ido nayi tare da ɓata rai nace.
"Wallahi kai kam, anshiga uku dakai zan gudu gidane abuna"
"Haba dagske Yan mata. Har nafi keda kike ririkeni tare da kuka faɗa min miye sirrin kukanki nan ne."
"Ai kaima kanayi, ranar har ce min kai na faɗi nawa nake so kabani, ka bani sabuwar motarka da kasaya. Ka ban...."
"Hmmm karya dai haramune."
"Eh nasan haka zaka ce"
Daga nan kuma yaren ya sauya irin wanda ya ɗaurani akai, toh mi zance mi kuma zan iya nima karamar munafuka, son mijina nake wanda yasani gaza fahimtar yana cutar dani ko baya cutar dani burina kawai na faranta mishi koda ni zan kuntatta kaina.......
*Bayan wata hudu*
Wanda ya haɗa da watanin baya muna da shekara kusan ɗaya da aure dan ga shi mun fara hango watar azumi. Haihuwar Rahimah yasa Yan uwana suka tasoni a gaba ko bani da lafiya ne.
Nace lau nake lokacine baiyi ba. Bayan suna dake, Y'a mace ta haifa aka samata suna Mama Amarya Atika, sai muna kiranta Hibbatu.
......Muna zaune a falonshi kaina bisa cinyarshi kallonshi nayi cikin damuwa nace.
"Daddy kasan an dame nida maganar rashin haihuwa."
A tsorace ya kalleni cikin yace.
"Toh miye dan baki haihu dawuri ba."
"A'a Ya hayat da Aunty Hamdiyya sunce na sami lokaci nazo asibiti a dubani kasan Ya Hayat likitane, Aunty kuma Nurse....."
"Babu inda zaki, indai ba shishigi zakiyiwa Ubangiji ba miye sai kinje asibiti nidai abinda nasani, ki kara kaimi gurin kwanciyarmu sai kiga kin sami baby ko Jinjirar mata na."
Da wannan muka rufe hiran dan take ya shagalatar dani, wani batu dakyar muka shige ɗakinshi.
Haka rayuwarmu tacigaba da tafiya cike da abubuwan al'ajabi, kwatsam daf da azumi sai ga tafiya ta kamashi zuwa canada, duk ya haɗamu ya tambaya wacce zata rakashi, Fareeda takawo uzurinta, Aneesah ma haka, karshe balkisu tace.
"Kaima dason ɓatawa kai lokaci ka ɗauki maryam kayi tafiyar da ita, ba ɗa ba ciki mi kuma zaka damu kanka da nimar yar rakiya. A dawo lafiya Allah yasa ayi farar tafiya a tafi babu a dawo da..".
Dariya suka saka, irinta shakiyanci. Dukda ba wani shiri muke ba amma ynz babu wani tashin hankalia zamanmu, wani lokacin duk ranar girkin balkisu ce mishi take bata dalafiya yaje gurina kawai. Kuma hk zai zo.
Wannan tafiyar ta gaggawace, dan haka nice na shirya masa kaya, na haɗa da nawa.
Washi gari muka bar kaduna zuwa abuja acan muka tashi.
Mun isa lafiya, sai dai bai da nutsuwa kullum yana waje gurin kanfanin da zasu haɗa gwiwa da wasu mutane, sai da mukayi kwana uku ranar ya dawo a ɗimauce, sakamakon ganin wata shaiɗaniyar budurwa a gurin meeting ɗin, ko kallo bata isheshi ba. Ya dawo gida sai da yayi wnka ya huta sannan ya fara niman huccw gajiyarshi ta asali. Sai da yazo kan point ɗin ya shiga niman maganinshi bai samu ba kamar zaiyi hauka gashi yana bukace, dan dole yayi haka zuciyarshi cike da wasi wasi.
Koda ya gama kallona yayi yace.
"Maryam yaushe kika gama period ɗinki."
Kallonshi nayi nace.
"Da sauran lokaci banyi ba tukun."
Gyaɗa kanshi yayi ya faɗa wanka, tun daga lokacin ya rage fitinar da yake, sai kuma ya shiga taka tsantsar gurin mu'amalarmu.
Har ya tambaye ni banga cream ɗinshi ba, nace a'a.
Haka kawai naji ina zargin amfanin cream din, haka muka gama abinda ya kawomu.
Muka dawo gida, ni da muka dawo sai na ɗauki hoton kwalin abu a wayata zan turawa Ya Hayat ta tambayeshi sai na manta.
A haka mukayi azumi, inda na tsananta Addu'a Allah ya bani haihuwar nima na huta.
