OGA HABIB Bacewa da Samuwa by Faddy baby

Author :  Faddy baby Category :  Romance

Chapter   14 / 41

39K to 42K   out of 121.2K words

WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

Facebook group :
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Allah ka zaunar da k'asarmu lafiya, Allah kabamu kwanciyar hankali ak'asarmu, Allah ka tsare musulminka aduk inda yake, dan Allah jama mu daure murik'a karanta HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL 11 duk sanda muka idar da sallar asuba. A bisaga Allah ya bamu zaman lafiya ak'asarmu.


Shafi na 32&33.



Farida na rufe k'ofar ta gudu ta bar gurin cikin jin dad'i.
Habib ko nashan maganin da Hassana ta bashi baifi da minti goma ba, ya fara jin wani irin yar ajikin shi. Mik'a Habib ya farayi yana kuma damtse hannun Hassana da yake rik'e da shi, yana kuma jawo ta kusa da shi.
Ita dai Hassana kallan mamaki tabi Habib da shi dan, idan ya rik'e hannunta shikenan daga haka, bai jajjawota jikinshi kamar yadda ya ke yi yanzu. Hassana kallan Habib ta yi ganin yadda ya ke rintse ido yana kuma damk'e hannunta yana ja wota jikin shi, kamar zai sata kan cinyar shi. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce cikin sanyin muryarta, "Oga Habib baka da Lafiya ne? ". Habib shi dai kallan Hassana kawai ya yi, ita kuma Hassana Sannu tai mai ganin yadda ya ke makyarkyatar sanyi, yana kuma damk'e hannunta. Can Hassana sai dai taji Habib ya fisgota da k'arfi ta fad'a kan shi, dan sai da sukai karo yana yin yadda ya fusgota d'in. Kafin Hassana ta yi yin k'urin yunk'urawa ta tashi daga jikin Habib sai ta ji, ya finciko hijab d'in jikinta yana k'ok'arin cirewa".

Hassana rik'e hijab d'in ta tayi sosai tana kallan Habib dake ciku-cikun cire mata hijab.
Hassana ganin yau Habib d'in, wani iri bakamar yadda ta saba ganin shiba, ga shi wai har yana ciku-cikun cire hijab d'in jikinta. Hassana dak'arfi ta fusge hannunta a hannun Habib, sannan ta juya da saurinta da niyyar fita. Sai dai ina kafin ta kai bakin k'ofar Habib har ya risketa, yana juwa ya rik'ota ta baya, yana rik'eta kuma Allah ya bashi sa'a ya fisge hijab d'inta"

Kafin Hassana ta gama tunanin lafiya sai dai taji Habib na k'okarin yaga rigar da ke jikinta. Nan fa kusan damme ya b'arke tsakanin su. Habib k'okarin cire rigar dake jikin Hassana ya ke, Hassana kuma tak'i bashi damar haka.
Da yake zani ne single ajikinta, hakan yasa Habib yana jan shi ya kwance. Hassana k'ara ta saki ganin Habib ya kwance zanin jikinta. Hassana mak'alk'ale Habib ta yi sosai tak'i bashi dama. Habib ko da dama bacikin hankalinshi ya ke ba, kuma ank'ara birgera k'wak'walwar, hakan yasa ya zamarma Hassana mahaukacin asali. Habib da k'afin tsiya ya yi wurgi da Hassana kan caution, sannan ya yi saurin binta, kan caution d'in.
Hassana ko kafin Habib ya zo tayi sauri ta tashi zata gudu. Habib garin ya jawo Hassana yana jawota ya jawo rigar jikinta ta yage . yarage daga Hassana sai brazier da pant. Habib cikin fitar hayyaci ya cire komai da ke jikin shi ya tsaya haihuwar uwarci".

Hassana cikin rud'ewa ta fara ihu tana kiran Hajiya Turai , da Oga Bilya.
Duk yadda Habib zai yi ya kwantar da Hassana ya kasa, dan firgitar da Hassana ta yi sai hakan yasa mata k'arfi. Habib ko cikin rashin sanin meye ya zai aikata, meye ya ke yi bai sani ba. Ya damk'i breast d'in Hassana. K'ara Hassana ta yi jin azabar yadda ya damk'i breast d'in ta. Cup d'in da ke kusa da Hassana na maganin da Farida ta bata ta ba Habib, ta d'akko ta buga ma Habib shi tun k'arfinta akai".

