OGA HABIB Bacewa da Samuwa by Faddy baby

Author :  Faddy baby Category :  Romance

Chapter   6 / 41

15K to 18K   out of 121.2K words

murya ta ce, "Hassana ki ke ko me!?, mun da katar da ke aiki a k'ark'ashin sanat yoghurt Company ". Hassana cikin tsoro da fargaba jin abinda Billy ta ce mata, ta ce, "Supervisor dan Allah ki yi hak'uri insha Allah daga yau haka bazai kuma faruwa ba". Billy ko inda Hassana ta ke bata kalla ba ta ce, "Nariga na gama magana, ki kalli time kigani ko yanzu k'arfe nawa kikazo aiki?, bama aiki da wanda bashi da experience, fitar min daga Office! ". Hassana fita ta yi batare da ta k'ara cewa ko mai ba, Hassana na fita ta nufi Office d'in Manager ".manager na zaune Hassana tai mai nocrking. Izinin shiga manager ya ba Hassana. Hassana shiga ta yi,Hassana cikin girmamawa ta gaida manager. Manager cikin sakin fuska ya amsa ma Hassana, ya ce, "Hassana lafiya dai ko? ". Hassana kamar zata yi kuka ta ce, "Manager supervisor ta dakatar da ni aiki". Manager cikin tsoro ya d'aga kai yana kallan Hassana. Shiru manager ya yi na d'an wani lokaci sannan ya kalli Hassana ya ce, "me kika yi mata? ". Hassana cikin sanyin muryarta, ta ce, "Banzo aiki ba kwana uku, bani da kud'in napep, ko yauwa ak'asa nazo". Shiru manager ya yi, sannan ya ciro kud'i yaba Hassana ya ce, "Hassana amshi kud'innan kinji sai ki amfani da su, ki yi hak'uri kinji naso kiyi aiki anan, tom amma inda haka ya faru sai dai hak'uri ". Hassana amsa ta yi taima manager godiya jin abinda ya ce, ta fita daga Office d'in. Hassana na ta fito daga Office d'in manager ta had'u da staff d'in da ta bata sak'on supervisor na kiranta. Staff d'in cikin tausayama Hassana ta k'araso inda Hassana ta ke, ta ce, ta koreki ko? ". Kai Hassana ta d'aga mata ta ce, " Ta kore ni, na yi ma manager ma magana ma ko zai sa baki, amma ya ce min inyi hak'uri ". staff d'in kallan Hassana ta yi ranta ad'an bace, ta ce, "Ni da nasan zaki gurinsama da na hanaki, ai indai supervisor ta yanke hukunci bai iya yin komai, sai dai ya baka hak'uri bai iya sab'a maganarta". Hassana sallama ta yi ma staff d'in ta tafi dan maganar ma da kyar ta ke yinta. Cikin kud'in da manager ya ba Hassana ta hau napep ta koma gidansu Oga Habib, duk da zuciyarta cike ta je da bargabar komawa gidan, in da yanzu tabar aiki ak'ark'ashin