Matar So 1 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   11 / 64

30K to 33K   out of 190.6K words

buda abubuwan bukatar da zasuyi amfani dashi, a china wayoyi ukune a gabanshi ɗaya ce karama sosai, duk sauran biyun manyane.

              Karamar cikin ce tayi kara ya ɗaga, ya kara a kunne cikin sanyin murya yace.
"Barka da hutawa Alhaji."

       "Yawwa Babana gani a kaduna abin arziki ya kawoni da fatan bazaka watsa mana kasa a ido ba, idan ka sami lokaci kazo gidan da Abokinka aman ya auri yarinya mun gama magana akan sauran Yan matan nida Alhaji Saminu bature Kawun abokinka mun nima muku auren Yan matan kai mun nima maka Maryam Sajida, ita Hassana Rahimah wa Ahmad, nan da wata uku."

     "Hmm" iya abinda ya cewa Alhajinsu knn,

  Yayi jifa da wayar ranshi a ɓace, *Ba dai yan uwan jinjiran da Aman ya aura ba, amma gayen nan anyi ɗan kutm ɗan iskan mutum yajanyo min reno.*
    Abinda mai nasara yake faɗa knn yana nanatawa, karshe kashe laptop ɗin yayi ya mike zuwa ban ɗaki.

          ****
      Tuna baya...
   "A gaskiya Hajiya anci mutuncin yaran nan da mahaifiyarsu, ni dama Bakar nake so mai nasara ya samu ko za'ayi dace ta sauya mana alkiblashi." Inji Mama kilishi.
   
             "Naji bakin cikin abinda ya faru, sam yaranmu aure suke ba tare da sunsan matan suka  dace ba dasu, kalli tijaran da Yarinyar nan tayi gashi abin ya juye mata ta kare da kishiya."
 

   Haka suka cigaba da tattaunawa, har Alhajinsu Mai nasara ya shigo nan suka mika mishi bukatarsu na nimawa mai nasara auren maryam sajida,.
     
    Zama yayi yasa aka masa bincike akansu sannan ya tafi nimawa mai nasara aurenta yana zuwa sai ga kawun Ahmad wanda Hajiya firdausi ta turoshi nimawa Ahmad auren rahimah an tsaida magana nan da wata uku.

          ****
   Bayan tafiyarsu muka shigo gida zama nayi a kusada Mama Amarya kaina a kafaɗarta nace.
" Mama ku barmu muje gidan two mana,"

         Murmushi Mama tayi cikiɓ kewar Yartata tace.
"Babu ruwana, ai kinji abinda Malam yace."

            Shiru mukayi Rahimah ta kalleni kallon geran kayan niman aure nayi nace.
"Mama auren waza akuma."

           Kai tsaye tace.
"Keda Rahimah."
   
    Mikewa mukayi sai ɗakinmu muka zauna, muna jimamin Rahilah ashe namu na tafe.

           ****
     Parking mota Aman yayi ya fito, a hankali sanye yake da london suit, wani dark blue har wani haske yake suit ɗin rigar cikin suit ɗin sky blue, takalmin kafarshi bakine sai a gogon da yake ɗaure a tsintsiyar hannun na arzufane,

          Kwaso kayan yayi ya shige cikin gida, tana zaune a falon ita ɗaya tana cire lallen hannunta ya shigo da sallama, mikewa tayi ta fara kokarin saka hijab ɗinta,

    Sannan ta amsa sallamar tare da cewa.
"Barka da zuwa, Ya Aman."

       Lumshe idanu yayi sakamakon karewa jikinta kallo tana sanye da, doguwar riga na English wear mai dogon hannu, karɓan kayan ta isa gabanshi zatayi ya ajiye a gurin ya rungumeta, tare da sunsunar kamshinta wanda yake tafiya da nutsuwarshi.

   Kanshi ya ɗaura, a kanta yace.
"Barka dai Cutie. Ya kwana biyu ko kiyi kewana, kin barni can inata azabtuwa da kewarki."

         Shiru tayi kanta na kirjinshi, jin sautin bugun zuciyarshi take, a can kasan makoshinsa yace.
"Taimaka min ki cire min wannan kayan nauyin, na gaji sosai."

         Bottums ɗin rigar ta shiga cirewa,  dukkansu kanta asunkuye ɗago kanta yayi ya bata karamin sumbata a goshi, sannan ya riko hannunta suka cire nitie ɗinshi zarewa yayi ya ajiye a gefe, sannan ya riketa sosai yana kallon yanda ta rufe idanunta yanda gashin idanunta dana giranta suka kwanta, sai goshinta suma sun kwanta luff, gwani ban sha'awa.