Habib jin azaba ya sakin Hassana yana tab'a gurin da Hassana ta buga mai cup d'in".

Hassana ko Habib na sakinta ta tashi ta ruga da gudu. Tana rugawa Habib ya bita. Kafin ya kamata Allah ya bata sa'a tab'ud'e toilet d'in bedroom d'in Habib ta shige ta rufe tana nishin wahala".

Habib ko bakin k'ofar ya tsaya yana jijjiya k'ofar kamar zai b'alleta".

Hassana sosai ta rud'e dan yadda ta ji Habib na jijjigar k'ofar gani ta ke zai b'alleta. Habib ko gajiya ya yi da jijjiga k'ofar ya zauna jikin k'ofar ya jingina da ita".

Hassana tana jiyo nishin Habib daga toilet d'in. Hassana shiru ta yi da kukan da take yi tanaaa sauraron nishin Habib tare da tunanin me ya sa mai haka. Wani tunani yazoma Hassana, dan tabbas idan bazata manta ba, itama kusan shigan haka ta yi lokacinda Farida ta bata magani ta sha ta ce mata inji Hajiya Turai. Tom wannan wana irin magani ne haka?, kuma meyasa nima da nasha naji haka?, sannan meyasa Hajiya bata tab'a ban da hannunta ba sai dai ta aiko Aunty Farida ta kawo min?, shiru Hassana ta yi, tana nazarin tambayoyin da tai ma kanta, tana naiman amsarsu. "Kai gaskiya wannan maganin akwai alamar tambaya atare da shi,tom amma kuma Aunty Farida ai bazata aikata abinda zai cutar da Oga Habib ba, ko da yake ai bashi zai cutar ba ni zai cutar, dan idan har tunanina haka ne da ace Allah yaba Oga Habib sa'a akaina tom da Fyad'e ya ke k'ok'arin yi min, kai gaskiya ban yarda da Aunty Farida ba, tom wai meyasa ma rannan ta maran dan nace mata banba Oga Habib maganin da taban in bashi ba?, tom kuma nima ai aranarne nashiga irin kusan halinda Oga Habib yashiga yau, dan idan bazan mantaba nima ranar haka naima kaina tsirara, kai gaskiya ban yarda da Aunty Farida ba, tom ni yanzu wazan fad'amawa abinda ke faruwa ya taimakan da amsar tambayoyina?. Gaskiya bazan iya fad'ama Hajiya ba, kuma bazan iya fad'ama Oga Bilya ba,inajin Jimmai zan fad'amawa dan nayarda da Jimmai tana ban shawarwari masu kyau, amma gaskiya ban yarda da maganin nan da Aunty Farida ta banba".

Hassana ta dad'e a toilet d'in Habib tana tunane-tunananta. Tun tana jiyo nishin Habib har taji shiru bajin nishin shi. Hassana ta dad'e sosai a toilet d'in, dan har sai taji kiran sallar azahar sannan ta lallab'a ta bud'e k'ofar a hankali ta lek'o kanta. Kwance Hassana taga Habib akasa kusa da toilet d'in yana bacci.Hassana sosai hankalinta ya tashi ganin yadda taga Habib, dan ita sai yanzu ta kallai, sauri ta yi ta kauda kanta tana jinta duk wani iri bad'i. Hassana fita zata yi daga bedroom d'in Habib sai kuma taji tsoran Bilya yazo yaga Habib a haka, gudin zargi Hassana badan ta so ba, ta je falon ta yi sauri ta jira hijab d'inta ta d'aura zaninta, rigar kuma ta riga ta yage sosai bazata sawuba, hakan yasa ta k'udin-dine rigar ta tusata a kayan Habib, sannan ta d'akko kayan Habib tana rinrintse ido ta samai, tana samai tana duk addu'ar da tazo bakinta dan tana tsoran karya tashi. Hassana nagama sama Habib kayan shi ta yi sauri ta fita daga d'akin Habib d'in".

