Author : Faddy baby Category : Romance
nufi gidan Mahaifiyarta, da letter a hannunta".
B'angaran Habib ko bayan ya gama shirinsa ya fito, ya nufi part d'in Hajiya Turai. Bilya ne ya yi saurin da katar da shi ta hanyar cewa, "Barka da safiya Oga Habib, ga shi inji Hajiya ta ce in baka".
Habib amsar letter da Bilya ya mik'a mai ya yi yana mamakin ta me ye. Habib bud'e letter ya yi ya fara karantawa kamar haka. :Habib raina b'ace na kema magana, hak'ika na ji zafin maganganunka na jiya akan Hassana, kuma ina son ya zama farko da k'arshe da zaka k'ara furta mata wata kallama mai muni irin haka. Habib na koma wajan aiki, hak'ika idan na kalli fuskarka ayanzu tana tuna min ne da kalmomin da ka fad'ama Hassana marasa dad'in ji. Daga k'arshe idan har ka saki Hassana koda ko ita ce ta naimi hakan Allah ya isa ban yafema ba Habib!!! ".
Wata irin zufa ce ke keto ma Habib lokacin da yagama karanta letter. Sosai ranshi ya b'ace da furicin Mahaifiyarshi akan shi, akan me za tai mai haka, koko ana zaman aure ba so ne, tom idan ma anayi gaskiya shi ba zai iya haka ba. Habib wayar shi ya ciro ya kira Hajita Turai, amma har ta gama ringing bata d'aga ba".
Habib ranshi b'ace ya kalli Bilya ya ce, "Bilya kiramin waccan yarinyar ". Bilya ko tunda yaga haka ya yi tunanin babu lafiya, dan lokaci guda idon Habib ya kad'a ya yi ja sosai".
Bilya kallan Habib ya yi, ya ce, "Oga Habib wata yarinyar? ". "Bansani ba Bilya!, ai kasan yarinyar da nake nufi".
Bilya ta fiya ya yi yana mai tunanin anya ko ba k'arya zai koma ya yi ma Habib ba, anya idan yaga Hassana ahalinda ya ke yanzu , ba zata ji da kyau ba, tom amma kuma nasan halinshi sare zai iya zuwa da kanshi kiranta. Bilya na wannan tunanin ya isa falon Hajiya Turai............ ✍️
Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝.
Idan naga Comment da yawa gobe insha Allah zaku ga Update da wuri Allah.
Idan na raina comment tom zafa kuji shiru🤐🤐🤐.
Share
&
Comment please 🙏.
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
Shafi na 54&55.
Bilya ta fiya ya yi yana mai tunanin anya ko ba k'arya zai koma ya yi ma Habib ba, anya idan Habib yaga Hassana a halinda ya ke yanzu ba zata ji da kyau ba, tom amma kuma nasan halinshi sare zai iya zuwa da kanshi kiranta. Bilya na wannan tunanin ya isa falon Hajiya Turai. Sai dai ko da ya shiga ba kowa Falon, sallama Bilya ya yi da k'arfi, amma shiru. Bilya fita ya yi yana mai jin dad'in rashin ganin Hassana da bai ba , dan shi dama ba son isar da sak'on ya ke ba, aganin shi hakan bai kamata ba ".
Habib na tsaye inda Bilya ya barshi, Bilya ya dawo. Bilya kallan Habib ya yi ya ce, "Oga Habib inajin bata side d'in Hajiya, dan na yi magana naji shiru, babu alamun mutum".
Habib batare da ya tankama Bilya ba ya shiga mota. Bilya ma ya shigaya yaja motar suka tafi".
