OGA HABIB Bacewa da Samuwa by Faddy baby

Author :  Faddy baby Category :  Romance

Chapter   12 / 41

33K to 36K   out of 121.2K words

yake kai sanin kanka ne, Hassana bata isai kallo ba, dan haka ka saisaita kalamanka". Bilya cikin jin haushi maganganun Musa, ya juya ya tafi yabar Musa agun tsaye.
Musa ma biyan Bilya ya yi suka tafi".

Hassana ko najin maganganunsu Bilya sama-sama amma batajin me suke cewa. Hassana haka taita malelekuwarta a gadon Habib. Habib ko duk inda Hassana ta yi ya na biye da ita, ahaka bacci ya kwashe Habib yana rik'e da hannun Hassana.
Hassana ko sai gab da asuba taji sauk'i daga yadda ta ke ji, nan fa bacci ya d'auketa".
Habib ko koda ya tashi ya ga Hassana kwance tana bacci, kwanciya ya yi shima gefanta ,ya na rik'e da ita".

Hassana sai 7:00am ta farka. Cikin mamaki da tsoro Hassana ta ke kallan kanta, jikinta babu kaya ga ta kwance da Habib a gado d'aya, ya na rik'e da ita. Hassana tsabar tashin hankali da tsoro kawai sai ta sa kuka ta tashi da sauri ta nufi falo dan d'akko kayanta.
Habib kuma na ganin Hassana ta sauka kan bed d'in shima ya yi sauri ya sauka ya bi bayanta. Hassana ta d'akko rigarta kenan zata sa sai ga Habib ya fito, tasan gurinta zaizo hakan yasa Hassana cikin kuka ta d'aga ma Habib hannun, alamun da katarwa, ta ce, "Oga Habib karka k'araso inda nake Wallahi! ".Hassana ta fad'i maganar cikin kuka. Habib ko da kallan Hassana kawai ya ke ba gane meta ke cewa ya ke ba, inda ta ke ya zo, yana zuwa ya rik'e hannunta kamar yadda ya saba".

Hassana ko naganin Habib ta yi sauri ta jira rigarta,dama doguwar rigace.Sannan ta d'akko Hijab d'in ta ta saka.Ta ci gaba da kukanta. Har yanzu Hassana kuka take, zaune ta ke kan Caution d'in Falon tana kuka Habib kuma na rik'e da hannun yana aiki kalkonta".

Hassana tunanin ta farayi ahankali, tana tuno abinda ya faru da ita ya fara dawo mata kad'an-kad'an. Tabbas idan bata mantaba tabbas tunda tasha maganin da Farida ta bata, ta rasa natsuwarta, Hassana kallan wanda ta bata taba Habib ta yi. Alhamdulillah Hassana ta ce, ganin wanda Farida ta bata tace taba Habib bata bashi ba, dan tabbas wanan maganin nada wani sinadari na b'atar da hankali cewar Hassana, amma kuma ai Aunty Farida "yar'uwar su Oga Habib ce, bazata bashi abinda zai cutar da shiba, tom amma ni meyasa maganin ya yi min haka?, haka dai Hassana ta gama tambayar kanta ba amsa, kuma still bata bar kukan da take ba. Hassana nan zaune tana kuka, ta ji nocking. Share hawayanta ta yi, sannan ta je ta lek'a ta window ".

Hassana Bilya ta gani tsaye ya yi crossing d'in hannun shi yana mata wani irin kallo da yasa ta sha jinin jinin jikinta. Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, tana didduk'ar da kai kamar muna fuka, ta ce, "Oga Bilya ina kwana". Me makon Bilya ya amsa ma Hassana gaisuwarta sai cewa ya yi, "Hassana jiya me yasa da muka buga k'ofa biki bud'e mana ba? ". Hassana cikin rawar murya ta ce, "Oga Bilya bacci ne ya kwasheni". "Amma meyasa baki kwanta falo ba! , kika shiga bedroom d'in Oga Habib? ". Hassana sosai ta tsora da kalaman Bilya da yana yin yadda ya ke mata magana, hakan yasata, cikin rawar murya ta ce, "Oga Habib ne ya kaini". Bilya kallan Hassana ya yi, ya dad'e yana kallanta sannan ya ce, "Hassana me yasaki kuka? ". Shiru Hassana ta yi tana wasa da fingers d'inta. Bilya k'ara mai-mai ta ma Hassana tambayar shi ya yi, ya ce, "Hassana nace me yasa ki kuka? ". Hassana kuka ta sa, still ta kasa yin magana".