su, haka nan Hassana ta koma inda bata da yadda zata yi.Jimmai cikin mamaki ta ke kallan Hassana ganin Hassana ta dawo gida yanzu.Jimmai k'arasawa inda Hassana ta ke ta yi, ta ce, "Hassana lafiya kuwa naganki kin dawo? ". "Supervisor ta koran aiki". Jimmai ta fe k'irji ta yi tana salati, ta ce, "manager kuma ya sani? ". "Eh ya sani, wai budurwarsa ce ba ya musu da abinda ta ce, inji wata staff". Jimmai shiru ta yi, tana jimamin abinda ya faru. Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Jimmai tom kina ganin babu damuwa inci gaba da jama gidannan yanzu bana aiki ak'ark'ashin su? ". Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, "Tom nima dai ban sani ba, amma dai yau Hajiya turai zata dawo ai, shiyasama kikaga ko ina gidan aiki ake, tom ki bari ta dawo mugani".
WACECE HAJIYA TURAI?.
Hajiya turai babbar macece cikakkar 'yar boko. Ita kad'ai ce awajan mijinta wato Alhaji Idris mai kanti. Tun Habib na yaro Mahaifinsa ya rasu, hakan yasa Habib bai san Mahaifinsa ba. Hajiya turai babbar 'yar jarida ce, yanzu haka Hajiya turai a B. B. C, London ta ke aiki, hakan yasa kusan koda yaushe Hajiya turai bata Nigeria.Ji da kai da miskilanci Habib duk a gurin Mahaifiyar shi ya gada. Hajiya turai tun da ta haifi Hassana k'anwar Habib ta tsaida haihuwa, dan ita gani ta ke baza ta iya d'awai niyar yara uku ba. Hassana ta yi girma kusan 18 years sannan Allah ya yi mata rasuwa, sanadiyar wata bak'uwar 'yar aiki da Hajiya turai ta d'auka aiki, ashe had'in kai ne akai da ita aka zuba ma Hassana guba ta ci, wannan ne sanadiyar mutuwar Hassana har lahira. Mutuwar Hassana sosai ta d'agama Habib hankali dan idan ka cire Hajiya turai mahaifiyar Habib, tom babu wanda Habib ya ke zama dashi sunyi hira su ci abinci tare sai Hassana, yana kiranta da sanat, wannan shine dalilin da koda zai bud'e Company yin yoghurt ya sa ma mai suna Sanat yughurt. Tun rasuwar Hassana ya sa Hajiya turai ta bar yadda da kowa yana shigo mata gida barkatai. Wannan shine dalilin da yasa Hajiya turai har 'yan Aiki ta daina d'auka tuma ta ke rik'e wa inda ta ke dasu da mahimmanci bata yadda Habib ya koresu ko sun yi wani abun, duk da ta yi kashedi sosai akan d'aukar wata sabuwar mai aki bata nan, wannan shine dalilin da yasa koda aka kai mata labarin zuwan Hassana taima Habib fad'a. Wannan ke nan".


