Matar So 1 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   4 / 64

9K to 12K   out of 190.6K words

jinjinawa wanda zai auri Huda, dakyar yace.
"Don Allah princess jeki drvn yakai ki, na gaji sosai."

Mikewa tayi ta ɗauki side bag ɗinta tace.
"Ok Bye, hajiya mi zan sayo miki?"
"Ke tafi can magananiya."
Inji Hajiya knn, fita tayi tana dariya, har wajen gidan,

Shigewa ɗakin yayi ya kwanta, taɓe baki Hajiyarshi tayi cike da mamaki wato hali zanen dutse, halinshi ba iyakan mutane tsiraru yakewa ba, har da Yaranshi toh ai dole yasamu matsala da matanshi suma dake shashashune basu san yanda zasu bi dashi ba.

Haka ta ɓata lokaci tana nazarin halayar ɗanta da matanshi tana niman ta ina mafitar take.

***
A nutse muka ka dawo gida, dukda tulin gajiyar dake bibiyarmu dan dakafa muka shafo, daga makarantarmu, wai ma da zamu tafi a napep dawowa kuma asayidarmu, ga rana da ake tsulawa ajiyar zuciya na sauke lokacin da muka shiga harabar gidanmu, ganin motar Aunty Shukra da na Aunty Hamdiyya.

Da gudu khalifa ya fito ganinmu yasa shi komawa da sauri tsabar k'iwuya, Dariya Rahila tasaka tace.
"Baby Khalifa, ko kuntuna maganarmu na daren jiya..."


Kafin ta kai aya na shige a guje Rahima itama ta rufa min, dariya take lokacin da taga mun zaune muna sunne kai, tace.
"Annamimai, wallahi tunda kuka nuna min kuna jin kunya sai na cire muka kafin mu bar gidan nan"
Kasa kasa take maganarta wanda iya mune zamu jita, mikewa nayi na shige ɗakin Maman Amarya shewa tasaka, har da buga cinyarta, da sallama a bakina na shiga ɗakin Aunty Shema'u, da sauran Yaran gidanmu mata, har da Aunty Gausiya, zuɓewa nayi a jikin Aunty Hamdiyya ina dariya, waya take muryanta kasa kasa, idan baka ga wayar ba sai ka rantse ba waya take ba, kurawa bakinta ido nayi yanda take motsawa.
"De Aunty Hamdiyyarmu knn, kanwar sharuhkhan yayar Amisha sharma, irin wanga luv ɗin Aradu ko uwar gulmar da ta zuba miki ido bata san mikike cewa ba, Allah zan zo gidanki ɗaukar class."

Katse wayar tayi ta wawuro wani laida ta wurgawa Rahilah, dariya Auntys ɗinmu suka saka basu ɗaya ba, har da Mama da take gadonta,

"Rahima ɗauki kayan can ki kaiwa Ummarku, ni sun isheni"

Mikewa Rahimah tayi ta shiga ɗaukar kayan fruit ɗin da aka kawo can idanun Rahilah ya faɗa kan Ayaba, ɗauka tayi ta gutsura, daga jikim uwar haɗa ido mukayi da ita aikuwa ta kashe min ido da sauri na ɗauke kaina, daga gareta dan na lura iskanci take ji a ranta.

Kallonmu Aunty Shema'u tayi tace.
"Mama wai yaran nan basu da tsayayyune, ko jiya sai da Hayatu mukayi magana dashi, wai ana ta binshi akan ana niman izini akan su saura kwanaki su gama, scndry amma har ynx babu samaruka,"

Dariya Mama tayi cikin jin daɗi, tace.
"Yan ukuna har ynx Allah bai kawo musu mazaje ba, sai dai ina da Yakinin mazajensu suna hanya, toh da kike maganarki shema'u yaran nawa suke, sha bakwai ne fa da watanin biyar, kuma ai koke a sha tara malam ya aurar dake, sai jariraina ne za'a saka musu ido,"

Da dariya Rahilah tabar ɗakin zuwa ɗakinmu na yan mata, tasamu na cire kayana ina jiran rahimah tafito wanka, sai gata rike da ayabar tana min bayani tace.
"Kinsan lokacin da aka sani a zubar gado fans ina jin ana banana banana, Yaseen sai nazata nacine, asheeeee"

Mikewa nayi nabar ɗakin babu shiri, dariya tasake har da rike cikinta, Rahimah da ta gama wanka ta kasa fitowa tsabar, mun gaji da iskancinta.

