OGA HABIB Bacewa da Samuwa by Faddy baby

Author :  Faddy baby Category :  Romance

Chapter   31 / 41

90K to 93K   out of 121.2K words

M. D, kanta ne ta ke wannan iskancin, kuma shi bai d'auketa komai ba, danma shi mai biyayya ne ga Mahaifiyar shi, ki barni da ita zanyi maganinta".


Billy cikin jin dad'i ta kashe kiran, dama a speaker ta sa wayar Farida ta ji duk abinda manager ya ce. Billy kallan Farida ta yi, ta ce, "Muje mu sami shegiyar, Kafin manager yazo muci uban 'yar iska, haba ni dama nasan jin kan Oga Habib ne zai kula wannan, sai dai biyayyar kamar yadda Manager ya ce".


Hassana na zaune kan wata rubber chair, Farida da Billy suka zo suka sa meta, Farida kallan Hassana ta yi,ta nuna ta da hannu, ta ce, "Ke kikiyayi kanki dani, nifi k'arfinki nafi k'arfin iskan cinki, dan na girmi shekarunki, ni sa'arkice da zaki fad'amin abinda kika ce min d'azu? ". Hassana murmushi ta yi, ta ce, "Tom da ke da wadda ta rakoki duk na dakatar da ku sai nan da sati d'aya, dan itama ba Aiki ta ke ba, akwai wasa a aikin nata, sannan kuma dama na fad'a miki".


Billy wani gigitattan mari ta wanka ma Hassana sannan, ta ce, "Shi wanda kike ta k'ama da auran shi, shi yaban matsayin da nake kai, shakarya mai tak'ama da abinda bata ita yake ba. Hassana tashi ta yi daga zau nan da take tana dafe da kuncinta, ta ce, "Masha Allah garani ko bata ni yake ba, da akwai abinda zanyi ta k'ama da shi, dan nasan hakan ma girma ne, akirani da matar Oga Habib, Allah sarki ku kuma dukkanku da kuke hauka akan shi, ko 'yan matan shi baza akiraku ba". Hassana na fad'in haka ta sa hannu ta wanke Billy da mari, ta rama marinda tai mata, sannan ta ce, "Ki ki ya yi kanki da harshanki Wallahi! ".Hassana bata rufe baki ba, Billy da Farida suka rufe ta da kuka kota ina, suna bugunta tana ramawa , amma ina hauswa sun ce sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, hakan yasa su Billy suka ci nasarar Hassana".


Kafin kace me staff's d'in gun an taru ana rabo, amma ina fad'a yak'i rabuwa, dan su Billy so suke su yi ma Hassana dukan da zata kiyaye su, ita ko Hassana duk irin buguwar da take gurin su Billy be sa ta hak'ura ta barsu ba, suna bugunta tana ramawa,daga k'arshe suka danneta yadda bata iya ramawa , suka ci gaba da bugunta kota ina. Bilya babu yadda bai yi ba ya raba fad'an amma ya kasa. Hakan yasa Bilya shiga Office d'in Habib ya sanar da shi abinda ke faruwa. Habib tare da Bilya suka zo gurin, Habib tsayawa ya yi bai cema ma su Billy komai ba, yana kallan su. Bilya ganin basu lura da Habib da ke tsaye ba, ya daka masu tsayawa ya ce, "Baku da hankali ne, Oga Habib ke muku magana! ". Farida da ke zaune kan Hassana tashi ta yi tana nishi, inda ita kuma Billy ta tashi ta zauna, ita ma tana nishi. Hassana da suba bari kwance tana nishin wahala ko kanta kasa d'agowa ta yi. Habib gurin Hassana ya je da ke kwance, tana nishin wahala, yana zuwa ya sa hannu ya juyo da i ta, jini sosai ke ziba abakin Hassana, dan bakinta su kaita bugu wai bakin rashin kunya".


Habib d'aukar Hassana ya yi ya yi Office d'in shi da ita.


