Matar So 1 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   36 / 64

105K to 108K   out of 190.6K words

nutsuwa iya tarerayar Miji, kulawa uwa uba bashi dukkannin abinda yakw bukata kuma zata tashi akan tsarin da ya kafata, duk yanda ya koya mata haka zata mike, babu gardama ko reni, kuma bazan ɓoye maka ba nayi farin cikin nima maka ɗaya daga cikin Yaran sabida zata yi kokarin sauta maka ɗabi'arka wanda matanka suka gaza gyara maka dan da ace tun fil azal kasami macen da ta mikar da kai, da babu amfanin tara mata kayi kokarin kaje kaga Yarinyar da aka zaɓa maka, karkayi tunanin an shiga persional life ɗinka ka duba al'amarin da idon basira."

   Taɓe baki yayi cikin ko in kula yace.
"Mu bar maganan kawai." murmushin takaici Ahmad yayi  ya mike tare da zira hannunshi cikin aljuhun rigarshi yace.
"An jima mai walda zai zo ya duba get ɗin."

           "Duk ɗan iskan da yazo min sai na saka yan sanda sun mishi rashin mutunci, jarabarsu ta mata ya kawota kuma ta bar gidan so ni bana kaunar damuwa."

  Mikewa yayi yabar ahmad a tsaye ya shige abinshi fita ahmad yayi, zuciyarshi na mamakin halayar Abokinsu mutum sai kace mai tambutsai, koda ya isa gidanshi kintsa kanshi yayi cikin waganbari darka blue tare da takalminshi haf cover baki sai hularshi itama black, ya fito cikin wata prado black sai ɗaukar ido take,
       Turare kuwa bai san wanda ya bulbula ba, ya kwashi wayarshi ya fito tare da rufe gidan.
  Yana shiga motar mai nasara na kiranshi manna wayar yayi a kunne yace.
"Ina jinka."

   "Ina jiranka kazo muje naga jaririyar da ake maganarta."

    Katse kiran yayi Ahmad ya sakw murmushi yace.
"Munafiki zaka sani"

  Sannan yaja motarshi zuwa anguwar sarki yana shiga gidan ya sameshi akan kujeran hutawarshi ya zauna, horn yayi mishi dakyar ya ɗago kanshi sannan ya mike shigowar motar makarantarsu Huda yasashi tsayawq dan ya kwana biyu bai ga yaranshi ba, da gudu mufida ta fito tayi kanshi ɗagata yayi sama yace.
"Hajiyata kin girma yanzun samee kawai zan na ɗagawa sama."

    Cike da kishi ta kalli Uban tace.
"Dama ai mamanshi tace baka son mu."

  Fuuuu tayi cikin gida, Huda ce ta karaso tace.
"Daddy barka da dawowa, akwai magana idan kadawo dan naga Uncle Ahmad yanw jiranka,"

  Murmushi yayi ya shafa kanta cikin jin daɗi yace.
"First lady. Idan na dawo sai kixo kinji."

  Gyaɗa kanta tayi ta tsaya har ya shiga mota, tana ɗaga mishi hannu,

  Murmushi yayi cikin jin daɗi yace.
"Duk namijin da yayi dace da Huda yayi sa'a a rayuwarshi."

       "Bak'in tuwo mai fida farin tuwo kenan." Inji ahmad,

    Sun isa kofar gidanmu, muna ciki aikin abincin dare, sai ga yaro ya kwaɗa sallama "wai Maryam Sajida da Rahimah sunyi baki a waje."

        Ruwa ne a hannuna bansan lokacin da ya kwaɓe ba, a tsorace nace.
"Kaii Nura anya nan ne."

        "Kaii jeka abinka, kace suna zuwa."

   Inji Mama amarya,
Bansan wani irin tsorone ya shigeni ba, amma na tsinci kaina da fashewa da kuka, umma tana lazimi tana jin kuka na amma ko a jikinta, tsaki Mama amarya tayi cike da ɓacin rai tace.
"Na rantse zan zabga miki mari sakarya kawai zaki wucce ki wanke fuskarki ko ya-ya."

