Author : Faddy baby Category : Romance
sannan ta d'akko wani bargon ta mik'ama Hassana, tai mata good night ta wuce".
Hassana koda ta sake tab'a jikin Habib sanyi ta ji sosai, alamun zazzab'in ya sauka, Alhamdulillah ta ce sannan ta ja masu bargon ta rufe su".
Washe gari Hassana sai 6:50Am ta farka, da sauri ta sako gado ganin gari ya yi haske, Hassana na sakkowa mutuminta ya biyota. Alhamdulillah dan yauma tare sukai alwallah duk yadda ta yi ya yi, Hassana ko ga yadda taga Habib na kazar-kazar d'in shi tasan sauk'i ya samu".
B'angan Farida ko tunda taji ihun Hassana tana nai man agaji, ta shirya ta bar gidan, dan cewar ta zatafi farin ciki tazo ta iske Habib ya yi ma Hassana irin wujijjigar da yake ma mutane, ala bashi sai ta taho maganin da malam ya ce zata bar gidan da kanta ba sai an koreta ba, indai aka zuba shi ta taka ko ta k'etare".
Washe gari Farida da wuri ta yi sammakon dawowa, sai dai abinda idonta ya gane matane ya tada hankalinta, Hassana da Habib zaune a derning space, suna break fast, hannu Habib rik'e da na Hassana, ga Hajiya Turai gefe guda. Farida cikin rud'u ta juya zata fita, Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, "Farida zonan!! ........... .. ✍️
Idan kin karanta d'aure ki yi Comment sister 🤝
Share
&
Comment please 🙏.
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
Shafi na 44&45.
Farida gefan Hajiya Turai ta je, ta tsaya ta ce, "Mommy gani? ". Hajiya Turai ta dad'e tana kallan Farida sannan ta ce, "Farida daga ina kike? ". "Daga gidan Mommyna". Shiru Hajiya Turai ta yi, tana kallan Farida sannan ta ce, "Farida kina so ki canza hali,saboda da duk inda zaki kina sanar min, amma yanzu sai dai ki fita kai tsaye, tom kar hakan ya kuma faruwa kar ki sake fita kibar gidannan bada sanina ba,ke koda ban gari karki kuma". Hajiya Turai na kai haka ta ce, "zaki iya tafiya".
Farida fita ta yi tana mai jin zafin Hajiya Turai ta na tuhumarta inda ta je gaban Hassana".
Hassana ko bayan sun gama break fast, kallan Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Mommy bari in d'akko kayan da zan sa ina son zanyi wanka". "A'a ki kama Habib ku tafi tare, abu daga zuwa gaisuwa ai anyimin k'ok'ari nagode".
Hassana ta d'an jima zaune, sannan ta tashi ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Mommy zan tafi, ina so zanyi wanka ne? ". "Tom daughter nagode sosai,dan Allah arik'a kulawa da rubutun Habib inda muna ta k'ara ganin sauk'i ". Cewar Hajiya Turai. "Insha Allah Mommy ".
Hannun Hassana cikin na Habib a haka suka jera suka koma part d'in Habib. Hassana na zuwa ta shiga wanka ita da mutu minta, inda ta cire mai shirt d'in jikin shi da dogon wandon jeans d'in shi, ta bar shi daga shi sai d'an garami na ciki. Suka shiga tare kamar yadda suka sabo, Hassana sai da ta gama wankanta sannan ta kalli Habib da ke ta famar jagwalgwalan wankan shi. Hassana amsar sosan ta yi daga hannun Habib ta wanke mai jikin shi tass, sannan suka fita".
Hassana lotion ta d'akko zata shafa, Habib ya mik'o hannu zai ta tsa kamar yadda yaga tana yi. Hassana d'akko ke man tayi tab'oye tana ta tsa kad'an-kad'an tana shafama jikinta, saboda Habib ko ta bar mai ba shafawa ya ke ba, wasa kawai ya ke yi da shi. Hassana sai da ta gama shafa man, sanna ta shafama Habib shima, tana gama shafa mai ta ciro mai wasu kayan ta sa mai kamar yadda ta saba sa mai tanayi tana rintse ido gudin kar tai mugun gani, tana gama sa mai kayan shi ta bashi rubutun shi yasha".