Hassana ko na jin Habib ta sake langwab'ewa tai kamar irin wadde ke asume din nan. Habib kwantar da Hassana ya yi kan Table d'in Office d'in shi. Habib Faro ya d'ago yana tsiyayawa a hannun shi yana shafa ma Hassana a fuska. Habib girgiza Hassana ya fara, yana cewa, "Ke bud'e idonki mana". Habib yana yi yana d'an bubbuga fuskar Hassana, yana girgizata kamar d'an rud'e-rud'e ya ke girgizata".


Hassana ko najin Habib tai banza da shi, Habib waya ya ciro ya yi kira. "Hello doctor kazo ka saman ina Company na, dan Allah kazo yanzu zaka duba wata yarinya ne".


Hassana ko najin maganar likita, ta yi mik'a mai tattare da sakin kuka. Habib da sauri ya matsa kusa da Hassana yana mai d'ago ta".


Hassana ko kukan gaske ta ke tana mai cewa, "Wayyo cikina, Wayyo kaina Oga Habib ". Habib shafa fuskar Hassana ya ke yi, ya na cewa, " yi hak'uri ga doctor nan zai zo ya duba ki, yanzu".


"Ni bana son doctor ya zo, kace mishi karya zo". Cewar Hassana. Habib na nan tare da Hassana a wannan halin doctor ya zo,nan dai Habib ya labarta ma doctor abinda ke faruwa, magunguna ya rubata ma Hassana, sai allura guda d'aya".


Hassana sosai ta ji dadi ganin likitan bai zo da magani ba. Bayan likitan ya tafi ne, Habib ya ce ma Hassana ta tashi ta je toilet ta wanke bakinta inda ke jini, Hassana cema Habib ta yi tana magana da kyar-dakyar, ita bazata iya zuwa ba. Habib hannu ya mik'a ma Hassana ya ce, "Zo in kaiki". Hassana k'iyawa ta yi tana mai ci gaba da kukanta, dan tana jin zafin bugun da su Billy su kai mata. Habib Bilya ya kira ya ba ya siyoma Hassana magungunan da aka rubuta mata".



Hassana baccin wahala ne ya d'auke ta. Habib waya ya ciro ya kira manager, manager na d'agawa ya ce, "Hello manager duk inda kake kazo yanzu". Habib na fad'in haka ya kashe wayar".



Bilya na kawo ma Hassana magungunan, Habib ya amsa ya ta data ya bata. Hassana nacikin shan maganinne Manager ya yi nocking. Kasan cewar Habib yasan manager ne yasa ya ce, "shigo". Manager cikin girmamawa ya gaida Habib. Habib amsawa ya yi sannan ya ce, "Manager dubu abinda Su supervisor Su kai ma yarinyar nan! ". Habib ya yi managar yana nuna ma manager Hassana".



Manager cikin nuna damuwar shi, ya ce, "Wallahi M. D, ban sani ba, kasan yau dama bana zuwa da wuri, bari in kira Su ".


Manager na fad'in haka ya fita Office d'in. Manager da Billy da Farida suka dawo Office d'in Oga Habib ".



Manager kallan Billy ya yi, ya ce, "Me ya had'aku da ita? ". Farida ce, ta amshe zan can da cewa, "Manager muna kan aikin mu tazo ta saman wai ta bamu suspection na one-one week,saboda bama Aiki, wai da nace mata ta bari sai Munji gurin manager sannan shikenan sai mari". Hassana da ke zaune saurin amshe zan can ta yi da cewa, "Duk abinda kuka ga dama ku fad'a , kuma Wallahi kunji na rantse sai kunyi hutun sati d'aya a gida, kamar yadda nace muku". Hassana ta fad'i maganar tana murguda baki, ba su Billy kad'ai ba har manager kallan mamaki ya ke ma Hassana".



