Matar So 1 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   59 / 64

174K to 177K   out of 190.6K words

nufin kin kai ɗaukar yaro a cikinki ne, ke ko tausayin kanki baki ji, dube yanda kika koma kin lalace baki ɗaya ba makeup ba kamshi ba komi a'a zan cire kema ki sami freedom yanda zaki murza rayuwarki kafin ki cika 20yrs sai ki sake ɗaukar wani."
Girgiza mishi kaina nayi cikin kuka nace.
"Ni ynz nake bukatar ɗaukar ɗana, bayan haka bazan iya ɗauka wani lokaci ba, Daddy da iliminka da saninka kake irin wannan maganar don Allah ka barni na ji kaman yanda sauran iyaye keji."

"Ba zaki bi umarnina bake nan?"
Ya jefa min tambayar,
"Eh indai akan sabawa mahaliccena ne na gwammaci ganin kiyayyarka da tsanar cikin amma ba zan saɓawa ubangijina ba, duk halin laulayi da nake ciki ladane dan haka kayi hakuri."

"Maryam ban isa dake bane, da zan bada umarni kice a'a."
A ynx zuciyata tayi tauri, wani masifaffiyar taurin kai nake ji, da tsabar bala'i cikin izza nace.
"Ka isa amma akan zubda cikin baka isa ba, ai shi yasa kake shan kwaya dan ka zubda min ciki, Allah sarki kainuwa dashen Allah ba dashen ɗan mutum ba, ko zaka kashe ni sai na haifa maka cikin. Hhhhhhh"
Na shafa cikin ina dariya nace.
"Magajin Yunus ko magajiyar Yunus, kinji abinda Daddynku yake cewa wai kar......"..

"Keeee kina hauka ne, wacece ke da zakina faɗa min magana.".
Ban barshiya kai aya ba nace.
"Wacce ka iya raba dare gurin rayuwar aure da ita, kuma ka nuna ɗimautarka da gigitarka, akanta, wallahi idan kana son zamanmu ya ɗuri toh karka taɓa min cikina dan zan fito maka sak maryam da baka taɓa sani ba, zan tsaneka tsana mai tsanani, zank'i ka fiyye dakima."
"Har kima kike dashi keda baki da daraja, mi kike dashi na darajar wacce iyayenki ma, badake suka....."..

"Yunus Muh'd Marafa!!!! Karka fara kuma karka sake ka taɓa min iyaye, kai ɗin banza ans canza miji ba'a canza iyaye, ai daraja da kimana yasa ka gaza hakuri akan yar zabarmawa, da zaran ka ganta duk wani jarabarka da fitinarka yake tashi cikine baza'a cire ba naga wanda zai cire min, kuma kasake buɗan baki kazagi iyeyana zan baka mamaki, dan na lura ilimin addininka bai amfanek....."
Gefen hanya ya koma tare da riko hannuna zai murɗa na kalle shi cikn zafin rai har jikina na rawa nace.
"Wanda yayi niyya ya fasa, ya rena mahaliccinsa."
Kallon yanda kwayar idanuna suka koma yayi, dukar kan motar yayi yana cizon bakinshi.

Lokaci ɗaya na tubure mishi da masifa da bala 'i, gyaɗa kanshi yayi cikin ko in kula yace.
"Ok nidake wanda ya fasa."

Banza nayi dashi na kauda kaina, raina na kara ɓaci kuka ne ya tawo min, na kifa kaina akan cinyata. Sosai nake kuka duk abinda mutum zai min a duniya kar ya taɓa kimata, ina jinshi har cikin raina ne. Musaman iyayena lallai Daddy bai sona, dama can abu ya nima kuma ya samu.
Haka na cigaba da kuka, koda nasanin abinda ya aikata baiyi ba saima kokarin ganin ya samawa kanshi mafita.

Karfe goma sha ɗaya har da rabi muka shigo kaduna, ɗago kaina nayi naga ya sake hanya, juyawa nayi na kalle shi cikin tashin hankali nace.
"Kayi hakuri kasake ni, kaga babu wata damuwa iyayena zasu rikemu nida abin cikina."

"Ai bance bazan iya rikeku ba, idan goma ne ma zan iya rikesu sabida Allah ya hore min takowa ni sako da lungu dan haka. Karamar mara kunya bazan sake ki ba, sai nayi niyya cikin jikinki da zan cire gata zan miki dan har ynx baki san ciwon kanki ba balle kisan ciwon wani, dan ina kwanciya dake bashi zai sani kula da lafiyarki ba, idan kika kai lokcin ɗaukar ciki ni da kaina zan kaiki a duba ki, dan matuƙar aka cire wannan cikin toh zan idona akanki yanda bazaki sake ɗaukar ciki ba, sai na shir....."