B'angaran Farida ko tana isa gidan Hajiya Murja, ta wurga ma Hajiya Murja letter da Hajiya Turai ta ba Hassana, ta ce, "Mommy nikam nagaji!, sai yaushe zan zama mai sa'ane, kince muje wajan wancan wai shi mai biyan buk'ata dole, ya ce sai Oga Habib ya yi hauka zan samu in aure hankali kwance, ya yi haukarshi ya gama k'arshe mai-mai kon a had'a auran da ni da wata aka had'a, yanzu munyi takakkiya munje gun wannan shima kinga shirman da yabamu, nifa nagaji zan yanke hukuncin da zai min dai-dai in huta da rayuwar bak'incikin nan da nake, Mommy koda yaushe ina fad'a miki Oga Habib shine cikar farincikina, duk wani farinciki indai ba ina tare da shiba tom jabu ne, dan haka ni yau d'in nan zan yanke hukuncina na k'arshe! ". Hajiya Murja sosai hankalinta ya tashi da furincin Farida dan ta san Farida babu wani hukuncin da zata yanke wanda ya wuce ta ce zata tafi ta barta".
Hajiya Murja hannun Farida ta kama ta ce, "Farida ki yi hak'uri kinji, bari in kira Hajiya Zaliha in mata bayanin halinda nake ciki nasan zata tai maka min da wani abun".
Hajiya Murja wayrta ta d'auka ta kira Hajiya Zaliha kamar yadda ta ce. Hajiya Zaliha na d'aga Kiran Hajiya Murja tai mata bayanin halinda ta ke ciki. Hajiya Zaliha cewa ta yi ta bari anjima zata shigo unguwar zata biyo".
Hajiya Murja kallan Farida ta yi ta ce, "Farida ki yi hak'uri kamar yadda kika ji nace miki, indai kika sa hak'uri aure zakaninki da Habib babu fashi, kinga ma dai shi Habib ba son yarinyar ya ke ba, son Hajiya Turai ko ai na banza ne inda ba ita zata zauna mai da ita ba, dan haka ke dai ki yi hak'uri ki ban nan da isowar Hajiya Zaliha". Hajiya Murja na nan sai aikin ba Farida baki take, sunanan zaune Hajiya Zaliha ta iso.
Bayan sun gaggaisa ne Hajiya Zaliha ta kalli Hajiya Murja ta ce, "Hajiya naji duk ba yaninki, amma yanzu zamu gwada da basirar da Allah ya bamu ne, dama ai k'issar baka tafi ta malam, dan haka inda Malaman sun kasa sai mu yi da k'isssar mu ta mata". Hajiya Zaliha kallan Farida ta yi, ta ce, " Haba Daughter kina so kiban kunya sai kace wata 'yar kyauye, yanzu ke baza ki iya yaudarar namiji da kalaman bakinki ba ya soki, sai kin had'ashi da Malam, Tom ni Wallahi a zamanina da kallo nake yaudarar d'a namiji, bare ke da kike da dama kina zaune gidansu. Yanzu dai ki bud'e kunnanki da kyau ji ji abinda zan fad'amiki, amma fa sai kin jure, dan shi dama mai nema sai ya jure indai kika sa juriya tom zakiga ribar abin. Yanzu dai da farko zakina yawan tusa kanki aduk abinda ya shafi Habib agidan, amma zaki yi abin a Sannu, dan karki kuskura kina nuna zak'ewa wajan tusa kanki,duk wani abu da ya dan ganci Habib ki yi k'ok'ari ya kasance ke zaki mai, ke idan zai yuwuma duk wani abu nashi ya dawo hannunki, ita kuma yarinyar dama kunce ba sonta ya ke ba, zakina nuna rashin iyawarta duk abinda tai a gabanshi, ko da ya yi kinuna mata ba haka ake ba. Shi kuma Habib d'in kina nuna mai kina jin tausan shi na had'a shi da yarinyar da akai , dan kwata-kwata ba ajinshi ba ce". Hajiya Zaliha kallan Farida ta yi ta ce, "Daughter ina fatan kina fahim tata?, yawan kwalliya ko ki dage da saka kayan da zaija hankalinshi, ita ko yarinyar in ma mai son kwalliya ce ki sanyadda zaki kina hanata".
Farida cikin jin dad'i ta rungume Hajiya Zaliha, ta ce, "Wayyo Mommy, dama nasan hakane ai da tuntuni gunki nazo da yanzu na auri Oga Habib anwuce gun".Dariya Hajiya Zaliha ta yi, ta ce, "Banni da shi daughter, k'aryar muskilanci yake. Sannan kina yawan kirana awaya ina k'ara miki wasu darisan".