Can tayi shahadar kuɗa ta fito, suna haɗa ido ta ɗaga mata gira, dake ita rahimah tana da sauri kuka take ta fashe da kuka tace.
"Wallahi sai na kai karanki."

Fuuuuu tafita, kiciɓis suka yi da Umma cikin shashekar kuka tace.
"Umma kinga Rahilah ko! Ta addambemu wallahi ku mata addu'a ko Allah zai aiko mata shirya."

Duk Yayunmu suka fito, sai kallonsu ake ita rahilah dariya yaci karfinta, ke Rahimah kuka, sai da Umma ta daka musu tsawa sannan tace.
"Bana son shiririta wucce ku bani guri."

Sunsun suka wucce, suna shiga ɗaki, aunty shukra tana bin bayansu, a bakin kofar ta tsaya tana jin dariyar Rahilah tace.
"Mi yasa baki ce ina kiran Banana bane, Allah da gske yaren novel ne, ki ji sunce joy stic.."

"Rahilahhhhhh" a firgice ta yarda ayabar, tura kofar Aunty shukra tayi tana mata wani irin kallo daga sama zuwa kasa.

"Kinsan abinda kike kira kuwa, gaban ɗa namiji a ina kika taɓa, gani yau zanci kaniyar." take jikinsu ya ɗauki rawa, tace.
"Don Allah Aunty kiyi hkr wallahi ban san wani abu akanshi ba, na rantse miki da Allah nima a online nake ji a novel Aunty ki rufa min asiri kiyarda dani bansan kome ba."

Buɗe kofa tayi ta kwala min kira da sauri na fito, na shiga ɗakin, nan ta shiga mana tambaya da bin didiginmu har da kwanakin da muke Period ɗinmu, kaii karshe cewa tayi sai ta duba kasarmu zata yarda dake Nurse a nan kaduna a wani prvt hospital take aiki kuma ba laifi babba ce, a gurin aikinta kuka nake cike da tashin hankali nace.
"Aunty Yau na fara bin month don Allah ki yarda damu bamu san kome ba "

Ganin yanda muka gigice yasa jikinta sanyi faɗa tayi mana sosai sannan ta karɓi wayar ta goge Whatsp ɗin ciki da face book, tace.
"Idan nasake kamaku kuna irin wannan maganar a kunen malam wallahi."

Cikin rarrashi tayi mana nasiha sosai wanda ya shiga jikinmu, tace.
"Wayarku sabida karatu da wasu uzuri aka saya muku bawai dan ku lalace ba, idan da a gidan mazajenku kuke wallahi bazan taɓa damuwa da ku ba, don Allah ku rufa mana asiri mu aurar daku, lafiya aikuna jin yanda ake sukar iyayenmu akan gausiya don Allah ku zame mana jakadu na kwarai."

Bamu iya kome ba, sai gyaɗa kai kaman kadangaru a jikin bango,(lolx kun tuna inna wuro kuwa)
Fita tayi tabarmu a ɗakin bayan ta bimu da addu'a shiriya,...

*****
"Hello Adda Nafi'a bazan sami zuwa wunin gidansu Sailuba ba, sabida Ahmad ya dawo, amma ki karɓa min nawa."

Daga can ɓangare aka " kutt yanzun zama zakiyi dan yana gari dalla kifito shi yarone da zaki bashi nono, a gidan common ma dear ki zo."