Sosai 'yan aikin gidan Hajiya turai ke shirin tarbar ta. K'arfe hud'u na yamma jirginsu ya sauka, idan Habib da kan shi ya je ya d'akkota. Habib har falon Hajiya turai ya kaita, sanan ya kalleta yana murmushi ya ce, "Mommyna kin gaji ki yi wanka ki kwanta ki huta, sai kici abinci ko? ". Murmushi Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Tom Habib ko na kwanta worker's d'in gidan baza su barni in yi bacci ba, nasan yanzu zasu fara yimin aikin sannu da zuwa". Habib d'an b'ata rai ya yi, sannan ya ce, "Mommyna ki kwanta ni zan yi gadinki babu wadda zata shigo falon ki sai in kin tashi". Habib na fad'in haka ya fita ya ce, yana zuwa.
Habib b'angaran 'yan aikin gidan ya je, kafin ya k'arasa ya samu Hassana da Jimmai suna wanki tare. Habib wani kallo ya yi masu wanda ya rikirkitasu du kansu, duk suka daburce. Bakamar Hassana ba da ta ke tsoran ko gurinta yazo yasan ankore aiki yazo ne ya koreta shima, hakan yasa Hassana cikin sark'ewar murya ta ce, "Ina wuni Oga Habib ". Habib banza ya yi da Hassana, sannan ya kellesu dukan su ya ce, "Hajiya ta dawo, kar wadda ta yi kuskuran shiga gurinta yanzu, sai bayan magriba". Habib na fad'in haka ya juya. Hassana ko da Jamila kusan tare suka had'a baki wajan cewa, "tom babu wanda zai shiga zamu fad'a ma sauran". Habib na tafiya, Jimmai ta kalli Hassana ta ce, "Ni dai Hassana duk da halin Oga Habib na wulak'anta mutane Wallahi yana burgeni sosai". Kai Hassana ta jinjina ta ce, " Ni dai abinda nasani kawai, nasan Oga Habib mai kyau ne shi, dan duk inda ake nai man maza masu kyau za asa shi, amma Wallahi bai tab'a burgeniba". kai Jimmai ta jinjina sannan ta ce, "Hassana bari in je in sanar da sak'on Oga Habib, dan yanzu za kiga 'yan iyayi sun fara shiga". Jimmai sak'on Habib ta je ta sanarma duk wata wadda ke aiki agidan. Bayan jimmai ta dawo ne ta kalli Hassana ta ce, "Hassana zaki gaida Hajiya ko?, dan idan ma baki jeba sai magulmata sun kai mata gulma, kuma in dai suka rigaki zuwa gaskiya akwai damuwa". Shiru Hassana ta yi, sannan zuwa can ta ce, "Zan je, kawai dai ina fargaba ne idan tak'i amintar zamana". "A'a insha Allah zata zauna da ke, ai Hajiya bata da wani damuwa sosai". Nan dai Jimmai taita kwantarma Hassana hankali akan zuwa gaida Hajiya Turai da zasu anjima.
Aiko kamar yadda Habib ya tsara haka akai, dan babu 'yar aikin da tashiga gaida Hajiya Turai, kamar yadda suka sabayi da. Hajiya Turai bayan tata shine masu kai mata abinci sun kai mata taci, ta gama ci, tana zaune a falon ta, nan fa worker's d'in gidan suka fara zuwa da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai suna gaidata, Habib na zaune gefan Hajiyarsa suna fira, dan idan Hajiya Turai ta dawo dama indai yana gida tom yana falonta, babu inda zaka ga Habib sai a falon Hajiya Turai.
