OGA HABIB Bacewa da Samuwa by Faddy baby

Author :  Faddy baby Category :  Romance

Chapter   39 / 41

114K to 117K   out of 121.2K words

kai ta d'aga ma Habib". Habib kama hannun Hassana ya yi suka nufi asibitin da aka kwantar da Farida...... โœ๏ธ



Idan kin karanta daure ki Comment Sister ๐Ÿค



Share
&
Comment please ๐Ÿ™.


๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).



Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusa๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa ๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ

VIP group 300 Only๐Ÿ‘Œ , normal kuma 200 ne, zaki yi transfer ta account d'in nan 2111619333.
Account name Fadila Sani.
Bank Name Zenith bank.
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan Number๐Ÿ‘‰ 08063830828


Shafi na 90&91.



Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Sanat za ki bi ni ne? ". Hassana kai ta d'aga ma Habib. Habib kama hannun Hassana ya yi suka nufi asibitin da aka kwantar da Farida".


Habib na rik'e da hannun Hassana su shiga d'akin da aka kwantar da Farida. Lokacin Hajiya Turai bata nan ta ta fi kiran likita ya duba Farida ganin yadda ta ke ta aman jini, Habib da Hassana da sauri suka k'arasa in da Farida ta ke. Habib cikin tausayin Farida ya ce, "Sannu Farida". Farida ko da ta ji Muryar Habib kamar a mafarki, cikin rauni irin na marasa lafiya Farida ta rik'a lalibar Habib. Hassana ganin haka da sauri ta rik'o hannun Farida. Farida ko a tunaninta Habib ne ya rik'e ma ta hannu".



Farida cikin dauriya da jarumta ta fara magana kamar haka, "Oga Habib ko da Mommy'na ta ce min zaka auran ban yarda ba, duk da ka fad'a aga bana, tabbas kai d'in raban Hassana ce, Hassana ta kasan ce mai sa'a arayuwa, Oga Habib ina ji ajikina mutuwa zan yi sonka shi zai zama sanadin ajalina, zan sanar da kai abin da baka sani ba ayau. Oga Habib ni ce nai silar auran ka da Hassana, na yi abubuwa da dama dan ganin ka zama miji agareni, amma ina abin bai yuwu ba". Farida shiru ta yi sabo da yadda taji numfashinta na fusgar mata, Farida sai da ta share wasu hawaye masu d'imi da ke zubar mata, sannan ta dafe gefan zuciyarta ta ci gaba da magana cikin kuka-kuka kamar haka, "Oga Habib ni ce sanadin haukarka, na yi haka ne ko zaka zama miji a wajena, amma da ya ke kai d'in ba rabo na bane, sai abin ya fad'a ma Hassana, mai makon karik'a yaddar da ni ni ka d'ai kamar yadda naso, sai ya zama mana da Hassana ka d'ai ka ke yadda,
Inda tunanina ya bani, idan ya kasan ce dani ka d'ai ka ke yarda na san kowa zai yi tunanin had'a ni aure da kai, tom abin sai ya fad'a akan Hassana". Nan ma Farida shiru ta yi sannan ta ci gaba da cewa, "Oga Habib duk da Mommy ta had'a auranka da Hassana ban yi hak'uri ba nayi abubuwa da yawa ganin na raba auranka da Hassana, shima bai yuwu ba, na tura b'arayi akan su d'auke Hassana shima bai yuwu ba. Shi ne nayi tunanin fara aiki a Sanat ko zan ja hankalinka".kukan da ya k'wace ma Farida ne ya sa tai shiru, sai da tai kukanta ta gama sannan, ta ci gaba da cewa, nayi k'ok'ari sosai ganin na ta kurama Hassana".


Farida kuma rik'e hannun Hassana ta yi d'ayan kuma ta dafe saitin zuciyar ta, da ta ke tunanin hannun Habib ne ta ci gaba da cewa, " Oga Habib kai da Hassana ku yafe min dan.....". Tarin da Farida ke yi ne, mai tattare da aman jini ya hana ta fad'in abin da ta ke so".


Allah sarki Hassana da tausan Farida ya kamata kuka ta kama, dai-dai lokacin kuma Hajiya Murja ta shigo da likita".

Wata doguwar Hajiyar zuciya Farida ta ja, daga nan tarin ya lafa. Likitan duba Farida ya yi, sannan ya kalli Hajiya Murja ya ce, "Hajiya Allah ya yi ma mata rasuwa!? Ihu d'aya Hajiya Murja ta yi ta yanke jiki ta fad'i".