"Taɓ akan haka kina jinshi yana ikirarin kara aure sai na fito, bikin wasu na lalata nawa kicewa sailuba tayi hakuri, da baya gari zan zo amma ynx yana gari, nasan mi yake shirya min, tunda Yan uwanshi basa zuwa ko sunzo koransu nake da masifana kawai ki bata hakuri."

"Wai nikam yaushe kika koma haka, ne wato namiji yafi, bikin besty frnd ɗinki "

"Ai bashi yafita ba, kishiyar da yake ikirarin zai min tafita muni a idanuna kinga sai an jima dan ɗazun yagama f**ck ɗina son ranshi boons ɗina har ynx ciwo na suke min, yanzun zansan yanda zan shawo kan kayana clear."

Tana kai aya ta datse kiran, cike da takaici ta mike zuwa ban ɗaki wanka tayi sosai, har ynx tana jin zogin kirjinta sunce towel ɗin tayi cikin nutsuwa taga yanda bakin nipples ɗinta sukayi jajjur, dake fara ce, tsaki tayi tace.
"Banza mayye kawai, ko Jannart bata cinye min bakin nono haka ba."

Shiryawa tayi cikin riga da skirt na lace, purple tayi kyau ba laifi kitchen ta shiga tayi musu tuwo miyar wake, wanda yaji kifi da nama, a leda ta ɗaure tuwon ta kawo table ta ajiye sannan ta koma ɗaki tasake wanka sosai, ta canza kaya, tafito.

Zama tayi a falo ta kunna kayan kallo, wayarta da yake kashe tun jiya ta kunna a can tashiga niman inda zai ɗauke mata kewa.

Mbc bollywood ta saka, tana kaiwa suna fara hoob Ghaad, nan tasamu ya ɗauke hankalinta, data wayarta ta buɗe a hankali sakon Whatsp ya fara shigo mata kafin ta fara ganin na IG, Whatsp ta buɗe ta cikaro da hidimar bakin da suke yanda ake shagali, kwalla ne ya fara bin fuskarta,

A hankali ta fashe da kuka dan har jin kafarta tayi yana mintsininta, Ig ta buɗe anan ta ɗaura hannunta akanta ta fashe da wani irin kuka zaka rantse sakon mutuwa ta gani a'a tsabar shagali ya wucceta ne, take bakin ciki fushine ya cika zuciyarta yau ita ko Ahmad.

****
Kallon Rahilah mukayi sannan muka fashe da dariya cikin zolaya nace.
"Don Allah yaren novel nike son ki min."

Kwanciya tayi, daga ita sai zanin kirji tayi rigingine juya kanta tayi tana murmushi tace.
"Kuyi lokacinkune, zan kamaku bebs"

Zama nayi akan stool ɗinmu ina duba chemstry, dariya mukayi tashi tayi ta zauna, tana kallonmu tace.
"Wai shin dariya nake baku ko?"
Girgiza mata kai mu kayi nace.
"A'a baki bamu dariya, kawsi muna mamakin duk rashin kunyarki da bakinki daga ance za'a faɗawa Umma da Malam duk kin gigice sai kuka kike kina yarfe hannunki, hahahah."

Dariya Rahimah tayi cike da tsokana haka muka hanata sakat, sai da ta dawo mana da halinta dan ba tare da mun ankara ba ta zare xaninta tace.
"Zafi nake ji."

Da gudu muka fita daga ɗakin, gyara zaman zani ta tayi, ta shiga ban ɗaki wanka tayi ta fito sannan ta saka, doguwar riga tafito, tsakar gida ta karɓi busar shinkafan da Umma take nima ajiye buƙ ɗin nayi, na karɓi aikin yin miya, munayi muna hira.

"Maryam Sajidah kin kaiwa Hajiya Falmata hand out ɗin nan kuwa."

A raxane na ɗago kai nayi cike da tsoro dan Umma yanzun zata balbaleka, sake robar da ake ajiye garin kuɓewa nayi, na fito daga ɗakin girkin a tsorace ina yarfe hannuna nace.
"Wallah.."