           "Yunwa nake ji," ya faɗa mata a hankali.
              Sake shi tayi, jiknta na tsuma, sabida kwana biyu haka kawai take jin wani feelings sosai musaman idan ta tuna, ranar da ya rutsata sai taji tsigar jikinta na mikewa,

                Abinci ta haɗo mashi, da duk wani abun bukata ta kawo mishii, zama yayi tayi serving ɗinshi tuwon shinkafa miyar eguse, sai farfasun bindin saniya.

       Zubawa cokalin da tasaka mishi yayi ido kafin ya ɗago yace.
"Plss ki bani naci."

   Mikewa tayi ta koma kitchen ta wanko hannunta, zama tayi ta shiga bashi abincin lomar farko ya rike mata hannu da hakorinshi.

       Sakewa yayi ganin wani shu'umin murmushi da tayi mishi, a haka tayita bashi abincin, daga ya rike mata hannu sai ya tsiri tsotsan hannunta, a haka har suka gama ta kwashe kayan zuwa kitchan, wanke hannunta take sonyi amma sai ta tsinci kanta da lashe hannunta itama tare da tsotse hannun. 

   Rungumeta yayi ta baya, tare da saka kanshi wuyarta a hankali yace.
"Kina son lasar hannunki shine baki faɗa min ba, nabar miki."
   Yana maganar tare da goga mata hancinsa a wuyarta, rike hannunshi tayi gam sabida sakonshi dake shiga jikinta, juyata yayi ya haɗe bakinsu yayi ya shiga bata wasu irin kiss, wanda masu matukar shiga jiki.

                     Zare hajib ɗin yayi ya wurga kasa, a hankali yayi sama da ita, sai ɗakinta ya direta a gado runtsa idanunta tayi, ɓalle shirt ɗin rigarshi yayi ya rufa mata, sosai yake juyata son ranshi,

       Shiru tayi tana rike da kanshi da yake wuyarta, duk tafita hayacinta sabida maganin da Mamie take bata ya gama bin jiknta sosai, wani irin yanayi  take ji, mara misaltuwa dakyar take jan numfashi tare da rumgumeshi.

    Jin karan get yasashi mikewa da sauri ya fita ya gyara kayanshi kafin mamie tashigo, zama yayi kaman maraya har mamie tashigo kallonshi tayi tsaf ta hango rashin gaskiyarsaa kitchen ta nufa taga Hijab ɗin Rahilah a kasa.
   Fitowa tayi ta zabga mishi harara sannan tace.
"Bana ce sai na nime ka ba,"

             "Eh mamie na kawo mata wayartane." ɗaukar jakar yayi a ajiye sannan ya saka takalminshi yace.
"Sai anjima."
"Malam kuɗin turarena"

    Juyawa yayi yace.
"Ai tuntuni na turo miki."

      Fita yayi yana murmushin saura kwana huɗu yayi kidnafi(😹)
    
           ****
   Kusan kwana uku kenan tunda aka kawo tambayarmu da sadaki babu wanda yazo a ɓangare maneman. Duk mun addabi kanmu da tsoro da fargaba, kullum Nasiha Mama ke mana, domin Umma tace tayi mana bata da lokacin mana wani abu,
     Gashi wani tsirfa ada ke mana nasamu lalle,yana gogewa zamuyu wani.

                 .......
     Zaune yake shidasu Aman yana son faɗa musu amma yasan dariya sasu mishi wayar Ahmad ne tayi kara, ya ɗauka, sabida ganin First lady.
      
   Gaisawa sukayi da umminshi sannan yayi shiru sai murmushi yake dokawa, kallon Aman yayi godiya ya shiga zuba mata sannan ya katse kiran.

         Cikin wani irin murmushi yace.
"Kaiii mutumina, ashe mun kusan zama ango, kaji an nima min auren kanwar matanka."
  Tsume fuska mai nasara yayi dan kar ahmad sakoshi cikin zance dariya Aman yayi yace.
"Ina passport ɗin matata, tunda tafiyar ta amjima ce, gara na rike abuna a hannuna. Kafin nasatota."

        Murmushi ahmad yayi sannan yace.
"Ai bani ɗaya bane har da Mai nasara aka nimawa maryam."