Farida ko da zuwanta kenan tazo ganin k'wak'waf, da sauri ta lab'e tana mai jin dad'in ganin Hassana da ta yi tana kuka, dan ko ba afad'a mata ba, tasan mai faruwa ta faru, tsakanin Hassana da Habib. Farida cikin jin dad'i ta koma d'akinta, tana zuwa ta fad'a kan bed d'inta tana jin dad'in abinda ta gani, dan tabbas Hassana kukan da ta ke yi na kusantarta ne da Habib ya yi, acewar Farida.waya Farida ta d'akko ta kira Mahaifiyarta, Hajiya Murja dan yi mata albishir.
Hajiya Murja na d'auka Farida ta ce, cikin jin dad'i, "Mommyna albishirinki? ". Daga can b'angaran, Hajiya Murja ta ce, "Goro fari k'ar kato". Farida cikin murna da d'oki ta ce, "Mommyna Wallahi na yarda da aikin Malam mai biyan buk'ata dole, Mommyna aiki ya k'arye dan Oga Habib ya kusanci Hassana, yanzu haka maganar da nake miki kuka ta ke, yanzu Mommy ki je gun Malam ya baki na barinta gidan sai kizo da shi, dan ni Wallahi bana son ta k'ara kwana a gidannan". Hajiya Murja itama cikin jin dad'in nasarar aikin da su kayi ta ce, "Tom Farida yanzu sai hankalinki ya kwanta ko, kinga dai alamun nasara, yanzu bari inyi breakfast , idan nagama inyi wanka sai in je gun Malam d'in, daga can zo nan"."Tom Mommy sai kin zo". Farida na fad'in haka ta kashe wayar, tana mai jin farinci aranta".

Can b'angaran su Hassana ko, Bilya cikin damuwa ya ce, "Hassana please mana, dan Allah karki sani confused mana, me yasa kike kuka? ". Hassana cikin shasshek'ar kuka ta ce, "Oga Bilya bana son k'ara zuwa gurin Oga Habib dan Allah ". Shiru Bilya ya yi yana mai kallan ganin yadda ta ke kuka. Sannan ya ce, "Shikenan Hassana ki shiru haka nan kar kanki ya yi ciwo,in dai gurin Oga Habib ne ki yi hak'uri, insha Allah daga yau bazaki k'ara zuwa ba, nina san mai zan cema Hajiya ".

Duk maganar nan da Hassana da Bilya su ke yi, ta Window su ke yinta. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce, "Bari in kira Musa muzo mu fidda ki". Kai Hassana ta d'aga ma Bilya, ya juya kai ya tafi".

Bilya ya tafi ba dad'ewa sai ga shi ya dawo da Musa. Musa kallan Bilya ya yi ya ce, "Bilya abata abin breakfast ta bashi mana, inda naji kana cewa daga yau ba zata k'ara zuwa bashi abinci ba". Shiru Bilya ya yi sannan ya ce, "Musa Wallahi anfara shiga hakin yarinyar nan, yanzu haka maganar da nakema kuka nazo na sameta ta nayi, amma bari in amso abin breakfast din in kai mata ta bashi". Bilya wajan Baba Lami ya je, ta had'o mai abin breakfast d'in Habib".

Bilya amsa ya yi, yana zuwa ya yi nocking d'in k'ofar. Hassana ta sowa ta yi. Bilya kallan Hassana ya yi ya ce, "Hassana ga breakfast d'in Oga Habib nan dan Allah ki bashi, ni nai miki alk'awari daga yau ba mai kuma k'arasaki kawo ma Oga Habib abinci ko magani". Hassana amsa ta yi tashiga da shi, kunun gyad'a abinda Habib ya fi so. Hassana zuba ma Habib ta yi ta mik'a mai ya amsa ya shanye. Doya da kwan ta bashi ita kuma ya k'i ci. Habib na gama shanye kunun Hassana tai ma Bilya magana da ya ke, Bilya na bakin k'ofar suna jiran Hassana ta gama ba Habib abin breakfast d'in .
Hassana juyowa ta yi tana kallan Habib da ke rik'e da hannunta, sannan ta kai wasu mintoci tana kallan Habib sannan ta ce, "Oga Habib sakan min hannu zan tafi, sai watarana bazan k'ara shigowa inda kake ba, jiya nariski kaina awani kallan yanayi mai wuyar fassarawa, bana fata haka ya k'ara faruwa dani, bansan nan gaba mai zai faruba, idan haka ya kuma faruwa". Hassana rik'e hannun Habib ta yi, ta ce,"Oga Habib ina maka fatan alkairi, Allah ya baka lafiya".