"Kana da tabbacin zan sake kara wani wa'adine, Don Allah ka bar min cikina kaji zan fanshe shi da komi har da aurena zan fanshi cikina. Daddy ka wulakantani amma karka taɓa lafiyar abin cikina wallahi yanzan nake jin masifar sonshi, idan kace nabar garin kaduna na ɓace na shiga duniya zanyi dan cikina ya rayu, kuma namaka alkawarin bazan taɓa nuna mishi kai ba, don Allah badan nima dan darajar fiyayyen Halitta, ka barshi shima ya rayu kamar kowa, kabarshi shima yayi farin ciki kamar kowa, karka zubda hawayen Mahaifiyar da zata iya mutuwa dan ɗanta ya rayu mana, karka sani jin tsanarka fiye da kima. Wallahi bazan iya jure wannan zaluncin ba."
Wayata na ɗauko a jaka, na shiga niman nomber Ummana.
Yana shiga cikin sauri tare dafashewa da kuka nace.
"Ummana...."
Fincike wayar yayi tare da jifa da ita waje bayan ya buɗe window.
Hannuna nasaka akai sai kuma na tuna akwai Allah, abinda ya fara fitowa a bakina shine innalillahi.... Da wasu addu'o'i har muka isa asibitin. Motar Aneesah ya gani da sauri ya fita, tare da sakawa motar key, dake tasan da zuwanshi. Har ciki suka shiga can sai gasu tare da wasu nurse harsu biyu suka zo. Buɗe motar yayi suka shiga tare taren kamani dan kar na gudu. D'aga hannuna nayi nace.
"Basai kun tare ni ba." bin bayanshi nayi har ciki ina zubda kwalla, ofishin likitan muka shiga.
Zama mukayi dake baya cikin ofishin, dafa shi nayi muryana na rawa nace.
"Don Allah na fanshi cikina d aurena, ka sakeni wallahi daga nan zan shiga duniya na ɓata baki ɗaya kowa ga huta."

"Karki damu kanki, ciki zaki sake samun wani, banda ma ɗaurawa kai damuwa. Kinga Aneesah sai huɗu tana cire ciki kuma babu abinda ya sameta, balkisu rufe mata bakin mahaifa akayi, Fareeda kan mahaifar aka cire. Kina karama yaushe zaki damu kanki akan cikin da bai da muhalli, ki kwantar da hankalinki a cire nayi miki alkawarin zan baki naira million goma ki fara kasuwanci sannan zan kaiki Sudan ko U.S. ko Dubai kiyi karatunki har ki zama cikakkiyar likita, nd bayan haka zan mallaka miki komi zan mai dake saraun..."

"Bazan fansar da cikina haka ba, bazan karɓi ko sisinka ba..."
Shigowar likitn yasani ɗago kaina wani garjejen inyamuri da shi tare da nurse su biyu, ɗaya tana rike da tire ɗaya da takardu. Mikawa Daddy tayi ya karɓa ya cika komi, me ɗauke da tiren ci ta ajiye ta fasa alluran ta suke a cikin siring. Sannan tasake fasa wani, ta zuke har uku.
Juyawa nayi na kalleshi cikin zubda kwalla masu zafi nace.
"Duk sabida son kai ko?"
Juyar da kai yayi yna kallon gefe, matsowa matar tayi na juya na kalleta, nace.
"Ke mace ce kika zaɓi, saɓawa Allah sabida kici abinci? Nasan cikin zai zuba tunda gani a hannunku saidai kusani kamar yanda na zubda kwalla haka kuma sai kungani akwaryan tuwonku, kai likita ka buɗe inda za'a na zubda rayukan bayin Allah bayan Ubangiji nasane da wanzuwarsu ka zaɓi kaucewa a hanya sabida kuɗi. Insha Allah daga yau kun daina dariya kamar yanda na tsayida sallah, da wasu ibadodin Ya Allah nayi tawwasalida sunayenka kyawawa ka ɓarar da farin cikin duk wanda ya ɓarar da farin cikina, Ya Allah ka kuntatta musu kasasu su kaunaci mutuwa fiyyeda rayuwar duniya, Ya Allah ka ɗaiɗaita Rayuwar wanda suka bada kofar a..."
Fincikoni yayi ya juyar dani tare da janye zanin jikina suka tsikara min allura. Ajiyar zuciya na sauke tare da komawa na zauna bayan sun gama murmushi likitan yayi nima nayi ni masa dariya nace.
"Allah Kana gani kana ji, suka cutar da ni Ubangiji ka hanasu sukuni."
"Alhaji karki damu just five min zaka ga aiki but kace ba se anyi woke ciki ba, zaka keshi asibiti wani."

