi ba? Ko kinfi son zuwa cikin maza kina kamshi, karshe duk inda kika ratsa duk wanda yaji kamshi alhakina kanki."
Cikin rawan murya tace.
"Wallahi an hanamu sakawa a gida kuma ka tamvayi su Maryam Sajida humra kaɗai muka shafa ko Rahimah."
Kukan da batayi ba sai gashi mu munayi, ɗaga wayarshi yayi yace.
"Mamie don Allah ki fito haka, kin haɗani da wasu babes sai kuka suke min, ni bazan iya ba."
Yana gama wayar ya kashe ciro tissue yayi ya mika mata ita kuma ta bamu, muna cikin haka Mamienshi tazo matsa mata mukayi ta zauna tace.
"Har ynz baku daina kukan ba?" shiru mukayi, ya tadda mota muna cikin tafiya yace.
"Mamie nawa kike saida Miski me kyau."
Satar kallon rahilah yayi wacce ta firgita, sai yanzun ta tuna da ta ɗiga a ruwanka tayi dashi, kallonshi tayi shi ma ita ya kalla ya sake mata murmushi, irin kin zata bansan turaren bane,
"Hmm waye zaka sayawa kasan hawa biyune akwai manyan kwallaba akwai kananun kwalla, sannan kalla biyu ne, akwai fake akwai original original ɗin ya kai, 200k kwalin kananun kwalin ba, babba kuma ya kai 450k, sai mai tsadar kwalin baya wucce 50k xuwa sama shine ake saida ko wani kwaya ɗaya 1k,"
"Mamie babu ragine, yaronki bayi da kuɗi fa," ya faɗa mata haka, dariya tayi sannan tace.
"Waima dan kaine zan dayar maka da tsada, idan wani ne da araha zan saya masa."
Shuwa ya juya mata, suka karasa maganar, suna isa gurin muka fita saka key yayi a gurin motar Rahilah, yana binta da wani irin kallo a hankali ya kai hannunshi zai buɗe, mata kofar ita kuma ta zata taɓata zaiyi aikuwa ta rufe idanunta gam, jikinta na rawa, dake akwai wadatacciyar haske wuta a gurin wayar shi ya ciro yayita ɗaukarta hoto, idanunta na rufe, buɗe kofar yayi yace.
"Kee barmin motana, kin wani rufe ido kamar nace zan miki wani abu wato ga dodo ko?"
Da sauri ta buɗe motar tayi ta inda taga munbi fita yayi yabi bayanta, after ya rufe motarshi, ganin irin saurin da take yasa shi kiranta.
"Keee Raheeelah."
Cak ta tsaya tare da dafe goshinta, yana isowa gurinta ya,zabga mata harara yace.
"Ina zaki haka? Kina tafi ba kintsi maza sai kallonki suke."
Juyawa tayi taga ta ina mazan suke, aikuwa ya cika fam yace.
"Karya nayi miki ko?"
Shiru tayi suka jera tare har cikin hall ɗin, take kallo ya koma kansu, kawota yayi har seatɗinmu...
"Ikon Allah Falmata kiga wani haɗin Allha, wallahi sun dace da Aman, za'a iya kiransu da ma'auratan shekara, kuma zai mori mace gata ɗanya ga kuruciya,"
"Kaiii Yabi har yanzun kina nan da Halinki," Inji wata a gurin, sai Murmushi Mamien shi take dokawa,
****
"Shegis ina kasamo ɗanyan haka jagwab, gaskiya mutumin ka kawo wuta." Inji Ahmad,
Mai nasara na gefensu bai ɗago ba balle yasan da wa suke,
"Hmmm! Ahmad kenan, dakyar Allah ya sake haɗamu da ita sati biyu da suka wucce sunzo gidanmu ni kuma naje, anan na tsnci dami akala, kuma hmm nasan zan durza amarci dan i can't wait, nasoma ji wai bata gama scndry ba, su bani ita zata gama a hannuna, kaii idan taji kayan aiki tuni zata mance.."
D'ago kanshi yayi cike da mamaki yasan Aman bai da irin wannan surutu.
"Hmm da fatan ba under 18 bace, dan naji yanda kake bayanin nan..."
"17+ ne, akwai matsala da haka ne, ?" ya jefawa mai nasara tambaya,
"Haba da matsala mana kaje ka nemi 21+ zaifi maka ina zaka kai kayan reno, kuma wallahi lalata mata kuruciya zakayi dan na lura babu so sha'awace ke damunka."