Billy ce ta yi, k'arfin halin cewa, "Tom mu dai munsan aikinki a gunnan, shara ne da goge-goge, kuma duk wanda za aba matsayi a gunnan meeting ake yi abashi gaban kowa.. ". Ai Billy bata aje zan can ta ba, Hassana tai wuf ta ce, "Ai da yake ga Oga Habib d'in nan agaban shi nake magana, kuma shi yaban matsayin idan akwai wanda ya isa sai ya cire ni in gani, ni ce ma tai makiyar manager dan haka Billy ke da Farida abisa ga matsayina da mijina kuma shugabana a masana antar nan ya ban, na dakatar da ku Aiki na sati d'aya, kamar yadda nace miki Farida idan kika kuma zuwa irin yadda kika zo yau zamu koreki baki d'aya, ke kuma Billy bisa ga biyema Farida da kike yi, kema mun da katar da ke na sati d'aya, idan kuma kuka sake mai-maita irin haka korar ku zamuyi baki d'aya, zaku iya tafiya.............✍️



Ko ya hukuncin da Hassana ta yanke ya ke????? 🤭🤭🤭



Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝.



Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7


https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Dan Allah ina barar addu'ar ku Mahaifina baida Lafiya 🙏.



Shafi na 72&73.




Hassana tai wuf ta ce, "Ai da yake ga Oga Habib d'in nan agaban shi nake managa, kuma shi ya ban matsayin, idan akwai wanda ya isa sai ya cire ni in gani, ni ce mataimakiyar manager , dan haka Billy da ke da Farida abisa ga matsayin da mijina kuma Shugabana a masana'antar nan ya ban, na dakatar da ku Aiki na sati d'aya. Kamar yadda nace miki Farida idan kika kuma zuwa irin yadda kika zo yau, zamu koreki baki d'aya. Ke kuma Billy bisa ga biyema Farida da kika yi, kema mun da katar da ke na sati d'aya, idan kuma kuka sake maimai ta irin haka korar ku za muyi baki d'aya, zaku iya tafiya! ".


Duka gurin Shiru kowa ya yi da abinda ko ke fad'a azuciyar shi. Manager ne ya yi jarumtar kallan Habib ya ce, "M, D, dokar Company nan kowa ya san ba'a bada matsayi sai anyi meeting, sannan aba mutum gaban staff's dan su shaida, tom amma yanzu kaji abinda ita tace, tom ya maganar ta ke, Shin ka bata matsayin ne ko-ko ? ". Ai Kafin Habib ya yi magana, Hassana ti yi wuf ta ce, "Manager ina tunanin koda ace k'arya nake bazan yi ba agaban Oga Habib, dan haka ina mai tabbatar maka shi yaban matsayin nan jiya, dan haka ina ganin zasu iya tafiya".


Manager da sosai ranshi ya b'ace ganin Habib ya yi mai Shiru, wannan k'aramar yarinyar na nai man rugaza soyayyar shi. Manager kallan Billy ya yi ya ce, "Supervisor ku saman a Office d'ina". Manager ya yi maganar daga gani kasan ranshi ya b'ace ya ke, da shirun da Habib ya yi mai"


Manager na fita su Billy ma suka bi bayan shi suka nufi Office d'in shi kamar yadda ya ce. Bayan duk sun gama fita ne Habib ya kalli Hassana ranshi b'ace, ya ce, "Dama kin rok'an in baki matsayine dan ki kore su?". Hassana Shiru ta yi tana mai wasa da hannunta, dan yadda ta ga Habib ya d'aure tasan ba wasa. Habib ko cikin daka ma Hassana tsawa ya ce, "Nace dama kin rok'an in baki matsayi ne dan ki kore su!? ". Hassana girgiza kai ta yi, ta ce, "A'a Oga Habib, amma kamar yadda kaji na fad'a Allah haka ne, Supervisor bata aiki, ita kuma Farida..... ". Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce yasa ta yi shiru. Habib hanyar fiya ya nuna ma Hassana da hannun shi, ya ce, "Barnan! ". Hassana fita ta yi, tana fita ta ta yi tafiyar ta caktrea school d'in ta, tana mai addu'ar Allah yasa Habib k'arya da wo da su Farida, idan ma zai dawo dasu, tom Banda Farida, dan tafi jin zafin Farida".