Mikewa yayi ya ɗagani muka fita har munkai bakin kofa, nace.
"Bazaka sake ganin haske ba a rayuwarka, sai dai duhu hakkin cikina da kuka zubda sai ya hanaku farin ciki, sai mahaukata sunfiku daraja."

Janyoni yayi da karfin tsiya har waje yasakani a mota, sannan ya zaga gefenshi ya ja motar da sauri yana kallon agogon hannunshi.
Kallonshi nayi ynx fuskarshi a sake, kamar bashi ba murmushi nayi sannan nace.
"Tabbas sunanka mai nasara, sai dai daga yau ka zubda duk wata nasarar da kake da ita sonda nake maka dabance da ta kowa, kamar yanda kazubda ciki jikina Insha Allah ka zubda soyayyarka a cikin zuciyata ka lalata duk wani soyayyarka Insha Allah bazaka kum.."

Dafe cikin nayi sabida wani mugun ciwo da kuma zafin da ya ziyarce ni, lokaci guda kuma nayi daukar ruwa mai ɗumi, kallonshi nayi hawaye na zuba a idanuna.
"In Allah ya yarda sai ya bimana hakkinmu da ni da ɗan da ka zubda min, sai kayi nadama mara amfani Allah ya gani na kiyayye hakkinka kai ka shiga namu, amma ba damuwa ni nabarka da Allah shizai bi mana hakki."

"Waini kam maryam duk wannan addu'a dan an zubda cikin jikinkine, kina bani mamaki."
Jiri nake gani, tare da duhu na rike cikina ga wani zufar dake bin jikina kamar ina cikin zafi. Jinine ya tsinke yaje zuba sosai komawa nayi da baya ina runtsa idanuna, duk ilahirim jikina rawa yake, sosai ya taka motar ganin yanda lokaci guda nake sauke haki.
Babbar asibiti yayi dani sannan yakira dr Nafe ya faɗa mata, kwatancen matenity tayi mishi, da gudu ya isa gurin,.

Parking yayi ya fita tare da zagayowa ta gurin da nake ya buɗe, sannan ya cironi ganin yanda jini ya jika min kayana daga kan zanina har hijab ɗin jikina, ga kuma wanda yake zuba.

Cak ya ɗaukeni bai taɓa ganim jini haka ba, sai yau. Yana shiga dani ciki kowa sai binmu yake da ido tsabar tashin hankali.
Gadon marasa lafiya dr nafi da wasu nurse suka turo, ya ɗaurani akai, da sauri suka wucce dani ɗakin yan ɓari, lokacin bansan waye akaina ba, jikinshi duk ya ɓaci, kita yayi ya shiga mota sai gida. Kayan jikinshi yake son sakewa, a falo ya sami Fareeda da Balkisu, ganinshi cikin tashin hankali ga jini na bim jikinshi, kallonshi Fareeda tayi, cikin tashin ɗimauta tace.
"Ka zubda cikin ko? Ka zubda hankalinka ya kwanta, hmmm amma kasani kasayi tashin hankali da hannunka, ka zubda abinda zai hanaka barci, ka zubda namu ka kwana lafiya wannan da ka zubda sai ya zame maka alakakai kaida ganin farin ciki har abada, mi zanyi da azzalumi irinka mugu fasiki, dan shine yake aikata duk abinda Allah ya haramta, ka kuma turo min da sakina dan na gama zama da kai."

Bakin ciki ya hana balkisu magana itama sama ta haye ta ciro kayanta daga wardrob ta shirya a wani babbar jakanta, tare da fashewa da kuka, tabbas duk abinda Yunus ya aikata da sa hannunta, dan da ta zama mace ta gari da babu yanda Yunus zai taɓa zubda cikin wata ba, itace ta fara nuna mishi bazata iya rike huda ba, yau gashi kuskurenta yaja kowa ya rasa farin cikinsa. Da yau ta cire mulki da son jiki da babu wacce zata zubda hawaye da yunus da ta amshi matsayinta na mace da Yunus bai zama abinda ya zama na mugun hali ba, ina zata kai hakkin Maryam. Mi zata cewa Ubangiji sabida kuskurenta Yau Iowa yana Kuka.