Ita kanta Hassana kuka ta fasa,cikin rud'ewa ta ke "Innalilahi'wa inna ilaihirraju'un! ". Habib rasa yadda zai yi da Hassana ya yi, ganin ta rud'e da yawa, ga kuma Hajiya Murja a sume".


Habib waya ya ciro ya kira Hajiya Turai, tana d'agawa Habib ya sanar da ita mutuwar Farida yan zu haka suna asibitin. Ai Hajiya Turai bata gama saurara ba ta kashe wayar".


Cikin minti goma Hajiya Turai ta iso asibitin, tana zuwa lokacin kuma dai-dai za atai da gawar Farida gida, haka aka tafi da gawar Farida gida, da Hajiya Murja keta rusa kuka tana kiran ta bani ta shiga uku, wa'iyazubiiya, Innalmaiyata layu'azibi bibika'ilhai, lallai mamaci ina masa azaba da kukan Wanda ya ke da rai. Allah ka ki ya ye mu kasa mu dace".



Haka akai zana'idar Farida aka kaita gidan ta na gaskiya. Sai da aka gama komai sannan Habib ya d'auki Hajiya Turai da Hassana suka koma gidan Hajiya Turai ".


Hassana da zazzab'i ke damunta tun acan daurewa ka wai ta ke, suna zuwa ta kwanta kan Three seater Falon Hajiya Turai, Habib kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Mommy Sanat fa bata ci komai ba".Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter me zaki ci? "."Mommy tea ". Hajiya Turai Maimuna tasa ta had'ama Hassana tea ta kawo mata. Habib buga k'afar Hassana ya yi kad'an ya ce, "Tashi ki sha tea d'in ". Hassana tashi tai dama kuma yunwa ta ke ji, dan ma d'azu Habib ya kaita wani restaurant ta ci abinci. Hassana amsar tea d'in ta yi ahankaki-ahankali ta samu ta shanye tea d'in".



Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib ina son ka yafe ma Farida dan ta aikaita abubuwa masu girma gareka, ban yi niyyar sanar da kai ba, amma zan fad'a maka sabo da nai man mata yafiya da zan yi". Habib kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, "Mommy duk abin da kike son sanar da ni Farida ta sanar da ni da kan ta, shine ma maganar ta ta k'arshe. Tabbas alokacin da take sanar da ni abin da tai min raina ya b'ace sosai, amma kuma bayan mutuwar ta sai naji tausan ta, na yafe mata Mommy Allah ya yafe mana baki d'aya ". 'Ameen". Hajiya Turai ta ce".


Hajiya Turai ta shi ta yi ta nufi ciki ta watsa ruwa. Habib ko naganin Hajiya Turai ta tashi ya bubbuga Hassana ya ce, "Sanat tashi mu tafi kafin Mommy tazo please ". Hassana kafad'a ta mak'ema Habib ta ce, "Naki d'in, Habib tada Hassana ya yi zau ne, ya ce, "Sanat dan Allah kin san tun jiya Mommy ta so in dawo da ke, tom yan zu idan ta fito ta kangi Allah na san ba zata bari ba mu tafi". Hassana kwanciya ta yi kan kafad'ar Habib ta ce, " Ni kam yau ba zan bika ba". Habib da ke jin tsoran kar Hajiya Turai ta fito, tashi ya yi yana tada Hassana ya ce, "Sanat ki tashi mana, kar Mommy ta zo".Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Ni fa ba zan bika ba". Habib da fe kai ya yi, ya ce, "Sanat kizo muje ina son muyi maganar tafiyar ki garin ku ne". Hassana cikin jin dad'i ta kalli Habib ta ce, "Allah da gaske kake? ". Kai Habib ya d'aga ma Hassana.
Hassana tashi tai suka tafi".


Bayan su Hassana sun tafi ne Hajiya Turai ta fito falon tan bayar Habib shi mai zai ci. Amma abin mamaki Hajiya Turai bata ga kowa ba. Dariya Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Allah sarki Habib wai guduwa ka yi da matar taka ba Sallama, in banda abin ka ai tun da naga Hassana ta kwaremin baya na hak'ura, Allah ya baku zaman lafiya". Hajiya Turai kiran Habib tai awaya, yana d'agawa ta ce, "Habib tafiya kuma babu sallama". Habib da ga can, sosa kai ya yi, ya ce, "Mommy na zaci kin kwanta ne, shine wai kar in tada ki". Hajiya Turai dai dariya kawai ta yi, ta kashe wayarta".