BAYAN SATI D'AYA.
Yau sati d'aya kenan da zuwan Hassana part d'in Hajiya Turai ita da Habib, kuma tun daga ranar bata k'ara zuwa ba, sai dai Hajiya Turai kullum zata shigo ta ga jikin Habib. Maganar abinci ko Hajiya sosai ta jama Maimaina kunne akan karta kuskura ta ka mata da aikata mata rashin gaskiya, Hajiya Turai duk da kunnan da ta jama Maimuna hakan bai mata ba, duk lokacin Maimuna zata yi girki takan je gun ta zauna. Farida ko Hajiya Turai ta hana ta fita gaba d'aya, dan tana jin tsoran fitarta gani ta ke kamar wani abun zata iya zuwa ta yima Habib".
B'angaran Farida ko, sosai ta shiga damuwa da fitar da Hajiya Turai ta hanata yi yanzu,Hassana sosai ta dage wajan kula da Habib, dan yanzu ta gama sabawa da mak'ale mata d'in da Habib ya ke yi, na duk inda zata ya ke binta, toilet ko ta gama sabawama da binta d'in da ya ke yi. Sosai Hassana ta ke kula da ba Habib maganin shi, duk da dai har yanzu babu wani cigaba da suka k'ara gani game da Habib d'in, sai dai yanzu babu ruwan shi da kowa. Yanzu haka Hassana zaune ta ke tana ba Habib magungunan shi, Hajiya Turai ta shigo, Hassana cikin jin dad'in ganin Hajiya Turai dan ta fara sakin jikinta ta ita, ta ce, "Oyoyo ga Mommy ". Murmushi Hajiya Turai ta yi, sannan ta zauna kusa da Hassana, Hajiya Turai waya ta mik'ama Hassana ta ce, "Daughter ga wayar nan kirik'eta a hannunki zan rik'a kiranki akoda yaushe inajin jikin Habib, gurin aiki sun matsamin da kira, yau zan tafi jirgin 6:00 pm zan hau"
.Numfasawa Hajiya Turai ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, "Daughter zan sama muku kayan abinci a kitchen ki rik'a girka muku, kinga yanzu bananan, duk da dai na hana Farida fita ko ina, daughter ki kula sosai dan Allah,Farida kuma duk lokacin da ta kuma zuwa ta sa meki tai miki magana ki fad'amin, kuma karki yadda ta kuma baki wani abun ta ce injini kiba Habib ki amsa".
Sosai Hajiya Turai taita ankarar da Hassana wasu abubun, duk da bata fito fili ba ta fad'a mata dalilin ciwan Habib d'in ba".
Hajiya Turai fita ta yi tasa aka shigomasu Hassana da duk wani abinda zasu buk'ata na girki, aka samu su a kitchen d'in Habib, sannan Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, "daughter bari zan shirya nan da minti 30 zan tafi".
Hajiya Turai cikin k'ank'anin lokaci tagama shirinta ta, sannan ta shiga part d'in Habib, Hajiya Turai cikin sanyin muryar ta ce, "Daughter na tafi kirik'a aje wayarki kusa da ke ". Hassana cikin sanyin murya mai cike da rauni ta ce, "Tom Mommy Allah ya kiyaye hanya ya kaiki lafiya".
Haka Hajiya Turai ta tafi tana mai jinta duk ba dad'i, tana mai tunanin aje aikin kawai zatai ta zo ta zauna da d'anta".
Haka Hajiya Turai wannan karan ta yi tafiyar duk bata jin dad'in tafiyar, ko da Bilya ya kaita airport Hajiya Turai kallan Bilya ta yi, ta ce, Bilya dan Allah karka manta da amso rubutun Habib duk k'arshe sati". "Insha Hajiya bazan manta ba". Hajiya Turai kud'i ta ba Bilya sannan ta tafi".
Hassana ko jin abinda Hajiya Turai ta ce mata baza a kawo masu abincin dare ba yau, , ya sa Hassana na idar da sallar magriba ta shiga kitchen tai masu jolop d'in indomie".
