Author : Faddy baby Category : Romance
nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.
Paid book
Akan farashi mai sauk'i da rahusa ๐๐
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number๐ 08063830828.
Shafi na 79&80.
Managerrrrrrrrrrrrr.... ". Habib da fitowar shi ke nan daga Office d'in shi, ya ci karo da marin da Manager ya yi ma Hassana, manager ya kuma d'aga hannu zai k'ara mata ne Habib ya yi mai wannan kiran. Habib ranshi b'ace ya k'ara so gun, yana zuwa ya d'aga hannu sai da ya yi ma manager mari kwarara guda uku, sannan Habib ya nuna shi da hannu ya ce, "Manager ashe baka da tunani ban sani ba, yau fa ta dawo aiki daga Suspection d'in da ka bata, haka bai yi ma ba yanzu ta dawo zaka d'aga hannu ka mareta a company'na kuma!, ba komai ba laifinka ba... ". Maganar Hajiya Turai da Habib ya ji ce, ya yi saurin juyowa. Hajiya Turai zuwan ta kenan, ta hango Hassana zuk'un ne agun tana kuka, Hajiya Turai ita duk tunaninta ma Habib ne ya mari Hassana, hakan yasa, tana zuwa ta kamo hanun Hassana da ke zuk'unne agun ta ce, "Yi hak'uri daughter tashi muje gida". Daga ganin yadda Hajiya Turai ke magana kasan ranta a matuk'ar b'ace ya ke".
Habib ko da kallo ya bi Hajiya Turai, dan yama rasa ya zai ce mata, Habib bin Hajiya Turai ya yi, dai-dai zasu shiga mota, ya ce, "Mommy ki.... ". "Bana son magana a condition d'in da nake! ". Habib jin abinda Mahaifiyarsa ta ce ne yasa ya ja bakinsa ya yi shiru".
Habib Office d'in shi ya koma, ga ba d'aya ya rasa abinda ya ke mai dad'i, ana cikin haka ne, manager ya shigo, manager cikin hikima ya fara magana kamar haka"M'd ka yi hak'uri na kasa control d'in fushina, dan Allah ka yi hak'uri, ta kira ni da sunan da nakasa control d'in kaina ne... ". Tsawar da Habib ya yi ma manager ce tasa ya yi shiru. Habib kallan manager ya yi, ya ce, "Manager wai hak'uri zaka ban!?, kasan abinda ka aikata kuwa? , mari fa!?, tom bari kaji naji haushin korarta aiki da kayi, amma ban nuna ma ba, amma haka bai ma ba..., manager bana son yawan magana dan Allah ka fita kawai! ". Manager kallan Habib ya yi, ya ce, "M. D, dan Allah ka saurare n.. ". "Kafita nace ko!? ". Habib ya fad'i maganar da k'arfi".
Manage fita ya yi. B'anga ran Hajiya Turai ko, bayan sunje gida kallan Hassana ta yi ga sawun marin da manager ya yi mata nan kwance a fuskarta, Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, "Habib d'in ne ya mareki haka daughter? ". Kai Hassana ta girgiza ma Hajiya Turai ta ce, "A, a Mommy ba shi bane manager ne". Hajiya Turai da mamaki ta ce, "Manager kuma?, yanzu har Habib ya ba su manager damar da zai d'aga hannu ya mareki!?, dama da nace ma Habib kar ya sake kije Sanat aiki, da ya ke yaga na tafi shine sai da ya tura ki , ba damuwa ". Ita dai Hassana bata ce ma Hajiya Turai komai ba, dan ta ga tsan tsar b'acin ran Hajiya Turai a fili, na Marin da akai mata".
Habib sai bayan magriba ya je gidan Hajiya Turai. Lokacin Hajiya Turai na falo, Habib ya shigo, tun daga yadda Hajiya Turai ta amsa ma Habib sallamar shi yasan akwai matsala. Habib d'an nesa da Hajiya Turai ya zau na, sanna ya gaida ta, Hajiya Turai da lafiya ta amsa ma Habib. Sannan Hajiya Turai ta kalli Habib ta ce, "Habib dama da nace ma kar Hassana ta je Company'ka tai aiki, shi bayan tafiya ta ka tura ta ko!?, shi ne ka wulak'anta ta gaban worker's d'in ka, har kaba wasu damar marina, babu komai bani ka wulak'an ta ba, kuma ita ma ba'ita ka wula k'anta ba, auranka ka wulak'anta". Habib kai ya d'ago ya kalli Hajiya Turai ya ce, "Mommy ki yi hak'uri, insha Allah haka ba zai k'ara faruwa ba". "Tom Habib ai hak'uri ya zama dole, idan ban yi hak'uri ba, zan sa a kama manager ne?, na yi hak'uri saboda wasu 'yan da lilai". Habib jan bakin shi ya yi ya yi shiru, dan bai san mai zai kuma cema Hajiya Turai ba kuma" Hajiya Turai ko tashi tai ta bar Habib shi ka d'ai agun".