"Wallahi kin manta ko? Toh ai yayi miki kyau sai ku tashi ki ɗauko ɗari biyu ku kai mata, dan yau zatayi amfani dashi sokuwa kawao kuma ki kwashe min garin kuɓewana kafin na raɗeki........
\(-ㅂ-)/ ♥ ♥ ♥
'''Ita Rayuwa saukine da ita ɗauketa yanda ka ganta'''
[4/3, 7:53 PM] Addah Ramlah: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Dedicater To Hafsat Abubakar💋


*BOOK ONE👈*

*Page.5*

Jikina na rawa na kwashe garin kuɓewar sama sama, na mayar cikin robar na rufe kallona umma tayi cike da mamaki yanda Allah ya ɗaura min tsoron jaraba, gashi na iya laifi amma cikina cike ya da tsoro, bani ɗaya ba harsu Rahilah haka muke da tsoron kata'i.

Da sauri nabar kitchen ɗin zuwa ɗakinmu, na ɗauko sakonta na fito kallonsu Rahilah nayi cikin nutsuwa nace.
"Jiranku nake kar lokaci ya kure."

"Amma dai kya jira na gama sai mutafi ko?" tace min,

Ina zaune ina jiranta har ta wanke shinkafar tuwon, ta jika Rahima tana gurin Mama dan ba zata bimu ba,

Da sauri muka fito ni ina sanye da Nikk'af ita kuma taki sakawa, muna tafiya muna hira har muka fito daga unguwarmu, abin hawa muka tara muka faɗa mishi sunan unguwar da zai kaimu, ba tare da wani gardama ba ya kwashemu zuwa unguwar,

A kofar gidan aka saukemu, unguwar sabon gurine dan kamar manyan mutane ne, suka sayi filayen, tura get ɗin mukayi da sallama, mai gadin gidan ne ya mike gaisheshi mukayi, sannan nace.
"Malam hajiya tana gida kuwa?"
"Eh tana ciki," ya bamu amsa a takaice.
Godiya muka mishi sannan muka shiga gidan da sallama abakinku, duk suna falo a zaune da murmushi ta amsa mana tana cewa.
"Yau nice da manyan baki haka? Malama Rahilah tare da Malama Maryam Sajida barkanku da zuwa."

Ture kanshi tayi a cinyarta tace.
"Aman! Tashi bana son shirme kazo ka min bake bake akan cinya da Allah ya baka haihu ai da jikokina zan ɗauka tashi nayi bakine."

Dakyar ya buɗe idanunshi tar akan Rahilah, gyara kwanciyarshi yayi ya sake lumshe idanunshi, wani bakon yanayi yake ji na daban.

"Ina wuni Hajiya, Ya gida" Na gaida hajiya falmata.
"Lafiya lau, ya Malama Hasina? Da jikin Malama Atika."

"Alhamdulillah, humm dama aikinkine umma ta bani toh na manta ne dan tun safe ta bini na kawo miki, amma sai na lura kaman baki zo ba." na faɗi haka a takaice,
"Eh wallahi mai gidane ya dawo, jiya toh kuma sauran Yan matan da nake bari suna makaranta shi ya hanani zuwa."

Jinjina kaina nayi sannan na buɗe jakar makarantana na fito mata dashi, na mika mata tare da mikewa zamu bar gidan,

"A'a da wuri haka nagode, amma ga aikinta nakice mata inji Iyayen Zakiya, daga zari'a suna gayyatarta walimah auren zakiya naso da naje yau da kaina zan bata sakon, amma ki bata hakuri bikin saura sati biyu."
Ture kanshi tayi akan cinyarta aikuwa ya tura bakin da cewa.
"Mami zata karya min wuya, tun bada ga jikokinta ba."

Juyawa yayi ya tsare Rahilah da ido, itakan bata san yanayi ba dan game take a wayarta.

Ni kuwa mamakin yanda yake iya kallon mutune haka ya bani, basar da abin nayi na cigaba da leka game ɗin rahilah muna magana kasa kasa, tare da sake dariya.

