Matar So 1 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   20 / 64

57K to 60K   out of 190.6K words

fasa marinshi ba, sai da Hajiya Yabi ta rike hannunta, tace.
"Haba don Allah, Falmata me yayi zafi haka," jikinta na rawa tace.
"Ahmad ko Mai Nasara waninku yazo ya maidamu zaria,"

       Take gurin bikin ya ruɗe da tashin hankali,gaba mai nasara yayi zuciyarshi na zafi,
Ahmad ya ɗago Aman, wanda jikinshi ya gama mutuwa, mika mishi keyn motarshi yayi, cikin wani irin fitar numfashi yace.
"Yarinyar tana cikin motana, ka kaisu gida."

           Sakamu a gaba tayi muka fita muna kuka, sabida tozartamu da mahaifiyarmu, muna fita mai Nasara ya kawo motarshi, juyawa Mamie tayi cikin ɓacin rai tace.
"Ina ya kai musu yar mutane."

    "Mamie bari na kawota," inji Ahmad, bin bayanshi mukayi ya isa gurin motarshi ya buɗe ɗago kanta tayi cikin kuka, ganin mu yasa tafito da sauri ta zuɓe a jikinmu tace.
"Ku kaini Ummana bazan kara kwana anan ba, zata kasheni."

  Riko hannunta Mamienshi tayi ta janyota jiknta tace.
"Muje yau zaku kwana a jikin Ummanku."

       "Don Allah girman shi da isar mulkinshi ki bari gobe ku koma. Gida, Hajiya Falmata na haɗaki da mahaliccinki"

        "Kin min dabaibayi Iyami, Kaman Aman bai san yanda zai iya da gidanshi ba, sai matarshi ta tozartani a bainar mutane, kinsan yaran nan basa iya rabuwa da iyayensu nasa Mahaifiyarsu ta barmin su, shine zata lalata musu suna, Wallahi tallahi billahi azim gobe da Auren Rahilah Aman zan wuni, idan banyi haka ba, toh Usman Kyari da Kubra Goni, shegiyata sukayi, batace karuwai bane, ni sai nasa rahilah zama karuwar a gidan Aman yanda ko ita sai yayi mata kallon doki."

           Cike da tashin hankali Aman ya faɗa cikin motarshi zai tadda, amma Ahmad ya dakatar dashi fitar dashi yayi daga gabar motar ya mai dashi baya, shi kuma yaja motar suka can gidan bakin Mai Nasara Ahmad ya kai Aman,

       Tsabar tashin hankali da zaran yace zai yi magana, sai ya makale dan dole ya kwanta kashin na masa mugun ciwo,

           ......
    "Wallahi kinyi asara Hindu, wannan wani irin bala'ine haka zaki zo ki rusawa mutane taron da suke, jinki abinda kikayi zai hanashi kara aurene banza shashasha, a wannan zamanin wake kishin jahilci,"

   Inji Fareeda,
   "Kyaleta Hindu kinsan ita anshata ta warke, kuma wallahi duk wannan abotar da suke da mijinku yasa Aman tunanin Aure ni Ahmad ya isa yace zai fara wannan haukarne tuni ban takawa kowa birki ba, keni har mahaifiyarshi zan iya shiga tsakaninsu dan karta kawo min shamaki da mijina."

           "Lallai kuwa Hafsat sai ki ɗaura ɗan mara, sosai."

     Inji Fareeda.

     ****
   Tunda muka koma gidan bikin muka cure guri guda, muna kuka duk aka rasa wanda zai rarrashimu, haka muka kusan kwana muna kuka goshin asuba bacci yayi gaba damu, ina tsakiyarsu Rahilah, mun sarkefe hannun juna.

     Karfe shida na safe, Mamien tashigo tasamemu a cure, tausayinmu ya cika mata,zuciya buga pillow tayi muka farka da kyar, juyar da kanta tayi cikin damuwa Tace.
"Takwas nake son mushiga kaduna, kutashi."

    Mik'ewa mukaya Nice na fara shiga nayi wanka alola na fito, sai Rahimah sannan Rahilah abin karyawa aka kawo mana sama sama, muka ci, sannan muka fito ana ganinmu aka fara kuskus sai duk muka tsargu da kanmu, ɗakin muka koma ina jin wata nacewa.
"Bakarce fa, akace yayi sex da ita ba faran ba."
      "A'a ita ɗaya dogowar matar tace fa, aisu daga bayane suka ankara bata nan, namiji shege amma ai kinsan shi iyayenshi manyan ne maganar zata ɓoya,tund.."

