Author : Faddy baby Category : Romance
ya k'osa ya ji, ya ji Hajiya Turai ta ce ta da tse auran shi da Hassana".
Hajiya Turai, ta kuma cewa, "Habib, ada nayi niyyar raba auranka da daughter, amma ayanzu na fasa saboda wasu da lilaina, sannan auranka da ita wani rubutancan al'amarine, dan haka na soke maganar raba auranku, Ina fatan da ga kai har Hassana zaku min biyyya akan k'udirina? ". Habib shiru ya yi bai tan kama Hajiya Turai ba, sai zuwa can, ya fara magana cikin wata irin murya ".
Habib ya ce, "please Mommy idan maganar aure ce da kike min zanyi yanzu, kiban duk lokacinda ya yi miki, amma ki fahimci abinda nake nufi Mommy, da farko ni ban tab'a sha'awar rayuwa da mai aiki a k'ark'ashina ba, sannan Mommy Friend's d'ina zasu yi min dariya suji Ina auran staff d'ina, kuma cleaner, dan Allah Mommy ki fahimtan, ni zanma yarinyar duk abinda kike so, amma banda wannan Mommy ". Habib ya idasa maganar cikin damuwa ".
"Habib ba wai kai ba, Hassana ma ayanzu inajin na isa da ita akan maganar nan, nariga na gama magana, yau-yau d'innan zaku tare a gidanka! ". Habib tashi tsaye ya yi daga zau nan da ya ke, yana kallan Hajiya Turai, dan sosai maganarta ta k'arshe ta furgitashi".
Habib kusa da Hajiya Turai ya dawo ya zauna, ya ce, "Mommy naji na yarda zan zauna da ita, amma Mommy a gidannan dan Allah ". Hajiya Turai kallan Habib ta yi yadda ya wani rud'e ta ce, "Habib na yanke wannan shawaran ne saboda Hassana idan taci gaba da zama a nan Fad'a zasu yi ta yi da Farida, ni kuma inada kawaici bana iya korarta, shi yasa kawai na yanke shawarar ta koma gidanka da zama". Habib cikin sauri ya ce, "Mommy ni zan kori Farida yau-yau d'innan idan ke baza ki iya ba". "Habib nagama magana dan tun jiya kafin in dawo na sa anke komai agidan, dan haka bana son wata doguwar magana nariga nagama magana, dan haka zaka iya tafiya". Cewar Hajiya Turai ".
Habib bai k'ara magana ba ya tashi ya fita. Hajiya Turai saurin juyawa ta yi tana kallan Hassana jin shashshek'ar kuka. Hajiya Turai, hannun Hassana ta kamo, ta ce, "Daughter ki yi hak'uri idan na b'ata miki, amma nasan insha Allah watarana daga ke har Habib zaku fahimce ni, dan Allah daughter ki yi hak'uri na rok'eki, idan ma zaman kad'aici kike tunani zan baki Maimuna ta rik'a d'ebe miki kewa, ke dai abinda nake so da ke karki biyema miskilanci Habib dan Allah , ki gaida shi ko ba zai amsa miki ba, mahakurci mawada ci ne, yanzu kije ki yi wanka ki kwanta ki huta".
Hassana kamar jira ta ke, da sauri ta tashi ta shiga bedroom d'in ta. Hajiya Turai da kallo tafi Hassana".
Farida ko cikin tashin hankali ta fita ta kitchen ta nufi gidan Hajiya Zaliha friend d'in Mahaifiyarta".
Farida nazuwa, ta sama Hajiya Zaliha kuka. Da kyar Hajiya Zaliha ta samu ta lallashi Farida, sannan ta ce, "Yanzu daughter fad'amin me Habib d'in ya kuma yi miki? ". Farida cikin kuka ta ba Hajiya Zaliha labarin duk abinda ya faru, ta had'a mata da tarewar da Hassana za ta yi yau, kamar yadda taji Hajiya Turai ta ce".
