OGA HABIB Bacewa da Samuwa by Faddy baby

Author :  Faddy baby Category :  Romance

Chapter   36 / 41

105K to 108K   out of 121.2K words

kai ki ". Habib zai sake magana kenan Hajiya Turai ta shigo. Hakan yasa Habib yin shiru".


Hassana tashi ta yi ta amshi abincin da Hajiya Turai ta kawo mata tana ci kad'an-kad'an dan tasan ko ta cema Hajiya Turai ta k'oshi Hajiya Turai ta kura ta zata tai sai taci, shi ya sa ma ta daure tana ci. Wayar Hajiya Turai ce ta yi ringing Hajiya Turai na dubawa ta ga Hajiya Murja mahaifiyar Farida ce. D'aga wa Hajiya Turai ta yi tasa a kunne".


Bayan Hajiya Murja ta gaida Hajiya Turai ne, Hajiya Turai ta tambayi jikin Farida, Hajiya Murja ta ce, "Yauwa dan Allah Hajiya idan Habib yana kusa bashi wayar". Hajiya Turai mik'a ma Habib wayar ta yi, Habib amsa ya yi. Bayan ya gaida Hajiya Murja ne ya tambaye ta mai jiki. Hajiya Murja ta ce, "Habib jiki sai dai ace da sauk'i. Habib da ma naki raka ne, game da maganar auran Farida da kace za kai, shine nace ka turo namiji muyi magana inda kaga abu ne da za ai da wuri dan ceto rayuwar Farida, Wallahi yan zu haka baka ji ba, yadda ta ke kiran sunan ka, dan Allah Habib idan zai yuwu kazo yan zu". Kasan cewar wayar a speaker ta ke hakan yasa Hassana da Hajiya Turai sun ji duk abinda Hajiya Murja ta ce".


Habib ko bayan Hajiya Murja ta kashe kiran, kallan Hajita Turai ya yi, ya ce, "Mommy bari inje in duba jikin nata". Hajiya Turai, tsabar ta kai ci, "Tom".ta ce ma Habib". Habib kuma tashi ya yi ya fita. Bayan Habib ya fita ne wani kuka ya kwacema Hassana wanda bata shirya yi ba, cikin kukan ne Hassana ta ce, "Mommy dan Allah ina son zuwa garin mu gobe dan Allah karki ce a'a". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Shikenan, daughter ki share hawayan ki gobe insha Allah zan kai ki".


Hajiya Turai ta san kukan Hassana gaba d'aya duka ta gane manufar kukan, ita dai tunaninta yana bata akan kishi ne, in da Hajiya Turai bata san Habib ya saki Hassana ba, ita kuma Hassana tana son fad'a ma Hajiya Turai ta kasa".


Hajiya Turai hannun Hassana ta kama ta ce, "Daughter dan Allah ki yi hak'uri Ki bar yawan kukan nan ni bana son Habib yaga kina damuwa haka akan shi, Maganar saki kuma ba bu na janye , ni dama wasa nake, ina so ne in gwada son da Habib ya ke miki, tom na gwada kuma nagani, ki bar yawan kukan, aure kuma ki barni da shi bai isa ba ya auri Farida ". Hajiya Turai tana fad'i ma Hassana haka ne ko hankalin Hassana zai kwanta, dan ta lura Hassana ta tada hankalinta sosai, shi yasa ta fad'a mata haka ko zata kwantar da hankalinta, idan ma Maganar Habib ya sake ta ne da ta yi".


Hassana ko azuciyarta cewa ta ke, "Mommy kin makaro Oga Habib ai har ya sake ni ma ya gama".


Hajiya Turai ko ta dad'e tana lallashin Hassana sannan taba Hassana gu".


B'angaran Habib ko ya na zuwa Farida ta ke jin jiki ta tashi ta zauna. Farida cikin murya irin ta mara lafiya ta ce, "Oga Habib dan Allah ka aure ni, auran ka ka d'ai ne zai iya zaman towa sauk'i gareni, idan baka auran ba mutuwa zan yi... ". Habib rufe ma Farida baki ya yi, dan sosai ya tausayama halin da ta ke ciki, Habib cikin miskilancin shi ya fara magana kamar haka" ki bar yawan magana kin ga baki da lafiya, kuma nina ce zan aure ki, ba sai kin sake min Maganar ba, ina sa ne". Habib ya d'an jima sannan ya yima Mahaifiyar Farida sallama tare da ce mata zai samu Mommy shi su yi magana".