Mikewa tayi zuwa d'akinta Fareeda ta take zube a gabansa abin sallah tana Kuka mai con rai. D'agota Balkisu tayi cikin Kuka tace.
"it's my faults, banyi deserve yafiyarku ba, dan nice na nuna mishi yara basu da daraja, haka ma mace tana da lokacin da ta dace ta d'auki ciki, kosa halinshi nice na fara lalata shi, dan dama ance matar fari ce ke lalata miji kuma na yarda da haka Fareeda ku yafemin Dan nasan hakkinku bazai tabari barina na zauna lafiya ba, Ynx a wani hali maryam take ciki."

Mikewa Fareeda tayi daga duken da take ta janyo gyalenta suka fita, duk suka zauna a falo.
Can sai gashi ya fito jikinshi a sanyayye ya fita, bin bayanshi sukayi suka Shiva mortar fareeda.
Juyawa yayi yaga sun shige motarta, jan motar yayi har suka fita, daga gidan suna bin bayanshi.
Koda suka isa asibitin, har inda aka shiga dani.
Koda suka iso kiran Dr Nafi yayi, yace ya dawo.
Dama suna can ana rikici akan karfin alluran da aka min, koda ta fito ba tare da damuwa ba tace.
"Yallaɓai badan ina ganin kimarka ba da babu abinda zan taɓa yiwa matarka. Ka dubi abinda ka janyo min ana ganina da kima kasa an farq zargina da cewa ko nice nayi mata alluran da yafi karfin jininta, kasa manysn.likitoti suna cin mutuncina kimanin shekara goma sha biyar ina nan ban taɓa samun matsala da kowa ba, sai akan case ɗinku ka kaita am mata allura mafi hatsri wanda ba lallai bane tasake ɗaukar ciki. Wallahi baka kyauta min ba ka nemo jini a saka mata dan jininta yayi matukar zuba badan Allah ya takaita cikin ya fita ba a cikin jini da bansan yanda zanyi da wannan tashin hankali."

Tana gama faɗar haka ta juya tabar gurin kowa sai masa kallon Allah wadarai suke, dan da da farko sun tausaya masa jin abinda yayi muka bai musa ba, yasasu, ji haushi har wani mutum yace.
"Wallahi kayi asara, cikin sunnah ba shege ba, ni ynx zuwana asibiti na goma sha ɗaya kenan ina niman ko ɓarine Allah ya bani a cikin gidana kai da kasamu har kana kai matarka wa i gurin aka zubda cikinta kasan kuskuren da ka aikata kuwa, Kai da Allah."

Kuka balkisu take, sosai can wata nurse ta fito akan jinin da za'a karamin, lab suka nufa aka ɗibe jininshi, dake grp (O) jininshi.
Koda aka saka min amadadin jinin ya gwauraya. Kusan awa ɗaya da saka jinin sai ga borin jini, sosai ya feso har kan fuskana dole suka cire jinin, dr Nafi ta fito cikin jin haushi tace.
"Toh jinin yaki, zama dan ya feso mata da borin jini, dan jininta A+ ne kuma da nakan zai mata, amma dole sai an nimo mai irin jininta sak."
Rike kanshi yayi ciki tashin hankali ys laluɓi nomber Yaya hayat ys kirashi dake a cikin asibitin yake, kallon dr Nafi yayi yace.
"Don Allah ki taimaka min kar yasan abinda ya faru, Kanwar Dr Hayat Omer ne."

Zaro ido tayi cike da mamaki, can sai ga Yayan ya iso, faɗa mishi halinda nake ciki Dr Nafi tayi da jinin da ake bukata, lab ya wucce aka ɗabi leda biyu sannan ya kira Hamdiya da shema'u da Suhaima matarshi. Ya faɗa musu,.lokaci kusan guda suks iso asibitin.

Cikin damuwa, har an wanke min mara sannan aka turoni a gadon bayan an sauya min kaya da wani dark green. Aka gunguroni zuwa ɗakin yan ɓari,

Sharaf nake kwance babu alamar numfashi, sai ma wani irin haske da nayi, fuskana a kumbure. Idanuna sun shige ciki, sau uwar karan hanci. Har za'a shiga dani yace.
"Ko zaku maidata aminity ne." karkata gadon sukayi zuwa wani keɓetacciyar shashi daban. Daki na biyu aka sakani a ward B....