Kwatsam ranar muna hira a grp ɗinmu na yan yan uwa, na tura musu hoton da tambaya cewa wata kawata ce take son sanin miye amfaninshi kuma.
Dogon sharhi Ya Hayat ya turo min da cewa ai cream ɗin na hana ɗaukar cikine, da kuma bayanai da Aunty Hamdiya tayi min, ajiye wayar nayi na koma ɗakinshi na shiga duba kwalin nasamu yasaya dayawa. Kaɗa kaina nayi nabar ɗakin zuciyata na zafi. Wato burin Daddy ya cutar dani bayan yana kasancewa dani.
Ban nuna mishi komi ba sai dai gabaki ɗaya na kauracewa bukatar shi, dake azumi ake kuma farkonta sai na tsananta addu'a baji ba gani.
Ana cikin haka yayi tafiyar kwana huɗu, a cikin kwanaki nayi period ɗina nayi har nagama. Ranar da ya dawo ya nemi ne ni kuwa fir naki dama kuma girkin Balkisu ce furrr naki amince masa jin haushi haka yassashi fita zuwa ɗakinta nan yasamu tana up, dole nice yazo min. Nan kuwa nace.
"Ni nagaji bazan iya ba."
"Kamar ya bazaki iya ba?"
Share shi nayi na shige ban ɗaki, nayi wanka sannan nafito. Duk yanda yaso na bashi hakkinshi ki nayi karshe yaci da zuciya, inda ya murɗeni ya biya bukatarshi, sai da ya gama ya koma gefe. Na fashe da kuka nace.
"Dole kayi rape ɗina mana, ga sexer machine kasamu. Bayan ha'intata da kake wai nikam miye na tare maka ne, da ka tsane ni ove kana amfani da cream dan kar na ɗauki ciki ka maidani gidahuma mara lissafi bansan mi nake ba, Allah zai min sakayya."
Shiru yayi cike da mamaki ya akayi nasan da haka. Kai hannunshi yayi zai taɓani na buge na bar kan gadon na shiga bayi nayi wanka.
Tun daga ranar, muka shiga takun saka dashi dan yana taɓa ni zai ji magana marasa daɗi, tun yana jurewa har ya fusata.
Koda aka kusan gama azumi yace na shirya muje zaria kamar bazani ba, haka nashirya muka tafi.
Can mukayi sallah dakyar ya shawo kaina muka dawo kamar da, satinmu ɗaya muka dawo gida, a hankali al'amuranmu suka sauya a cikin gidan dan balkisu ta shigo jikina munayi da ita, har su karatu. A binda batq sani ba zata tambaye ni na bata amsa.
Anyi sallah har da wata guda, a cikin wani dare muka tashi Sameer ba lafiya ciwon ciki da amai, ko kafin su isa asibiti Allah ya amshi rayuwar Yaron,
Tashin hankalin da muka shiga ba iyaka, dan Fareeda har da suma ga sambatu, shima Uban na tausaya mishi.
Yanda mutuwar ta girgizamu yasani na fara wani zazzaɓi da ciwon kai gabaki ɗaya na fita hankalina, a gida Dr Nafi tasami ruwa. Sannan ta ɗiba jinina taje tayi text, sannan ta kawo cikin ikon Allah sakon ya faɗa hannun Balkisu. Dake gidan da mutane har ɗakinmu ina kwance ta shigo ta zauna a bakin gadon ta mika min, takardan kallonta nayi cike da son karin bayani, itama kallon takardan tayi sannan tace.
"Inji Dr Nafi"
Mik'a mata nayi nace.
"Hmm mommy ki buɗe mana."
Kura min ido tayi ganin yanda ta ko ina ya nuna akwai dashen Mai nasara yasata murmushi tace.
"Idan naga sakon ciki mi xaki bani."
"Komi mommy kika gani kina so zan baki."
Sai muka burge yan uwana da wasu mutanen.
Tace.
"Ok nidai abinda tunani na yake hasasho min za'a bani, idan ban son kaina ba."
"Ba batun sonka da kai da kaya mallakar wuya ce."
Buɗewa tayi a hankali ta warware takardan, tana bi a sannu har takai kan gwajin. Cikin sati bakwai cik.
Murmushi take tare da zubdar kwalla tace.
"Koda banyi ɗawainiya dasu huda ba don Allah idan kika haife abin cikinki ki bani shi nima na gwada tawa tarbiyan mana, Allah mai iko Sameer ya tafi Allah ya kawo mana wani Allah yasa sameer ɗin ne."
Da sauri tafita zuwa ɗakin Fareeda da take kwance, zama tayi a bakin gadonta tace.