             Kallon Rahimah nayi tafito fiskarta tsaf har da kara kajol a cikin idanunta ni kuwa kuza kuza na ja hijaɓ ɗina na fito,

Fita mukayi ina bayanta tana gaba har kofar gida, Ahmad na jingine  jikin motar shi kuma yans cikin motar, gaishe shi Rahimah tayi nima daga bayanta na gaishe shi.
"Wacece Maryam Sajida."

         Janye kanta tayi daga ɓoyar da nayi a bayanta, sannan tace.
"Ko zamu iya shiga cikin gida."

     Murmushi yayi cikin nutsuwa yace.
"Baki da case, Rahimah Hassana ko?"
  D'aga mishi kai tayi haka suka wucce suka barni ds ɗan iko a waje, tunda muka fito ya ɗago ya kallemu bai kuma ɗaga kai ba,sai da yaji  gurin yayi tsit sai masu wuccewa, sauke glass ɗin motar yayi yana kallona taɓe baki yayi, bai kuma magana ba nima kuma ban kalleshi ba,

         Can naji muryanshi yace.
"Mate ɗinki suna kokarin zuwa jami'a da burin cima nasara ke kuma kina nan kina tunanin aure,zan baki shawara kice baki sona dan ni banga mace a gurin nan ba, sai kwaila."

   D'ago kaina nayi idanuna na cika da kwalla, tsuke fuska yayi tare da zabga min harara ya kauda kai taɓe baki yayi *ga irinta nan wai matar da zaka aura itace take kuka tsabar shagwaɓa*

        Kankance idanu yayi yace.
"Keee shigo mota."

         A razane na kalleshi tare da girgiza kai kwalla na bin fuskana muryana na rawa nace.
"U..m..m..a!!!"
         Fusata yayi yace.
"Kishigo ko nafito na ɗaukeki."

  Zaga ɗaya gefen nayi jikina na rawa na shiga ban rufe kofar ba.

       Wata uwar tsaki ya buga wanda yasa ni cusa kaina cikin cinyoyina ina shashekar kuka.

           "Ki min shiru ko, na miki rashin mutunci."
  Haɗiye kukan nayi naki ɗago kaina.

    Tunda na shiga babu abinda ya kuma ce min har su Ahmad suka fito fiskarsu a sake alamun, kwalliya tabiya kuɗin sabulu, kallona yayi yace.
"ki ɗago kanki ki kirkiro fara'ar dole dan bana son abokina yasan kinyi kuka, idan haka ta faru zan baki mamaki wallahi."

    Haɗiye kuka na nayi na shiga murmushin dole, bai kalle ni bs yace.
"Get out."

   Kamar zan kifa nayo waje, har kaina na bige jikin kofar motar sai da idanuna suka sake hada kwalla rike gurin nayi, ina mulmulawa, da sauri Rahimah ta karasa dai dai ina ɓoye ruwan hawayen da suke shirin zubo min,

        "Sorry Sajida, kin buge sosai ko?" Inji Ahmad,

        Murmushin yake nayi dan idanuna sunyi ja, dan mugunta ko lekowa bayi ba.......
[4/3, 7:56 PM] Addah Ramlah: 🌹🌹🍀
         *MATAR SO*
                 🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Dedicater To Hafsat Abubakar💋

     _Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

*BOOK 1👈*

*Page...12*

Ganin Ahmad yayo kaina kaman zai taɓa ni yasashi fitowa, wani tsare gida.
"Mr Bature don't dare touch her."

   Cak Ahmad ya tsaya cike da mamaki, for the first time ɗago idanu yayi ya kalle Mai Nasara, aikuwa yasake tamke fuska, cikin wani irin iko yace.
"Maryam zaki wucce gida."
    Jikina ba laka, na shige Rahimah zatabi bayana Ahmad ya tsayida ita, buɗe bayan motar yayi ya fito mata da tsarabar da ya kawo daga, china sai wanda Umminshi tabashi ya kawo mata, dakyar ta amsa sabida tsoron iyayenta.

              Ganin haka yasa Jikin mai nasara yayi sanyi, koda rahimah ta shige cikin gida, cewa yayi.
"Kaiii ni store."

         Kallonshi Ahmad yayi zai yace.
"Kana son Yarinyar kenan irin wannan kishin?"