Habib ya dad'e zaune, sannan ya tashi ya shiga bedroom d'in Hajiya Turai ya yi mata sallama zai wuce. Hajiya Turai ba tare da ta kalli Habib ba, ta ce, "Sai da safe". Habib ganin Hajiya Turai ba tai mai maganar Hassana ba, kuma bai ga Hassanar ba, yasa ya yi tunanin tana gidan shi".
Habib yana zuwa ya shige bedroom d'in shi, ya yi duk abinda zai yi har ya kwanta shiru bai ga Hassana ba, dan kullum Hassana ta saba sai ta damama Habib kunun shi ta kawo mai, a haka zasu yi ta fira da Habib, idan zata tafi ta kwanta Habib ya raka ta".
Habib jin shirun ya yi yawa, yasa ya tashi ya nufi side d'in Hassana. Habib ko da ya shiga bai ga Hassana ba, hakan ya tabbatar mai da tana gida kenan. Habib ko mawa ya yi bedroom d'in shi ya kwanta".
Washe gari Habib bayan ya gama shirinsa na tafiya aiki, sai da ya biya ta gidan Hajiya Turai. Habib zau ne ya iske Hajiya Turai da Hassana a derning space suna break fast. Habib zama ya yi, sannan ya gaida Hajiya Turai. Hajiya Turai sama-sama ta amsa ma Habib, sannan ta tura mai flaks d'in tea, Habib tsiyaya wa ya yi. Sai dai abinda ya d'aure ma Habib kai ganin Hassana ko kallan inda ya ke bata yi ba, bare ya sa ran zata gaida shi. abinda Habib ko bai sani ba, Hajiya Turai ce tasa Hassana karta sake ta gaida Habib ko da yazo. Ita kuma Hassana ta yi hakane kawai dan bin umar'nin Hajiya Turai, amma ita bata ga abinda Habib ya yi mata ba, acewarta, Manager ne ya mareta ba Habib ba, ko a yan zu Hassama ji tai ba dad'i gaida Habib d'in da ba tai ba, hakan yasa Hassana na gama shan tea d'in ta ta shi ta bar gun,Habib da kallo ya bi Hassana. Habib ka d'an yasha tea d'in ya yi ma Hajiya Turai sallama ya tafi".
Habib na zuwa babu da d'ewa manager ya shigo Office d'in, manager kallan Habib ya yi, ya ce, "M. D dan Allah... ".Habib hannu ya d'a gama manager ya ce, "Manager dan Allah kaje kawai sai na ne me ka!". Manager fita ya yi".
Billy da Farida ne suka tare manager, Billy kallan manager ta yi, ta ce, " Manager ya ku kai da Oga Habib d'in ? ". "Wai inje sai ya nai man". Manager ya basu amsa".
Farida kallan manager ta yi, ta ce, "Wai dan ka mari yarinyar nan ne ya ke ma kora da hali haka? ". "Eh haka ne". Cewar manager. Farida ranta b'ace ta bar gurin bata sake iya yin managa ba. Manager kuma fita ya yi daga Company baki d'aya . Inda ita kuma Billy ta koma ta ci gaba da aikinta".
Habib yau ma kamar jiya yana tashi aiki ya yo gidan Hajiya Turai. Babu kowa a falon, Habin zama ya yi yana jiran fitowar Hajiya Turai, yana nan zaune ko Hajiya Turai ta fito. Habib koda ya gaida Hajiya Turai da sakin fuska ta amsa mai ba kamar jiya ba, Habib ganin haka, ya sa ya ce, "Mommy kunu na ke so please ". Hajiya Turai da kanta ta shiga kitchen ta dama ma Habib kunu ta kawo mai.Hajiya Turai na ba Habib kunu ta nufi bedroom d'in ta inda ta bar Hassana, Hajiya Turai kwance ta iske Hassana, Hajiya Turai gefan Hassana ta zauna, ta ce, "daughter tashi mu yi magana". Hassana tashi ta yi ta zau na".
Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter dama ina tsoran Allah ya kamani da shiga hak'inki da nayi a matsaynki na marainiya, ina tsoran kar Allah ya ka mani da laifi. A kwanakin baya kin nai mi zaki tafi gida na hanaki, saboda ina ganin kamar zaku dai-dai ta tsakaninki da Habib, ashe tunanina ba haka bane, tabbas na yi kuskure saboda aure ya na tafiya yadda ake so ne idan akace akwai Soyayya tsakanin ma'auraratan, amma idan ya kasan ce babu Soyayya tom zaman auran zai ka sance wani iri ne, ko wa ba zai iya jure abinda abokin zaman shi ya yi masa ba, ko ya ya ya ke, tabbas na yi kuskure, amma dan Allah ki yafe min, yanzu haka maganar da nake miki na gama shirya komai na tafiyarki garin ku, yan zu haka idan kin shirya gobe ma za ki iya tafiya, ni zan rakaki, amma sai nayi wani tunani naga bai kamata ba ki tafi da auran Habib akanki ba, dan haka yan zu haka yana Falo ki je ki sa mai ya baki ta kardarki, karki tafi da aure kan ki". Hassana cikin wani kallar ya nayi wanda ita kanta ta kasa gane kallar halin da take ci ki, ta d'ago tana Kallan Hajiya Turai, tama rasa abinda zata ce mata".
Hajiya Turai ko hannu Hassana ta kama ta tadar da ita tsaye, ta ce, "Daughter je ki ki amsa kinji karya wuce, gobe nake son mu tafi". Hassana ta na fiya zufa na keto mata kota ina, Hassana tsayawa ta yi ta d'an jin gina da k'ofar bedroom d'in Hajiya Turai, dan jinta ta ke kamar zata fad'i, Hassana tsayawa ta yi tana maida numfashi kamar wadda ta yi wani aiki,Hassana ko so take ta dawo natsuwarta sannan ta tafi, dan sosai ta ke jinta duk a rikice. Hassana ta dad'e sosai gun a tsaye sannan ta samu ta daurar da zuciyarta ta shiga Falon".
Habib tun daga nesa ya ke Kallan Hassana , da mamaki ya kuma kallanta ganin ta da ya yi tsaye, kuma, daga gani kamar tana cikin damuwa. Habib ganin Hassana bata da niyyar k'ara sowa inda ya ke, kuma yana yinta ya nuna kamar tana cikin damuwa, Habib tashi ya yi yak'a ra sa inda Hassana take, Habib Kallan Hassana ya yi ya ce, "Sanat lafiya? ". Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib gobe zan koma mahaifata, tom bana son in tafi da aure kaina, ina son ka datse igiyar da ke tsakanin mu.......... โ๏ธ
Idan kin karanta daure ki Comment sister ๐ค.
Share
&
Comment please ๐.
๐ OGA HABIB ๐
๐ซ๐ซ
*๐
๏ธARUMAI ๐
ฆ๏ธ WRITERS ๐
๏ธSSOCIATION๐๐๏ธ*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐ช*_
*๐ซ(๐
๏ธ.๐
ฆ๏ธ.๐
๏ธ)๐ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://www.facebook.com/groups/301023561618950/
ALLAH karaya mu dan manzon Allah, ina ma duk kan d'aukakin musulmi barka da juma'@t mubarak, Allah ya had'amu da albarkar da ke cikin wannan rana๐๐๐.
Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa๐๐.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.
Paid book
Akan farashi mai sauk'i da rahusa ๐๐
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number๐ 08063830828
Shafi na 81&82.
Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib gobe zan koma Mahaifata, tom bana son in tafi da aure kaina, ina so ka datse igiyar da ke tsakanin mu". Habib da ke rik'e da hannun Hassana, sakin hannunta ya yi, ya koma kan caution ya zauna, ya yi shiru yana kallan Hassana, dan yama rasa abinda zai ce mata. Hassana ko ganin Habib ya yi mata shiru ya sa ta matsa in da ya ke, cikin sanyin muryarta , ta ce, "Oga Habib ka yi shiru? ". Habib kallan Hassana ka wai ya yi ya rasa abinda zai ce mata, daga k'arshe ma tashi ya yi zai tafi, Hassana ta yi saurin bin shi ta rik'o hannun shi, ta ce, "Oga Habib gobe da wuri zamu wuce, babu lokaci". Habib cikin masifa ya fusge hannun shi daga na Hassana, ya ce, "Ko yan zu ma ku wuce ma na, sai me!, ita kuma Mommy da ta aiko ki ai bani na had'a abin ba , tun farko, ita da ta had'a, zata iya datsewa ba tare da sani na ba, inda dama bada sani na ta had'a ba! ". Habib na kaiwa nan yaja k'ofar falon da k'arfi ya bud'e ya fita, ya bar Hassana nan tsaye".