Mikewa yayi a fusace zai bar gurin Aman ya ɗaga murya yace.
"Ango jaririya har zaka tafine Allah ya nuna mana karshen miskilanci."

     Ko ɗaga kai bayi ba haka ya shiga motarshi yabarsu a gurin...

            ......Karfe bakwai da rabi yana zaune a gaban Abbanshi suna hira Mamie ta shigo gaisheta yayi sannan yace.
"Mamie ina son kai Rahilah, gida ta gaishesu naga kamar tana kewan gidan."..  

   Shiru tayi kafin tace.
"Eh nima ɗazun nasameta tana kuka amma tace min wai babu kome."
      
   Bari nasata ta shirya sai kutafi.
      Mikewa  ta fita, murmushi yayi sannan yace.
"Abbana nagode da bani wannan shawaran, kaga gashi ta faɗa tarkona."

           "Karka nuna rawan jikinka akan tafiya da yarinyar kawai ka matse."

   Dariya sukayi sannan Abbanshi ya cigaba da mishi nasiha har ta shigo tace.
"Tana falo."

    ok kawai yace sannan ya fita a falon, sanye take da wata faran atamfa, mai jar fulawa da Bakin, hijab dinta fari sai tayi kyau.

      Sakata yayi a gaba suka fita, ya buɗe mata gaban motar ta zauna, sannan ya koma ya shiga, sai da suka biya kasuwar zamani yayiwa su Umma  da mu siyayya, sannan ya kawota har ciki suka ya shigo muka gaisa sannan ya fita nan muka sakata a gaba muna kallonta, ita kuma tana jikin Umma tana shagwaɓa dakyar tashiga ɗakin Mama nan kaman mi, ɗakinmu muka shiga, Inda Aunty gausiya ke ciki duk ta lalace babu me kulata sai Ya Hayat.

    Auntynce take faɗa mata an turo niman aurenmu, sosai tayi murna har da ce mana.
"Yara kun kusan shigowa, yasen  idan aka kama kirjin yarinya sai tayi jinya."

    Zaro ido mukayi cike da tsoro anan take kwankatsa mana, ai kowannemu ya nemi maɓoya dariya tayi sosai har da rike cikinta.
      Karfe tara na dare yazo ya ɗauketa, daga nan airport suka wucce, inda ya mika mata nikk'af, suna isa ta ɗaura suka shiga ciki tana son tambayarshi amma yaki bada fuska,

          Kamansu ake jira, ganin yanda take ɗari ɗari yashi janyota kallonshi tayi a cikin nik'af ɗin yace.
"Kalle hanya"..

           A hankali suka shige cikin jirgin  ta rike mishi riga, zaunar da ita yayi ya ɗaura mata belt, ana gama sanarwa jirgin ya tashi.

   Rike hannunta yayi gam, ɗaura kanta tayi a kafaɗarshi.......
[4/3, 7:54 PM] Addah Ramlah: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Dedicater To Hafsat Abubakar💋

_Idan kinsan baki saya karki karanta sabida na kuɗine, idan kika samu an sato toh karki faɗa min maganar banza dan zan iya miki Allah ya isa, duk wacce ta fitar min Na barta da Allah_

*BOOK ONE👈*

*Page...10*

Shafa fuskarta yayi cikin sanyi murya yace.
"Ki nutsu."

Sake kwantar da kanta tayi, tare da sauke ajiyar zuciya tsavar tsoro ko runtsawa batayi batayi ba har suka isa lagos.
Suna sauka ya shiga kasuwar zamani dake cikin airport ya saya mata kayan sawa sai na ciye ciye, da manyan rigunan sanyi sabida kakar sanyi ake a china,

Tana zaune wata matashiya tazo ta zauna a kusada ita, bata ɗago kai ta kalle yarinyar ba, sai da tace.
""Sannu ko? Kema china zaki?"
Gyaɗa mata kai Rahilah tayi, haka yarinyar tayita surutu, har Aman ya dawo ya zauna akusada ita ya riko hannunta, wanda suka sha gyaran mamie yace.
"Cutie ga abinci."

D'aga nik'af ɗin tayi xata mishi magana, buge hannun yayi tare da dalla mata harara, sunkuyar da kanta tayi, tace..
"Ya Aman na koshi."

Murmushi ya cigaba dayi yana kallon yanda mai nasara yayi crossing leg yana karanta jarida. Cigaba yayi da lallaɓata dan ya fara hango botsarewarta, ta hanyar share kwallarta da yace miye na kuka sai ta sake kukan tana cewa ita kam ya maidata gurin Mamie.