"Karɓa ki gani."
karɓa Fareeda tayi ta duba, ai bata san lokacin da ta hantsilo ba, tafita da gudu zuwa ɗakina ina kwance ina, kwalla nabi fuskana rike hannuna tayi tace.
"Maryam cikine dake? Alhamdulillah Sameer ya tafi Sameer ya dawo, kaiii Allah nagode maka daka sake azurtamu ta wani hanya."
Fita tayi sai gata da key kamar ba mutuwa aka mata ake zaman makoki ba, tashigo " faɗa min mike so, a sayowa Lil Sameer."
Shiru nayi ina kallonta ta bani tausayi nace.
"Maman Sameer zauna, baki da lafiya bana sha'awar komi,kinga gidan da mutane yau kwana biyar da rasuwa zaki fita."
"Wancan dama ba nawa bane wannan ne nawa."
"A'a Fareeda karmuyi haka dake, nawa ne wnn Sameer idan aka sake samun wani sai abaki."
Rike hannun balkisu tayi cikin kuka tace.
"Don Allahki bar min sameer, dan nayi imanin bazan kuma haihuwa ba, dan an cire mahaifartawa don Allah ki bar min. Kuma nasan Maryam nada babbar zuciya zata barmin itama ko maryam."
Ba Umma hatta Hajiyarsu sun kaɗu da jin musayar kallona Umma tayi sannan tayi min murmushi tana kallon Fareeda, kirjina ne ya buga dammm idan na fahimci Umma nabawa Fareeda ɗan cikina tun baizo duniya ba, sai dai idan na tuna itama Uwa ce tarasa ɗanta tilo sai naji jikina yayi sanyi.
Sunkuyar da kaina nayi. Karshe tazo bakin gadon ta zuba gwiwarta tare da rike hannuna, Hajiya nakalla naga itama kwalla take sharewa tare da min kallon na sadaukar da cikina ga Fareeda.
Shigowa yayi ɗakin ganin abinda ke faru amma baisan komi ba, juyawa Fareeda tayi cikin kuka tace.
"Don Allah kubar min, yaron nima mana."
D'agowa nayi na kalleshi, dan na lura bai fahimci komi ba, ga kukan da Fareeda take ga alkawarin da nayiwa Balkisu sai narasa tacewa.
Sake rike hannuna tayi cikin kuka tace.
"Zuciyarki tana da kyau, baxan iya faɗar alkhairinki dan ki bani ɗanki ba amma nasa...."
"Karki damu Maman Sameer, kowa ya zama shaida na mallaka muku abin cikina keda Mommy."
"A'a maryam nima na barwa Fareeda dan ita zata fini bukatarshi ni inada Mufeeda ke kuma mun bar miki huda ko Daddy."
Dammm yaji kirjinshi ya buga, maryam sajida ce da ciki? Yaushe? Taya haka ta faru? Wayyo Allah na dole nasan abinyi.
Murmushin dole ya kakaro tare da fita a ɗakin, ji nake sam banji daɗin rashin kulawarsa ba,
Zan iya cewa ga baki ɗaya Fareeda da balkisu sun tattara kulawarsu akaina, kamar su amshi cikin gashi ana sanin shi ya tsifo min da fitina zubda yawu amai, kwaɗayi har akayi addu'ar bakwai. Duk wani abinda masu ciki suke so Fareeda na hanya kamar ba rasuwa aka mata ba, ga Umma tana kokarin aiko min da kayan kwaɗayi, Balkisu kuma ana fama da girki karshe dai mikewa tayi ta zama matar gida.
Hmm a bangaren Oganmu kuwa watsar da al'amarinmu yayi, baki ɗaya abinda na fahimta shine yanda Balkisu da Fareeda suke kaf kaf dani, ko abu ya kawo basu bani sai su nima min wani.
Ranar ina jin ana rigima a kasa, tskaninsu su uku dakyar na lalluba na fita sabida jiri da rashin karfi, abinda kunena ya jiyo yasani tsayawa da Mamaki.
"Ina ruwanku da Mata, ehhe idan ba salon munafuci ba kun katangeni da ita, meye alakarku da ita, tunda bazaku bani goyan baya ba toh kufita harkanra."
"Hhhhhhh wllhi baka isa ba, kamar yanda kasani kuka, haka bazan taɓa barin ka zubda kwallar yar mutane kacuce mu Yunus gashi nayi biyu babu, kuma ka kuskura kayi wani abu wallahi sai na faɗawa Iyayenka ta'asar da kamana," Inji Fareeda,
Zai magana balkisu tace.