Hassana na fad'in haka ta juya zata fita, Habib ya rik'e hanunta.
Hassana cikin sanyin muryarta ta kira Bilya, ta ce, "Oga Bilya nagama ku shigo".

Bilya ko da Musa suna tsaye bakin k'ofar, dama Hassana suke jira suzo su fitar da ita".

Da k'arfi su Bilya suka b'amb'are Hassana daga hannun Habib kamar yadda suka saba. Hassana ko mai-makon ta je Falon Hajiya Turai, b'angaran su na "yan aiki ta wuce".

Farida ko da taji shiru, Hassana bata shigo Falon Hajiya Turai ba, tashi ta yi ta nufi part d'in worker's d'in gidan. Farida nesa da b'angaran su Hassana ta tsaya yadda babu wanda zai ji abinda zata cema Hassana. Farida na nan tsaye d'aya daga cikin worker's d'in ta zo wucewa, Farida kiran ta ta yi, ta ce ta kiramata Hassama".

Hassana ko na kwance tana jinta duk ba dad'i, ga halinda ta tashi taga kanta duk ya da meta, dan har yanzu ko mai batasa abakinta ba. Binta kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana Aunty Farida na kiranki". Hassana batare da tace mata komai ba ta tashi ta fita, dan amsa kiran Faridar".

Tsaye Hassana ta iske Farida tana jiranta. Farida kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ke kukan me d'azu naganki kinayi? ". Hassana da mamaki ta kalli Farida dan tambayar tazo mata abazata.Farida ko jin Hassana ta yi shiru tana kallanta ya sa cikin k'osawa ta ce, "Nace me yasa ki kuka d'azu?, da naganki tsaye da Bilya a wajan window Falon Oga Habib ". Hassana rasa abinda zata ce ma Farida ta yi, ka wai sai ce mata tayi. "Aunty Farida banda lafiya ne". Farida cikin d'aga murya ta ce, dan tana tunanin Hassana so take ta b'oyemata Habib ya yi mata Fyad'e, hakan yasa cikin d'aga Murya , Farida ta ce, "K'arya kike Wallahi, me kika ce ma Bilya Oga Habib ya yi miki?, ko kina tunanin banji bane? ". Hassana da mamaki ta ke kallan Farida, sannan cikin sanyin murya ta ce, "Wallahi Aunty Farida bance ma Oga Bilya Oga Habib ya yi min ko mai ba, kawai dai ina kuka ne shine ya ke tambayata abinda ya sani kuka". Farida da saurinta kamar wani zai rigata ta ce, "Tom meye yasaki kukan? ". Hassana kallan Farida ta yi kamar za tai kuka ta ce, "Nagaji da kaima Oga Habib abinci ne, shine yasani kuka". Wani murmushi Farida ta yi ma Hassana , dan ita a d'aukarta Hassana tana karewa ne, bata son taji Habib ta yi mata Fyad'e ne. Hakan yasa Farida ta d'aurai fuska, ta kalli Hassana ta ce, "Hassana ni zaki yi ma k'arya, saboda kina tunanin bansan abinda ya faruba".