Habib ta gidan shi ya biya ya d'ebo wasu daga cikin kayan sawar shi, sannan ya wuce gidan Hajiya Turai, dan can zai koma baya jin dad'in zaman shi nan shi ka d'ai"


Habib a falo ya samu Hajiya Turai. Zama ya yi sannan zuwa can ya kalli Hajiya Turai ya ce, "Mommy dama Maganar yarinyar nan da nace zan aura, shine mahaifiyarta tai min magana yan zu". Hajiya Turai wani ban zan kallo tai ma Habib sannan ta ce, "Zan yi abu ne yan zu, zuwa gobe kazo sai mu yi magana". Ita ko Hajiya Turai ta yi haka ne, dan tafi son ta ce ma Habib tom ya yi auran karta nuna mai ko mai, tasan idan ya farga yaga ba Hassana, tana da tabba cin ba zai samu na tsuwar auran ba, inda tafi kowa sanin Habib auran tausai zai ma Farida ba wai so ba".


Habib ko jin abinda Hajiya Turai ta ce ne yasa ya tashi ya nufi bedroom d'in Hassana da niyyar duba ta. Hajiya Turai dakatar da Habib ta yi, ta hanyar cewa, "yan zu bacci ya kwace ta karka shiga ka tada ta". Habib ba dan ya soba ya juya ya koma side d'in shi".


Bayan Habib ya yi sallar issha'i ne ya nufi side d'in Hajiya Turai, amma abin mamaki a rufe Habib ya iske k'ofar falon, waya ya ciro ya kira Hajiya Turai, amma bata d'aga ba. Habib sai da ya yi ma Hajiya Turai kira kusan biyar sannan ta d'aga, ta ce mai ta yi bacci sai gobe kanta ne ke mata ciwo wai ta riga ta kwanta".


Habib cikin sanyi ya ce, "Mommy dan Allah ki turo min number Yarinyar nan dan Allah in ji ya jikinta". Hajiya Turai kashe wayar ta yi, ta tura ma Habib number Hassana, tana tura mai ta nufi bedroom Hassana, Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, "Daughter za'akiraki yan zu kar ki picking Habib ne". "Tom". Cewar Hassana ".


Habib ko ta ke Hajiya Turai na turo mai number ya kira Hassana, amma bata d'aga ba. Habib sai da ya yi ma Hassana kira Uku sannan ya hak'ura ya tura mata Text kamar haka.:Sanat Please na san biki bacci ba, ki zo ki bud'e min k'ofar falo ina son ganin jikinki kafin in kwanta".


Hassana share hawayanta ta yi da ta gama karanta text d'in , Sannan ta gyara kwanciyarta". Habib ko haka ya gaji da tsayuwa ya tafi. Sosai ya ji haushin shasshare shi d'in da Hassana ke yi, gashi yana son ya rabu da ita amma ya kasa. Habib yana tsaki ya koma side d'in shi".


Hajiya Turai ko cikin dare ta shirya ma Hassana kayanta na tafiya,dan tafiyar wuri ta ke so suyi, dan yau zata dawo, Sannan bata son Habib yaga tafiyarsu, tasan zai fi jin zafi idan yazo yaga ba Hassana ".


Asubar Fari Hajiya Turai ta tada Hassana ta yi wanka ta shirya cikin wani brown less, masha Allah Hassana ta yi kyau sosai. 7:00Am Hajiya Turai ta fito da babar jakar kayan Hassana taba Bilya ya sa a but. Habib ko da fitowar shi kenan da niyyar zuwa gaida Hassana.Habib tun daga nesa kafin ya k'ara so ya ke mamakin Kayan da yaga Bilya na sawa abut, ga Hajiya Turai da shirin tafiya a tsaye, Habib cikin zuciyar shi ya ke cewa dama yau Mommy zata tafi bata fad'a min ba..... Tunanin Habib cak ya tsaya ganin Hassana ta fito daga side d'in Hajiya Turai da alamun har da ita za ai tafiyar, ta ke tafiyar Hassana danginta ta fad'o ma Habib".


Habib kusan atare da Hassana suka isa wajan motar, Hassana ko naganin Habib ta yi saurin d'auke kanta, inda shi kuma Habib ya kema Hassana kallan mamaki".


Habib cikin sanyi ya gaida Hajiya Turai. Hajiya Turai ko da taji haushin ganin tafiyar su da Habib ya yi, dan taso ace sai bayan tafiyarsu ya sani tasan haka sai yafi bashi haushi, hakan yasa Hajiya Turai ta k'ara shan mur, Habib kuma cikin alamun damuwa ya ce, "Mommy yau zaki koma ne? ". "Eh". Hajiya Turai ta ba Habib amsa".