           "Ko ɗaya bana sonta bana jin zan iya sonta kawai naga rashin dacewar kane nason taɓata, da fatan ka fahimce ni, batun kishi ni baya cikin agenda ne, dan banyi Imani da akwai soyayyar da zata sani kishin wata aba ba, musaman wannan jaririyar wacce komi kayi mata sai kuka." Ya faɗa tare da kauda kanshi.

               Sahad store suka tsaya koda suka shiga, tsayawa yayi yana kallon kayan a hankali ya shiga min sayayya kamar hauka,  sai da  Ahmad ya dakatar dashi sannan suka biya kuɗin, kallonshi Ahmad yayi cikin nutsuwa yace.
"Ni ban gane ba, kana nufin duk wannan shirgin babu so a cikinshi."
           Cak ya tsaya da wayar da zaiyi da Aman yace.
"Amma kai kan anyi ɗan kutumar uba, Mi zan so a jikin wancar abar ne nama fasa kai mata."

      "Ai baka isa ba, sai munje dan Ubanka." haka suka kaure da faɗa har kofar gidanmu sannan suka kira wani yaro suka mika mishi kayan da yayi mishi nauyi suka sake kiran wani suka bashi, tare da ɗan abin hasafi.

   Yaran suka kwashe kayan suka bar kofar gidan,

     .......
Tunda muka shiga gida nake haɗiye kukana, har nasamu damar shiga ban ɗaki, kuna fanfa nayi tare da fashewa da kuka na dafe goshina, nace.
"Ni Maryam Sajida mike shirin faruwa dani ne? Haka daga zuwanshi sai matsala na shiga uku.."

      Kuka nayi sosai sannan ina gamawa nafito bayan na wanke fuska nafito amma naki yarda nayiwa kowa magana, kayan Rahimah muka shiga buɗewa muna tayata murni nida Aunty Gausiya,, muna cikin haka sai ga yara da nikinnikin kaya wai nawa.
      Aikuwa Umma ta fara faɗa sosai ita bata so, abinda suka kayi mana kiran mamie tayi ta faɗa mata, dariya tayi kawai tace.
"Kyautatawa ne, ba renin bane"

            "Nidai don Allah su daina nafi son, mutunci fiye da kashe kuɗin nan Allah yayi mana jagora."
    Haka suka katse kiran, tare ds girmama juna.

          .......
  Zaune take a gaban Uwarta tans ruzga kuka ɗago jajjaye idanunta tayi cikin kuka tace.
"Ammy kishiya fa, taya zan bar shi ya kwana da wata bayan ina ɗauke mishi lalurashi."

    Harara kannwarta tayi cike da takaici tace.
"Madalla wani shege ne zai ajiye mace irinki kina juyashi son ranki, idan yazo kice kar ya taɓa miki nonuwa sabida ke matar aljanna ce an halicce daga suffa na musaman gwara yayi auren, tunda kika gaza rike y'ar cikinkin Aunty na tattara al'amarinki na watsa gefe Allah yasa yarinyar da zai aura ta rabaki dashi har abada, kina ji kina gani mijinki yafi karfinki."

   Tana gama faɗar haka ta juya tabar gidan ranta a ɓace.
      Kuka Hafsat ta cigaba dayi kaman zata cire ranta duk iskanshi da takewa Ahmad tana masifar sonshi.
" Hmm kiyi hakuri ki koma ki zuba mishi ido ni kuma zan san abinyi" Inji uwarta knn.
         ****
     "Hmmm namiji ba amana, ya kusan wata biyu kenan tunda yayi aure ya suka tafi da matar,ku bani shawara." inji Hindu a grp ɗin zubar gado.

            💃💃💃💃
    "Kice ansha dake kenan in nice kashe amaryan da mijin zanyi dan bazan raba makwanci da kowacce shegiya ba."

         "Kaiii Nancy_Cool wannan ba shawara bace, kawai ki bata hakuri amma kyace ta kashe mijinta da kishiyarta." Inji Oum Walda,

         Kafin kace me grp ɗin an  sake hira, wasu da shawaransu maikyau wasu, mara amfani.

          Can Nancy tace.
"Mrs Mandara ki bamu hoton shege mugani."

    Jikin Hindu na rawa ta turo musu motar ranar wuninsu Rahilah.