Hajiya Zaliha ta dad'e tana kuma koyama Hassana dabarun da zata ja hankalin Habib, batare da ta had'a shi da boka ba ko malam".
Farida ko nagama jin k'issoshin da Hajiya Zaliha ta koya mata, ta tashi ta ce, "Ai tafiyama za tai".
B'angaran Habib ko bayan sun isa Sanat yughurt, kallan Bilya ya yi, ya ce, "Bilya ka tabbatar da yarinyar nan gobe tazo aiki! ". Magana Bilya ya ke son yima Habib amma baiga fuska ba, sai dai cewa ya yi, "Tom insha Allah Oga Habib".
B'angaran Hassana ko tsabar kukan da ta yi ne ya saukar mata da ciwan kai, hakan yasa ta kwanta, ba ita ta farka ba sai azahar, bayan ta yi sallah ne ta je derning space ta ci abinci, duk da bawani na kirki ta ci ba, danma yunwa ta ke ji inda tun jiya rabon ta da abinci".
Gaf da magriba Farida ta shigo gidan. Sai dai ko da tazo Falon bataga Hassana ba, hakan yasa ta zarce room d'in ta, wanka Farida ta yi sannan ta zauna ta rangad'a kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar kyau. Falo Farida ta dawo ta zauna, duk da tana mai fargabar kar Habib yak'i ganin wannan wankan, inda in Hajiya Turai bata nan Habib ba ya dawowa da wuri. Farida na nan zaune Hassana ta fi to ta nufi kitchen tana son had'a tea dan shi kawai ta ke jin zata iya sha".
Hassana wucewa ta zo yi zata shiga kitchen, Farida ta ce, "Ke! ". Hassana juyowa ta yi tana kallan Farida, amma harga zuciyarta bata jin dad'in ke d'in da Farida ke ce mata ba".
Farida kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ki taho min da abinda zanci". "Tom". Hassana ta ce, ta juya ta shiga kitchen ta had'a tea d'in ta, sanann ta d'iboma Farida abincin ta kai mata . Hassana mik'ama Farida abincin ta yi ta tafi, Farida kallan Hassana ta yi, ta ce, "Da hannunki zan ci? ". Hassana batare da ta tanta mata ba, ta koma kitchen ta d'akko mata spoon ta kawo mata".
Washe gari da wuri Bilya ya shigo falon Hajiya Turai yana sallama. Hassana da taji yo sallamar Bilya , fitowa ta yi, bayan sun gaisa ne Bilya ya kalli Hassana ya ce, "Dama Oga Habib ne ya aikoni ya ce, "Yau ki je aiki". Bilya na fad'ima Hassana haka ya juya ya fita".
Hassana dama ta yi wankanta, cikin kayan da Hajiya Turai ta sai mata, ta d'akko wata abaya da yake duk kusan dogayan riguma ne, tasa. Sannan ta d'auki ma yafin rigar da yake yana da girma ta yafa, takama hanya zata tafi.
Farida da fitowarta kenan, kallan Hassana ta yi damamaki ta ce, " Ke ina zaki? ". Hassana batare da ta kalli Farida ba ta ce, "Aiki". Hassana na fad'in haka ta juya ta tafi abinta. Tabar Farida gun tsaye, ko ba komai taji dad'in hakan dan hakan ya tabbatar mata Habib bai damu da Hassana ba".
Hassana ko kasan cewar babu kud'i a hannunta wajan Jimmai ta je. Jimmai da murnarta ta rungume Hassana ta ce, "Dama talaka irin mu na ganinki!, Wallahi bacin sanin da naimi ba d'an ka d'an bane da babu yadda za ai in gane ki. Hassana kinganki ko yadda kika dawo, kinyi fari kinyi k'iba.. ". Hassana murmushi ta yi, ta ce, "Uhm Sister Jimmai kenan, ni wata k'iba zan wani yi, ni dai yanzu sauri nake ban 1k a kud'innan,". Shiru Jimmai ta yi tana kallan Hassana, sannan ta kauda tunanin da ta ke yi, ta ce, "Wai Hassana ina zaki ne haka? ". "Aiki zani". Cewar Hassana ".
