Author : Faddy baby Category : Romance
mutum, dan haka ki samu dogayan riguna guda Shida (6) ki saya".
Hassana kallanta ta yi, sannan ta ce, "Tom taya zan siya, nida bansan ko inaba? ". "Nizan siyo maki gobe a wuse market ". Shiru Hassana ta yi, Sannan ta ce, "Shikenan ki rik'e kud'in awajanki goban sai ki yi amfani da su". Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Sister Jimmai zan tafi, Hajiya na jirana".
Hassana kayanta ta d'akko sannan ta tafi".
Jimmai ko har kusan part d'in Hajiya Turai ta raka Hassana tana k'ara kwantar mata da hankali, tana cewa"Wallahi Hassana ki saki ranki kici arzik'i kibar arzik'i". Nan dai Jimmai ta tafi tabar Hassana".
Hassana kan abin Sallah ta iske Hajiya Turai. Hassana zama ta yi tana jiran Hajiya Turai ta idar. Hajiya Turai ko na idarwa ta kalli Hassana ta ce, "kin yi Sallah? ". "A'a, banyi ba". Hassana taba Hajiya Turai amsa".
Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Shiga bedroom d'ina ki yi alwallah kizo ki yi".
Hassana tashi ta yi tashiga bedroom d'in Hajiya Turai tashiga toilet d'in ta. Hassana ta dad'e tsaye tana yaba tsaruwa da had'uwa na toilet d'in Hajiya Turai, dan sai yafi burgeta fiye da na Habib. Hassana alwallah ta yi tazo bayan HajiyaTurai ta tada sallarta".
Bayan Hassana ta idar da sallar ne tana nan zaune har ake sallar isha'i ta tashi ta yi. Bayan duk sunyi sallah ne, Hajiya Turai ta kalli Hassana, ta ce, "Hassana ki d'auki kayanki sai ki kai site d'in Habib d'in, zan aiko miki da abinci da maganin shi. Rubutun farar roba shine nadare d'ayan kuma na safe da rana sai dare". Hassana tom ta ce ta tashi ta tafi tana jinta duk ba dad'i".
B'angaran Farida ko cema Mahaifiyarta ta yi, bazata dawo gidansu Habib ba sai zuciyarta ta lafa, dan hankalinta atashe ya ke game da maganar auran Habib da Hassana. Duk da mahaifiyarta tana ta yi mata kalamai masu sanyin akan auran, acewarta bazai je ko ina ba, dashi da babu duk d'aya ne, dan hakakama karma ta d'aura makanta damuwa".
B'angaran Hassana cikin sanyi ta bud'e k'ofar Falon Habib tashiga. Allah sarki Habib zaune yake yana jin alamun shigowar mutum ya tashi da sauri, dan wannan ita ce d'abi arshi. Shiyasa kusan duk lokacinda Hassana zata shiga sai gabanta ya fad'i, dan in yayo kanta sai ta ga kamar itama wujijjigata Zai yi irin yadda ya ke ma mutane. Hakan yasa indai ya taho jikin k'ofar ta ke jingina da d'an alamar tsoro. Habib na k'arasowa inda Hassana ta ke, Kamar yadda ya saba ya rik'o hannunta ya k'arasa da ita cikin Falon. Habib kan caution ya zauna ya zaunar da Hassana kusa da shi kamar yadda ya saba".
Hassana ko kanta ak'asa ta kasa kallan Habib, dan gaba d'aya yau ta kasa sakewa da Habib kamar yadda ta ke yi kullum. Hassana na nan zaune Baba Lami tai mata nocking , tana kiranta.Hassan da saurinta ta tashi ta nufi wajan k'ofar. Nan fa shima gogannata ya tashi da sauri ya bita. Hassana bud'e k'ofar ta yi da niyyar amsar abincin. Habib ya yi kan Baba Lami. Hassana da sauri ta irik'e Habib, Baba Lami kuma ta yi saurin aje abincin da rubutun hannunta ta ce, "Kai Hassana Sannu da k'ok'ari dama haka yakema mutane aini bansani ba". Hassana cikin sanyi ta ce ma Baba Lami "Eh Baba haka yake yi". Hassana rufe k'ofar ta yi sannan ta kalli Habib da ke rik'e da hannunta ta ce, kamar za tai kuka"Oga Habib kasa kar min hannu dan Allah in d'auki abincin in shigar da shi ciki". Habib kafad'a ya mak'ema Hassan. Alamun bazai saki ba. Hassana bakin k'ofar Falon ta zauna ta ce, "Tom sai kaci abincin anan inda kak'i sakina in shigar da shi ciki".