          Ran Mamie ne ke kara ɓaci ta kallesu sannan ta shiga ɗakin ta fito da Rahilah ta tura musu gabansu cikin ɓacin rai tace.
"Wallahi ban taɓa zina ba, haka Mahaifin Aman itama yarinyar iyayenta tsarkakkakune masu kima, shine kuke jifanta da kalmar zina, ina shaidarku, ina tabbacinku budurwa wacce bata taɓa sanin namiji ba, ana ganota ta hanya mai sauki ku duba min ita idan Aman ya lalata musu yar mutane, budurwan da tasan namiji kuwa ana gane haka ne ta hanyar buɗewar mazauninta,kee Rahilah cire hijab ɗin jikinki su tabbatar, kaiiii koda Aman yasamu damar kusantarta toh zanyi bakin ciki amma na yarda da kaddara kuma ashirye muke mu nima mishi aurenta, ku matane iyayen kuma, Allah ya gwada muku kwantankwancin abinda kuka jefi bayin Allah dashi."

   Kamo hannun rahilah tayi wacce take kuka kaman ranta zai fita, tasanya mata hijab ɗinta muka bar gidan, gaskiya rayuka sun ɓaci sosai, muna cikin mota sai share kwalla muke, ita kuma rahilah kuka take sosai har muka shigo kaduna, kaitsaye gidanmu ta wucce,

    Tasamu malam bai fita ba, tunda muka shiga gidan muka sami Yan uwanmu a gidan ɗakin Umma muka shige, itama Mamie ta shiga ɗakin Mama.
      
  Gaisawa sukayi cike da mutunta juna, sannan ta basu hakuri da abinda ya faru,

              Dr Mohmud Mandara ne yazo suka tattauna tare da bada sadaki.

       A cikin mutuntaka aka tsayida kome sai an sako jumma'ah.

                    Godiya Mamie tayi sosai sannan tabar gidan.
          
     Ina zaune kan rahima na cinyata Rahilah na kwance akan jikinta, Umma ta shigo mikewa mukayi cike da tsoro muka ja baya,

               Zama tayi ta mikawa Rahilah Zuma dafaffe me ɗauke da dabino, a cikin wani bowl na tangaran tace.
"Ina son a cinye min sannan, a shanye min zumar."

           "Hmm naji abinda ya faru, da nasan haka zai faru da ban barku a gurin ba, amma kaddara ta riga fata,"

            "Rahilah zaki shiga wata rayuwa ce mai ɗauke da abin mamaki da alajabi, zaki ganshi tankar wata tafiya ce da bata da iyaka, Rahilah rayuwace wacce bata da farko balle karshe, yakine a gabanki mara makami, amma idan kika so zaki ya sayan makamanki ki shiga dasu, sabida baki san mi zaki tarda a inda zaki jeba, dan tafiya ce mai cike da tsire gashi dajine mai cike da kayoyi,
         A tafiyarki da zakiyi akwai bukatar guziri, wanda zaki nemi hakuri,juriya, biyayya, ladabi, amana, gaskiya, Iya magana, girki, tsafta, uzuri, da yafiya,fahimtar juna..... Idan kika duba kalamar yakin dake gabanki wancar bayanin yake bukata, haka idan kika duba kalamar daji me cike da kayoyi wancan jawabi yake bukata, Rahilah bansan waye Aman ba, amma ke zaki fini saninshi sai kinyi hakuri da halayarshi dan ba kabir bane ko Yayanku Hayat, ba kuma malam bane da zaki ce kinsan halinshi kece zaki san meyake bukata, miye baya bukata wani abinci yafi so, wani irin rayuwar aure yake so dake, shi yana da hakuri ko ma faɗacine, Rahilah, Rahimah, Maryam,ina faɗa muku ne, dan ya amfaneku badan raɗin kowa ba, ni baxan muku, show glass na kayan mata ba, dan bazai baku namiji a hanunku ba, idan kuka maida alamarinku ga Allah shine yake rike da zuciyar mijinku, kuma shine yake tallafe da al'amuranku, bazance rayuwar aure nada daɗi ba, amma nasan wuyarshi sabida ɗaɗinshi kalilane, kuyita addu'a da azkar ku yawaita sallar dare, idan ya barku ku rike axumin nafilla, iyayenshi da danginshi su zama sune, asama da iyayenki karki fifita iyayenki sama da nashi, haka zai kara miki daraja da kima a idanunshi, sai gaɓɓa na musaman, shine jikinki za'a wayi gari ya mallaki duk wani abu naki, a cikin yanayinda koda kiranshi kikayu ko rokonshi, kaiii duk abinda zakiyi kiyi bazai taɓa jinki ba, sabida kudirinshi da hakkin kasancewa dake zai bijiro masa,Maryam, Rahilah, Rahimah wannan ranar idan yazo ku kira kowa dan su taimakeku bazasu iya taimaka muku ba, sabida nauyi ne da ya rataya akanki ki sauke kuma zaki sauke shi, da zaran haka ya faru toh kin fita sahun yara kinshiga kwaryam Manyan, duk abinda muka sani kunsani, koda wasa karki bari mijinki ya gano kazantarki ko wani nakasu a jikinki, zan baku misali akanmu kun taɓa ganin Malam yace wani abu mara kyau akanmu,"