           A cikin min 1 sama da mata arba'in suka buɗe,

      "Laaaaa! Malama Rahilah ce kishiyarki kuttt ta kare miki Mrs Mandara dan kin rasa mijinki." Inji Farisa,

       "Kuttt Yar gidan Malama Atika kan uba dama itace kishiyarki babban bula uba, kuma ance ya tafi da ita kasar waje wani hauka ne yasa kika haɗa miji da Yaran gidan Malama hasina, duk cikin yaransu mutum ɗaya ce taki zaman aure amma tana cin bakar izaya, Malama Rahilah kuwa hmmm wayayya ce dan tafi yan uwanta rawan kaii kedai ki jata a jiki ku zauna lafiya matuƙar kika ce zaki shiga ki fita wallahi karshe kece zaki rasa mijinki dan Uwarsu a tsayw take akansu kuma bazata taɓa barin a cutar mata da yara ba, shawara kyauta..."

         Ai duk wanda yasan Umma sai da yayiwa Hinduh kashedi da karta fara ɗaga hankalinta da nufin cutar da rahilah.

   Can wata maman dady tace.
"Ku da kuke bata hakuri kun manta Shi mijin ɗan Hajiya falmata ne, fa kuma auren ita Hajiya falmata ta nima mishi, indai har mace irin hajiya falmata zata nimawa ɗanta mace daga gidan Malama hasina ku tambayi mrs Mandara miye matsalarta da mijinta har uwar miji ta nima mishi aure, kiyi hkr@ mrs Mandara tayu ke baki sanni ba amma ni nasanki wallahi babu na mijin da zai iya da halinki kuma baxaki fahimci haka ba sai kun zauna guri ɗaya da Rahilah..."

    Aikuwa Hindu ta fusata ta fara rashin mutunci sosai.

      Manna mata hauka sukayi kowa ya samfee.
        
             ****
   Bacci take idan kaganta zaka rantse irin halfcas ɗin nan ne a cikin wata biyu da barinsu gida tayi wani kyau ga kibar da ta haɗa, kumatun nan masha Allah, sake jan bargon tayi sosai ta cigaba da baccinta, Rahilah knn yanzun ko fita yawo bata so bata da wani aiki sai bacci, dan ynx bata da wani aiki da ya wucce bacci. Ga ɗan zazzaɓin da ya tasotaa gaba shi ya hanata walwala, yana tsaye akanta yaye bargo yayi, abinda idanunshi ya gani yasashi haɗiyar yawu.
    
   Jin babu bargon yasata buɗe idanunta akanshi ai zubur ta mike, tayo kanshi tare da faɗawa jikinshi, tana goga fuskarta a kirjinshi riketa yayi yace.
"Yau zamu koma gida, naga zazzaɓinki yaki sauka."

        Ɓalle mishi  ɓotir ɗin rigarshi ta fara, rike hannunta yayi cike da damuwa yace.
"Baki da lafiya, kinji yanda jikinki yayi zafi kuwa don Allah kiyi hakuri nima azumi nake.."

          Kuka tasaka mishi tare da tsaga rigar baccinta jikinta na rawa ta shiga zuke mishi zip ɗin wandonshi, yana tausayinta amma ita sam bata tunanin haka, janyoshi tayi suka faɗa gadon sannun a hankali take binshi karatun da ya koya mata take mishi bitar kowani layi da kowani shafi da aya, sai da ta kawo mishi, cike da damuwa yace.
"Miye damuwarkine ynz da son Ayi make love dake."

     Idanunta da suka kankance ta buɗe cikin rawan murya tace.
"Wallahi ban sani ba, amma kayi hakuri bazan kuma damunka ba."