Hajiya Zaliha lallashin Farida ta yi, sannan ta ce, "barni da su daughter in sun san wata ai basu san wata ba, yanzu bu d'aya ya rage mana inda tabar gidan da zama, ganin Habib da ita zai miki wuya, dan haka abinda zaki yi yanzu aiki zaki naima a Sanat yughurt". "Aiki kuma Mommy? ". Cewar Farida".
"Eh aiki zaki naima Farida acan, dan dole sai kina tare da Habib burunmu zai cika idan ki kai nisa da shi abin ba zai yuwu ba, dan haka gobe ki shirya kije neman aiki gun"Wani murmushi Farida ta yi, ta ce, "Tabbas wannan dama ce babba Mommy, ni kuma zanyi amfani da dabarunki in had'a da nawa". Dariya Hajiya Zaliha ta yi, ta ce, "Yauwa daughter kin fara ganewa, yanzu sai goban in kin samu aikin sai mu tsara yadda abin zai kasance". Haka Hajiya Zaliha tafa tsarama Farida yadda zata kasan ce idan ta samu aikin".
B'angaran Hassana ko, ko da ta kwanta kasa bacci ta yi, juyi kawai ta ke, dan sosai ta ki jin furgici idan ta tuno wai yau zata tare a gidan Habib. Hassana ganin kwanciyar bayi mata za tai ba, tashi ta yi ta nufi part d'in worker's d'in gidan, ta je wajan Jimmai ko zata ji sauk'in yadda ta ke ji, dan Jimmai ta bata shawarwari masu kyau na kwantar da hankali".
Hassana inda ta saba ganin Jimmai ta sameta , Jimmai da fara'arta ta tari Hassana, tana cewa, "Tom yau kuma me yafaru, dan ni dai tunda kika bar nan na bar ganinki sai taki ta kawo ki". "Aunty Jimmai ki yi hak'uri, Ina cikin damuwa Nazo ne ki fad'amin magana mai dad'i ko zanji dad'i". Cewar Hassana ".
Jimmai hannun Hassana ta kama suka zauna, sannan ta kalli Hassana ta ce, "Fad'amin damuwaki kinji Hassan? ". Hassana cikin damuwa ta ce, "Sister Jimmai yau zan tare a gidan Oga Habib, Hajiya ta nuna min fin k'arfi ta ce bazata raba auran ba, Wallahi Sister Jimmai idan kikaga yadda Oga Habib ya rud'e tsabar bai son zama dani abin zai ta damiki hankali, ni kaina nasan Hajiya ba taima Oga Habib adalci ba, saboda Oga Habib ya taka mata kai ma su girma da kwari arayuwarshi, ya kamata Hajiya ta had'ashi da dai-dai dashi amma bani ba". Hassana ta idasa maganar tana share hawayanta".
Jimmai hannun Hassana ta kamo ta ce, "Hassana ki kwantar da hankalinki Oga Habib bai isa ya raina miki ba, dan haka karma kiwani k'ara tunanin wai ya wuce da ajinki. Yanzu Hassana idan kin ce ma Habib ya sakeki, kin san kin b'atama Hajiya, kuma kina tunanin zata ci gaba da zama da ke, idan kuna kince ki koma garinku, ko kin san zaki fuskanci wata irin rayuwa fiye da wadda kika baro,dan haka ni Ina baki shawarar ki yi hak'uri ki zauna da Oga Habib lafiya, duk abinda zai miki ki yi hak'uri, watarana sai labari. Yanzu me ye kika san Oga Habib naso? ". "Ni ban san abinda ya ke so ba". Cewar Hassana ".
Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce," tom ni zan fad'amiki abinda Oga Habib ke so ai farkon zuwana gidan nan, b'angaran Hajiya na fara aiki, Oga Habib na son kunu sosai, dan haka ya kamata ki koyi kunu kala-kala". Hassana Kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Tom ta ya zan koya, idan ma na koya kina tunanin zai sha idan nayi? ". "Tsab ma kuwa zai sha, ai ke zaki sashi ya sha, akwai wata makaranta ta koyan girkegirke idan kin wuce national assembly na nan apo School d'in take, tom amma gaskiya da tsada fa, amma zaki iya girgi kala-kala, yanzu babu yadda za ai ki samu kud'i gurin Hajiya Turai? ".
Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Babu, amma tunda na fara aiki a Sanat yughurt basu tab'a biyana ba, dan haka zanma Oga Bilya magana idan suka ban sai in yi amfani dasu". "Yauwa ki mai cikin satin nan ki fara zuwa". Hassana godiya taima Jimmai sannan tai mata Sallama ta tafi".
Da daddare bayan Sallar Issha'i, Hajiya Turai jin Habib shiru har yanzu , kiran shi awaya tai, ta ce, "Hello Habib kazo yanzu Ina son ganinka". Hajiya Turai na fad'in haka ta kashe wayarta, sannan ta tashi ta shiga ciki , tana kallan Hassana da ke zaune. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Wai daughter har yanzu biki shiga wankan ba ga Habib nan zuwa, shikenan in bazaki wankan ba in kinje can kinyi ai".
Hassana batare da tace komai ba, ta tashi ta shiga wankan. Kafin Hassana ta fito Hajiya Turai ta d'akkoma Hassana wata doguwar riga fara mai ratsin pink da tazo mata da ita, rigar ta yi kyau sosai".
Hassana na fitowa Hajiya Turai ta bata rigar, sannan ta fita ta bata gu ta shirya".
Hassana sama-sama ta shafa mai ta sa rigar. Masha Allah sosai rigar ta amshi Hassana ta fito mata sosai da sharp d'in ta. Hassana bayan ta shirya ci gaba da zamanta ta yi".
Can Falo kuma, Habib zaune gaban Hajiya Turai, Hajiya Turai kallan Habib ta ti, ta ce, "Habib ga Hassana nan amana na baka ita, idan ka cutar da ita ba baki naima ba, amma Allah ba zai barka ba , Habib ko dan halaccin da taima dan Allah karik'eta amana, idan kuma ba kai mata dan haka ba, ka yi dan maraicinta, kasan dai hukuncin wanda ya zalinci maraya, bari in kirata ku tafi, ka sa Bilya ya kaima kayanka ko? ". Habib ciki-ciki ya amsa ma Hajiya Turai da cewa, "Eh ya kai".
Hajiya Turai ta shi ta yi, ta je bedroom d'in ta, zaune ta iske Hassana ta yi ta gumi. Hajiya Turai hannun Hassana da tai ta gumi ta koma, sannan ta d'akko oud aribian perfume masu k'amshi ta shafama Hassana, ta ce, "A akayanki da nasa miki, kirik'a shafawa kinji daughter, nasan kuma ke dama mai son tsabta ce, na ba tailor na d'in kayanki, ya d'inka miki, Bilya zai amso miki, dan Allah daughter karki biyema Habib kinji, ko ba komai kinga yanzu yana matsayin miji gareki ki ne, ki kyautata mai kodan kwad'ayin lada agurin Allah, ki rik'a girki da shi kullum koda ba zai ciba karki ki hanashi kinji, daughter, Allah ya yi miki Albarka Allah ya albarkaci auranku, Allah ya kauda fitina a tsakaninku".
Hassana kuka take sosai, a haka dai Hajiya Turai ta kawota Falon. Habib na zaune da wayar shi yana danne-danne. Hajiya Turai zama ta yi, ta kalli Habib ta ce, "Habib ga daughter nan nabaka amana, kaji min da ita sosai, karka sake kabar hawayanta su zuba k'asa". Habib tab'e baki ya yi".
Hajiya Turai kamo hannun Hassana ta yi, ta ce, Muje in rakaku".
Hajiya Turai har Mota ta kai Hassana wadda har yanzu ta ke kuka. Bayan Hajiya Turai ta sa Hassana mota ne Habib ma ya shiga".
Hajiya Turai tana nan, tsaye Habib ya tada motar yaja suka tafi.
Sannan Hajiya Turai ta koma cikin gida tana hawayan farinci......... ✍️
Idan kin karanta daure ki Comment Sister 🤝.
Idan naga Comment da yawa, Gobe zaku ya Update idan naga kad'an tom zafa kuji🤐🤐🤐.
Share
&
Comment please 🙏.
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://www.facebook.com/groups/301023561618950/
Shafi na 62&63.