   Girgiza kai mukayi, cikin kuka, tace.
"Yawwa sabida, mun yarda da kanmu karku bari mazajenku su gano illarku, a fagen girki da tsafta nasan renonane ku, a fagen hakuri da juriya renon Mamanku ce, sai iya magana wanda nasan wannan renon malam ne, kuma Alhamdulillah ta kowani fuska bamu da aufi akanku, sai da Rahilah kina da kishiya, kuma nasanta nasan halinta bazan ce miki komi akanta ba, ke dakanki zaki gano halinta karki rena mishi mata, naso da sai kon gama karatunki amma Mahaifanshi sun nuna bukatarki zaki karasa a gidan don Allah ki rufa mana asiri ki bawa mara ɗa kunya, ki tayamu ganin lafiyar Amarya ya inganta tunda gausiya ta dawo kullum sai Amarya ta shaki Inhelarta, sannan ki ajiye kunyarki washi garin ranar da kika zama Mace dan daga nan zaki mori aurenki, iya abinda zan faɗa miki kenan kuma Wallahi naji labarin yarinya tace kasuwar ganye ko wata banzar mata ta kawo mata maganin matq ta saya na rantse da Allah sai na mata shegen duka, idan kina son maganin mata, kiya shema'u magana balle hajiya falmata bazata barki haka ba, naji daɗi da kika sameta a surikarki, Rahimah kema an nan za'a zo niman aurenki, saura Uwar masu gida yarana sun mata wayo."

          Tana gama mana nasiha da huɗubar da yasamu cusa kai a cikin cinyoyinmu, tafita kuka Rahilah tayishi ba iyaka, musaman da aka zo ɗaukarta za'a mata wanka da lalle mai haɗi da miski, tana fitowa akasata a gaba sai da tashanye zumar nan, tana kuka tana kome,

            Abin tausayi, sai muka zama kamar wasu kala aure zai rabamu da Rahilah, kukanmu yaki karewa, sai da Umma tazo ta balbalemu da masifa sannan mukayi shiru, karshe sai ga Rahilah tana janmu da hira da wasa da dariya.

            ****
      A zaria kuwa sai da aka dangana da Aman asibiti, sabida jininshi da yayi masifar hawa, a daren suka kai shi, gari na wayewa, ya farka wajen karfe tara nasafe ya gabatar da  sallah yana idarwa ya juya ga  Ahmad, yace.
"Abokina ka yarda dani wallahi ban aikata abinda hindu ta faɗa ba, asalima kwato yarinyar nayi daga mugun hannun, Abokin.."

      "Toh mr romeo, aimunsan da haka, kawai ka rufe mana bakinka ka tashi mu wucce kaduna dan karfe biyu da rabi za'a aura maka jinjirar da kake suma akanta." Inji Mai nasara,

       Mikewa Aman yayi ya naɗe abin sallar Ahmad ya amsa, sannan ya koma bakin gadon ya zauna, ɗago jajayen idanunshi yace.
"Ba auren yarinyar bace mafita, fahimtar Mamie shine mafita, dan nasan halinta akan wannan abun zata iya daina min magana."