"Dakata malam wallahi ban ji sha'awarta ba, sau ɗaya na kalleta na mutu akanta, a cikin sati biyu, jal idan sha'awa nake ji ina da mata fa, kawai ko kai kasami ɗaya cikin yaran zaka fahimci me nake nufi yaran sun sha madaran tarbiya fiye da kima, wallahi duk damuwata da hindu bana jin sha'awar kusantar wata mace bayan ita sabida nasan itace halalina, wanca yarinyar da aure nake bukatarta."
"Hmmm! Tabawa Yarka Huda shekaru huɗu da watanin knn shine zaka shiga dan niman janyowa kai reni."
Da fashi Ahmad yayi cikin nutsuwa yace.
"Ina tayaka murna, nima Allah ya amsa min Addu'ata ko kamar hudan nasamu, na huta da wulakancin matanmu."
[4/3, 7:54 PM] Addah Ramlah: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋
_Idan kinsan baki saya karki karanta sabida na kuɗine, idan kika samu an sato toh karki faɗa min maganar banza dan zan iya miki Allah ya isa, duk wacce ta fitar min Na barta da Allah_
*BOOK ONE👈*
*Page.8*
"Amin Ahmad, rabu da ɗan iska yaje yayita fama da guzumayenshi kai ba sa'ar Huda ba, ko Sa'ar Samee ne i don't care tunda mace ce, kuma zata ɗauki lalurata da damuwata ai da sauki ko ɗaura min mai shekaru 21+ akayi a kafa finciketa zanyi na kara gaba."
Aman ya faɗa musu a fusace,
Shiru Mai Nasara yanda yaga Aman ya ɗauka da zafin nan, shi kuma baya son tsawaita magana, sai ya kyalesu ya cigaba da abinda ke gabanshi ta waya.
........
"Hindu baki ga mijinki ya shigo da yar malaman nan bane, kin zauna kin buɗe baki da hanci kina kallon mutane, lallai fa dani ce Ahmad yayi wannan gigin haukar da tuni na hautsina taron nan." Inji Hafsat,
"Hmm kyaleni da bakin ciki zan sami yarinyar naci Uwarta babu abinda ya dameni," haka hafsat ta cigaba da zugata,
.......
Wayar hannun Rahilah ne ya kama haske tasaka a kunne amma sabida sautin, wakar da aka saka ya hanata ji mikewa tayi tace.
"Maryam Sajida bari nayi picking call, yanzun zan dawo."
Da sauri tafita sabida an sake kiranta a karo na biyu, yanda take tafiyar Ahmad ya kalla cike da bakin ciki dan gani yake idanun sauran mazan akanta yake, jiknshi na tsuma ya tashi yabi bayanta.
Taɓa Hindu Hafsat tayi tace.
"Kinga ni, ko kinga abinda nake faɗa mishi har ya kirata kije kice ubanta shegiyar yarinya sai kace aljana."
Fita hindu tayi itama ranta a ɓace, tabi bayansu.
.......
Lokacin da Rahilah tafita kiran Yaya Hayat ne, ɗauka tayi cikin dariya.
"Kaiii Bro irin wannan kiran haka. Ko Aunty ta juye mata yan biyu."
"Auta ina wasa dake, dama na shiga gida ɗazun aka ce min kuna zaria biki shine nace bari na kiraku ina sauran yan uwan naki." Inji Hayat,
"Eh wallahi Yaya suna cikin hall, nima sabida wayarka na fito, amma ynx zan koma,"
"Toh ku kula da kanku sai kun dawo ko."
Sallamah sukayi da juna, sannan ta juya zata, Wani matashi ta gani a bayanta sai murmushi yake dokawa, "Princess har kin gama da Bro ɗinmu, kinsan da za'ayi gasar kyau dole ma kicinye dan haskenki ya dushashe na sauran matan tunda kika shigo nake bin motsinki har da kika fito waya, da fatan Yariman zazzau bai takura gimbiyar zuciyarshi ba."
Dafe goshi tayi cike da gajiya da surutunshi, raɓa gefenshi tayi zara wucce, yayi masa ya riko hannunta cikin murmushi yace.
"Baki ce min kome ba,kuma..."
Fincike hannunta tashiga yi.