Hajiya Turai tana nan tsaye Habib ya tada motar yaja suka tafi.
Sannan Hajiya Turai ta koma cikin gida tana hawayan farinciki.
Kasan cewar bawani shahararran nisa bane tsakanin gidan Hajiya Turai da gidan Habib, hakan yasa cikin mintina kad'an suka isa. Gida ne babba masha Allah, kallo d'aya za kaima gidan kasan ankashe kud'i sosai wajan yinsa. Habib na yin parking bai bi takan Hassana ba ya fita daga motar ya barta nan, tana aikin kuka. Hassana ko jin Habib ya fita, itama fita ta yi tabi bayan shi".
Falon mai ma dai-dai cin girma, wanda ya k'oshi da kayan more rayuwa. Inda akaima falon adon Orange & White, color d'in sai ta kuma fito da madarar kyau na Falon".
Habib na shiga falon ya yi side d'in shi, inda ita kuma Hassana ta baje ko linta a falon, ta zauna kan two seater".
Haka Hassana ta gama kukanta daga k'arshe ta lallashi kanta ta yi hak'uri ta yi shiru. Hassana na nan zaune ta na tunane-tunane a haka bacci ya kwasheta, batare da ta cire kayan jikinta ba, ko ta naimi inda bedroom d'in ta take ba".
Habib ko da ya shiga bedroom d'in shi, toilet ya shiga ya watsa ruwa ko zai ji sanyi a zuciyar shi, shima dai kusan haka ta faru da shi yana fitowa ko mai bai shafaba ya zauna kan lover chair yana tunanin yadda zai yi ma Hajiyarsa idan ta huce Hassana ta koma can da zama ala bashi shi sai ya barmata gidan Hajiyar shi yadawo nan ya ci gaba da zaman shi, Habib na wannan tunanin bacci ya kwasheshi shima anan".
Cikin dare yunwa ta tada Habib, dan tun break fast d'in safe raban shi da yasama cikinshi wani abu,dan tunda Hajiya Turai tai ma Habib maganar ta rewar Hassana ya hana kanshi sukuni. Habib tashi ya yi ya je kitchen ko ruwan zafi ya samu yasa tea, dan sosai ya ke jin yunwa".
Habib mamaki ya yi da yazo yaga Hassana kwance sai baccinta ta ke. Tsaki ya yi ya tab'e baki ya ce, "Wannan yarinyar bata da hankali kwata-kwata. Habib kitchen d'in yaje, ya samu ya dafa ruwan zafi yazo yasha tea".
Hassana tunda ta kwanta ba ita ta farka ba sai 6:00AM, tana tashi, side d'in da ta ke da tabba cin nata ne ta shiga, anan taga kayanta na sawa, Hassana sallah ta farayi, sannan ta cire doguwar rigar jikinta ta samu wata wadda bata kai waccan nauyi ba tasa, ta shiga kitchen ta d'ora ruwan tea, sannan ta soya wainar kwai. Hassana na gamawa ta d'auki na Habib ta kai mai kan derning, ita kuma nata ta shiga bedroom d'in ta dashi. Hassana sai da ta yi wanka ta shirya cikin wata doguwar rigar, inda kayan duk sune, sannan ta zauna ta fara break fast ".
Habib ko bayan ya tashi ya yi sallar asuba, komawa ya yi ya kwanta. Sai 7:52AM, Ya farka da sauri ya shiga wanka, yana fitowa ya yi shirinsa na fita. Habib da bai san Hassana ta yi wani abun break fast da shiba, yana gama shirinsa ya fita abinsa".
Zaune Habib ya iske Bilya acikin mota yana jiran shi, hakan yasa Habib na zuwa, Bilya yaja motar zasu tafi".
Bilya har ya tada Motar Habib ya tsayar da shi ya ce, "tsaya ina zuwa". Bilya da katawa ya yi , Habib ya shiga ciki. Dai-dai nan ma Hassana ta fito itama tana sauri zata tafi dan tasan ta makara sosai".