Hankalinshi ya gama tashi, a tsorace yake da kowa, musaman matanshi da kuma ni.

Kiran Umma Aunty Shema'u tayi, can sai gasu tare da Mama suka shiga har ɗakin da nake ban sani ba.
Kallon yanda Fareeda ke kuka Umma tayi, cikin murmushi tace.
"Kiyi hakuri mana, Allah da ya amshi wannan shi zai baku wani, cikin ikonshi da buwayarshi, karki manta itama maryam ɗin bata wuci Allah ya amsheta ba, kinga kenan kukan ya kare,kuyi addu'a Allah ya maida muku, wanda suka fi wanda ya tafi Allah ya bata lafiya yasa masu cetone, ya kuma sake baku mai amfani da inganci."

"Amin, Umma Amin." Inji shi, har bakinshi na rawa.

Komawa gida Umma tayi, tunda Mams tace zata zauna. Gurin Azhar sai ga Rahilah da Aman, sunzo har da abinci suka zo dashi. Aunty Hamdiyya da Auntƴ shema duk sun koma gida, sai matar Yaya aka bari da Rahilah.

Balkisu itama ta koma gida, Fareeda kan gidan iyaƴenta ta wucce.
Can bayan La'asar sai ga Mamie, itama Ahmad da Rahimah har zuwa wannan lokacin ban farka ba, sai bin likitoti yake. Suna zuwa suna fita hankalinshi duk ya tashi. Bai taɓa shiga tashin hankali haka ba.

Yakira Hajiya zai faɗa mata tace mishi.
"Nagode ! ka zubda cikin ba? Ai balkisu ta faɗa mana komi."

"Hajiya kuskure aka samu."
"Ba kuskure bane Yunus, son kaine ita yarinyar ka sameta a sauki ba, dan babu sisin kwabonka akanta duk kuɗina ne, sannan ka cire mata cikinta da karfin tsiya, ka sata zubda kwalla. Yunus ni bazan maka baki ba sai dai fatar shirya Amma tabbas hakkin maryam sai ya tambayeka, yarinyar da tunda ta shigo gidanka kake wahalar da ita, bata taɓs faɗawa Iyayenta ba. Tsabar tana ganin zata iya da kai, kasan tulin zalincin da akayi gurin aura maka ita, yarinyar da batafi sha takwas ba, ka ganawa azaba ta hanyar rabata da farin cikinta, zaka ribanci abinda ka aikata, kuma zaka biya shi lokaci na zuwa da zaka ɗanɗana kuɗarka dan wannan bashine hakkin maryam kuma sai ka biya shi."

Tana gama maganar ta kashe wayar.

Dafe goshinsa yayi kaman zai tsage.
Har dare ban farka ba, dole yasashi tafiya gida amma badan yana son haka ba.

....... Koda ya isa gida wanka ya shiga, yana kwance ruwa na ratsa shi, tunanina da kukan da nake yasashi buɗe idonshi a gurguje ya fito ya sauya kayanshi na barci, ya kwanta dake yayi sallah a can masalacin asibitin.

Karfe biyu da hamsin da uku na dare, zaune yake a ɗaki tare da laptop ɗinshi ya nutsu yana, aiki. Kukan jarirai da shashekar kuka yake ji. Sosai kukan ya hanashi sukuni, mikewa yayi ya fito. Har falonshi baiga kowa ba, can sama yaji kukan dan haka ya haura yana bin kukan, har bakin kofar falona saka hannunshi yayi zai murɗa kofar yaji ya taɓa abu kamar ruwa, ɗaga hannunshi yayi yana dubawa, jini ya gani.
Ƙifar ɗakin ce tq buɗu ya kutsa kanshi, kwance ya hangoni cikin jini. Ga jarirai akwance a jikina muna kuka tare dasu. Sai kuka suke, suna kara rikeni tare da shigewa jikina, jikinsu duk jini.

Takowa yayi ya nufi kaina d sauri aka janyeni zuwa cikin duhu. Dariya aka mishi sannan aka ce, "Dole kabiya abinda ka aikata."

Muryan ce ta sauya irin tawa aka ce mishi "daddy karka zubar min da cikina" ta bayanshi juyawa yayi ya sake ganina a duke ina zubda jini, da sauri yayi kaina, aka sake mishi magana.
"Karka zubda min da ɗana."

Lokaci guda ya birkice ga jariran da suka rufa mishi, a jiki suna hayewa jikinshi, tare da zubda jini, ga

59 / 64