Hassana ko rud'ewa ta yi jin abinda Farida ta ce, sai ta ke ganin kamar ko taganta ne lokacinda jiya ta cire kayanta , bayan shan maganin da ta kawo mata. Hakan yasa Hassana cikin zubba kwallah ta ce, "Aunty Farida Wallahi babu komai, amma idan baki yadda ba ki kira Oga Bilya ki tambaye shi". Wani tunanine yazoma Farida, kallan Hassana ta yi, ta ce, " nasan dai kinsha maganin da na baki ko? ". Kai Hassana ta d'aga ma Farida. "Ok, tom na Oga Habib fa da nace ki bashi, kin bashi? ". "Aunty Farida ki yi hak'uri banba shiba, wani na bashi wanda Hajiya taban in bashi, nama zaci wanda kika banne, sai yau da natshi nagan shi, amma yanzu zanje in bash.......... ". Marin da Farida taima Hassana ne, yasa Hassana tai shiru. Farida nuna Hassana da d'an yatsa ta yi, ta ce, "Dan uwarki ni zaki sa in yi asara, tom Wallahi baki isaba kin yi kad'an..... ".

Ringing tone d'in wayar Farida ne yasa ta yi shiru ta maida kanta da kallan wayar. Farida na dubawa taga Mahaifiyarta ce, hakan yasa Farida ta yi saurin barin gurin, sannan ta d'aga kiran.
Hajiya Turai sanar da Farida ta yi gata nan zuwa. Farida cikin tashin hankali ta ce, "Mommy dan Allah ki yi sauri ki zo , Wallahi akwai damuwa sosai".

Farida ko cikin damuwa ta koma falon Hajiya Turai dan sanar da ita zuwan Mahaifiyarta".

Farida zaune ta iske Bilya da Baba Lami da Hajiya Turai a falon, Farida gu ta nema ta zauna, dan tana son jin tattaunawar da suke.
Hajiya Turai kallan Bilya ta yi, ta ce, "Bilya kai fa muke sauraro baka ce mana ko mai ba, kace kuma kana son magana dani". Hajiya Turai ta idasa maganar cikin damuwa".

Bilya sosai ya ji yana jin tausan Hajiya Turai saboda abinda zai ce, amma ganin ta matsu da ta ji, yasa, cikin sanyin murya ya ce, "Hajiya dama akan Oga Habib ne, jiya kince muje mu fito da Hassana bayan ta ba Oga Habib magani, amma Hajiya Oga Habib kinsan bai barin yarinyar nan fita, dan yanzu abin yafara cin tura ma, dan ko yau da safe dakyar nida Musa muka kwaceta daga hanun Oga Habib, Wallahi Hajiya biki ga yadda yarinyar ke kuka ba, tana rok'ona dan Allah ita dai bazata k'ara zuwa kai ma Oga Habib ko mai ba". Shiru Bilya ya yi sannan ya ci gaba da cewa, "Tom Hajiya shine nake son dama musan yadda zamu b'ulloma lamarin, inda ita yarinyar ta nuna gajiyawarta, duk da zuciyata na zargin kamar wani abun ya yi mata".

Hajiya Turai cikin tsantsar damuwar da ta kasa b'oyewa ta ce, "Bilya ya zanyi da Habib, dan Allah kakiramin ita ta rik'a ba Habib magani ni Wallahi konawa ne zan biyata, dan Allah Bilya, ku tai makeni, Habib shikenan min, shi kad'ai ne wanda yarage min nake kallo inji dad'i, dan Allah Baba Lami kisa baki, wa zai ba Habib magani idan yarinyar nan tak'i? ". Hajiya Turai ta idasa maganar cikin rud'ewa".

Shiru Bilya ya yi, dan gaba d'aya tausan Hajiya Turai ya cika zuciyar shi. Baba Lami kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, "Hajiya ni inada wata shawara duk da dai kamar ba mai yuwuwa bace, amma idan aka so zata yuwu? ". Hajiya Turai kamar zata sa ihu ta ce, ", Baba Lami wata shawara ce, ina jinki? ". Shiru Baba Lami ta yi tana tunanin ta inda zata fara ba yani, dan ita kanta tasan lamarin babba ne, sai da Baba Lami, ta d'auki dogon lokaci sannan ta ce, "Hajiya ni gani nake, inda Oga Habib bai yarda da kowa sai yarinyar nan, ko abinci in bata gu bazai ciba, bare magani, rok'onta zamu taru muyi,ta auri Oga Habib kafin nan da yaji sauk'i, Allah bashi sai ayi auran asirri babu wanda zaima sani, Allah bashi duk radda Oga Habib ya warke shikenan, ki naimi zaki bata konawa ne, amma ya kika gani Hajiya? ". Hajiya Turai cikin sanyin ta ke cewa, "Dan Allah Baba Lami ku taimaka ku rok'anmin ita, Wallahi nima tunanina kenan, amma inajin shakkar furtawa dan kar aimin kallon mai son kanta da yawa".