Hassana tsayawa ta yi ganin Habib, kuma kamar gunta yazo, Hasssana baki ta bud'e ta gaida Habib, Habib ya katseta da cewa, "Karki sake kizo aiki yau, sai Hajiya ta koma". Habib na fad'in haka ya juya ya tafi, dan yasan indai Hajiya Turai tasan Hassana na zuwa Sanat yughurt aiki, yasan zata hana, shi kuma baya son hakan ".
Hassana ko cikin jin dad'i ta koma ciki, dama ba son zuwan take ba, dan tun abinda Billy tai mata taji ta tsani Sanat Company gaba d'aya.
Hassana komawa ta yi tana mai jin dad'in hakan".
Wajan misalin 12:15PM, Hajiya Turai da Hajiya Murja mahaifiyar Farida suka zo gidan, lokacin Hassana na zaune a falon tana game awayarta da Hajiya Turai ta bata".
Hassana cikin nuna jin dad'in ganin Hajiya Turai ta tarbe su, inda Hajiya Murja sai tab'a baki take, dan acewarta gidan da Farida ya dace ba da Hassana ba".
Hassana ruwa ta kawoma su Hajiya cikin fresh, sannan ta gaida su cikin girmamawa, sun d'an jima da zuwa Kafin suka tafi. Dan ita Hajiya Turai bata so zuwan ba ma, Hajiya Murja ce ta matsa mata, ita kuma gulma ta kawota, dan ganin yadda gidan yake".
B'angaran Farida ko kamar yadda su kai da Hajiya Zaliha haka akayi, da wuri ta shirya, ta nufi Sanat yughurt nai man aikin".
Koda Farida ta isa direct Office d'in Habib ta naimi izinin shiga. Lokacin Habib nata aiki a laptop, Bilya ya shiga Office d'in, ya ce, "Oga Habib Farida ce ke son ganinka, zata iya shigowa? ". Habib shiru ya yi yana tunanin lafiya Farida ke son ganin shi,kai ya d'aga ma Bilya, alamun zata iya shigowa ".
Farida shiga ta yi. Bayan ta zauna ne, ta gaida Habib kamar yadda ta saba, sai kuma taja bakinta ta yi shiru. Habib da katawa ya yi da abinda ya ke yi ya yi, ya kalli Farida ya ce, "Lafiya dai ko? ".
Farida sosa kai ta yi, sannan ta ce, "Uhm, Oga Habib dama nagaji da zamane haka nan, shine na yanke shawarar inzo nan ko zan samu aiki". Habib kallan Farida ya yi, ya ce, "Gurin manager zaki, bani ke d'aukar aiki ba". Shiru Farida ta yi, sannan ta ce, "Oga Habib ba lallene manager ya d'aukan ba, saboda wata friend d'ina ta tab'a zuwa nai man aiki anan manager yace mata sun b'ar d'aukar aiki suna da wadatattun ma'aikata". "Kije ki ce mai nina turoki, zai d'aukeki". Cewar Habib yana mai ci gaba da abinda ya ke yi".
Farida badan ta soba ta tashi ta fita daga office d'in Habib. Office d'in manager Farida ta shiga. Cikin girmamawa da mutunta juna Farida suka gaisa da manager, inda manager yasan Farida sosai a gidansu Habib. Bayan sun gama gaisawa ne, manager ya tambayi Farida lafiya".
Farida cikin hikima ta fara magana kamar haka, "Wallahi manager nagaji da zaman gida ne, shine nace bari inzo nan in rik'a ta ya ku aiki".Dariya manager ya yi, ya ce, "Tom ai shikenan, wani b'angare kike so? ". Farida shiru ta yi dan in son samu ne, b'angaran da Hassana ta ke ta ke so, tom amma kuma bata san b'angaran da Hassana ta ke ba, hakan yasa Farida ta ce, "Manager ni ko ina da ruwana". "Ok, tom shikenan, hakanma ya yi ai". Cewar Manager. Hassana kallan manager ta yi, ta ce, "Manager zan iya fara aiki yau? ". "Sosai ma kuwa, zaki iya farawa".
Farida cikin jin dad'i ta fita Office d'in manager, haka Farida tai ta aikin duba ko ina ko zata ga Hassana amma bata ganta ba,