Jimmai da Hassana sune kusan k'arshen zuwa, Hassana cikin fargaba da fad'uwar gaba ta shigo falon Hajiya Turai, dan sallama ma sai dai Jammai ce ta yi masu. Tun kafin su zauna Hajiya Turai ta nuna Hassana da hannu ta ce, "Jimmai wacece wannan? ". Kafin Jimmai ta yi magana Baba lami wadda ke aiki cikin falon Hajiya Turai, ta ce, "Hajiya ai wannan zata yi sati biyu agidannan, nima dai ina ganinsu da Jimmai, dan rashin wayar da nayi ne ma da na sanar da kai ". Hajiya Turai kallan jimmai ta yi da ta yi shiru tana kallan Baba Lami, tana cewa azuciyarta dama ita ce me kaima Hajiya Turai gulma in bata nan. Hajiya Turai ko cikin alamun son d'aga murya ta ce, "Jimmai bakya ji ne?, na ce wacece wannan? ". Ta fad'i maganar tana nuna Hassana da hannu". Jimmai cikin dabir cewa, ta ce, "Hajiya sabuwar 'yar aiki ce ". Hajiya Turai kallan Hasssana ta yi ta ce, "Waye ya d'auke ki aiki? ". Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "manager ne". Hajiya Turai cikin mamaki ta ce, "Manager kuma, wana manager? ". Hassana ada barce taba Hajiya Turai amsa, da cewa, "Manager me aiki Company sanat yoghurt". Hajiya Turai mai da kallanta ta yi ga Habib da ke zaune kamar bai jin abinda ake cewa, ta ce, "Habib wai me yarinyar nan ta ke son ce min ne?, nina cema manager Ina naiman k'arin mai aki da zai d'aukar min 'yar aiki, kiramin manager kabanshi awaya". Habib kallan Hajiya Turai ya yi yadda ta ke fad'a daga cewa an d'auki me aiki. Habib cikin sanyi ya ce, "Mommy ki bari anjima zan kira miki shi please ". Hajiya Turai mai da kallanta ta yi gun Hassana ta ce, "Ki je sai kuzo da manager ". Hassana tsuk'unnawa ta yi, kamar za tai kuka ta ce, "Hajiya dan Allah ki yi hak'uri, bansan gidan manager ba, hasalima ya koran aiki".Hajiya Turai rasa takan zancen Hassana ta yi. Hajiya Turai magana ta za ta yi, sai ji tai Habib ya ce, "Me yasa manager ya koreki aiki? ". Yadda Habib ya yi maganar babu yadda za ai ka ce da Hassana ya ke". Hassana kallan Habib ta yi, sannan ta ce, "Bani da kud'in napep ne, kwana uku banje aiki ba, ranar da aka koranma ak'asa naje, amma ko da naje sai aka ce Supervisor ta ce in je office d'in ta tana kirana, shine da naje ta ke sanar dani ta dakatar dani aiki, da nafad'ama mana yace sai dai in yi hak'uri ". Hassana ta idasa maganar cikin fargaba dan tana tsoran kar Habib ya ce sai dai tabar masu gida. Habib batare da ya kalli Hassana ba ya ce, "Go be ki koma aiki, kuma karki yadda ki wuce magriba baki dawo ba, Hajiya ta dawo dawuri zamu rufe gida, wuce ku tafi".
Hassana da Jimmai da sauri suka tashi suka bar falon. Bayan su Hassana sun tafi ne, Hajiya Turai ta ce, "Habib bangane ba, kasan dai bana buk'atar k'arin mai aiki ko? ". Habib kallan Hajiya ya yi, cikin na tsuwa ya bata labarin yadda akai suka tsinci Hassana shida Bilya, da kuma labarin Hassana gaba d'aya haka Habib ya ba Hajiyarsa dan hankalinta ya kwanta, dan ya lura ta tsorata sosai da abinda ya faru shekaru biyu da suka wuce.
Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Shikenan ba damuwa ta ci gaba da aikinta ".
Nan Habib ya zauna suka cigaba da hira da Monmynsa sai dare sannan ya je ya kwanta.
Washe gari Hassana da wuri tata shi ta yi shirin zuwa aikinta da kud'in da manager ya bata da su ta biya kud'in napep. Hassana cikin fargaba da fad'uwar gaba tashiga sanat yoghurt, dan tana tsoran yadda zasu kwashe ita da supervisor.................