Habib na ganin Hassana ta zauna shima ya zauna. A gurin Hassana ta zubama Habib tuwan shinkafa da miyar a gushi. Habib sosai Ya ci abincin, sannan sauran da yarage Hassana ta d'auka itama taci dan tun kusan safe bataci komai ba".
Bayan Hassana ta gama cin abincin ne ta ta ta shi takoma kan caution d'in Falon ta zauna, Habib ma zama ya yi kusa da ita yana mai rik'e da hannunta. Nan dai Hassana ta fara gyan-gyad'i , dan jiya kusan bata yi bacci ba. Hassana ganin zata fad'i yasa ta kwanta kan caution d'in da yake 3 seater ce".
Habib ma ganin Hassana ta kwanta, shima bin bayan Hassana ya yi ya kwanta, akan caution d'in kusan kan Hassana, inda gurin ya yi masu kad'an. Hassana da sauri ta ta shi tana kallan Habib, ta ce, "Oga Habib ka tafi bedroom d'in ka ka kwanta". Habib mak'ema Hassana kafad'a ya yi, irin nak'i d'in. Hassana tashi ta yi ta kai Habib bedroom d'in shi, ta zauna bakin bed d'in ta ce, "Tom kakwanta". Habib kallan Hassana ya yi, yana zaune kusa da ita dan shima zama ya yi kamar yadda yaga ta zauna".
Hassana hawa ta yi kad'an kan gadon ta kwanta, inda taga sai abinda ta yi ya ke yi. Aiko take shima ya kwanta bayanta. Hassana tashi ta yi da sauri ta ce, " tom ka kwanta ka yi bacci ". Tanu falon. Tana tashi Habib ma ya tashi yabi bayanta". Hassana na zuwa ta kwanta kan caution d'in duk ta tattare yadda babu yadda Habib zai yi ya kwanta, dan bata bar guba, duk ta babbake caution d'in. Habib ko nazuwa yabi kan Hassana ya kwanta".
Hassana cikin tsabar nauyin shi da taji ta ture shi ta milmilo k'asa da sauri tana nishi ta kwanta. Habib d'in ma k'asan ya biyota ya kwanta shima. Hassana juyowa ta yi tana kallan Habib, dariya ma ya bata, aiko ta haudariyarta. Damamaki sai taga Habib d'in shima yana murmushi. Hassana kallan shi ta yi ta girgiza kai. Dan baccinma sai taji ya wuce. Hassana cigaba da kwanciyarta a k'asa ta yi, ahankaki-ahankali ta ji bacci na son d'auketa. Tashi ta yi ta zauna dan tasan indai ta yi bacci tom bazata iya tashi ba taba Habib maganin shi, hakan yasa tana tashi ta d'akko wayar Habib da ta ke gani a Falon ta duba taga. 11:57Am. Hassana maganin Habib ta tashi zata d'akko da mamaki tabi Habib da kallo ganin ya tashi ya biyota dan duk atunaninta bacci ya ke. Hassana rubutun ta d'akko ta tsiyaya a cup. 12:00Am nacika ta mik'ama Habib maganin. Habib k'in amsa ya yi. Hassana ta san dalili dan ya k'oshine, dan ta lura indai ya k'oshi kome zata bashi baya amsa. Hakan yasa Hassana ta kai Cup d'in bakinshi ta ce, "Tom sha". Habib bud'e baki ya yi yana sha. Nan ya shanye wanda ta zuba mai".