Baba Lami kallan Bilya ta yi tace, "Bilya baka ce komai ba, ya kagani? ". "Eh gaskiya Baba Lami wannan kam shine abunda zai fi, amma kuma shi Oga Habib d'inne, baku tsoran ranar da zai farka ya riski wannan labarin? ". Shiru Baba Lami ta yi, Sannan ta ce, "Bilya ni kaina nasan Oga Habib ba zai zauna da Yarinyar nan ba, dama dai auran kafin yaji sauk'i ne".

Sosai Bilya ya amsu da shawarar dan yafi kowa sanin waye Oga Habib.
Hajiya Turai kallan Bilya ta yi, ta ce, "Bilya kiramin Hassana yanzu ". Bilya tashi ya yi zai fita dai-dai kuma Hajiya Murja ta shigo , shigo warta kenan".

Dakyar Hajiya Turai ta daure wajan sakin fuskarta ta yi ma Hajiya Murja sannu da zuwa.
Nan dai suka gaggaisa da kyau kamar kusan yadda suka saba gaisawa. Hajiya Murja kallan Baba Lami ta yi, ta ce, "Baba Lami wannan meeting d'in fa ,na meye? ". Baba Lami ko da yake tasan abinda ke faruwa, da gayya ta ce, "Na auran d'anki ne, Habib". "Haba-haba aure kuma shidawa? ". Nan Baba Lami ta labarta mata komai game da yadda suka tsara na had'a Hassana aure da Habib kafin ya samu lafiya".

Da kyar Hajiya Murja ta iya b'oye damuwata tana washe baki ta ce, "Hakan ko ya yi ya yi kyau sosai"

Shigowar Hassana da Bilya ce, tasa Hajiya Murja ta yi shiru ta maida kallanta ga Hassana. Hajiya Turai ko hannun Hassana ta Kama, ta ce, "Hassana zaki ji". Hajiya Turai shigar da Hassana bedroom d'in ta ta yi".

Bilya ko na kawo Hassana ya Kama gaban shi, Baba Lami ma hakan ta ke. Falon ya rage daga Farida sai Hajiya Murja".

Farida ko tunda ta ji maganar had'a Hassana da Habib aure, ta tusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka, mai had'e da tashin hankali".

Hajiya Murja ganin Falon ba kowa sai su kad'ai tashi ta yi, ta je inda Farida ta ke tana kuka. Hajiya Murja hannun Farida ta kamo ta ce, "Kishiru Farida dan Allah, karki d'orama kanki wani ciwan". Farida kai ta d'ago tana kallan Mahaifiyarta ta ce, "Mommy ko mai bai yi ba, dan yarinyar nan bata ba Oga Habib maganin nan ba, kuma yanzu kinji maganar da suke yi, Wallahi Mommy idan har haka ta tabbata tom baki sake ganina, Mommy zan tafi wani gu wanda nima bansan inane ba, bazaki k'ara ganinba". Farida ta idasa maganar cikin matsanancin kuka". Hajiya Murja cikin tashin hankali da jin abinda Farida ta ce dan tasan zata yi fiye da abinda ta ce, Hajiya Murja kallan Farida ta yi, ta ce, "Farida Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!, kinji narantse, Wallahi auran nan ba zai yuwu ba, dan haka kima kwantar da hankalinki, ko yanzu bada ga gurin Malam me biyan buk'ata dole bane matsala ta samu, daga gurin mune, dan haka karma ki d'aga hankalinki, da ke za a d'aura auran nan, karma ki sama kanki damuwa ko d'aya". Farida kallan Hajiya Murja ta yi, dan sao taji hankalinta ya d'an fara kwanciya jin abinda Mahaifiyarta ta ce, dan tasan akanta babu abinda Hajiya Murja ba za tai ba, bakamar ce mata d'in da tayi bazata k'ara ganin ta ba".

Farida rik'e hannun Mahaifiyarta ta yi, ta ce, "Mommy ina tsoran asamu kuskure irin wannan karan? ". Murmushi Hajiya Murja ta yi ta ce, "Farida Wallahi Habib bashi da

12 / 41