sannan yace.
"Koda wasa karka fara, dan zata iya tsanarka da zaran ka taɓa mata mafarkinta na zama uwa, yanzun a duniya babu wanda ya isa taɓa cikin nan ya kwana lafiya sai wanda ya halicceta, don Allah in akwai wata manufa aranka ka cireshi ka bar mata cikinta zata iya, tunda Allah ya bata ikon ɗaukar nauyinka toh ba makawa zata iya ɗaukar cikinta."
Shiru yayi yana nazarin abinda Aman ya faɗa mishi bawai dan ya saduda ba, sai dan kar ya nuna maitarshi a fili har aman ya ɗago manufarshi, dariya yayi wanda bai saba yinta ba yace.
"Haba dai ni tausayinta nake bazan taɓa cutar da maryam ba, dan tana sanyani farin ciki, Aman ina matukar alfahari da samun yarinyar wallahi."
"Munafuki da kasan cewa mune muka wurga maka kwaya a cikin lemonka, da an ɗibi yan kallo da kai."
Dariya yayi tare da kwantar da kanshi yace.
"Haka da kuka yi yasani fahimtar ni ɗin ashe cikakken me lafiya ne,dan gashi har da ɗ'a ko y'armu."
Hira sosai suka yi, suna cikin haka sai ga Aman nan shima suka baje ana aiki ana hira har lokacin tashi yayi.
****
Zaman gidan yunus ya fita kaina sam, bana jin daɗinshi ganin zai kasheni da sauran kwana na, yasani haɗa kayana na gudu zaria. Inda drvn gidan yakaini da taimakonsu Balkisu, har zuwa lokacin bansan miye takamaimai abinda nayi yake horani ta hanyar saduwa ba.
Ina isa zaria Mama suka kaini asibiti sabida bani iya tsayuwa, likitan na gani na yace.
"Haba hajiya so kuke ku kasheta, babu wadataccen ruwa a jikinta ga ɗan cikinta yana bukatar kulawarku don Allah ku duba al'amarin."
Nan dai aka samin drip, sannan mama ta kira Hajiya tace ta min abinci. Tambayata mama tayi ni dai nakasa cewa komi, asalima sunkuyar da kaina nayi nace.
"Babu can ɗine bana son zama, kuma idan naje gidanmu Ummana korata zatayi."
Gyaɗa kai tayi kawai amma bata yarda ba, kiran balkisu tayi itama dai bata faɗa mata komi ba.
........Da dare ya dawo yaci abinci ya ɓali maganin desires ɗinshi ya zuba a drink ya sha dan har da wani na sachet wanda yake kamar garin tea, ya haɗa ya sha yana tuna abinda mai saida maganar yace mishi ai wannan sai kayi kusan kwana kana murza mace, kafin ka samu lafiya.
Da wannan ya hauro ɗakina, dan yayi imani cewa matukar ya ɗauki lokaci yana abu ɗaya dani toh cikin idan yaji wahala sai ya fita.
Koda ya isa ɗakin wayam ya gani fitowa yayi a rikice dan har ban ɗaki ya duba bani ciki, falon sama ya fito ya dankarawa balkisu kira, daman tasan da haka bata damu ba tafito tace.
"Lafiya?"
"Ina Mata ta?"
Kallonshi tayi fesss tace.
"Tana zaria"
Zaro ido yayi waje cike da ɓacin rai ya nufeta, ko gizau batayi ba, dan ita a tunaninta dukarta zai yi amma ina, rashin mutunci bawan Allah nan yayi mata, wanda sai da tayi kuka da idanunta, ya mikewa yace.
"Ai nasan bake ɗaya bace har da fareeda, itama zata gaya musu bari naje ɗakinta."
(😂) hmmm
A daren kan sun faɗi gaskiyarsu dan kaman mahaukaci haka Mai nasara ya koma laifin duk ya tattara musu, ya gurje su son ranshi kafin ya samu nutsuwa sai da ya dawo hankalinshi ya kuma buɗe musu rashin mutunci.