Hassana da sauri-sauri kamar munafuka ta koma site d'in su na 'yan aiki. Hassana na zuwa taga Jimmai sai aikin bama flower's d'in site d'in su ruwa ta ke, Hassana inda Jimmai ta ke ta k'arasa ta ce, "Sannu da aiki". Murmushi Jimmai ta yi ta ce, "Yauwa Hassana aike ke aiki, ke da ke kula da Ogan mu". Hassana hannun Jimmai ta kamo ta ce, "Jimmai dan Allah zoki ci wata magana, Wallahi abinda ya daman, narasa wanda zan gayamawa". Jimmai jan hannun Hassana ta yi suka samu guri suka zauna, Jimmai kallan Hassana ta yi da damuwa dan ita har ga Allah bata son damuwar Hassana, Jimmai cikin sanyin murya ta ce, "Hassana karkiji komai kinji kifad'amin duk da muwarki, ni kuma zan baki shawara irin wanda zan ba k'anwata, ko kuma kaina". Hassana kallan Jimmai ta yi ta ce, "Jimmai ya Aunty Farida su ke da Oga Habib ne? ". Shiru Jimmai ta yi jin tambayar da Hassana tai mata, sannan ta ce, "Kin san Hajiya Murja ai ko?, friend d'in Hajiyar Oga Habib, tom ita ce ta haifi Aunty Farida, Farida 'yar k'awar Hajiya Turai ce". Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana meyasa ki kai min wannan tambayar? ". Shiru Hassana ta yi, sannan zuwa can ta ce, " Sister Jimmai Shekaran jiya Aunty Farida ta kawomin wani magani ta ce, wai inji Hajiyar Oga Habib, ta ce insha in ba Oga Habib shima yasa, nayi mamaki sosai jin wai insha, tom amma da naima Aunty Farida magana sai ta balbaleni da fad'a wai ita bata da hankaline da bani aka ce taba ba zata ban, wai suma duk sun sha dan haka nima insha. Haka na d'auki maganin nasha". Shiru Hassana ta yi sannan ta ci gaba da cewa, "Sister Jimmai aranar d'akin Oga Habib na kwana, dan ina shan maganin nafita daga hayyacina, wani irin abu narik'a ji ajikina, haka na tashi naganni tsirara haihuwar uwata, muna kwance tare da Oga Habib guri d'aya . Wannan shine dalilinma da yasa kikaji nace bazan kuma kaima Oga Habib abinci ba, ko magani. Tom bayan nabar part d'in Oga Habib na dawo nan sai ga Aunty Farida tazo tana tambayata wai me Oga Habib ya yi min, na bata amsa da bai min komai ba, wai k'arya nake in fad'a mata dan tasan komai wai ai ta ganni ina kuka Ina fad'ama Oga Bilya, nan dai nace mata ta tambayi Oga Bilya ni bance mai ko mai ba, na dai ce mai bazan k'ara ba Oga Habib abinci ba, ko magani. Shine ta ke tambayata wai na ba Oga Habib maganin da taban in bashi. Wallahi sister Jimmai bikiji ba marinda tai min da nace mata ban bashi ba na manta. Tom jiya ba tazo kirana ba? ". Kai Jimmai ta d'agama Hassana. Hassana ko ta ci gaba da cewa, "Tom abinci ta rok'an in kaima Oga Habib, bayan na kaimai abincine ta biyoni da wani magani wai in ba Oga Habib inji Hajiya, ni kuma na amsa bayan Oga Habib ya gama jin abinci na bashi. Wallahi sister Jimmai tunda naba Oga Habib maganin ya fita daga hayyacinsa, ya kamani ya rik'e". Hassana d'agama Jimmai hijab d'inta ta yi, ta ce, "kin gani sister Jimmai harta rigata sai da ya yagata".

Jimmai cikin tashin hankali ta ke, tambayar Hassana, ta ce, "Hassana baidai miki komai ba ko? ". "Eh sister Jimmai bai min komai ba, amma Allah ne kawai ya k'watan ahannun shi, amma niya yayi ya yi min Fyad'e Allah ya amsheni daga wajan shi".