Hassana nagama ba Habib maganin ta ci gaba da kwanciyarta ak'asa Habib ma k'asan ya bita ya kwanta. Hassana duk yadda zatai ma Habib ya tafi bedroom d'in shi ya kwanta ta yi mai amma yak'i. Hassana kwanciyarta ta yi tana jan tsaki, dan duk sai taji badad'i yadda Habib duk ya kanannad'eta, gashi yasa hannu d'aya ya rik'o k'ugunta, hakan yasa ta kuma jinta wani iri ba dad'i. Hassana hannu Habib ta kama ta rik'e dan ba tajin dad'in yadda ya rungumota ta baya. Shiko Habib hannun shima da ta rik'e ya isai, dan dama gani ya ke kamar zata gudu ne, yana ko jin ta kama mai hannu shikenan".
Hassana cikin dare ta tashi domin yin fitsari dan ita tana da tashin fitsarin dare. Abin mamaki tana tashi Habib ma ya tashi".
Hassana da kallo tabi Habib, sannan tanufi bedroom d'in shi dan acan ne toilet d'in shi ya ke. Hassana na tafiya Habib ya bi bayanta. Hassana ta bud'e k'ofar toilet d'in ta shiga, kusan tare da Habib suka shiga. Hassana kallan Habib kawai ta ke, sannan ta ce, "Oga Habib kafita mana, baka ganin nan toilet ne". Shidai Habib da ido ya bi Hassana da kallo. Hassana ganin Habib ba fita zai yi ba, kuma fitsari ya matseta ya sa ta zuk'unna ta yi fitsarinta".
Hassana na zuk'unnawa Habib ma ya zuk'unna bayanta shima yana fitsarin. Hassana na gamawa ta fito shima Habib ya tashi ya fito. Wato so dadama idan Habib ya yi wani abun, Hassana sai taga kamar mai hankali, sai dai in yayi wani abunne zaka tabbatar da k'wak'walwar ta tab'u".
Hassana komawa kan bed d'in Habib ta yi ta kwanta, d'an ak'asan sanyi gashi ana sanyi-sanyi". Habib bayan Hassana yabi ya kwanta, Hassana ko kojuyowa bata yi ba, jin ankwanta bayanta dan tasan kowaye".
Kiran sallar asuba, Hassana ta farka ta ga Habib kamar wanda ke shirin shigewa cikinta, yadda ya kanannad'eta ga hannu d'aya yasa ya rik'e k'ugunta da shi. Hassana cire habnun Habib ta yi daga jikinta, sannan ta d'an ture shi daga jikinta ta tashi. Tana tashi yana tashi yabi bayanta. Atare kusan sukai alwallar dan duk abinda ta yi sai ya yi. Sallarma tana ta dawa shima yazo kusa da ita ya tsaya yana yin duk yadda ta yi, ahaka dai suka idar da sallar. Sai da ka gari ya yi haske sannan Hassana ta tashi. Ta koma kan caution zata kwanta sai ta tuno daga ta kwanta mutuninta shima zai ce zai kwanta kuma gurin ba isarsu zai ba, hakan yasa ta fasa ta koma kan sallayar ta kwanta. Aiko shima kusa da ita ya kwanta".
Bacci mai nauyi ya d'auke Hassana, dan bugun da akema k'ofar ne ya sa ta tashi a furgice ...............
Idan kin karanta d'aure ki yi Comment sister π€
Share
&
Comment please π.
π OGA HABIB π
π«π«
*π
οΈARUMAI π
¦οΈ WRITERS π
οΈSSOCIATIONπποΈ*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπͺ*_
*π«(π
οΈ.π
¦οΈ.π
οΈ)π«*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
*YAN UWA KULLUM KARA KUSANTAR KABARI MUKE KWANAKINMU SUNA KAREWA AJALINMU YANA KUSANTOMU AMMA BAMA FARGA DA HAKAππ!*ALLAH KASA MU CIKA DA IMANIπππππππ.
Shafi na 38&39.
Hassana cikin furgici ta tashi tsabar yadda ake buga k'ofar. Hassana tashi ta yi da saurinta dan zuwa ganin mai bugun k'ofar. Baba Lami ta gani tsaye da abin breakfast d'in su a hannunta. Hassana kallan Baba Lami ta yi tana murza ido ta ce, "Baba dama ke ce, Wallahi har naji tsoro! ". Dariya Baba Lami ta yi, ta ce, "Haba wannan wana irin bacci ne, tun d'azu fa nake tsaye nake buga k'ofar nan, amma shiru". Hassana mutsitsika ido ta k'arayi ta ce, "Ina kwana Baba ". "Lafiya k'alau Hassanan, ya mai jikin? ". Hassana cikin alamun kunya tace ma Baba Lami, "Da sauk'i ". Baba Lami kallan Habib ta yi dake tsaye kusa da Hassana ta ce, "Hassana ki matsar da mutumin naki sai in shigo in kawo muku abin k'arin,". Hassana bud'e ma Baba Lami k'ofar ta yi ta matsa da Habib daga jikin k'ofar. Amma duk da haka bai hana Habib yunk'urowa ba ya ce zai kamo Baba Lami. Baba Lami ko da saurinta ta aje abin breakfast d'in ta gudu".