Fitowarta yasa muka mike, mika mana wani jaka tayi, me ɗauke da tambarin Wani mall na dubai, sai ta sake bamu aikar umma shima a wani jaka daban tace.
"Wannan na farkon nakune ku uku, wannan kuma na Malama Hasina ita da Malama Atika, akwai katin bikin a ciki, idan nasami shigowa gobe zan mata bayani, ga wannan ku rike kuɗin napep."

K'in karɓan kuɗin mukayi cike da kunya, Rahilah tace.
"A'a don Allah ki barshi faɗa umma zata mana, kiyi hakuri,"

"Lallai kuwa toh ku zauna babu inda zaku je tunda bazaku amsa ba." ta faɗa mana hk.

Babu yanda mukayi haka muka karɓa kaman zamuyi kuka, godiya muka mata sannan muka bar gidan.

Sai a lokacin ya buɗe idanunshi ya gyara kwanciyarshi, yace.
"Mamie!"
Sai kuma yayi shiru bai kuma magana ba, tasan halinshi shi yasa tace.
"Yaran Malamarmu ne, ita mai nikk'af a fuska itace maryam Sajida, sai ita ɗayar Yar kishiyar malama ce, Rahilah"

Gyara kwanciyarshi yayi ya cigaba da lumshe idanunshi, sautin muryan Rahila na yawo a kunnenshi, juya bayanshi ya saka hannunshi a kunnensa yana yaki da zuciyarshi.

*Ina dukkansu ma yaudaranw basu san kome ba sai kyalkyale banza awaje da zaran sun shiga ciki su xama kaman jakuna*

Hira sukayi sama sama har Mahaifinshi ya shiga, Dr Mahmud Mandara, zama yayi cikin nutsuwa tare da zubawa Aman ido cikin harshen shuwa yake tambayar, Hajiya Falmata mike damunshi.

Dariya tayi tace.
"Hali a jikin rai, kazamar matarshi yake tunawa."

Juyowa yayi cike da jin ba daɗi yace.
"Kaiii Mamie In-law ɗinki ce fa, itace kazama, toh ki nemo min mi tsafta."

Dariya Dr Mandara yayi kamar me yace.
"Falmata kinji ba, yana kalubalartaki na kiran Hindu kazama, toh ni dai babu ruwa."

Mikewa zai bar falon,
"Aman ashe cigaban da kuka samu kenan bamu sani ba, ɗazun Alhaji Muh'd Yunus yake faɗa min ds muka haɗu a fadar zazzau, wai gwnatin naija tabarku ku buɗe kamanin software."

Murmushi Aman yayi cike da jin daɗi. Yace.
"Abba Nasaran ba tamu bace mu ɗaya, jigon Nasaran Mai Nasarane, Abba kaga kuɗin da ya narka ne, kashi 59% na shine kashi 20% nawa, 21% na Ahmad Zailani Bature, Abba da zuwanmu Dubai kome ya rigada ya tsara, babu abinda muka ɓatar namu, Ya Allah ka jagoranci al'amuran Yunus Mai Nasara,"

"Amin" Iyayenshi suka ce, nan yake warware musu halayar Mai Nasara,

Cike da jin daɗi sukayita samu su albarka.

****
Karfe uku, na rana ya isa garin katsina, a jirgi yan kasuwa dama drvn gidansu yasan da xuwanshi, ba tare da bata lokaci ba ya isa inda drvn yake, jikin drvn na rawa yazo ya buɗe mishi kofar motan, yana shiga ya koma gurinshi ya zauna yana cewa.
"Barka da zuwa Yallaɓai, ya hanya."
"Alhamdulillah Malam Nuhu ya iyalanka."

"Muna lafiya, barka da zuwa ashe karaman madam tasan zaka zo shine take ta murna."