Manager ko a office d'in shi kallan su Billy ya yi, ya ce, "Supervisor ku yi hak'uri kuje gida koda na yau ne kad'ai, zan samu M, d, muyi magana zuwa anjima". Billy kallan manager ta yi, ta ce, "Idan har na bar gurinnan da sunan wai waccan bagidajiyar ce ta koran, tom kasani ba zan dawo ba". Manager cikin rashin sanin yadda zai yi ya ce, "Ki yi hak'uri Billy idan har kika tafi ni kuma nayi miki alk'awari zaji dawo da matsayinda take ta k'ama M, d ya bata, ki ce zaki koma kan matsayin". Billy cikin jin dad'i ta d'ago tana kallan manager, ta ce, "Manager ka tabbata? ". "Billy ba wai tabbata wa ba, alk'awari nayi miki, ke dai kin san yadda nake da M,D, ni ke tsara komai na gurin nan, dan haka nasan yadda zan mai , in ma ya bata mataimakiyar tawa da gaske , nasan yadda zanyi na dawo da shi kanki, amma yanzu ina so ki yi hak'uri ki je gida na yau kad'ai, zuwa gobe zaki dawo da matsayinta". Billy cikin jin dad'in kalaman manager, ta ce, "Godiya nake dearie". Sunan da ke kashe manager kenan, dan har Billy ta gano shi. Billy kallan Farida ta yi, ta ce, "Ya kika ji tsarin? ". Dariya Farida ta yi, ta ce, "reshe ya juye da mujiya". Dariya sosai sukai, sannan su kai ma manager sallama suka tafi ".


Hassana k'arfe 3 na rana bayan sun tashi ta biya ta Sanat dan ganin, su Billy suna nan ko sun tafi. Hassana babu inda bata duba ba, amma bata gansu ba, hakan yasa ta samu k'awarta Amina, ta tambayeta ko supervisor na nan".


Amina kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana Amma dai akwai releshanship tsakanin ki da Oga Habib ko? ". Hassana kai ta girgiza ta ce, "Babu komai tsakanin mu, malam ki ban amsa ta supervisor na nan ko ta tafi?, ita da Farida? ". "Eh naga tafiyar su, ita da Aunty Farida". Cewar Amina, tana kallan Hassana, dan bata yadda da cewar da Hassana ta yi ba babu dan gantakar komai tsakaninta da Habib".


Hassana kallan Amina ta yi, ta ce, "Nina wuce, sai gobe insha Allah ".


Habib yau da wuri ya koma gida. Hassana ko tana dawowa gida taima Habib kunun shi d'an kullun. Hassana ba ita ta shiga side d'in Habib ba sai da ta tabbatar ya gama komai sannan ta shiga, da kununta a hannu. Lokacin Habib yana waya da Hajiya Turai tana sanar dashi da wowarta gobe. Hassana guri ta samu ta zauna ta zauna tana jiran Habib ya gama wayar. Hajiya Turai ko, fad'a tai kema Habib ta ce yaba Hassana waya ya k'i tun da tazo basu yi waya ba, kuma tana kiran wayarta a kashe, dan haka yanzu ya bata. Habib mik'ama Hassana wayar ya yi. Hassana ko kallan Habib ta yi, tana tambayar shi waye Oga Habib? ". "Kisa a kunnanki kiji". Habib ya ba Hassana amsa".


Hassana sosai tayi murna jin Muryar Hajiya Turai da ta yi. Bayan sun gaisa ne, Hajiya Turai ke tambayar Hassana lafiya tana kiran wayarta bata zuwa? ". "Mommy ruwa ta fad'a nayi-nayi tak'i kawowa". Hassana taba Hajiya Turai amsa ".