D'akinshi ya koma jikinshi ba laka, dan duk energy ɗinshi ya tafi a can.
.....Da rarrafe Balkisu ta shige ban ɗaki ruwa ta haɗa sosai ta shiga ciki, tana share kwalla tace.
"Ko kasheni zakayi baxan taɓa barinka ka cutar da Maryam ba, kamar yanda ka lalata min nawa rayuwar."
Haka ma Fareeda dan nata yafi muni, ga bakin cikin rashin ɗanta ga na cire mahaifarta, wanka tayi ta kwanta gari na waye wa ta nufi gidan Iyayenta tana kuka tana tuki tana cin alwashi ko nawa zata kashe sai ta nemo haihuwa dan ta cusawa Yunus bakin ciki.
Sai da ta isa gidansu kuma taji bazata iya faɗan ga abinda tayi ba fita da motar tayi ta nufi asibiti.
****
"Ammy ki taimake ni na koma gidan Ahmad wallahi mutuwa zanyi bani da tsuntsu bani da tarko naji wai ya ɗauko Chuchu yabata don Allah ki san yanda zakiyi na koma gidan mijina."
Kallon hafsa mahaifiyarta tayi kafin ta taɓe baki tace.
"Nima bason ganinki nake ba, kina kaɗa ɗuwawu ina kaɗa ɗuwawa, waye uwar waye yar ai sabida haka nacekarki fara amma sakw kunnen kashine dake kika yi toh gashi nan ya sakoki, kuma da kike haukarki kin manta babu aure a tsakaninku, dan uku yayi miki a haihuwar Chuchu yayi miki ɗaya a ynz kuma ya baki biyu."
"Na shiga uku na lalace wallahi malamai suna gyarawa, don Allah kisa baki ya mai dani wallahi zan zauna lafiya da matarshi."
Mikewa Uwar tayi tana dariya tace.
"Eh toh da kamar wuya, dan babu aure a tsakaninku, gashi kina da zawarawa mi yasa bazaki cire Ahmad a ranki ba."
"I can change anything in my life but i can't change Ahmad."
Dariya Uwar tayi har da shewa sannan tace.
"But you can change ur destiny."
"Indai akan Ahmad ne baxai canzu ba." ta faɗawa mahaifiyarta cikin kuka,
"Zai canzu idan kikayi auren kisar wuta."
A kiɗime ta ɗago kanta tana girgiza shi, cikin kuka tace.
"Baxan iya ba, ki nima min wata mafita wannan yayi min tsauri da yawa, bazan iya raba shimfiɗa dawani namijin ba, ni ɗin mallaki Ahmad Zailani bature ce bazan iya ba."
"Good Job" Uwar tace mata.
*****
Kwance yake duk jikinshi ciwo yake, toh ba dole ba ya tsangwami kanshi da masifa sai ya cima manufarshi, karan wayarshi yaji ya laluba ya amsa.
"Kai haka ake baka kira Maryam kaji lafiyarta ba sai kayi shiru ka manta da ita, tun jiya tazo ynx haka tana asibiti ba laifi."
"Kar dai Cikin Ya zuɓe?"
Ya tambayi sulaiman da ya kirashi.
"Wani irin zubewa kuma ciki lafiyarshi lau, itace dai ba lafiya, kuma ana kokarin ganin taji sauki."
Shiru yayi ranshi kamar tayi waje ciki ciki yace.
"Ok zanzo next week ina da wani aiki a gabana."
Yana gama faɗar haka yayi jifa da wayar kamar wanda aka faɗa mishi sakon mutuwa.
Wanka yayi ya fito yana nazarin asibitin da Aneesah ta faɗa mishi.