Hassana komawa ta yi ta zauna kan caution tana mai da numfarfashi kamar wadda ta yi gudu. Hassana kwanciya ta yi kan Three seater, tana magana da zuciyarta ita kad'ai, Wata zuciyar ta ce, "Mommy me yasa kiki so ki ma rayuwata illa?, haba mommy tun-tuni me yasa biki raba ni da Oga Habib ba sai yan zu da zuciyata ta saba da shi... ". Haka Hassana ta kwanta a falon sai zan can zuci ta ke, gaba d'aya ta rasa abinda ke mata dad'i".
Hajiya Turai ko jin Hassana shiru ya sa ta biyo Hassanar, kwance ta iske ta a falo, daga gani ta yi ni san kiwo a duniyar tunani. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter ya ba ki ko? ". Hassana tashi ta yi ta zau na, ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Mommy cewa ya yi, wai lokacin da akai bai sani ba ai, wai yan zu ma za a iya warware wa bai sani ba". "Ok, haka ya ce ko?, bari in kira shi a waya ". Cewar Hajiya Turai ".
Hajiya Turai kiran Habib ta yi, awaya, Habib lokacin yana kwance ko mawar shi kenan gida, yana zuwa ya fad'a kan bed d'in shi ya kwanta sai juyi ya ke shi kad'ai. Yana a wannan halin ne kiran Hajiya Turai ya shigo wayar shi. Habib kamar kar ya d'aga amma kuma sai ya ga garama ya d'aga ya ji abinda zata ce, hakan yasa Habib ya d'aga ya kanga wayar a kunnan shi".
Daga can b'angaran kuma Hajiya Turai ta ce, "Hello Habib, naji sak'on ka, tom bari kaji da ina da mar datse igiyar da ke tsakaninka da Hassana da na datse ta tun jiya, tom amma a musulinci ban da huru min hakan, zan iya had'a wa amma raba wa kuma dole sai kai ne zaka yi ta, dan haka gobe kazo da wuri ina sauraranka , ka kawo min takardar ta, idan kuma ba haka ba, ranka zai b'ace sosai! ". Hajiya Turai na kaiwa nan ta kashe wayarta, bata saurari abinda Habib zai ce ba".
Hassana ko da ke sauraran magan-ganun Hajiya Turai, ji tai kamar ta fasa ihu, ko Hajiya Turai zata fahimci halinda ta ke ciki. Hajiya Turai kuma kiran Hassana ta yi, ta ce, "Daughter tashi ki je ki kwanta kab bacci ya kwashe ki anan". "Mommy anan zan kwana ". Cewar Hassana ". Hajiya Turai hannu Hassana ta kama ta ce, "Tashi mu je ba za ki kwana a falo ba". Hassana tashi ta yi, ta bi Hajiya Turai ".
Washe gari Habib bayan ya yi shirin ta fiya aiki, gidan Hajiya Turai ya biya, Yana zuwa ya iske falon ba kowa, ya da d'e zau ne Hajiya Turai bata zo ba, Habib da ya gaji da zama tashi ya yi ya tafi".
Hajiya Turai ko da bata san Habib ya zo ba tada d'e tana sauraran zuwan shi amma taji shiru, hakan yasa ta kira shi awaya, yana d'aga wa, Hajiya Turai cikin masifa ta fara fad'a kamar haka"Habib ni zaka raina ma hankali ko?, nace kazo yau ina jiranka, shine kai min banza kai wucewar ka aiki ko? ". "Mommy nazo banga kowa ba, na dad'e zau ne a falon". Cewar Habib. "Ok kazo yan zu ina jiran ka! ". Hajiya Turai na fad'in haka ta kashe wayar ta ".
Hajiya Turai na nan zau ne Habib ya shigo, Habib zama ya yi, Hajiya Turai ta kallai ta ce, "Yau na cema zan raka Hassana mahaifarta, kuma yarinyar nan ta saman ta ce min bata son tafiya da aure kanta saboda idan ta tafi bazata dawo ba, dan haka