B'angaran Farida ko tana ganin Hajiya Turai ta tafi, ta kira Mahaifiyarta awaya, dama kuma Hajiya Murja ce ta ce ma Farida ta yi hak'uri da fita kamar yadda Hajiya Turai ta hanata, sai ta tafi inda ta kusa ta fiya. Hakan yasa Farida yin hak'urin dole ba dan ta soba. Hakan yasa Hajiya Turai na tafiya Farida tashirya ta nufi gidan Mahaifiyarta".
Bayan Farida ta isa gidansu ne, Hajiya Murja kallan Farida ta yi, ta ce, "Farida ki ka ce min Yaron nan har yanzu bai kusanci yarinyar nan ba? ". Shiru Farida ta yi kamar ba za tai magana ba, sannan ta ce, "Mommy nifa banyi niyyar kuma mai mata maganarnan bama, na ce miki babu abinda ya shiga tsakanin su, kuma Mommy ni daga yau bazan k'ara zuwa gurin Malamin nan ba, wai shi mai biyan buk'ata dol..... ". Hajiya Murja saurin rufe ma Farida baki ta yi, ta ce, "Farida ki yi shiru mana, kibar fad'in haka, amma ni nasan Malam Mai biyan buk'ata dole ya iya aiki, kawai dai akwai kuskuran da aka samu, ki yi hak'uri ki tashi muje". "Kin san Allah Mommy bazan tafi ba na gama zuwa gun mak'ary.... ". Nan ma Hajiya Murja saurin k'ara rufe ma Farida baki ta yi, ta ce, "Farida kiban dama ta k'arshe daga wannan karan in dai mukaje gurin Malam buk'atarmu bata kuma biyaba, tom Nijar zamu tafi". Farida kallan Hajiya Murja ta yi, ta ce, "Kin d'auki alk'awari?". "Wallahi Farida dagaske nake miki, ni kaina nagaji da sab'anin nan da ake samu, yanzu tashi mu tafi, indai wannan karanma bai yi ba, sati mai zuwa Wallahi Nijar zamu tafi, kima kwantar da hankalinki, sai kin auri Habib koda ko abinda na mallaka zai k'are Wallahi sai kin aurai". Farida kwanciya ta yi jikin Mahaifiyarta cikin raunin murya ta ce, "Mommy kina ganin Hajiyar Oga Habib zata bari kuwa in auri Oga Habib? , ni fa 'yan kwanakin nan naga d'auke min kai ta ke, tabar zama dani ta yi fira kamar da, Wallahi mommy yanzu Hajiyar Oga Habib tafi ji da 'yar iskar yarinyar nan akaina". Farida ta idasa maganar tana kuka".
Hajiya Murja cikin damuwa ta kama Farida ta ce, "Yi hak'uri My sweet daughter kibar zubar da hawayanki kinji, Hajiya Turai kuma nina san tana sonki, kawai dai tashin hankalin ciwan Habib ne yasa kike ganin kamar tana shashshareki, ita kuma Hassana sunan ta kome?, tana janta ajikine ganin yadda ta ke kula mata da Habib, amma karki damu, auran ki da Habib babu bashi Wallahi, tashi mu tafi gun Malam kinga dare nak'arayi, danma babu wani nisa".
Hajiya Murja da Farida zaune agaban Malam mai biyan buk'ata dole. Bayan su Hajiya Murja sun gaida shine, Hajiya Murja ta ce, "Tom Malam ni dai ina d'aya daga cikin wa inda zasu yaba k'warewarka a aiki, dan kai min aiki ba d'aya ba, ba biyu ba, kuma duk naga biyan buk'ata, amma Malam wannan karan aikin yazu da matsala, dan har yanzu Yaron nan bai kusanci yarinyar nan ba, kuma gashi kace dole sai ya kusanceta shine makarin amintarshi da ita, tom amma Malam kaga yadda abin ya ke ta faruwa".