Murmushi yayi ya saka suit ɗinshi, haka kawai sai yaji yana matukar kewata, dan yasan da ina nan da nice zan shirya shi, ina saka mishi kaya yana taɓe taɓe, wani lokacin dakyae nake korashi ya tafi dan manne min yake kaman danko.
Tsaki ya sake sannan yace.
"Maryam ina sonki, amma haka bazai hanani ganin kinyi rayuwa irinta mata masu daraja ba, har nawa kike da zakiyi tunanin ɗaukar ciki."
Haka ya gama surutanshi ya fice a gidan.
*****
Zubawa Dr Fatrick Zubairu ido tayi likita a babban asibitin koyarwa na Ahmadu Bello T.H.
Zare gilashinsa yayi yana sauraronta, cikinta kuka tace.
"Sabida bani da lokacin kaina da kuma ra'ayin mijina, dan shima baya son tara yara,,,!" numfashinta taja sannan ta cigaba da cewa.
"Sai yace na kara koda ɗaya ne, sai na dakatar da haihuwa tunda lokacin ina da cikin yarona da ya rasu, banyi tsamanin namijine ba, sai da na haihu, yaron na da shekara ɗaya na sami wani cikin dukda na ɗauki allura amma sai da cikin ya shiga, ina faɗa mishi yace na cire bayan na cire wani tafiya da zaiyi india tare muka je aka juya mahaifar, muka dawo abin mamaki shekaran yaron biyu sai ga ciki mahaifar ta juya, shima wannan karon cire cikin mukayi."
Kuka ta kara sakawa mai cin rai, buɗe karamin freezer ɗin ke cikin officer ɗin yayi, ya ɗauko mata goran ruwa ya tura mata, gabanta ɗauka tayi ta buɗe ta kafa kai sai da tashan ye tass sannan ta ajiye.
Sannan tace.
"Fatrick nasanka kasan ni, munyi zaman unguwa ɗaya, dukda addininmu ya banbanta nasan zaka fahimci halinda nake ciki. Bayan an zubda cikin kawai sai ya bani shawaran muje a cire mahaifar, da farko naki yarda amma daga baya na amince sabida ni kaina ba zaman gida nake ba, always am busy bana fita ko ina iyakata a kaduna nake kasuwancina, haka na amince mashi muka je aka cire min mahaifa a wani zuwanshi Turkey, gashi an wayi gari bani da mahaifa bani da D'an ina jin ciwon haka a ynz Kishiyata ce ke ɗauke da ciki kuma yana son ya lalata cikin narasa yanda zanyi saving ɗinta da abin cikinta, karkayi mamaki dan har Matarshi ta farko yasa an rufe mata mahaifa."
Gyara zama Dr Fatrick yayi cikin nutsuwa yana kallon Fareedah, yace.
"Fairy(Sunan da yan unguwarsu da frnd ɗinta suke kiranta kenan tsabar kallon cartoon masu ɗan fifike kuma sai yazo dai dai da sunanta, dukda akwai abubuwa masu haɗi da fairy amma haka bai dameta ba) kunyi kuskure kuda annabinku yace ku Haihu dan yayi alfahari daku, shine kuke aikata abinda muma bazamu iya ba, Fairy Allah ya baki haihuwa baki san wanene arzikinki ba kika biyewa son zuciyar mijinki kika saɓawa Allah, nasan ni kiristane amma bazan taɓa aikata abinda kikayi ba, ko nasa matata tayi haka. Tunda nayi aure nake niman haihuwa har kasar waje munje amma babu labarin dan nine mai matsalar karewa dashen ɗan za'ayi mata nace a'a Allah nasane damu ban fasa kai kunans coci ba dan nasan Allah yana tare dani. Alkawari ɗaya zan miki shima bai zama dole hakan ya faru ba sai dai ai kunce Allah mai jin kaine mai rahama ne, zan miki hanyar wani likita a Germany ya iya dashen mahaifa tayu idan Allah ya nufa da rabo ki sake samun ɗanki na kanki idan kuma bai nufa ba sai kiga baki samu ba, da wannan nake kira da kiji tsoron Allah dan hakkin cikin da kuka zubda ba lallai bane ya barku, zai kuma cigaba da bibiyarku dake har shi maigidan naki, kuma kije gurin Malamanku ki tambaya ko abinda kika aikata akwai hukunci a kanki dan ki fara sanin inda zaki dosa, ni nasan zan miki kokarin ganin...........