Ajiyar Zuciya ya sauke sannan yace.
"Naji zan mai daki, amma muje kirakani satiɗaya zamuyi kawai."

Can kuwa aka fara shirin tafiya, a first class Vip, suka zauna kome na gurin a tsare yake, bino bini yana kallon Ahmad da ya surkurkuce,

Mutane na gama shiga, jirgin ya tashi nan ma, rungumeta yayi har jirgin ya dai daita asama.

****2:03Pm In China
Karfe biyu da minti uku suka sauka a birnin Jon, na kasar china sanyi ake har da kankara, tun a jirgi yasaka mata rigan sanyi da takalmi safar hannun da na kafa, sai fuskarta yasa mata wani mask, mai nasara na ganin haka ya taɓa ahmad murmushi Ahmad yayi cikin karamar murya yace.
"Na mishi uzuri dan ina ganin ni tawa jaririyar, ɓoyeta zanyi har sai na gama gyara mata sittings."

Taɓe baki mai nasara yayi sannan ya kauda kanshi, koda suka sauka motar wani hotel mai suna royal hotel, yazo ɗaukarsi ɗaya nasu Aman ɗaya nasu Mai Nasara.

Tafiya kaɗan suka isa, hotel ɗin, inda aka shiga ɗiban kayansu zuwa cikin ɗakunansu,a online Ahmad yayi musu booking, makullar ɗakunan yana, hannun masu kwaso musu kaya, koda aka buɗe ɗakin farko nasu Aman shiga yayi da matarshi wacce sanyi ya gigitata, ya kunna room heater.
Kayansu ya karɓa ya jera a wardrob, sannan ya sake labulayen da suke ɗage, tana kwance a dukunkune ɗagata yayi ya ya gyara mata kwanciya ya shiga rabata da kayanta, sannan suka nufi ban ɗaki, wanka yayi mata idanunta a rufe, alola ya fita yabarta tayi, tana gamawa ta buɗe dirowar da ya ɗauki towe itama ta ɗauka kallon kanta tayi, ganin inda towel ɗin ya tsaya, take kunya ya rufeta taki fita sai da ya buɗe yaganta a tsaye.

Riko hannunta yayi ya bata doguwar riga tasaka, sannan ta hau abin sallah tayi sallar asuba, sannan tayi Azahar, tana idarwa ana kawo musu abinci zama yayi suka ci, sannan ya mike yace.
"Zoki tayani shiryawa, zan tafi meeting sai dare."

Mikewa tayi ta ciro mishi wani suit, neavy colour, ta taimaka mishi yasaka, abin dariya sai da yabarta tazo gyara mishi nitie ya taɓo, boons ɗinta a zabure tayi baya cike da fargaba, murmushi yayi ya shafa kanta bayan ta mika mishi rigar saman, janyota yayi yace.
"Ki shirya yau kina da bako."

Yana faɗar haka ya janyeta ya shiga wanka da turaruka, sannan ya ɗauki abin ɗauka ya mata sallama gyara ɗakin tayi, sannan ta tattara sauran abinci takai falon ta ajiye itama shafe jikinta tayi da mai da yasayo mata,

Ta shiga duba kayan da yasayo mata babu rigar arziki, sai dogayen riguna,taso sakawa sai taga rashin dacewar haka, wani riga ta ɗauka mara hannu, ta ajiye ɗaukar bra ɗin da yasayo tayi cike da mamaki tace.
"Dama yasan size ɗina ne"

Haka tasaka bra ɗin mara hannu sai tasaka rigar wanda iya karta cinya sai jan pant ta ciki, gyara gashinta tayi sannan ta ɗauki body perfume ta fesa, ta gyara ko ina sannan ta kwanta tuni bacci yayi gaba da ita,

Bata tashi ba sai huɗu saura ta mike ta faɗa ban ɗaki, bata fito ba sai da alolarta, sallar la'asar tayi tana idarwa taje bakin kofar da ake nocking ta buɗe abinci aka kawo mata karɓa tayi, tazauna a falo taci, tana gamawa ta duba ɗakin ta zakolo alkur'anin a cikin kayanshi zama tayi tafara karatu.

Bata ajiye ba sai da shida da rabi yayi ta ajiye ta faɗa wanka ta gyara jikinta, sallah tayi can ta shaki kamshinsa ɗaga kai tayi, ta ganshi ya shigo, rufe alkur'anin tayi taje ta amshi jakar hannunshi.