Tun da Hajiya Murja ta fara bayani Malam mai biyan buk'ata dole ya ke ta zane-zane a kaskon da ke gaban shi, har ta kai bayanin ta, sannan shima ya tsaya daga zane-zanan da ya ke yi, sannan zuwa can cikin kausassar murya ya ce, "Wannan karan bada gunkuba aka samu matsala, daga Mahaifiyar yaron ce, ita ta taimakama yarinyar , ta tai maketa, ta kub'utar da ita daga hannun shi, amma bacin haka babu abinda zai hana bai kusan ceta ba". Hajiya Murja cikin sanyayyar murya irin ta masu rok'o ta ce, "Malam dan Allah atai maka aimana wani abun dan Allah ".
Wani farin abu mai laushi ya mik'ama Hajiya Murja ya ce, "Ki barb'ata masu wannan a hanyar da zasu bi, ana so ne suk'etarashi, ke da kanki zaki ban labarin abinda ya faru".
Hajiya Murja amsar maganin ta yi, tai ma malam godiya sosai sannan suka tafi".
Bayan sun isa gida ne, Farida ta kalli Mahaifiyarta ta ce, "Mommy kin matsamin mun sake komawa gurin Malam mai biyan buk'ata dole na je, tom amma fa ki sani daga wannan Wallahi idan har Oga Habib bai kusanci yarinyar nan ba cikin wannan ritsin, tom tafiya Nigar fa ta kamamu, dan gobe zan yi abinda Malam ya ce, idan bai ba, jibi zamu tafi nijar dan haka kima fara shiri". "Karki damu Farida ai bana son Hajiya Turai ta zo ta iske yarinyar , kodan haka nima na dage, dan haka ba fata muke ba, idan har wannan karan ko ba ayi as'a ba shima, tom ashirye nake ki zo mu tafi Nijar d'in ".
Washe gari Farida da wuri ta yi sammakon komawa gidan Hajiya Turai dan zuwa ta ida aikinta, tana zuwa direct ta nufi part d'in Habib, dan acewarta gudin kar Hassana ta ki fitowa har falon zata shiga ta barbad'a masu, inda taga yanzu Habib ya bar duka".
Lokacinda Farida ta isa bakin k'ofar falon, dai-dai lokacin Hassana suka fito wanka ita da Habib, daga ita sai d'an k'aramin towel iya cinya, tana cikin tsane jikinta ta ji nocking, Hassana tunani ta fara tom waye, dan jiya Bilya ya tafi zaria, Hassana ta fiya ta yi ta ji waye dan tana tunanin ko Jimmmai ce. Hassana na zuwa bakin k'ofar ta tsaya ta ce, "Wacece..............✍️.
Idan kin karanta d'aure ki yi Comment sister 🤝.
Share
&
Comment please 🙏.
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
*ISTIGHFARI TANA SANYA NUTSUWA A ZUCIYA TANA KAWO BIYAN BUKATU WAJEN UBANGIJI UWA UBA KUMA ISTIGHFARI TANA BADA TICKET NA ALJANNA DIRECT. ALLAH KASA MU DACE*
Shafi na 46&47.