*Don Allah kuyi hkr zaku ji ni shiru gobe, da jibi sai ranar monday Insha Allah abubuwa sun min yawa kuyi ta maneji* 🙏
[4/3, 7:56 PM] Addah Ramlah: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Mai Nasara Team😂
*BOOK 2👈*
*Page...7*
Fushi Umma tayi taki zama a jikina, Hajiyarshi ce ta zauna min, kullum sai yazo kamar maraya, ga tashin hankalin da yake ciki na mugayen mafarkai.
A haka muka ɗibe kwanaki, sannan aka sallameni. Gidanmu Hajiya ta kawoni. Dan tana son magana da su Umma, amma dole sai Alhajinsu Daddy yazo dashi da Sulaiman.
Karfe biyu suka iso, harda shima daddyn. Ina kwance a ɗakin Mama Aunty gausiya tazo kirana, mikewa nayi na fito. A nutse har falon baki, da sallama na shiga na gaida kowa na falon sannan na koma gefen Malam na raɓe, dan umma taki sake min fushi take dani.
Da sallama Alhaji ya buɗe taron da Addu'a sannan, yace.
"Da farko kafin nace wani abu ina bawa Maryam hakuri abinda abinda Yunus ya aikata mata, munyi haka ne dan kuma iyayenta kusan halin da take ciki, nayi bakin ciki da alhinin abinda Yunus ya aikata, amma ba komi kanshi yayiwa. Sannan abinda ya kawo mu anan shine.."
Har yakai aya, sannan ya ɗago kanshi yana duban malam da umma, wnda mamaki ya kusan sambaɗesu zuwa lahira, cigaba yayi da cewa.
"Allah ya gani nafita hakkinshi na masa komi da uba yakewa ɗa nayi na fita hakkin Yunus, amma idan bazaku damu ba zanso naji Ra'ayinku akan abinda ya aikata muku."
Sunkuyar da kai Malam yayi yana girmama al'amarin, shiru yayi sannan ya kalleni cikin sanyi murya mai bayyana tsantsar hakurinshi yace.
"Tabbas anyi kuskure, sai dai mu bamu da ikon hukunta mijin maryam, kuma idan muka ce zamu ɗauki mataki ai kimar zata iya zuɓewa, mi kike gani Hasina."
Kallon Malam Umma tayi cikin mamaki tabbas ranshi ya ɓaci, girgiza kai tayi, sannan tace.
"Malam!!! Kaine mahaifinta duk abinda kace ai duk ɗaya ne."
Kallonta Malam yayi tare da kallon Alhaji yace.
"Mu dai a matsayinmu na iyayenta, munyi hakuri babu wanda yafi karfin laifi, sai dai bazamu tauyeta ba gata nan idan ta hakura shiknn."
D'ago kaina nayi cikin matsanancin kuka ina kallon Malam bakina narawa.
Alhaji yace.
"Mun gode sosai da wannan dattakon, maryam muna jiranki."
Kallon Umma nayi na kalli hajiyarshi kauda kanta hajiya tayi, sannan na kalli Mama amarya gyaɗa min kai tayi, cikin murmushi umma kuwa bata iya kallona ba, shi nakalla. Ya gama zuba min ido, girgiza kaina nayi yanda nake tuna rashin imanin da yayita min, cikin wani irin murya nace.
"Bazan yafe ba, ya cutar dani, ya dakeni ya tunkuɗeni."