Duk wata kulawa da taimakawa ta bashi, dukda hijab ɗinta yayi mishi shamaki zare hijab ɗin yayi yana kallon shigar tayi, riga da wando tight sun kamata rigar dark purple, wando whiter, har kana iya hango black pant ɗinta, rigar ma kana ganin bra ɗinta shima baki,

Numfashinsa ne ya nime tsayawa cak, da yayi arba da yalwatattun kirjinta, wanda suke cikin ganiyarsu, sai ɗaukar ido suke janyewa yayi daga gareta ya zuba wardrob ya buɗe arabya gown ɗin da ya saya mata, ya ciro ya saka akan kayan sannan ya zura mata hijab ɗin ya janyota kan capter sukayi sallar isha, tare da shafa'i da wutir, bayan nan yasake jansu sallar nafila juyawa yayi ya dafe goshinta ya shiga karanto addu'ar da akeyi na ma'aurata tun daga nan jikin Rahilah ya fara rawa,

Mikewa yayi ya cire kayan shi ya ɗauko towel ya ɗaura, tana zaune a gurin laptop ɗinshi ya kunna ya cigaba da aikinsa,

"Idan kin gama ki kashe wutar ɗakin." ya faɗa mata.

Dakyar ta mike ta cire kayan ta ajiye ban ɗaki tashu tayi wanka tare da saka rigar baccin da ta shiga dashi, fitowa tayi tana raɓe raɓe, har tasamu ta kashe wutar ɗakin yana kallonta a ranshi yace..
*Ki gama raɓe raɓenki yau dai sai nayi abinda nayi niyya*

Zama tayi ta shiga shafa turarunkan jiki, da roll on, sannan ta kinkimo hijab ɗin ta saka.

Murmushi kawai yayi, tana gamawa ta ja kafarta ta ahaye gadon ta kwanta, bai kuma bin kanta ba, dan aikin da yake, inso samune nan da sati biyu yabar garin.

Addu'a tayi sannan taja duvet tun tana tsoron abinda zai mata har bacci yayi gaba da ita,

Ganin yanda take sauke ajiyar zuciya sai yaji gwara ya kyaleta ta saki jiki dashi, dan baya son tsoron shi ya hanata sukuni.

Yana gama aikin ya shiga duvet yayi yaja musu suka kwanta, rungumeta yayi ya cire hijab ɗin, ya gyara mata kwanciya a jikinshi. Addu'a yayi musu,

****
Da asuba ya rigata tashi, zareta yayi daga jikinshi yana kallon fuskarta, buɗe idanunta tayi ta zuba mishi tare da shigewa jikinshi, wani tunani ne ya zo mata tasake buɗe idanunta tags dagaske a jikinshi take. Da sauri ta bar jikinshi tana cewa.
"Ayya kayi hakuri, walla..."

"Hmmm badan Allah ya kwace ni a hannunki ba, da Allah kaɗai yasan irin fyaɗen da zaki min."

Waro idanunta tayi cike da mamaki tace.
"Ni ɗin?"

"Eh ke ɗin, hmm kina gigin barci ina zaki sani."

Sauka yayi daga gadon tana binshi da ido har zai shiga ban ɗaki tace.
"Ya Aman dama mata suna fyaɗewa mazane."

"Hmmm da Allah ya kwaceni a hannunki shine kike niman kariɓ bayani, ko baki ga yanda kika ƙ'amƙameni bane, Allah nagode maka da bata lalatani ba, tasani tafiya a ware...."

Da gudu ta koma cikin bargon ta rufe kanta, tana jin yafito ta sauka itama ta shige bandakin.

..... Rufe alkur'anin yayi itama tasha addu'a gyara ɗakin tayi sannan ta shiga banyi ta haɗa mishi ruwan wanka, a bakin kofa sukayi kiciɓis turata yayi ciki, tare sukayi wanka dukda ta rufe idanunta bai hanata jikin aikin da yake mata ba.

Haka suka gama wanka a shiririta da shirme suka fito, dukkansu ɗaure da towel, shiryawa yayi yau ma, cikin silver suit, kallonshi tayi tana murmushi tace.
"Duk kayan da kasaka yana maka kyau masha Allah."

Kallonta yayi itama tana sanya yan kune bayan tasaka qani dogowar riga mai gajeran hannun, english wear pink yayi mata kyau janyota yayi ya fesa mata turare, sannan ya zaro wayarshi dage gaban mirron

11 / 64