Farida da ke tsaye bakin k'ofa sosai ta ji zafin maganar Hassana, wai ita ta ke cema wacece. Farida danne zuciyarta ta yi, dan cikar burinta ta ce, "Hassana bud'e nice". Hassana ta gane muryar Farida sarai, amma sai ta nuna ma Farida bata gane ba, ta ce, "Bangane kice ba?, kece wa? ". Farida da ranta yagama b'aci cikin zafin rai ta ce, "Farida ce ki bud'emin zaki wani tsaya kina min shirman tambayoyi Saboda kina ganin kamar kin isa! ". Hassana daga can ciki, ta ce, "Ayyah Aunty Farida wai ke ce?". Farida cikin jin haushi ta ce, "Ke ki bud'emin mana, ko bikiji abinda nace ba ne?". Shiru Hassana ta yi, tana tunanin ma fita, sannan ta ce, "Ayyah dan Allah ki yi hak'uri duk da bangane mai magana ba, amma Hajiya kafin ta tafi ta hana komawaye yashigo inda Oga Habib ya ke, amma idan kanji haushi ki yi hak'uri dan Allah, ba laifina bane". Farida da ke tsaye tana sauraran Hassana tsabar al'ajabi ne yahana ta magana, zuciyarta ce ta bata amsa da cewa, "ki yi hak'uri ki fad'a mata kece mana, wata k'ila bata gane ki bane". Farida maganar zuciyarta ta bi, ta za wani uban tsaki sannan ta ce, "Ke da Allah can sakarya kawai 'yar k'auye wadda bata gane mutane, tom Farida ce ta gidannan". Hassana sosai ta ji zafin zaginta da Farida ta yi, amma sai ta shareta ta juya takoma ciki ta barta agun tsaye, dan tasan ba alkairi bane zai kawo ta, dama kuma Hajiya Turai kafin ta tafi ta jama Hassana kunne koda wasa karta ce zata bud'ema Farida ta shiga part d'in Habib, idanma tai magana ta ji ita ce, karta amsa mata. Dama kuma itama Hassana ko da taji Farida ce ba niyyar bud'ewa tai ba, kuma sai Faridar ma ta b'ata mata rai".
Farida ko da ke tsaye tana jiran Hassana ta bud'e mata k'ofa ta ji shiru, Farida cikin d'aga murya ta bugi k'ofar ta ce"Ke wai bakya jine!? ". Nanma Farida shiru ta ji, hakan ya tabbatar mata da Hassana tama dad'e da tafiya ta barta tsaye tuntuni. Shiru Farida ta yi tana tunanin yadda zata shiga part d'in Habib ta barbad'a maganin. Farida matsawa ta yi daga jikin k'ofar kad'an ta kira Mahaifiyarta, Hajiya Murja a waya".
Farida cikin k'asa da Murya gudin kar wani ya ji, ta ce, "Hello Mommy kina jina? ". Daga can b'angaran, Hajiya Murja ta ce, "Eh Farida inajinki, ya akai kin barbad'a musu maganin ne? ". Daga b'angaran Farida ta ce, "A'a Mommy Yarinyar nan ta fara rainani wai na yi nocking d'in door d'in part d'in Oga Habib yanzu, shine da tazo take ce min wai Hajiya ta ce karta bud'ema koma waye, shine yanzu nake tunanin yadda zan yi in shiga , dan bisa ga alamuma yarinyar kamar bata fitowa yanzu tunda Hajiya ta tafi, bale in zuba mata maganin ak'ofar d'aki, shine Mommy naki raki ki fad'a min yadda zanyi".
Shiru Hajiya Murya ta yi, sannan ta ce, "ki kira Hajiya turan sai ki ce mata kin zone kina son gaida Habib, amma kinkira Hassana ta ke kome?, ta ce wai kin hana, ke kuma kina son ganin Habib kiga ya jikinshi ". Farida cikin jin dad'in shawarar da Mahaifiyarta ta bata, ta ce, "Yauwa Mommy bari in kashe in kira".
Farida katse kiran Mahaifiyarta ta yi, ta kira Hajiya Turai, amma bata d'aga ba. Farida sai da taima Hajiya Turai kira goma amma ko d'aya ba tai picking ba".
Hajiya Turai ko tana ganin kiran Farida da gangan tak'i d'agawa, dan ta tsani Farida Sosai, kawai dai ita Allah ya yo ta mai kawai cice sai kai ta cutarta ta. Hajiya Turai ganin Farida tak'i daina kiranta, kashe wayar ta yi gaba d'aya ".
Farida ko koda ta k'ara kiran Hajiya Turai ta ji wayar kashe ba tai tunanin komai ba, dan atunaninta suna wani programs d'in ne, kamar yadda ta tab'a fad'a mata, in dai kakira kaga bata d'aga ba tom suna bakin aiki ne. Hakan yasa Farida ba tai tunanin komai ba, tunaninta ya bata kawai Hajiya Turai na bakin aiki ne".
Farida Mahaifiyarta ta sake kira ta shaida mata ta kira Hajiya Turai bata d'aga ba, dan haka ta bata wata shawar". Hajiya Murya cema Farida