Dafani malam yayi na ɗago kai cikin kuka nace.
"Kabarni na faɗa dan idan na cigaba da rike haka mutuwa zanyi, malam zuciyata kamar zata kama da wuta, ya sani kuka amma wancan ba komi bane, idan na tuna tsantsar rashin imanin da nagani a cikin kwayar idanunshi, bazan iya zama dashi ba, Umma kin koya min hakuri da yarda da kaddara, umma kin koya min abubuwa umma miyasa baki koya min fitar da damuwata zuwa gareki ba, umma na haɗiye bakin ciki dayawa. Don Allah ki kwatar min yancina, karki juyawa al'amarina baya, ki kwatar min yancina."
"Maryam!!! Mi kike bukata daga yunus?"
D'ago kaina nayi ina kallon hajiya cikin zubda kwalla nace.
"Hajiya kiyi hakuri,,, zama dashine bana so."
"Miye ne na bada hakuri, ai hakkinki ne. Yunus ka sawwake mata."
Tace mishi.
A gigice ya ɗago kanshi yana girgizawa cikin tashin hankali yace.
"Hajiya don Allah, kuyi hakuri ina son matata, maryam kiyi hakuri na sauya halina karki rabu dani wallahi ina sonki sosai."
Girgiza kai nayi cikin kuka nace.
"Ai nima haka na rokeka da karka zubda min farin cikina, wayasani ko shiknn bazan kuma samun wani ba, ka zubda min shi. Kaje mun barka da Ubangij...."
"Maryam!!!"
Umma ta buga min tsawa.
Tsabar tashin hankali baka hangi komi a idanun Yunus.
Kuka na fashe mata dashi nace.
"Ni..."
Gaban Umma yazo ya dukar da kanshi cikim mugun yanayi yace.
"Kiyi hakuri, ku bani damar karshe."
"Abaka damar kashe musu y'a ƙo wacce irin dama kake bukata." Inji Alhaji.
Hannuna na ɗaura akaina ina kuka nace.
"Umma!!! Cewa yayi fa bani da daraja da kima, sabida an bashini a banza ko?"
Cikin ko in kula tace.
"Eh toh nima dai naga rashin kimarki da darajar, ina suke? Ina darajarki take? Ina kimarkin take?"
Rike bakina nayi tare da kallon Umma, wani irin ajiyar zuciya nake saukewa tsabar tashin hankali da ɗimauta.
Murmushi tayi sannan tace.
"Idan D'iya ta garice ko tari bazatayi ba, sai dai tajira hukuncin da zamu yanke mata. Ina guje miki aikin danasani ne kar wata rana ki zubda kwallar da tafi wanda kike zubdawa, ita rayuwa ba'a binta a guje. A nutse ake binta tafi daɗin ganuwa."
Mikewa nayi tsabar bakin ciki in dakeni an hanani kuka. Ko gani banayi. Nasa kai zan fita ji nayi an rukoni,
"Dawo nan Mamana."
Inji Malam zuɓewa nayi ina wani irin haki, hawayen ya kafe sai zuciya zalla da take aikinta.
Kwantar da kaina yayi akan kafarshi yana shafa kaina tare da tofa min addu'a. Sai da yaji numfashina ya daidaita sannan ya ɗago kanshi ya kalle Yunus cikin damuwa tace.
"Wallahi baka kyauta min ba, dan tunda nake ban taɓa jin an rabata faɗa da kowa ba, bata taɓa kawo min karan wani ba nasan halin duk Yarana amma nata halin dabane, hakurinta daban ne, adalci ɗaya zan iya maka nabaka dama ka gyara tsakaninku, idan haka bai samu ba toh zan iya baka hakuri ka sallam...."
"Malam..." Mama ta kirashi raunane.
Dakatar da ita yayi, cikin murmushin ya cigaba da cewa.