Habib kallan Hassana ya yi da ke shirin shiga mota ya ce, "Ke fa, rako zaki yi? ". Kai Hassana ta d'aga ma Habib, Habib ganin haka, ya kalli Bilya ya ce, "Billya bari in kai Mommy ". Hajiya Turai cikin alamun ba wasa, ta ce, "Sauka Bilya zai kai mu dan tafiyar mu da nisa, yau Hassana zata koma dan ginta, ban dai so ta tafi da auran ka ba, amma inda kak'i sak'i sau wa k'e mata babu komai, ahaka zata tafi! ".


Habib da Maganar Hajiya Turai ta soki zuciyar shi kamar an buga mai mashi haka ya ji, ta ke zufa mai d'imi ta fara keto mai.Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, 'Daughter shigo mu wuce".


Habib hannun Hassana ya kamo da sauri ya ce, "Mommy ki yi hak'uri ba bu inda Hassana zata". Habib ya fad'i maganar cikin d'aurewa ".


Hajiya Turai wani banzan kallo tai ma Habib ta ce, "Idan ka isa ba sai ka hana in gani ! ". Hassana ko so take ta shiga cikin motar, amma Habib ya rik'e hannunta sosai, Hajiya Turai fitowa ta yi daga motar tazo taja hannun Hassana, amma Habib ya rik'e hannun Hassana da kyau, Hajiya Turai kallan Habib ta yi, babu alamun wasa ta ce, "Habib sakar ta ". "mommy ki yi hak'uri Hassana babu inda zata".,


Hassana ko cikin murya irin ta mai son yin kuka ta fara magama kamar haka, "Mommy ki ce mai ya sakan, dan duk Maganar da yake bashi da wani iko akaina, a halin yan zu, dan ya ban takarda ta tun jiya, yan zu haka tana hannuna". Habib da mamaki ya kalli Hassana ya ma kasa magana. B'angaran Hajiya Turai ma da mamaki ta ke kallan Habib. Hajiya Turai Cikin b'oye fushin ta ta kalli Habib ta ce, "Habib da gaske ne ka saki Hassana? ". "Mommy ki tambayeta, amma ni ban sake ta ba".


Hajiya Turai mai da kallanta ga Hassana ta yi, ta ce, "Daughter fad'a min gaskiya, yau she Habib ya sake ki!? ". Hajiya Turai cikin fad'uwar gaba ta idasa Maganar, dan tana tunanin tabbas kukan da Hassana ta yi jiya, na sakin da Habib ya yi mata ne"


Hassana Cikin tabbatar wa ta ce, "Mommy Wallahi da gaske nake". "kawo min takardar na gani". Cewar Hajiya Turai ". Habib sakin hannun Hassana ya yi, Hassana kuma ta nufi bedroom d'in Hajiya Turai d'akko ta kardar".


Hassana babu inda bata duba ba amma bata ga takardar ba, haka ta dawo. Hassana kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, "Mommy na duba banga takardar ba, amma abinda na fad'a miki haka n... ". Tsawar da Habin ya yi ma Hassana ce ta sa ta yi shiru, Habib cikin b'acin randa Hassana bata tab'a ganin shi da shi ba ya ce, "Idan kina son tafiya ki tafi mana, sai me, amma akan me agabana zaki min k'arya! ".


Hajiya Turai sosai kanta ya d'aure da abinda Hassana ta ce, kuma tabbas ta yadda da Maganar Hassana, dan ta lura da halin da Hassana ta shiga jiya bayan fitowarta side d'in Habib.tom kuma a yananin Maganar Habib kamar bai saki Hassana ba. A zaman da Hajiya Turai tai da Hassana ta lura da yarinyar bata da k'arya, kuma ta lura Hassana na son Habib, ba za tai mai k'arya ba. Hakan yasa Hajiya Turai tai tunanin k'ila Habib d'in ne ya koma daga baya ya d'auke ta kardar, inda ta san shi da fushi, tom k'ila ya yi fushine ya saketa daga baya kuma ya koma ya d'auke ta kardar".


Hajiya Turai ranta b'ace sosai ta ce, "Daughter shiga mu tafi! ". Habib saurin rik'e Hassana ya yi, ya ce, "Mommy na yarda ta tafi, amma sai in ta fad'i gaskiya, dan ni k'arya ta ke min ban saketa ba". Habib ya fad'i maganar ran shi b'ace".