    Komawa gefe tayi tare da fashewa da kuka, tana dafe maranta wanda take jin kamar zai fashe, tausayinta yaji tare da zuba mata ido cikin nutsuwa ya xare kayanshi yayi mata rumfa da kirjinshi,  daga nan ta lumshe idanunta kwalla na zuba daga cikinsu.
                    Duk wani abinda yasan zai kunnata sai dayayi, kuma cikin dace yasamu har tasake dawowa yanda ta fara, jikinshi na rawa ya ratsata, kallon fuskarta yayi wanda yanuna alamun hakan take so, shi kuma jin yanda ko ina na jikinta yayi masifar zafi har inda yake yasashi sassauta mata yabi da ita a nutse har dukkansu bukatarsu tabiya, kafin ya gama dai daita kanshi bacci yayi gaba da ita,   komawa gefe yayi yana kallon fuskarta cikin nutsuwa yaga yanda tayi fayauuu sai yar ramar da ya bayyana a face ɗinta ga kirjinta sun cika sosai,  
Dafe goshinsa yayi yana kallonta wannan shine azuminshi na uku da yayi tana karya mishi dake ba farillah bane sai bai wani damu ba, mikewa yayi ya shiga ban ɗaki yayi wanka ya fito, ya shiga haɗa kayansu tsaf, sannan ya shiga ya haɗa mata ruwan wanka, cak yayi ban ɗaki da ita buɗe idanunta tayi ta fara mita,
"Ni wallahi bana son haka, kuma sai ka kara min karatun dan bai isheni ba."

                  Zaro idanu yayi yana mamakinta, bai kulata ba sai ma taimaka mata da yayi har ta gama wanka suna fitowa ya direta a bakin gado shiryata yayi fuskarshi a murtuke dan ya lura sam bata damu da kanta ba, yana gamawa yace.
"Idan yayi miki muje.."

    Mikewa tayi sanye da doguwar riga, ta fara takawa a hankali har suka bar ɗakin lifte suka shiga tana kallon yanda ya ɓata rai, rungume shi tayi ta baya tare da sake kuka, juyawa yayi ya rungumeta cikin rarrashi yace.
"Baki da lafiya, yawan rough sex zai baki matsala ki bari muje gida sai muga likita kinji."

             Lafewa tayi jikinshi har suka sauka, kasa buɗe kofar yayi suka fita daga hotel ɗin motar da zai kaisu, Airport na jiransu.

      Tunda suka shiga ta kwanta a jikinshi har suka isa airport ɗin, daga nan suka zauna har jirginsu ya fara ɗiban mutane.

              ****
        Yau muka fara waec cikin nasara muka fito, dake mun fara da biology practical,  ni ɗaya na dawo gida ina kutsa kai sanye da hijab da nikk'af ɗina nasamu mata a cike.

     Juyawa nayi na koma ta kofar falon Malam, na shiga akwatina guda uku na gani ɗaya purple, ɗaya Buberry sai ɗaya pink,

   An ware kowani sit sai hira suke da barkwace har suka mike da niyyar tafiya, abinda na fahimta shine kayanmu aka kawo, ni da Rahila da Rahimah.
   Dan naga har da yan uwan Mamie,

            Bayan fitarsu nima nafito, ganin Aunty gausiya na shigar da kayan, na kauda kaina.

    Zuciyata na cigaba da bugawa.

             Ganin naki kallon idan kayan yake yasata  kallona.

       *****
     "Daddy kacewa Momy tayi hakuri nikan bazanje bodin schl ba don Allah fa." Inji Huda tana matsar kwalla.

              Shiru yayi dan ya gaji ya rasa yanda zai mata, bayani ta fahimta shareta yayi ya cigaba da abinda yake gabanshi yana jin mikewarta tabar falon, shima ajiye abinda yake gabanshi yayi ya nufi ɗakin Balkisu, zama yayi abakin gadonta cikin nutsuwa yace.
"Ki hakura da kaisu bodi ɗin nan tunda basu muradin haka."

            Juya idanunta tayi ta sauke akan fuskarshi, taɓe bakinta tayi sannan tace.
"Ai nagama magana, ana dawowa hutu zasu wucce turkish sai dai suyi hakuri."

    Sam shi a rayuwarshi baya son musu ko taurin kai, shi yasa da yaga ta kafe dan ba jinsh zatayi ba ya bar mata ɗakin.

     Taɓe bakinta tayi cike da iko tace.
"Wallahi tafiya zasuyi."

               Yana komawa falonshi ya turawa kowacce dubu ɗari shida shida, ba tare da yayi musu bayani ba,

       .      Kamar an jefota haka ta shigo tana kallonshi cikin niman karin

36 / 64