"Ban goyi bayan Maryam ba, sai da na fahimci har ynx hasina bata kaunarta, kiga yanda take numfashi, idan ita bata son Maryama ni ina sonta, kuma zan tsaya mata, ai duk sauran mazajen ba haka suke ba, haka mijin Rahilah yake? Yaron da ko gidan nan Rahilah tazo yana makale a kofar gidan nan, Mijin Rahimah nine nan nasanya shi yajanye ɗaure da yayiwa uwargidanshi, sabida kimar da muke dashi a idanunshi."
Murmushi Malam yayi sannan ya kalli Alhaji yace.
"Manyan mutane irin Yunus, basu san darajar mace ba, sabida cuɗanya da turawa. Zuciyarshi ta girmama alamarinsu, kayi hakuri Alhaji Y'ata Lu'ulu'u ce, kima take dashi da daraja, yaje ya shawo kanta idan ya samu damar haka zan iya duba al'amrin da idon basira amma bazan miki mishi maryam ba, dan tana da kima. Duk laifin da yayi bai basu kai wannan muni ba. Ku gafarceni banyi haka akan zubda cikin ba nayi ne sabida kalmar bata da kima da daraja, ka duba yanda take bana son na zama silar lalacewarta, nafi son ta koma rayuwarshi dan kanta badan mun tirsassata ba da fatan kun fahimceni."
"Wallahi babu komi, malam ai kun mana dattako, tunda baku dubi girman laifin zubda ciki ba, wanda nake jin abun har cikin zuciyata, Insha Allah zan sashi ya sawwake mata, itama tasamu ingantacciyyar rayuwa ina kara baku hakuri da abinda ya faru."
Gyara zama sulaiman yayi wanda yake zaune cike da damuwa tunda aka fara rikicin yake kallonmu,*Allah kaga zuciyata ɗaya nake son Maryam Allah nagode maka gwara akashe auren nina sameta.* Ya faɗa a ranshi kallon Alhajinsu yayi cikin zakuwa yace.
"Hmm Alhaji, idan bazaka damu ba kasashi ya sauwake mata da wuri, in yaso ni sai na shiga niman aurenta, kuma zan riketa da kima, zan ɗaga darajarta a idanun duniya, Wallahi zan riketa fiyye da ruk....."
Tauuu.Yunus ya tsinke shi da mari, bai damu ba yace.
"Wllahi sai ka saketa na aureta, kasan kana kishinta da sonta ka zubda mata da cikinta, kai d kanka kace min, idan ka tuna yanda take rokonka sai hankalinka ya tashi, kayi biriss da ita zuciyarka tana ingiz...."
"Sulaiman zan kasheka."
Ya riko wuyar Baban arif, mikewa iyayenmu maza sukayi ran hajiya ya ɓaci, aikuwa tana mikewa ta shiga kifawa daddy mari takowani fuska, sabida bacin rai, tace.
"Sake shi, kuma sai ka rabu da maryam, Insha Allah sulaiman sai ka auri maryam."
Kallon hajiyarshi yayi tare da sake baki hawaye na sauka daga cikin idanunshi ya sauke kanshi kasa yace.
"Hajiya ina raye zaki rabani da farin cikin rayuwata, itace mafarkina fa, duniyata rayuwata hajiya karki min sassarin da bazan iya kwacewa ba."
"Allah sai ka rabu da ita, azzalimi, mugu maha'inci. Ina tsoron ganinka cikin sakayyar Ubangiji dan hakkin rayuka bazasu barka."
........Dakyar aka shawo kan hajiya, faɗa Alhaji yayiwa sulaiman da kar ya sake abinda yayi.
Rufe taron akayi da addu'a sannan suka fita daga ɗakin aka barni dashi ina kife a kujeran da Malam ya tashi, da sauri yayo kaina zai taɓa ni nace.
"Koda wasa! Karka fara taɓa ni, dan zan maka wulakancin da