   Shigowar likita yasasu sukayi shiru mika musu hannu yayi sukayi musabaha,, yace.
"Mr Mandara ko zaka iya kwanciya a dubaka."

    Kwanciya yayi likitan ya,shiga duba lafiyarshi, ya tabbatar musu da kome lafiya sai dai ya kiyayye ɓacin rai,

        Sannan ya sallamesu, daga nan ko minti ɗaya basu kara ba, sai kaduna, kwantar da kujeran yayi ya lumshe idanunshi, cikin tsananin damuwa yace.
"Dole na rabu da Hindu, dan haka ne mafi alkhairi a gareni."

     "Hmm aikuwa a jaridar Aminiya za'a wallafaka wani yasaki matarshi sabida zai auri jinjira waccw bata fara kirgan dangi ba," Inji mai nasara,

               Juyawa yayi ya kalli Ahmad da yake tuki, sai danne dariyarshi yake, juyawa Aman yayi ya kalle Mai Nasara cikin jin haushi yace.
"Eh gwara ni, jaririya zan aura kai da katara, jakuna a matsayin mata fa, wallahi mai nasara zan danna maka bahagon ashariya, wallahi ka kar kureni yanzun nasa Ahmad ya tsayida motar mu bawa Hammata iska,"

        "Haba ina ba dani zakayi haka ba ka kwantar da hankalinka ka kusan bawa jinjira iska da cinyoyinka." ya faɗa mishi,

      "Ahmad sauke ni naci uban wannan gaye, zai rena min hankali ɗan iska, wanda girman kai da miskilanci ya hanashi gyara gidanshi."
        "Naji ango baby."

        Haka mai nasara yayita kuna Aman har suka isa gidansu Aman, aka sauke shi ko kallon inda suke baiyi ba ya banka kofar motar, yayi gaba abinshi sauke glass Mai nasara yayi yace.
"Sauka lafiya ango jinjira,"

         Cak Aman ya tsaya, a fusace yayi kam motar, ya buɗe inda mai Nasara yake cikin huci da ɓacin rai ya caccumo Mai nasara zuwa waje.
"Dan Ubanka mi kake nufi dani ne."
    Fitowa Ahmad yayi daga motar yana raba tsakaninsu, luuuuuu Aman ya tafi zai faɗi, suka tare shi, cikin tashin hankali Mai Nasara yace.
"Wallahi bana nufinka da kome, asalima zolayarka nake, don Allah ka yafe min, ɓata maka rai da nayi."

   Lumshe idanunshi yayi yana jinsu suka ɗauke shi a kafaɗa har cikn gidansu,, Mamie na falon tana waya da yan uwanta da suka taso tun jiya,  dan tun da abin ya faru, taci alwashin aurawa Aman Rahilah, ta kira Babban Yayansu Sale Goni, ta faɗa mishi, dake suma gidansu malamai ne,  da asuba ya kirata yace aure fa zai tabbata, insha Allah karta ɗaga hankalinta zasu cigaba da addu'a,

    Yanzun ma da yayarta mace suke magana sun kusan isowa, dan samako sukayi,

       Shigowarsu Ahmad yasa ta yanke kiran ta zuba musu,ido take suka shiga kame kame, dakyar Mai Nasara yace.
"Bashi da lafiyane, jininshi ya hawu sosai, amm..."
"Toh  mi yasa baku kai shi gidanshi ba, sai nan."

      Tsagalgalesu tayi sannan tasa mi aikinta ta gyara mishi tsohon ɗakinshi aka sake har su zanin gado, da labule da duk wani abin bukata,, sannan ta kira family dr ɗinsu, tace.
"Ku kaishi tsohon ɗakinshi,dake wancan koridon"

          Daukarshi sukayi zuwa ɗakin dake zuba kamshi da sanyi daɗi kamar ya.

             Suna zaune likitan yazo ya duba shi, yasa mishi ruwa da allurai da kuma magunguna.