"Shiiiiiii, karka ce komi ka lallaɓa mu zauna lafiya kuma ka cire kudirinka akan Yar mutane ka bari mu binne abinda ya wucce."
Saukowa nayi ina dafa bango har na iso falon, niman ɗaya daga cikin kujerun nayi na kwanta, ina sauke numfashi. Kallonsu nayi na sake rufe idanuna nace.
"Lafiya kuke ta hayaniya haka?"
Dariya Aneesah tayi sannan tace.
"Eh ana yin hayaniya ne akan unwanted pre.."
"Keee jakar ina ce?" ya buga mata tsawa, sai da na mike zaune ina raba idanuna. Kallona yayi tare da haɗiye yawu dan na kara cika sosai ga kyan da nayi sabida shigar cikin. Kauda kanshi yayi, yabar falon mika min leda Fareeda tayi tace.
"Ga kilish da kika ce kina so."
Karɓa nayi nace.
"Maman Sam na gode"
Murmushi tayi kawai.
Haka zaman gidanmu ya kasance ba daɗi babu komi sai wani rigimar da ake a kasa, tashin hankali mara daɗi. Tsakanina da Mai nasara fushi da hantara, ko kuma yazo yayita kananun magana daga yace ina wari sai karni, sai yace min kazama. Haka zan zauna nayi ta kuka, duk abinda yake ban taɓa magana ba dan bazan iya damuwa ba, muna cikin haka ya tsiro min wani abu karfi da yaji zai zo ya tara min gajiya bata duka ba, na shimfiɗa sai yaga ina kuka wiwi tareda rike cikina sabida azaba da fitina zai kyale ni.
Ina matukar azabtuwa da Yunus dan yanzun ya rikiɗe min ya zama abin tsoro sai masifa wani lokacin kamar ya dake ni yake ji. Duk na rame na fita hayacina kuma ya hana a kira likita ta dubani yace.
"Ai laulayine kowa haka yake yi"
Da zaran naganshi jikina zai hau rawa, ranar da yazo dai turmusheni na jada baya kaman zan hantsila nace.
"Don Allah kabarni wallahi yau bani da lafiya gashi cikina na ciwo."
B'ata fuska yayi sannan yace.
"Ina kike son nakai abinda nake ji."
Yana faɗar haka tare da buɗe tin ɗin maltena ya jefa kwaya a ciki, komawa gefe yayi yana kallona yace.
"Zaki sha?"
Girgiza mishi kaina nayi sannan na cigaba da kallonshi. Tausayin kaina nake dan naga kwayar ba guda ɗaya bace ya jefa har biyu.
Mikewa nayi zan gudu daga ɗakin yana zaune har na fita, bai bi sawuna ba, sai da ya shanye abunshi tass sannan ya kwanta, bayan wani lokaci ya mike sabida fara aikin maganin.
Yana fita ya nufi ɗaya ɗakin yaga bana ciki. Sai ya nufi ɗakin balkisu ya tardani na koma bayanta bai ce komi ba yaje har inda nake ya ɗauko ni.
Kuka nasaka ina riketa nace.
"Don Allah karki barshi ya tafi dani, wallahi mutuwa zanyi."
Rike ni tayi tace.
"Babu inda zata, ni na fansheta kayi abinda yayi maka dani amma banda ita."
Gabanta yaje yana yake yace.
"Bazanyi dake ba, da ita nake so nake muradi."
Fauce ni yayi ya fice dani, ina ihu ina kuka ya sauko dani har ɗakinshi ya wurgani a gado ya ku faɗa min da gayya, kara nasake ina fincike shi bai fasa abinda yayi niyya ba............
[4/3, 7:56 PM] Addah Ramlah: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂
_Fatan Alkhairi Xuwa gareki Rahida Abubakar Manga, bazan manta ukubar da kika sha ba, bazan manta wahalar da kika sha Allah sarki Yau gashi Allah ya maidaki Matar So a gidan Alhaji Usman Fatan Alkhairi Mommy Jaheed😍_
Page....5
Da sanin shi ya buge min ciki, rike gurin nayi, cikin kuka nace.
"Karka zalince ni Daddy babu abinda zuciyata tasani sai sonka daddy idan laifi na maka ka faɗa min zan gyara amma wannan hanyar da kake bi dani zai haifar maka da ɗan danasani, bani da karfin da zan ɗauki laluranka ynx ada can ma ya aka da iya lafiyarka ynx kuwa akan idanuna kake shan magani."
Tsaki yayi ya fara niman kusantata, rike shi nayi ina girgiza kaina nace.
"Haka zaka zo min kamar yanda dabobi ke zuwa ga shashinsu, babu ɗan aike bal..."