"Tom Alhamdulillah". Cewar Jimmai, sannan ta yi shiru tana tunanin me yasa Farida ta aikata haka. Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana ke a tunaninki me yasa Farida ta ai kata haka? ". "Tom nima bansani ba, nayi nazari sosai na kasa ganowa". Shiru Jimmai ta yi sannan ta ce, "Tom ni dai nasan Aunty Farida na son Oga Habib sosai, dan ance saboda shinema ta ke zuwa gidannan. Tom amma kuma ai ba zata so wani abu ya faru irin haka ba, tsakaninki da Oga Habib ba, dan Aunty Farida na son Oga Habib sosai, saboda sun tab'a fad'a da wata itama yarinyar friend d'in Hajiyar Oga Habib ce, akan Oga Habib". Shiru Jimmai ta yi, Sannan ta ce, "Tom koda gaske ta ke Hajiyar ce ta aikota ta kawo maganin, dan gaskiya Aunty Farida ba za tai abinda zai sa Oga Habib ya kusance kiba, dan tana kishi akan shi sosai gaskiya". "Tom nima haka dai nake gani". Cewar Hassana".

Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana kin san me? ". Kai Hassana ta girgizama Jimmai. Jimmai ta ci gaba da cewa, " Idan har Aunty Farida ta zo ta tambayeki kin ba Oga Habib maganin, ki ce mata Eh, tom daga nan duk tambayar da tai miki, shikenan magana ta k'are zargi ya hau kanta". "Tom shikenan, Sister Jimmai sai in tazo d'in".

Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana yaune fa zaki fad'ama Hajiyar Oga Habib sak'onta na amintarki, dan haka ki tashi yanzu kije ki sanar da ita kin abince,Allah bashi kamar yadda ta ce duk abinda kike so za tai mik, ki ce mata kina son jali ke".Shiru Hassana ta yi, sannan ta ce, "Sister Jimmai Allah zan amsa ma Hajiya ne kawai, amma zuciyata ta k'i aminta da maganar har yanzu". "Karkiji komai Hassana dan k'ilama har ayi auran agama Oga Habib ba zai sani ba, inma shikike tsoro, dan itama Hajiya ta san halinshi sosai bazata bari ya sanda maganar ba, dan haka kije ki fad'ama Hajiya kin amince, dan kar taga kamar kina jamata raine".

Hassana ta shi ta yi tanufi part d'in Hajiyar Oga Habib, da tarin fargaba aranta, danma hankalinta nad'an kwanciya inda ance Oga Habib ba zai san damagar auran ba, daga ya warke shikenan. Hassana cikin sanyin muryarta ta yi sallama ta shiga falon Hajiyar Oga Habib ".

Hajiya Turai na zaune ta ji sallamar Hassana, d'agowa tai tana kallan Hassana. Hassana cikin girmamawa ta gaida Hajiya Turai, sannan ta ce, "Hajiya maganar da mu kai jiya, na amince...........




Tofa ko Hajiyar Oga Habib zata amince???,🀐🀐🀐


Koya Farida zata yi, idan ta gano gaskiyar Habib bai kusanci Hassana ba??? 🀐🀐🀐🀐


Idan kin karanta daure ki yi comment sister 🀝


Share
&
Comment please πŸ™.

πŸ“š OGA HABIB πŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI(Faddy baby).


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

Facebook group :
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Ina mai farin cikin taya k'asata Nigeria murnar cika shekara 61.Allah ka k'aro mana zaman lafiya, da kwanciyar hankali mai d'aurewa ak'asarmuπŸ‘πŸ‘πŸ‘.

*MUTUWA ZATA IYA RISKARMU DAGA YANZU ZUWA KOWANNE LOKACI KO A KUSA KO A NESA ALLAH SHINE MAI YANZU YANZU, ALLAH KASA MU CIKA DA IMANI.


Shafi na 34&35.



Hassana cikin girmamawa ta gaida Hajiya Turai, sannan ta ce, "Hajiya maganar da mu ka yi jiya na amince". Hajiya Turai cikin jin dad'i ta rungume Hassana, ta ce, "Nagode sosai my daughter, Allah ya yi miki albarka, me kika so in biyaki da shi". Shiru Hassana ta yi, dan ita harga Allah dan Allah ta yi, badan Hajiya Turai ta biyata ba".