Hajiya Turai da ranta ke ab'ace, kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib ni zaka raina ma hankali ko, ka saketa na ce!". "Mommy ki saurare ni Please, Wallahi ban aikata abinda ta ce ba".
Hajiya Turai d'aga hannu ta yi ta wanka ma Habib mari ta ce, "Sakar mata hannu na ce!". Habib wujijjiga Hassana ya yi, ya ce, " Fad'i ma Mommy gaskiya mai na rubuta miki jikin takardar da na baki........ โœ๏ธ



Idan kin karanta daure ki Comment sister ๐Ÿค.



Share
&
Comment please ๐Ÿ™.

๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy Baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7


https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa ๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ

VIP group 300 Only๐Ÿ‘Œ , normal kuma 200 ne, zaki yi transfer ta account d'in nan 2111619333.
Account name Fadila Sani.
Bank Name Zenith bank.
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number๐Ÿ‘‰ 08063830828



Shafi na 85&86.



Hajiya Turai da ranta ke ab'ace kallan Habib ta yi ta ce, "Habib ni zaka raina ma hankali ko?, ka saketa na ce! ". "Mommy ki saurare ni Please, Wallahi ban aikata abin da ta ce ba". Hajiya Turai d'aga hannu ta yi ta wanka ma Habib mari, ta ce, " Sakar mata hanni na ce!. ".
Habib wujijjiga Hassana ya yi, ya ce, "Fad'i ma Mommy gaskiya, mai na rubuta miki jikin takardar da na baki? ". Habib ya idasa maganar yana kuma wujijjiga Hassana da k'arfi. Hassana ko da ta tsorata da yadda taga Habib, cikin siririyar murya ta ce, "Ni ban karanta abin da ka rubuta ba, amma na san saki n... ". Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce tasa ta yi shiru bata k'arasa fad'in abin da ta ke fad'a ba. Cikin tsawa Habib ya ce, ", Wallahi zan fasa bakin ki kika idasa! ".


Hassana shiru ta yi tana kallan Hajiya Turai jin Hajiya Turai bata sake magana ba. Hajiya Turai ko tama rasa abin da zata cema Habib ya saki Hassana, hakan yasa ta tsaya tana kallan shi".


Habib kuma tura Hassana ya yi, Hajiya Turai na mai magama amma bai saurareta ba, ya ce, "Muje ki nuna min inda kika aje letter".


Hajiya Turai na ma Habib magana amma bai saurareta ba, haka ya ya tasa k'eyar Hassana har bedroom d'in Hassana".


Habib kallan Hassana ya yi babu alamun wasa ko fara'a afuskar shi, ya ce, "Nemo ta kardar ki ban". Hassana tsayawa ta yi, tana kallan Habib ganin yadda ya wani sha mur, Hassana ita kanta cikin ta kai cin hanata ta fiya da Habib ya yi ta ke, kallan Habib d'in ta yi, ta ce, "Oga Habib ni ina ganin babu wani amfanin sai na nemo takardar, saki ne ka rubuta min, tom yan zu kai zaka fad'i saki nawa ka rubut... ". Habib d'aga hannun da ya yi zai mari Hassana ne ya sa tai shiru, ta yi sauri ta b'oye fuskarta k'irgin Habib, tana wani irin kuka. Cikin kukan ne Hassana ta ke magana kamar haka, "Oga Habib me naima da zaka rik'a marina haka?, kasan me ke damuna?, kasan yadda nake ji azuciyata?, na had'a kayana zan tai mahaifata ka hanani, kuma bacin haka ka bini da mari, da me kake son inji? ". Hassana ta idasa maganar cikin matsanancin kuka. Habib d'ago kan Hassana ya yi da ta tusa a k'irjin shi tana kuka, sannan ya jata suka zauna bakin gadon. Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Sanat da gaske kike na rubuta miki takardar saki? ". Hassana kai ta d'aga ma Habib.Habib kallan Hassana ya yi ya ce, "kin karanta takardar ne? ". Kai Hassana ta girgizama Habib. Shiru Habib ya yi, sannan ya ce, " Tom me yasa zaki yan ke hukunci akan abin da bi ki sa ni ba?, Shikenan, zaki iya tashi ki bi Mommy ku tafi, ko ba komai kad'ai ci zai kare min, gobe za'a d'aura aurena da Farida". Habib na fad'i ma Hassana haka ya ja k'ofar bedroom d'in da k'arfi ya fita".


Hassana zubewa tai a gadon tana kuka. Hassana ta dad'e tana kukanta sannan ta gaji ta lallashi kan ta tai shiru.
Habib ko barin gidan ya yi baki d'aya".


Hassana had dare tana nan kwance Sallah ka wai ke ta data sai abinci da d'azu Hajiya Turai ta matsa mata sai ta ci, ta tashi ta ci. Hassana na nan kwance Hajiya

36 / 41