     Tunda aka samu yayi barci su kuma Ahmad suka tafi gidajensu da niyyar shiryawa zuwa masalaci,

              ****
   Bayan sallar juma'a alummar musaulmin dasukayi sallar juma'a suka shaida Auren Husaina Omer Hayat, tare da Angonta Dr Aman Mohmud Mandara, auren da yazo bazata a cikin unguwarmu dama, yan unguwar suna mana lakabi da bama auren kananun mutane sai manya,
              Tunda aka shigo akace Alhamdulillah, an ɗaura auren Rahilah sai gata tana shirin zuɓewa a kasa, sai da aka tareta wani fitinannen kuka tasaka wanda ya taɓa zuciyar kowa a gidan, mukan ai ba'a cewa kome,

          Shigar da ita Umma tayi ɗakin Mama Amarya wacce itama ta kunshe kanta a ban ɗaki tana kuka. Kwantar dani Umma tayi a bakin gadon mama,

                     Buga kofar ban ɗakin Umma tayi,  sai gata tafito kanta a sunkuye tana goge kwallarta murmushi Umma tayi tace.
"Gata nan, igiya ukun Aman ya ɗauru akanta, nayi iya nawa sai ki kara mata da wanda zaki kara, amma maganar gaskiya karki bari taga kwallarki dan zaki karya mata kwarin gwiwa,,"

      Gyaɗa kai Mama tayi, sannan Umma tafita tsakar gida, inda tasamu ana shigo da kaya cike da mamaki, ganin Yayar Mamie Aman yasa ta sake murmushi tace.
"Hajja Yanah kece a garinmu? Barka da zuwa, ku basu guri su shiga ciki."

          Dariya Hajja Yanah tayi tace.
"Malama Hasina,har yanzun kina nan da halinki na karɓan baki, fa mungode da abun arziki na bamu kyautar na musaman mungode."

             Murmushi Umma tayi, cikin jin daɗi tace.
"Ai bakonka sarkin ka, batun aure kuma karawa zumuncinmu karfine mune da godiya, wanda zai auri Yarka ai ya gama maka komi, a wannan zamanin da mazan suke tsada, mune da godiya bawai dan yaran sun mana yawa ba, sai dan nasan Hajiya falmata zata iya rike mana Rahilah."

            (Da fatan kun fahimci maganar Umma, kalma ɗaya mai kunshe da harshen damo bawai dan yaran sun mana yawa ba, nufinta ba wai muna niman kai da Rahilah bane ko sauran yaran, sai tasan ko babu auratayya Hajiya falmata zata rike Rahilah a matsayin Yarta🔛)

            
                         Godiya sukayi sannan suka shiga buɗe kaya, ɗaya daga cikin Auntys ɗin Aman tace.

"Ga kayan nan, amma bana lafe bane, kayan da muke na al'adace wanda akewa Uwar amarya da Uban amarya da danginta, bawai mun kawo dan ku biya mu baɓe, ai kun gama biyanmu tunds kuka ɗauki lu'ulu'u kuka bamu ko hka ma ya ishemu fatanmu nan da wata tara cif abin arziki ya sake taramu, dan mici daɗi, yanda take Husaina Allah yasa tana shiga ta juye mana, huɗu duk shekara muzo suna wallahi bazamu ki ba, ai abin daɗine haka."

      Dariya akayi sannan aka musu godiya, tare da abin arziki Umma ta basu.

      Har zasu fita,  Kanwar Baban Aman Hajja Qoise tace,
"Mu dai bama bukatar, kayan ɗaki idan da gaske ɗaya muke, toh mun yafe, Yarmu muke bukata."

         "A'a Hajja ku faɗa mana, inda za'a kai mata, kayanta koda bazatayi amfani dashi ba, itama tayi alfahari da kayan da iyayenta suka mata" Inji Umma,

  Haka suka rabu cikin mutunci da fahimtar juna,


Zama sukayi aka shiga ware kayan, bandir ɗin shaddane masu shegen tsada, sai atamfofi suma haka g wasu manyan liffaya,
Abin gwanin burgewa, kowa sai san barka yakewa su Umma da Rahilah.

****
"Wai duk wannan shirin na zuwa ɗaurin auren Aman ne, duk wancan munafikine ya koya mishi niman mata, Allah yasa bayi nasara akanka ba Ahmad." Cewar Hafsat da take kallon Ahmad na sanya wata muguwar yadin maza.

(Wayyo mai nasara tara matanka yajanyo ana kirania da munahuki😜)

Ganin yaki kulata yasa ta koma gefe, zuciyarta na raya mata tunda Aman yayi aure tabbas Ahmad na hanya, shima.
Mikewa tayi ta isa bayanshi tana goga mishi kirjinta, juyowa yayi fuskarshi a haɗe ya tureta gefe, cikin dakakkiyar murya

20 / 64