(Kalubale gareku Yan mata masu zuwa wani event na dare, karki kuskura tsautsayi ya fitar dake toh idan Allah bai kareki ba akwai ɓata gari a waje Allah ya karemu."
Kokarin fauce hannunta take, yayi saurin rungumeta da ɗayar hannun, cikin tsananin tsoro tace.
"Nikan kyaleni,nace ka rabu dani bana so."
"Haba baby babu abinda zan miki na shiryawa rayuwarmu tanadi me kyau bazan barki kiyi kuka ba, kawa...."
"Saketa dan ubanka, tayi maka kama da kananun karuwan da ke bine, dan Ubanka." Inji Aman, yana takowa gurinsu yayinda idanunshi suka birkice da tsabar ɓacin rai koshi bai shirya dadumarta a haka ba, wani ɗan iska ya rungume mishi tanadin shi.
Kin tsaketa Yaron yayi cikin fitsara ya kai kanshi zai sumbaci wuyarta, zuɓewa yayi a kasa tsabar yasha karfin naushin da Aman ya kai mishi, sakw binshi yayi da kafa duk ta ruɗe rike shi tayi cikin kuka tace.
"Don Allah ka rufa min asiri karka kashe shi."
Juyawa yayi ya ɗaga hannunshi zai mareta, ganin yanda ta rufe idanunta da kare fuskarta ya sashi sauke hannunshi, ya fincikota yana kallon yaron yanuna mishi yatsa yace.
"Rahilah Matar Aman Mandara ce, duk wanda ya kuskura ya kara zuwa inda take Allah ɓatar dashi zanyi."
Bari gurin. sukayi, aikuwa sai ga Hindu ganin irin rukon da Aman yayiwa Rahilah gashi sai kuka take, shi bai ma ganta ba, da gudu tazo ta rufe Rahilah da duka,
Tare da tara musu mutane, tana cewa.
"Shegiya karuwa, dan uwarki taxo tagama tallarku shine bari ki fara akan mijina da babu ruwanshi, sai na kasheki."
Da karfi ya tureta Aman yayi ya juya da Rahilah, suka koma gurin da ya ajiye motarshi buɗewa yayi ya jefata ciki, yace.
"Duk abinda ya faru kece sila, gobe zan mai daku gidanku tunda har kin fara haɗa crushe wa kanki."
Rufe kofar yayi ya kunna mata Ac, ya juya.
"Aman baka isa ba wallahi sai na lalata rayuwar yarinyar can dan Ubanta, kaima munafiki ananamimi kaje kaja yar mutane kazaka lalata ko mi zaka samu a jikinta waw..." Marin da baiwa Rahilah ba shi ya sakewa hindu cikn masifa tace.
"Ko kasheni zakayi sai na faɗa, karuwarka ce ai yarinyar wa yasani ko Uwarkac....."
Baisan lokacin da ya rufeta da wani irin bugu ba, a cikin mota kuma Rahilah na bubuga mota.
Dakw gurin parking ɗin babu mutane dukar tsiya yayi mata ya tsallakata ya wucce, bai taɓa dukar ko kanwarshi ba, amma hindu tasahi ya daketa dukar da zaiwa katon namiji, ciki hall ɗin ya shiga ta mike dan jaraba, ta biyo shi,
Mu kuma a ciki ganin rahila bata dawo ba hankalinmu ya tashi muka nufi gurin Maminshi hankalinmu a tashe muka faɗa mata Rahilah tunda tafita bata dawo ba,
Mikewa tayi, muka shiga nimanta a hall ɗin sai gashi ya shigo ganinshi ranshi a ɓace yasa tace.
"Aman ina rahila?"
Cikin harshen shuwa yace..
"Tana mota, kanta na ciwo."
"Karya kake munafiki, an gungumi, dan Ubanka tsinane la'ananen zuwa yayi ya kwanta da yar mutane itama dake karuwa ce, uwarsu ta gama wa'azin karya, gefe guda ta turo su karuwanci idan nai miki karya kije tana motarshi." Inji Hindu.
Juyawa Aman yayi zai rufeta da duka Ahmad ya rike shi, shi cikin konar rai Mamie ta tsinke shi da mari ba adadi, dole sautin dake hall ɗin ya tsaya cak sai karan marirrukan da Mamie ke zabga mishi, zuba gwiwawenshi yayi kasa kuma bata