Hassana zuwa tai ta rufe k'ofar, sannan ta je cikin kayanta da tazo da su, ta d'akko brush d'inta tashiga toilet d'in Habib ta yi brush. Habib ko tsaye ya ke cikin toilet d'in shima yana kallan Hassana, Hassana kallan Habib ta yi bayan ta gama brush d'in, ta ce, "Oga Habib kaima za kai? ". Habib dai da ido yabi Hassana da kallo. Hassana d'aya daga cikin tooth brush d'in da ta gani a toilet d'in ne ta matsama Habib toothpaste ta mik'amai. Habib amsa ya yi yana kallan Hassana. Hassana hannu Habib ta gama ta kai brush d'in bakin shi ta ce, "Yauwa tom wanke bakinka ko? ". Habib kafad'a ya mak'ema Hassana alamun bazai wanke ba. Hassana amsar brushi d'in ta yi daga hannun shi ta ce, "Tom bani ni in wankema". Habib sakarma Hassana brush d'in ya yi. Hassana ta ce, "Yauwa tom bud'e bakin". Habib bud'e bakin ya yi. Hassana ta tura brush d'in cikin bakinshi tana wankema. Sai dai fa mai makon ya zubar shanyewa ya ke. Hassana kallan shi ta yi, ta ce, "Kai Oga Habib ba fa shanyewa ake ba, karik'a zubarwa kaji?, yauwa tom zubar haka". Hassana ta tofar da miyau abakinta, tana gwadama Habib shima yadda zaiyi ".
Nan dai ashiririce aka dama wanke bakin. Hassana break fast d'in da Baba Lami ta kawo masu ta d'akko tana bud'ewa, kunun gyad'a ne ya yi haske sosai sai k'amshin kunun ya bid'e falon. Sai soyayyar doya da akai ma miyar k'wai. Hassana tsiyayama Habib kunun ta yi, tana bashi ko ya amsa ya fara sha. Hassana soyayyar doyar taba Habib amma ya k'i ci. Rubutunshi ta d'akko ta bashi, sannan itama ta zubama kanta kunun tasha, bayan ta gama shanyewa ne ta ci doyar. Habib shima ganin Hassana na cin doyar d'auka ya yi yana ci. Hassama sosai ta ci doyar. Bayan Hassana sun gama break fast d'in ne, taji tana son yin kwanka inda dama ta saba wankan safe ta ke, amma kuma bata san yadda zatai da Habib ba. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib ka zauna nan zanyi wanka, indai kuma ka biyoni tom zan b'ata da kai zan tafi in barka, kaji? ". Habib shi dai kallan Hassana ya yi da ido".
Hassana ko, tashi ta yi ta nufi bedroom d'in Habib.abin dariya kusan tare suka shiga bedroom d'in. Hassana tsayawa ta yi tana kallan Habib ta ce, "Oga Habib Allah yau zan b'ata da kai indai baka zauna ba kajirani nayi wanka, ka zauna nan kaji rani". Habib mak'ema Hassana kafad'a ya yi alamun yak'i d'in".
"Hassana ta ce, "Na shiga uku, tom wai kai komai zanyi sai ka bini". Hassana hannun Habib ta kama ta zaunar da shi bakin gado, ta ce, "Yauwa, tom zauna anan in yi wanka ". Habib kallan Hassana ya yi. Hassana ko ganin Habib bai mak'e mata kafad'a ba, sai ta yi tunanin bazai bita ba, ya hak'ura zai zauna, hakan ya sa,Hassana tashi ta nufi toilet d'in. Aiko tana shiga kusan atare suka shiga".