Hajiya Turai jin Hassana ta yi shiru, kan Hassana ta d'ago dake duk'e ak'asa ta ce, "My daughter karkiji komai kinji, fad'amin da me kike so in biyaki da shi". Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "A'a Hajiya, ba komai dan Allah nayi miki". Hajiya Turai k'ara rungume Hassana ta yi tana mata duk addu'ar da tazo bakinta, ta ce, "Nagode miki my daughter Allah ya saka miki da mafificin alkairi, yanzu zan kira Bilya in mai magana idan anshiga sallar azahar sai a d'aura auran lokacin". Hassana d'agowa ta yi tana kallan Hajiya Turai gabanta na fad'uwa ta ce, "Uhm Hajiya ba kince auran sirri za aiba?". "Eh My daughter, ko yanzuma ai auran sirrine, inda kinga ba friend's d'in Habib da zai san da maganar auran kod'aya, sannan nima babu 'yan'uwana da suka san maganar,dan haka karkiji komai, indai Habib ne ma bazai san da maganar auran ba, inda nalura tsoran shi kike ji". Hajiya Turai ta idasa maganar tana murmushi,dan sosai ta ji tana farinciki da amincewar da Hassana da ta yi".

HajiyaTurai kallan Hassana, ta yi, ta ce, "Shikenan my daughter nagode, kije anjima zan ne me ki". Hassana tashi ta yi ta tafi".

Hassana na fita daga falon Hajiya Turai suka ci karo da Farida. Farida da sauri ta kamo hannun Hassana ta ce, "Yauwa dama ke nake naima , naje nai manki site d'in ku banganki ba". Farida jan hannun Hassana ta yi suka matsa can gefe, sannan ta kalli Hassana ta ce, "Lafiya jiya bayan na baki maganin da Mommy ta ban tace kiba Oga Habib naji k'ararki? ". Hassana shiru ta yi tana kallan Farida, tabbas zarginsu ya tabbata".

Farida ko cikin k'osawa da Hassana ta bata amsa, ta bugama Hassana tsawa ta ce,"Ke bada ke nake ba!, zaki tsaya kallona, nace lafiya naji kinyi k'ara ? ". Sana cikin son taka ma Farida ta ce, "Auntu Farida k'ara kuma?, anya kuwa ni ce". Gaban Farida ne ya fad'i, amma sai ta daure ta ce, "Ke bansan shirme,angaya miki banji bane, me yasa me ki kikai k'ara alokacin?, ko Oga Habib ne ya yi miki wani abun? ". Hassana kallan Farida ta yi, sannan ta ce, "Eh Aunty Farida na tuna, Oga Habib ya yi min wani abu". Farida cikin sauri da k'osawa, ta ce, "Me ya yi miki? ". "Aunty Farida glass Cup ya bugamin a kai". Farida cikin jin haushin abinda Hassana ta ce, ta ce, "Sannu, bayan nan fa be miki komai ba, danni naji k'ararki sosai, kina kiran Mommy da Bilya, dan haka fad'amin gaskiya ". Hassana cikin danne mamakin Farida da ta ke yi, ta ce, "Aunty Farida Allah bai min komai ba, k'arar da kikaji nayi zafin Cup d'in ne yasani k'ara, amma babu wani abu". Shiru Farida ta yi tana nazarin maganganun Hassana azuciyarta, sannan ta ce, "Na bani kaddai ace Oga Habib bai kusanci yarinyar nan ba! ".
Farida cikin rud'ewa ta kalli Hassana ta ce, "Ke kinko ba Oga Habib maganin da nace miki Mommy ta ce abashi? ".

"Eh Aunty Farida na bashi". "Kinfa bashi kika ce? ". Farida ta tambayi Hassana. "Eh Wallahi Aunty Farida na bashi".Farida cikin rashinsanin me ta ce, ta ce, "Amma kuma kika ce Oga Habib me biki komai ba". Hassana cikin mamakin Farida, da al'ajabin dama da akwai abinda ta k'ula kenan, ta ce, "Aunty Farida na ce miki ya buga min Cup mana". Wata irin tsawa Farida ta bugama Hassana, ta ce, "Dan Uwarki abinda na tambayeki kenan!, tom nufina Oga Habib bai kusanceki ba? ". Hassana cikin tashin hankali da al'ajabi ta ke kallan Farida, sannan ta ce, "Subhalallah Aunty Farida wannan kuma wata irin magana ce? ". Shiru Farida ta yi dan sai alokacin ta dawo hayyacinta ta tuna da

14 / 41