Habib sai da suka biya ta Alheri suya ya sai masu gasassar kaza sannan suka tafi gida".


Suna zuwa Habib ya kamo hannun Hassan ya ce, "zo ki wanka , mun yi bacci da wuri, yau kin gaji da yawa".
"Uhm ni ban gaji ba, zan yi da kai na ma".
Cewar Hassana ".


Habib hannun Hassana ya kamo ya ce, "Haba 'yan matana, zan hutashshe ki ne, bazan kalli ko mai ". Habib haka ya shigar da Hassana toilet d'in ya taya ta tai wankan, tun tana nok'ewa har ta hak'ura Habib ya jajjagulata ahaka dai aka yi wankan aka gama".


Hassana na fitowa ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib sai da safe".Hassana ta juya ta nufi side d'in ta. Habib bai tan ka ma Hassana ba, rabuwa ya yi da ita sai da ya yi sallar issha'i ya gama duk abin da zai yi sannan ya nufi side d'in Hassana. Hassana ko lokacin har ta kwanta,ta fara bacci. Habib bai tada Hassana ba gefanta ya je ya kwanta ya rungumota ta gefe gudin karta farka".


Hassana ko sai asuba da Habib ya ta data yin Sallah sanan ta san d'akinta ya kwana, Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib yau she ka shigo". "Kina can kina bacci". Habib ya ba Hassana amsa".


Hassana ko bayan ta yi sallah batare da Habib ya sani ba, ta fita ta shiga kitchen ta dama mai kunun gyad'a. Lokacin da Hassana ta shiga bedroom d'in ta bata iske Habib, wanka ta shiga, tana fitowa ta zauna ta yi shafa, yau Hassana har da su safa powder da lipstick, sannan ta d'akko cikin atamfofin da Hajiya Turai ta d'inka mata tasa wata,ta d'au aribian perfume ta feshe jikinta da shi, Hassana na fitowa da Cup d'in kunun Habib ta ci karo da Habib ya fito. Kallan kallo aka tsaya yi, Habib ringumo Hassana ya yi ya had'e bakin sa da nata yana tsotsa sannan ya rad'a mata cikin kunnan ta ahankali ya ce, "Nayi missing d'in sweet lips d'inki, anya ko zan iya fita". Hassana murmushi ta yi ta ce, "Uhm Oga Habib ina zaka da wuri haka? ". "Zan je Company ne, yan zu zan dawo". Habib ya ba Hassana amsa ".


Hassana hannun Habib ta kama ta ce, "Oga Habib na dama ma kunu, kasha tukun, nima zan rakaka". Habib jama ya yi Hassana ta mik'a mai kunun ya amsa yana sha, ya kai Cup d'in kunun bakin Hassana. Hassana kauda kai tayi ta ce, "Nasha ".Habib sha ya yi yabar Hassana dan ya lura ita kunun bai da meta ba. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib manager ya dawo aiki? ". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Yauwa kin tuna min, bai dawo ba, na ce sai kin yarda". Hassana turo baki ta yi, ta ce, "Ni fa ban wani ji haushin manager , haushin Billy naji ai ita ce tasa ya maran". Habib da bai son Hassana ta je Sanat, kallan ta ya yi ya ce, "Sanat ki bari ba yau ba zaki je". Hassana mak'ema Habib kafad'a ta yi, ta ce, "Ni dai yau nake son zuwa, dan Allah, akwai abin da zan yi acan". Habib kallan Hassana ya yi ya ce, "Me zaki yi acan? ". "Mu je zaka gani".


Habib ba dan yaso ba ya tafi da Hassana Sanat Yoghurt".


Hasana bayan sun je, Habib ya nufi Office d'in shi, zai shiga Hassana ta yi saurin kamo hannun Habib ta ce, "Muje karaka ni in ga ya gurin ya yi, ka ga na rabu da zuwa ". Habib bin Hassana ya yi dan shima ya rabu da duba cikin Company yaga yadda ya yi. Duk in da su kai staff d'in gurin kallan su ka wai ake, inda duk in aka gaida Habib sai an gaida Hassana, Hassana da fara'arta ta ke amsawa.Dan yan zu kowa ya san matsayin Hasssana a Sanat. Billy tun daga nesa ta hango Hassana da Habib na zuwa. Hassana dai-dai saitin Billy ta tsaya ta kalli Habib ta ce, " Uhm Sweetheart yama sunan wannan? ". Hassana ta fad'i maganar tana nuna Billy. Habib ko sai da ya rintse ido dan jin dad'in su nan da Hassana ta kira shi da shi. Habib batare da tunanin komai ba, dan shi ya za ci Hassana da gaske ne ta manta sunan Billy, ya ce, "Billy ". Hassana kallan Billy ta yi, da fara'arta ta ce, "Sannu da aiki Billy gaskiya kina k'ok'ari, Ina manager fa? ". Billy bacin agaban Habib ne tabbas da babu abin zai sa taba Hassana amsa, amma babu yadda za tai dole ta ba Hassana amsa".