Murmushi Ahmad yayi har suka isa dutse tsafe quarts, inda gidan Ambasada Alhaji Zailani Bature,

Kunna kan motar yayi lokacin da aka buɗe tangamemen get ɗin gidan ya nausa hancin Motar ciki, tunds suka ga mai gadin basu ga kowa ba, mai gadin na rufe kofar shima yabar gurin,

A hankali suka fito ya kwashi wayoyinshi da jakar computer ɗinshi yayi cikin gidan.

Yana tura kofa, balloon na fashewa akanshi take wasu kananun abubuwa masu kyali suka zobo mishi,
Yana cikin mamakin haka suka shiga,wakar karin shekara suka shiga mishi, cike da mamaki yaga Yarshi rike da,cake yar kimanin shekara uku,.
"Happy Birth Day Dadda."

Durkusawa yayi gabanta, ya hure wutar jikin cake ɗin sannan yace.
"Thank kyau My ChuChu."

Yan uwanshi suka shiga murna da shewa, godiya yayi musu ya ɗaga kanshi step inda yake jin takun Mahaifiyarsu sanye take da doguwar rigar super wax, hannunta na dama rike da, casbi da 40 rabbana,
Takawa yayi har inda take, ya ɗaura kanshi a kafaɗarta, suka sauko tare.
Zama tayi a kujeran mai cin mutane uku, zuwanshi katsina yasashi manta wasu abubuwan ns ɓacin rai da ya kunso, a gurin Gimbiyarshi hafsat.

Sukayi kanenshi aka yanka cake, aka kaiwa masu aikin gidan da akayi murnan tare dasu, sai da suka nutsu ya kalle Mahaifiyarshi yace.
"Ummi !"
Zuba mishi ido tayi cikin nutsuwa tace.
"Ina jinka Deedat"

"Ummi auren zan kara."
Yanda yayi magana a sanyayya ɗauka baida gaskiyane,

Tausayi da soyayyar ɗanta, suka mata diran mikiya, san bata son ta tursassashi, akan abinda Matarsa take musu dan a haka ma bashiri suke ba, ina kuma ina ta goya mishi baya yayi aure murmushi tayi irin tasu ta manyan tace.
"Idan babu damuwa kayi hakuri mana, duk abinda hakuri bai bada ba, toh rashinsa bazai bada ba ka mata uzuri har zuwa nan da wani lokaci, idan bata sauya ba kana da damar yin kome."

Shiru yayi ya rasa yanda zai mata bayanin halin da yake ciki,musaman yanda rena danginshi da shi kanshi, rike chuchu yayi yana kallonta cike da tausayi kiran sallah yasasi zuwa masalacin dake jikin gidan.

****
"Toh Yau matarce a zaria, lallai abu yayi kyau, mi kika kawo na ɗaurenmu."

Ware ido huda tayi tana dariya tace.
"Alhaji nice ma zan kawo maka, kayan auren taɓ na fasa."

Dariya suka sannan ya kalleta yace.
"Kije gida ina zuwa, kinji."
Haka Alhaji Muh'd ya turo Huda gida.

****
Fitowa Fareeda tayi daga tayi ta rike da wayarta, akunne waya take akan kayanta da suke da da shigowa daga, lagos.

"Allah Managa baxan baku ba ai wanca da na baku biyani kuɗina ba, taɓ kuyi hakuri kawai wannan karan nima kayan bazu zo min da sauki ba, balle na bada bashin da bazai fito ba."

Tana gama faɗar haka ta kashe wayarta kallon Hasana tayi, tace.
"Sameer bangashi ya fito ba,"

"Ai tun ɗazun ya tashi yake tambayarmu ina Yayarshi shine muka ce mishi sun tafi zaria da alhaji shine ya koma ciki yana kuka."
Tsaki Fareeda tayi cike da jin haushin tafiyar da Mai Nasara yayi da huda ba tare da Sameer ba ai ko babu kome, Sameer ɗin shine magajinshi na gaba, ba Y'a mace ba dan gidan wani zata.

D'akin yaran ta wucce ta sameshi yanawa

4 / 64