"Zan kawo miki wata kinji daughter ". Hassana godiya ta yi ma Hajiya Turai dan tana son waya sosai. Bayan Hajiya Turai ta kashe ne, Hassana ta kalli Habib ta ce, "Ina wuni Oga Habib ". Habib banza ya yi da Hassana ya ci gaba da danna wayar shi. Hassana kuma cikin sanyin murya ganin Habib ya juya mata baya sosai, dan ko inda take yak'i kallo, kuma kwana biyu ba haka yake mata ba, hakan yasa Hassana cikin sanyin murya ta ce, "Oga Habib? ". Habib banza ya yi da Hassana. Hassana kuma bata gaji ba, ta kuma cewa, "Oga Habib! ". Nan ma Shiru ba amsa. Hassana kamar za tai kuka ta ce, "Oga Habib kaga ko hannuna inajin ya yi tsagewar k'ashi, bana iya d'aukar abu mai nauyi da shi, kuma bakaji ba yadda ya ke min zafi". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Muga hannun? ".Hassana da gaske hannun yana mata zafi amma ba sosai ba, mik'ama Habib hannun ta yi". Habib ko na amsar hannun ya rik'e ya na ja mata shi da k'arfi sosai, yana d'an bubbuga hannu".


Hassana da k'arya take hanun ba wani ciwan kuzo kugani hannunke mata ba, ai take ta fara kuka, tana cewa, "Wayyo Oga Habib basshi haka dan Allah ". Habib ko be bari ba cigaba da latsama Hassana hannun ya yi, ita kuma tana ihu, tana rirrik'e hannun Habib. Habib da katawa ya yi yana kallan Hassana, ya ce, "Kin sha maganinki? ". Kai Hassana ta d'agama Habib."banyar da ba, je ki d'akko in gani? ". Cewar Habib".


Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Nafa manta shi a Office d'inka". Habib shiru ya yi ya ci gaba da danna wayar shi. Hassana kuma so take taima Habib maganar su Billy ta rasa yadda za tai, sai zuwa can ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib dan Allah karka dawo da su Billy sai nan da sati, kaga nima ai kaji dad'i kace na fidda kai kunya ko?, dan Allah Oga Habib kabar su sai sun yi sati, dan Allah, kaji Oga Habib ". Habib ko kamar jiran Hassana ya ke, ya aje wayar hannun shi, ya kalli Hassana ya ce, "Wallahi! Wallahi!! Ida har aka kuma fad'a dake a Sanat... ". Habib kai ya girgiza. "Tom aini bani ke to nan su ba, suke to nona. Hassana kunun da ta damama Habib ta mik'ama mai ta ce, "Oga Habib ga kunun ka karya huce". "Bazan shafa".Habib yaba Hassana amsa".


Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib me yasa?". Kin b'ata min rai yau". Hassana dama tun a sanat da ta kori su Billy taga irin kallan da Habib yake mata, ita yanzu tashin hankalinta d'aya kar ya ce zai cireta a matsayinta".


Hassana kallan Habib ta yi, cikin sanyin murya, ta ce, "Oga Habib dan Allah ka yafe min, Allah bazan kuma ba, koma sun min zan rik'a banza da su, kuma dan Allah karka cireni a matsayina". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "da ga yau karki kuma fad'a da kowa!? ". Ya fad'i maganar cikin gargad'i ".
"Allah bazan kuma ba". Cewar Hassana, sanna ta d'akko kunun ta ce, tom gashi kashi".


Habib amsa ya yi, yana sha. da yake Habib kan 3 seater ya ke zaune,kafin Habib ya gama shan kunun Hassana da ke kusa da shi zaune, gafen kujerar ta kwanta, tana jiran Habib ya shanye kunun ta fita da Cup d'in. Sai dai Kafin Habib ya shanye kunun bacci ya kwashe Hassana. Habib ko yana gamawa ya ce, "Nagama tashi karki bacci, ki je ki kwanta". Abinda Habib ko bai sani ba, Hassana har ta yi baccinta".


Habib jin Hassana ta yi mai shiru, kallanta ya yi, abin mamaki sai yaga ashema baccin ta ke. Habib

31 / 41