COMMENT
&
SHERE
PLEASE
πŸ“š OGA HABIB πŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

Facebook group :Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

BABBAN MABUD'IN ALHERI SHI NE ISTIGFARI. IDAN KA YAWAITA SHI MATSALOLINKA ZA SU KAUCE, DAMUWARKA ZA TA GUSHE, SAUK'I ZAI ZO MAKA. ALLAH KASA MU DACEπŸ‘πŸ‘πŸ‘.


SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN πŸ‘‡πŸ»
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT πŸ‘‡πŸ»
08142904255.



Shafi na 16&17.



Hassana cikin tsoran Billy ta shiga cikin Sanat yughurt. Hassana direct inda ta ke sharewa ta nufa ta kama aikinta. Duk staff d'in da tazo da mamaki ta ke kallan Hassana, dan su asaninsu duk wadda Billy ta dakatar ta tafi kenan, hakan yasa suke bin Hassana da kallon mamaki. Hassana ta gama share gun tana morpping Billy ta shigo site d'in. Billy tun daga nesa ta ke kallan Hassana, dan tabbas idan idonta ba gizo ya ke mata ba, yarinyar da ta kora aiki jiya ce ta dawo yau. Hakan yasa Billy ta k'arasa inda Hassana ta ke.Billy kallan Hassana ta yi da kyau sannan ta ce, "Ke ba ke bace jiya na dakatar da ke aiki a Company nan? "? Hassana d'agowa ta yi tana kallan Billy sannan ta ce, "Ni ce". Wani kallo Billy taima Hassana sannan ta ce, "Ok, biki ji bane sai na kuma maimai tawa ko me!? ".Hassana kallan Billy ta yi, ta ce, "supervisor Oga Habib ne yace in dawo in cigaba da aiki". Billy kallan mamaki tai ma Hassana, dan tana da tabba cin k'arya tai ma Oga Habib. Hakan yasa Billy kallan Hassana ta ce, "Ke kafin insa ad'aukeke afitar dake daga nan, ki sauri ki bargunnan stupid kawai". Hassana kallan Billy ta yi ta ce, "Supervisor Wallahi Oga Habib ne ya ce in dawo". Shiru Billy ta yi tana tunanin tom ina Hassana zata ga Oga Habib, dan ko ita sai da dalili mai k'arfi ta ke shiga office d'in Oga Habib bare kuma Hassana, cewarta acikin zuciyarta. Hakan yasa Billy kallan Hassana ta ce, ki bar aikin kisaman office d'in manager". Billy na fad'in haka ta juya ta tafi office d'in manager. Hassana bayan Billy ta fi, ta sameta office d'in manager kamar yadda Billy ta buk'ata. Billy ko na shiga office d'in, manager ta kalli Manager tana nuna mai Hassana ta ce, "manager waya dawo da yarinyar nan aiki? ". Manager shima da mamaki ya kalli Hassana, ya ce, "Hassana waya dawo da ke aiki, bacin Supervisor ta dakatar da ke? ". Hassana kallan manager ta yi, ta ce, "Oga Habib ne ya ce indawo in cigaba da aiki". Billy ranta b'ace jin abinda Hassana ta kuma cewa ta ce, dan ita yanzu tafi tunanin manager ne yadawo da Hassana ya ce tace Oga Habib ne yadawo da ita. Inda ita a tunaninta Hassana ina zata ga Oga Habib, in ma taganshi tasan bata isa ba ta kai mai k'arar andakatar da ita aiki. Hakan yasa Billy ranta b'ace ta kalli manager ta ce, "Manager yau d'in nan zan aje aiki, Inda ni ban'isa in yanke hukunciba, in dai yarinyar nan bazatabar aiki anan ba, tom sai dai ni in aje aiki! ". Manager cikin damuwa ya kalli Hassana ya ce, "Hassana taya M, D, ya san ankoreki aiki? ". Hassana kallan manager ta yi ganin yadda ya damu jin Billy ta ce zata bar aiki. Manager dakama Hassana tsawa ya yi ganin Yana tambayarta ita kuma tunanin ta ke, ya ce, "Ke bakya jine?, nace taya M. D, yasan andakatar da ke aiki!? ". Hassana kallan manager ta yi ta ce, "Jiya Hajiyar Oga Habib ta dawo, tom bacin naje gaidata ne, ta ke tambar waya d'aukeni aiki, tom shine bayan nasanar da ita, nake fad'a mata amma andakatar dani aikin, tom da yake Oga Habib na gurin zaune, shine ya ke tambayata waya dakatar dani shine nace mai supervisor ce, shine yace yau in dawo aiki".manager kallan Billy ya yi yace tom kinji yadda akai". Billy itama kallan manager ta yi ta ce, "Wai bangane ba, idan nagane kana nufin yarinyar nan causing d'in Oga Habib ce ko me?, naji tana maganar gidansu ta ke ne kome ?". Manager kallan Hassana ya yi ya ce," je ki cigaba da aikinki". Hassana fita office d'in ta yi tabar manager da Billy".
Bayan Hassana ta fita ne, Billy ta kalli manager ta ce, "Manager ni fa gaskiya banyarda da dawowar aikin yarinyar nan ba". Manager cikin taushin murya ya ce, "Tom Billy yanzu ya ki ke so ayi, aidai kinji daga m, d, ne dawowar ta". "Eh naji daga Oga Habib ne, amma ai yanzu idan kaje kasamu Oga Habib ka ce mai kai ka dakatar da ita, nasan zai yarda, idan kuma bahakaba ni zan bar aiki anan, dan sai ta d'auka ita sa'atace, shiyasa ni na koreta aka dawo da ita". Manager kallan Billy ya yi, ya ce, "Billy Yarinyar nan da kike gani m, d, da Bilya driver m, d, ne suka tsinceta, tom bata

6 / 41