Jimmai kallan Hassana ta yi da alamun mamaki a tattare da ita, ta ce, "Aiki kuma?". "Sister Jimmai ban dan Allah, Allah akwai damuwa idan na je late". Cewar Hassana ".
Jimmai kallan Hassana ta yi da alamun tuhuma, ta ce, "Hassana ni na san jin sauk'in Oga Habib zaki fuskanci abubuwa da yawa agun Oga Habib, sannan zaki fuskanta agun Aunty Farida ma. Hassana ya auranki da Oga Habib yana nan ko ba ya nan?". "Bayanan". Hassana ta ba jimmai amsa. Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, "Bana son maganar wasa dan Allah, Hajiya ta raba auran ne koko? ".
Hassana shiru ta yi sannan ta kalli Jimmai ta ce, "Sister Jmmai dan Allah kiban in tafi, idan nadawo zanzo muyi magana". Jimmai shiga ta yi ta d'akkoma Hassana 1k kamar yadda ta ce, ta ba ta. Sannan Hassana ta tafi".
Hassana ba ita ta je Sanat yughurt ba sai 11:15PM. Abinda Hassana ko bata sani ba tuni Billy ta canza wata madadin Hassana. Hassana ko da ta je Sanat yughurt stuff's d'in gurin wa inda suka saba da da ita, da murnarsu suka tarbi Hassana suna tambayarta lafiya tabar zuwa shiru haka? ".
Duk wanda ya tambayi Hassana sai ta ce mai batada lafiya ne. Dariya sosai sukayi sannan Amina wadda tasu tafi zuwa d'aya da Hassana, ta kalli Hassana ta ce, "Sister ki canza wata k'aryar, amma wannan bata amsu ba, kallakki fa, yadda ki kai kyau, kika wani canza kamanni, da kyar muka iya gane ki, bacin ma wannan voice d'in taki da bazamu shaidaki ba, amma shine zaki wani ce mana kinyi ciwo ne ".ita dai Hassana murmushi kawai tai masu, sannan ta ce, "Ni yanzu tunanina d'aya yadda zamu k'arke da supervisor". Amina dariya ta yi, ta ce, "kuma kinsan rashin mutuncinta sai abinda ya yi gaba, dan Wallahi muna ganin mulkin mallaka".
Hassana kallan Amina ta yi, ta ce, "Sister Amina yanzu ya zanyi?, in da kince ta maida wata a mazaunina? ". "Zuwa zakiyi ki sa me ta sai ki mata bayanin rashin zuwaniki, amma fa karki ce mata ciwo kikai kamar yadda kika ce mana, dan Wallahi ba zata yarda ba, garama kice mata tafiya ce ta kamaki lokaci guda, k'ila idan kikaci sa'a ta yadda ki ci gaba da aiki".
Hassana da addu'a ta shiga office d'in supervisor. Hassana cikin girmamawa ta gaidata. Ita ko Billy bata gane Hassana ba, hakan yasa ta ce mata, "Lafiya?, kina son meye? ".dan ta zaci Hassana surpleaar ce. Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "Supervisor Hassana ce, wadda ta yi aiki wata Uku da suka wuce, ina b'angaran mopppiny, tom dama tafiya ce ta kamani lokaci guda shiyasa ban samu damar zuwa na sanar ba".
Kallan baki da hankali Billy tai ma Hassana, sannan ta ce, "Tom yanzu me kike so? ". "Na dawo aikina". Cewar Hassana. Kallan rainin hankali Billy taima Hassana, sannan ta ce, "Hassana ko da ace kin d'auki permission, tom mungama aiki da ke, bare kuma baki sanar ba, tuntuni mun maida wata ma zauninki, zaki iya tafiya".