Billy d'agowa ta yi tana kalli Hassana ta ce, "Bai zo aiki ba". Hassana cikin sakin fuska ta kuma cewa, " Lafiya bai zo aiki ba". Billy kallan Habib ta yi taga hankalin shi yana kan waya, ta harari Hassana ta ce, " an dakar da shine". "Ok, ki kira shi awaya yazo yan zu, idan ya zo ku zo tare". Hassana na fad'in haka ta kamo hannun Habib ta ce, "Wayyo Sweetheart wannan tafiyar da nai har nagaji Allah, mu koma Office d'in ka". Habib kama hannun Hassana ya yi suka koma ya ce, "Dama ke kika matsa sai kin biyoni ai".


Billy kamar zuciyarta zata fashe haka taji. Da harara tabi bayan Hassana da shi, sannan ta tura ma manager text massage akan yazo yan zu".


Hassana ko suna zuwa ta zauna kan chair d'in da Habib ya ke zama ta ce, "Oga Habib yau zan futassheka zan yi duk aikin da za kai". Murmushi Habib ya yi, ya ce, "Wane ke yarinya".


Habib suna nan zau ne suna fira da Hassana Manager da Billy su kai nocking k'ofar. Habib izinin shiga ya basu".


Manager cikin girmama Habib kamar yadda ya saba ya gaida shi. Habib babu yabo babu fallasa ya amsa ma manager. Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, "Barka da hutawa ranki shi dad'e". Hassana ma ta b'angaran ta babu ya bo ba sallasa ta amsa ma manager ".


Billy ko sosai taji ta kaicin gaida Hassanar da manager ya yi. Manager mai da kallan shi ga Habib ya yi, ya ce, "M.D, ance kana kirana? ". Habib nuna Hassana ya yi, ya ce, "Ga mai nai manka nan". Manager mai da kallan shi ga Hassana ya yi ya na jiran abin da zata ce".


Hassana kallan Billy ta yi ta ce, "Billy kawo min Yoghurt mai sanyi". Billy kamar ta ce bazata ba amma kuma babu damar haka ga Habib kusa, hakan yasa kamar zata sa ihu ta fita ta je kawo ma Hassana". Hassana kuma bata cema manager ko mai ba har sai da Billy ta dawo sannan ta kalli manager ta ce, "manager ka dawo kaci gaba da aikin ka, babu komai, ko mai ya wuce"."Godiya na ke ranki shi dad'e ". Cewar manager ".


Hassana kallan Billy ta yi da ke tsaye ta ce, "Ke fa lafiya? ". Billy cikin daurewa da yadda ta ke ji ta kalli Hassana ta ce, "ke ki ka ce in zo". Hassana kallanta ta yi sannan ta ce, "Babu da muwa zaki iya tafiya ki ci gaba da aikin ki". Billy fita ta yi tana mai jin zafin Hassana, sai dai ta san Hassana tai mata nisa nesa ba kusa ba, kuma tabbas yan zu Hassana duk wanda ta kora aiki ya koru".


Billy Office d'in ta ta koma tana kuka, Billy na nan tana kuka ta ga Manager ya shigo Office d'in. Manager cikin damuwa ya k'arasa gun Billy, manager kallan Billy ya yi ya ce, "Nasan abin da ya saki kuka, Billy hak'ik'a na soki kuma har yan zu ina son ki, tom amma wannan ita ce magana ta k'arshe da ke, ya maganar aure na da ke? ". Billy d'agowa ta yi tana kallan Manager ta ce, " Nayarda duk lokacin da ka shirya, zaka iya zuwa wajan kawuna". Manager cikin jin dad'i ya ce ma Billy, "zan je gobe". Billy kai ta d'aga ma Manager ".


Hassana ko sai 4:00Pm suka bar Sanat ita da Habib..... . โœ๏ธ



Idan kin karanta daure ki Comment

39 / 41