Shiru nayi sakamakon jin yanda ya shige ni, ji nayi kamar an cusa min karfe a jikina, kura mishi ido nayi na daina kukan kuma na daina rokonshi, sauko da kanshi yayi zai haɗa bakina da nashi na kauda kaina, karshe cikin kunena yasaka harshensa. Idan nace ga iya adadin lokacin da ya ɗauka nayi karya sabida tun ina fahimtar lokacin da yake har takai ko numfashina tsayawa tayi, ina sume ya gama. Kuna wutar ɗakin yayi ya duba ko hakarshi ta cima ruwa, amma ina babu komi a gurin, tsaki ya daki bangon ɗakin ranshi nakara ɓaci, bai ɓata lokaci ba ya haɗa min ruwan wanka yaje ya wurgani a ciki, sannan ya koma gefe yayi wankanshi, ganin har lokacin ban farka ba, yasashi ɗiban ruwa ya sheka min wanda yayi sanadin sake ajiyar zuciyana, lumshe idanuna nayi gurin na min ciwo har da jikina baki ɗaya.
Wanka nayi na fito ina ɗingishi baya dakin abin sallah na shimfiɗa sannan na ɗaura doguwar riga da hijab, sam na kasa furta komi tunda na tadda kabara na tsaya, kuka nake a hankali na ɗauko suratu rahama na karanta suran. Sannan na cigaba da sallah ban iya runtsawa ba sai da na gabatar da raka'a huɗu na nafilla, ina idarwa na zauna nayi kuka sosai.
A nan nakwana da zazzaɓi.
Dakyar nayi sallar asuba, shigowar balkisu da fareeda yasani tashi daga barcin bashin danake. Kallona sukayi cikin tausayawa, Fareeda ta zauna a kusadani idanunta cike da kwalla tace.
"Da fatan kina lafiya keda Babyna."
Gyaɗa mata kai nayi, Balkisu tace.
"Mi kike bukata."
"Tea yaji milo da madara sai low sugar." haka kawai naji yawona ya tsinke. Murmushi sukayi har Balkisu zata fita Fareeda tace.
"Mommyn Yara karki taɓa na kitchn bari nakawo miki wanda nasaya ko amfani dashi banyi ba."
Dakinta ta tafi sai gata ɗauke da katon gwangwanin madara da milo ta mika mata, kallon juna sukayi balkisu ta gyaɗa kanta. Tafita dashi zuwa ɗakinta, a can ta haɗa min ta kawo a katon cup. Jikina na rawa na amsa ina sha har wani gyaɗa kaina nake irin mugun daɗin nan nake ji, mai ɗauke da sinadarin garɗi, sai lumshe idanuna nake zufa na keto min tako ina, tass na shanye na kalle balkisu nace.
"Mommyn More."
"A'a maryam kiyi hakuri zuwa anjima a kara ko, kinga ynx sai ki iya amai."
"Don Allah sako mata" Inji Fareeda, haka tafita a falo tasami shi tare da Aneesah, binta ɗaki yayi yaga abinda take.
"Wato ban isa da gidana bako? Ban isa nace ga yanda nake so ba, ku gama shirinku Insha Allah nima ina nawa."
Ko ta tafasa bata ce ba balle a ɗauka fuuuui ya fice.
Har kasa Aneesah ta bishi cikin karairaya tace.
"Akwai wani inyamuru a can hayin rigasa, allura kawai zai mata Wallahi cikin kona wata tara ne buttttt zai waje."
Kallon karin bayani yayi mata nuna mishi waje tayi suka fita a can ta mishi bayani.
*****
Aiki yake amma ga baki ɗaya ranshi a cakuɗe take, tsaki yake akai akai, kallonshi Aman yayi cikin kulawa yace.
"Lafiya Mr Yunus."
Tsaki yaja sannan yayi shiru kamar yanda basu ɓoyewa junarsu matsalarsu sai gashi ya gaza faɗawa Aman gaskiya abinda yace.
"Yarinyar nan ce bata da lafiya nake son zuwa a dubata."
"Ayya Ranar Maman Sayeed take faɗa min ashe Maryam cikine da ita, toh Allah ya raba lafiya. Aini yanzun bakin a sake samun wani a gidana ba, dan ina son tara yara dayawa."
"Kaii kanada matsala haihuwarce za'a kara salon ka tsufar musu da yar mutane, ni wannan cikin maryam ma tausayi take bani dan tayi kankqnta da ciki ga laulayi, dan kar ace zan kwareta ne da na bata shawara a cire ta huta."
Juyawa Aman yayi cike da mamaki, girgiza kai yayi