Hassana a zaman da tai da Billy ta san halinta, hakan yasa bata kuma cewa ko mai ba, ta fita daga Office d'in. Hassana shiru ta yi tana tunanin komawa gida, tana kuma tsoran Habib, ga shi in tace zata gudu, bata son tafiya da aure kanta. Bilya ne ya fad'oma Hassana a rai, hakan yasa ta fita ta je side d'in da Bilya ya ke aiki ta sa mai".
Bilya cikin fara'a yace da girman kujerarki, amarya agidan Ogan mu, mai makon ki aiko akirani, sai kizo da kanki". Hassana b'ata fuska ta yi, ta ce, "Oga Bilya dan Allah bana son sunannan, dan Allah ". "Yauwa tom nima ki bar cemin Oga Bilya ". Cewar Bilya, dan shi yana ma Hassana yanzu kallan girma ne, dan ko ba komai, acewar shi akwai auran Ogan su akanta". Hassana kalla Bilya ta yi kamar za tai kuka ta ce, "Oga Bilya Allah ba zan iya fad'in sunan ka kai tsaye ba, kaine wanda ya taimaka min alokacinda banda yadda zanyi, kaine ka had'ani da manager, amma kuma in rik'a Kiran sunan ka kai tsaye, gaskiya bazan iya ba". "Shikenan nima zanci gaba da kiranki da amaryar Ogan mu". Hassana kauda maganar ta yi, dan tasan indai Bilya ne sai dai suyi ta ta yin ta , hakan yasa Hassana ta kauda maganar baki d'aya".
Hassana kallan Bilya ta yi, ta ce, "Oga Bilya Supervisor ta dakatar dani daga aiki, kasan ban sanar da itaba na daina zuwana". Shiru Bilya ya yi, dan ko ba adad'eba sai da Habib ya tambaye shi wai yarinyar nan tazo dai aiki ko.Dan haka yasan aikin Hassana dole ne, hakan yasa Bilya kallan Hassana ya ce, "Karki damu, bari in ma manager magana".
Bilya Office d'in manager ya shiga, bayan sun gaisane, Bilya ya kalli manager ya ce, "Manager dama Oga Habib ne ya ce Hassana ta dawo bakin aiki, tom ta dawo kuma supervisor wai ta kureta, shine nazo in ma magana kai mata magana".
Manager Kallan Bilya ya yi, ya ce, "Wai kana nufin yarinyar da Hajiyar M,D, ta had'a aure da shi, alokacin da yana ciwonnan? ". "Eh ita". Cewar Bilya. "A'a tom auran fa, ko kana nufin M. D, har ya warga tsa shi, dan nasan zaiyi wahala dama ya zauna da ita, dan gaskiya M. D, yana da damuwa, amma in ba hakaba ai yarinyar tana da kyau". Cewar manager yana kallan Bilya. "Tom abin na Oga Habib sai dai shiru". Cewar Bilya ".
Manager kallan Bilya ya yi, ya ce, "Babu damuwa bari in ma Billy magana ".
Manager tashi ya yi ya shiga office d'in Billy . Zama ya yi sannan ya kalli Billy, ya ce, "Sweetheart ki yi hak'uri dan Allah ki bar yarinyar nan ta dawo bakin aikinta". Billy kallan manager ta yi, sannan cikin fad'a-fad'a ta ce, "Na dai gama kula da son yarinyar nan kake, haka wancan karan da nakoreta akai ma kai min!, kuma banda ita babu wanda nake kora aiki kazo kai min magana sai akanta, dan haka Wallahi bazanyi magana biyu ba, sai dai ni in bar aikin! ". Manager kama hanun Billy ya yi ya zaunar da ita, sannan ya ce, "Sweetheart ki gane yarinyar nan bazata koru ba.. ". Billy saurin amshe zan can ta yi, da cewa, "Saboda me ba zata koru ba ?". "Saboda Oga Habib ke son ta yi aiki anan gun, kuma yanzu haka matar shi ce". Billy cikin firgita ta ce, "Matar Wa wai? ".
Manager cikin natsuwa ya ba Farida labarin yadda akai auran Hassana da Habib, daga k'arshe ya d'ora mata da cewa, " Habib yana son Hassana tai aiki anan ne dan