Hassana cikin jin haushin Habib d'in ta d'aure fuska ta ce, " Oga Habib fita".Hassana ta fad'i maganar tana nunama Habib hanyar fita. Habib ko da ido ya bi Hassana da kallo. Hassana ko ganin haka sai tafara tura Habib. Sai dai ko motsi Habib bai ba. Hassana duk yadda za tai da Habib ya fita yak'i dole ta rabu da shi ta fasa yin wankan ta fito, ta zauna bakin bed d'in Habib cikin jin haushin Habib ya k'ifita yabarta ta yi wanka".
Habib ko zama ya yi kusa da Hassana zai kama hannunta. Hassana cikin jin haushi ta fusge hannunta ta ce, "Da Allah ni sakarmin hannu, aina b'ata da kai tunda kak'i barina inyi wanka. Habib ko kallan Hassana kawai ya yi. Hassana na nan zaune taji yo nocking d'in k'ofa. Tashi ta yi da sauri, mutumin tama ya mara mata baya".
Hassana tana zuwa abin mamaki Hajiya Turai ta gani tsaye jikin k'ofar. Hassana cikin sanyin murya ta ce, "laa Mommy ki ce, bari in bud'e miki". Hajiya Turai da katar da Hassana ta yi ta ce, "A'a my daughter bari basai na shigoba, nazo ne in ganku, inji ya kuka tashi". Hassana cikin girmama Hajiya Turai ta ce, "A'a Mommy dan Allah ki shigo". Hajiya Turai murmushi ta yi tace, "My daughter so kike yau in kasa bacci, dan wujijjigawar da yayi min rannan har yanzu ina jinta ajikina, dan haka barni kawai ba saina shigoba". "Mommy Allah naga kamar ya rage, dan ko yau da Baba Lami ta shigo kawo abin breakfast naga bai ce zai bita ba, ki shigo ai ina nan". Hajiya Turai shahada ta yi ta ce ma Hassana tom bud'emin". Hassana bud'ema Hajiya Turai ta yi".
Habib ko da yake tsaye kusa da Hassana yana rik'e da hannunta yana ganin Hajiya Turai ta shigo ya yi kanta. Hassana da sauri ta jawo Habib ta ce, "Oga Habib Mommy ce fa?, kamanta ta ne, kabarta kaji? ". Habib mak'e kafad'a ya yi".
Hajiya Turai ko naganin haka ta ce, "My daughter rabu da shi bari in fita ". Hajiya Turai ta yi maganar kamar za tai kuka".
Hassana kai ta girgizama Hajiya Turai ta ce, "A'a Mommy dan Allah ki zauna babu abinda zai miki insha Allah ".
Hajiya Turai d'annesa da su Hassana ta zauna kan 1 seater. Hassana ma zama ta yi, kan 3 seater, Habib ma ya zauna kusa da Hassana".
Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Daughter ya jikin nashi kike gani tsakanin jiya da yau? ". "Tom da sauk'i inda naga kamar yanzu yarage cewa zai bugu duk wanda ya shigo sai dai hargagin zai bugun, inda kinga ko d'azu da Baba Lami ta shigo sai dai har gagin ya yi". Hajiya Turai cikin jin dad'i ta ce, "Alhamdulillah Allah ya kawo sauk'i gaba d'aya ". "Ameen ya Allah ". Cewar Hassana. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "My daughter inda naga alamun sauk'i yafara zuwa, inda gani har kusa da Habib bai min komai ba, abinda da bahaka ba, yanzu insha Allah nan da sati idan naga yanayin jikin zan je London, wajan aiki sun daman da kira, zan je ko sati d'aya inyi in dawo, yanzu baki da wata matsala ko? ". "Eh Mommy babu"."Ok, yau zanba Bilya kud'i ya sayo miii waya idanma kina buk'atar wani abun sai kikirani awaya, inda naga mutumin naki babarinki fita zai yi ba". Murmushi Hassana ta yi ta ce, "Tom Mommy nagode".
Hajiya Turai fita tayi tabar Hassana da Habib.Hassana na nan zaune tana tunanin yadda za tai tai wanka sai ta ji nocking d'in k'ofa, da yake tunda Hajiya Turai ta fita Hassana bata tashi